{"id":1827,"date":"2024-10-11T16:31:50","date_gmt":"2024-10-11T16:31:50","guid":{"rendered":"https:\/\/taskarnasaba.com.ng\/?p=1827"},"modified":"2024-12-02T20:36:03","modified_gmt":"2024-12-02T20:36:03","slug":"tarihin-sheikh-sharif-ibrahim-saleh-al-hussaini-con-rta","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=1827","title":{"rendered":"Tarihin Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Al-Hussaini CON, RTA"},"content":{"rendered":"\n<p>Fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya, wadda ya rubuta fiye da Littattafai 400 na addinin Musulunci.<\/p>\n\n\n\n<p>Malamin, wadda jigo ne a \u018aari\u0199ar Tijjaniyya a halin yanzu shi ne shugaban Majalisar \u0198oli ta Fatawa da Al&#8217;amuran Musulunci a Najeriya (NSCIA).<\/p>\n\n\n\n<p>Malamin ya kasance \u0257an \u0199abilar Shuwa Arab, kuma ya yi karatu a wurare da dama da suka ha\u0257a da; Makka, da Madina, da Masar, da Pakistan, da Iran, da Senegal da sauransu, a wajen manyan malaman Musulunci, ciki har da babban makarancin Al-kur&#8217;anin nan Mahmoud Khalilul Khusari, na Masar.<\/p>\n\n\n\n<p>An haifi Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Al-Hussaini, CON, a daren ranar Asabar, 12 ga Mayu, 1938, a Aredibe, wani \u0199auye kusa da Dikwa a Jihar Borno, da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.<\/p>\n\n\n\n<p>Mahaifinsa, Sheikh Muhammad Al-Salih bin Yunus Al-Nawy, shahararren malamin addinin Musulunci ne da ya yi fice a fagen ilimin addini daban-daban.<\/p>\n\n\n\n<p>Mahaifiyarsa Fatima bint Sheikh Muhammad Al-Bashir Al-Hussaini, Mace ce mai yawan karamci da tsoron Allah (SWT), sannan ta kasance abar girmamawa ga kowa a cikin al&#8217;umma.<\/p>\n\n\n\n<p>Ta kuma kasance mai ladabtarwa da tsananin sha&#8217;awar ilimi. Da yake Mijinta ya rasu sa\u2019adda \u0257ansu yake \u0257an shekara bakwai kawai, ta kar\u0253i horonsa har zuwa girmarsa.<\/p>\n\n\n\n<p>Babu shakka ita ce ta kasance mafi girmar tasiri a rayuwarsa, da ta sa a yau Sheikh Ibrahim Saleh ya zama babban malami a Duniya.<\/p>\n\n\n\n<p>Misali, ta ta\u0253a \u0199in amincewa da shawararsa ta yin watsi da neman ilimi maimakon tijarar dabbobi, lokacin ya na \u0257an shekaru 15 kacal.<\/p>\n\n\n\n<p>Shakka babu, ta taka rawar gani wajen tabbatar da Sheikh Ibrahim Saleh bisa gwadabe madaidaiciya.<\/p>\n\n\n\n<p>Sheikh Ibrahim Saleh, ya fara koyon Al-Kur\u2019ani mai girma tun ya na \u0257an \u0199aramin Yaro, in da koyaushe yake kasancewa tare da Mahaifinsa, wadda ya kasance mafi yawan dararensa ya na gabatar da sallar nafila (nawafil).<\/p>\n\n\n\n<p>Wannan ne ya sa ya fara haddace ayoyin Al-Kur\u2019ani tun kafin ya shiga makaranta gadan-gadan. Sau da dama, \u0257aliban da ke karatu a wurin mahaifinsa na yawan mamakin irin \u0199o\u0199arinsa da basirarsa sakamakon yadda yake cin su gyara a karatu duk da sun sha gabansa.<\/p>\n\n\n\n<p>Ya kuma fara karatunsa a makarantar Mahaifinsa, \u0257aya daga cikin shahararriyar makarantun islamiyya a Borno a lokacin.<\/p>\n\n\n\n<p>Daga shekarun 1944 zuwa 1964, ne lokacin da Sheikh Ibrahim Saleh ya yi gwagwarmayar ganin ya yi tasiri a fagagen karatun Al-kur\u2019ani da ilimin addini, da kuma sauran \u0253angarorin ilimi da suka ha\u0257a da kimiyyar lissafi, da falsafa da balagar harshe, da sauran wasu Littattafai.<\/p>\n\n\n\n<p>Bincikensa na neman \u0199warewa a ilimin Al-kur\u2019ani ya fara ne a gida, wadda daga baya ya koma zuwa wasu fitattun cibiyoyin ilimi wa\u0257anda aka fi sani da &#8220;Tsangayu&#8221; a Maiduguri da kewaye. Ba da da\u0257ewa ba shahararsa ta \u0257aukaka a fannin karatun Al-kur&#8217;ani.<\/p>\n\n\n\n<p>Bugu da \u0199ari, a duk wuraren da ya yi zamansa don neman ilimi, kamar su: Tarmuwa, Gulumba, Gide, Maishumari da kuma Maiduguri, ya kasance mai sau\u0199in sha&#8217;ani, har ma ga malamai wadda ya ha\u0257u da su a karon farko, sakamakon kyawawan \u0257abi&#8217;unsa, ladabi da biyayya, da zurfin karatunsa da kuma saninsa a cikin karatun Al-kur&#8217;ani.<\/p>\n\n\n\n<p>Akwai malamai da dama da suka yaba da \u0199o\u0199arinsa, tun ya na \u0199aramin yaro kuma a matsayin \u0257alibi, tare da yi masa kyakkyawar fahimta da cicci\u0257a shi domin kai wa ga tudun tsira a lokacin da yake tasowa a matsayin \u0257alibi.<\/p>\n\n\n\n<p>Akwai irin su; Sheikh Muhammadul Habib jikan Sheikh Ahmad Al-Tijjani (Abul Abbas), a ziyarar da ya kawo Maiduguri daga Aljeriya, Sheikh Muhammad Mustafa Alawi, Sheikh Al-kadi Lari Abani, Sheikh Mustafa Birshi, Sheikh Ahmad Ali Abulfathi, Sheikh Gibrima Dagira, Sheikh Tijjani Usman, Sheikh Abubakar Atiku da wasu da dama.<\/p>\n\n\n\n<p>Sheikh Ibrahim Saleh, ya shafe shekaru 20 ya na neman ilimi a matsayinsa na \u0257alibi, kuma ya koyi kusan dukkan karatunsa a Najeriya, amma ba hakan ke nufin duka malamansa \u01b4an Najeriya ba ne. Ya kuma karanci harshen turanci a birnin Landan.<\/p>\n\n\n\n<p>Karatun Sheikh Ibrahim Saleh, ya fi \u0199arfi a \u0253angaren Hadisai da Usulul Fi\u0199ihu da Ilmul Kalam, da kuma Tafsiri. Misali, duk wata aya daga cikin Al-kur&#8217;ani idan aka ambato ta, malamin zai iya fa\u0257in idan ta na da ala\u0199a da wani hadisi a tattare da ita. Malamin ya kuma yi nisa \u0199warai a karatun Tauhidi da Fi\u0199ihu.<\/p>\n\n\n\n<p>Wasu daga cikin malamansa su ne; Sheikh Al-Qadi Abanj Borno, da Sheikh Abubakar al-Waziri Borno, da Sheikh Adam al-Mahrusa Borno, da Sheikh Ahmad Abulfathi, da Sheikh Tijjani Usman (Zangon Barebari), da Sheikh Abubakar Atiku Sanka Kano, da Sheikh Muhammad al-Arabi bin Kubbani, da Sheikh Abubakar al-Kashnawiy, da Sheikh Muhammad al-Hafiz, da Sheikh Mahmoud Khalil Al-Hussary, da Sheikh Ahmad Nur al-Barni, da Sheikh Muhammad Zakariya al-Kandahlawiy, da Sheikh Ibrahim Nyass Kaolac, da sauransu.<\/p>\n\n\n\n<p>\u018aaya daga cikin mafi kyawun hanyoyin ilmantarwa mai inganci da Sheikh Ibrahim Saleh ya gano tun da wuri shi ne, duk \u0257alibin da ke son zama malami, dole ne ya za\u0199ulo wasu nau&#8217;ikan malamai daga cikin al&#8217;ummomin da suka gabata, kuma ya yi \u0199o\u0199arin koyi da su.<\/p>\n\n\n\n<p>Daidai da wannan dabara, ya tashi don yin koyi da tsara rayuwarsa a cikin tsarin Al-Ghazali. Al-Hafiz bin Hajaral Asqalani, dangane da Hadisi; da Abdulwahab Sha\u2019arani, ta fuskar samar da ilimi da dama, da kuma gwargwadon \u0199o\u0199arin sauran malamai na wannan zamani.<\/p>\n\n\n\n<p>Tasirin wa\u0257annan manya-manyan malaman Musulmi a rayuwar Sheikh Ibrahim Saleh ya haskaka.<\/p>\n\n\n\n<p>Ba kamar yawancin mutanen zamaninsa ba, Sheikh Ibrahim Saleh ya kiyaye rashin kwanciyar hankali a tsakanin tsarin zamani na neman ilimin addini, da kuma rungumar al\u2019adar Musulunci da ta da\u0257e ta na tantancewa da ba da shaida ga malamai.<\/p>\n\n\n\n<p>Ana cikin haka ne yun\u0199urin da ya yi na kwatanta rubuce-rubuce da sauran malamai, da kuma mi\u0199a kansa gare su domin a yi musu bincike mai zurfi, ya kai shi manyan Cibiyoyi masu daraja ta ilmin addinin Musulunci da ilmantarwa a Najeriya da ma Nahiyar Afirka.<\/p>\n\n\n\n<p>Misali, a shekarar 1963, Sheikh Ibrahim Saleh ya tafi \u0199asar Saudiyya a karon farko da nufin yin aikin Hajji da kuma samun takardar shaida ( Ijaza) a fannin Hadisi da karatun Al-kur\u2019ani da sauran rassa na ilimin addini.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img fetchpriority=\"high\" decoding=\"async\" width=\"530\" height=\"300\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/10003532344612000727777601174.jpg\" alt=\"\" class=\"wp-image-2473\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/10003532344612000727777601174.jpg 530w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/10003532344612000727777601174-300x170.jpg 300w\" sizes=\"(max-width: 530px) 100vw, 530px\" \/><\/figure>\n\n\n\n<p>Ya gana da wasu daga cikin manya-manyan malamai da ake girmama su da kuma sanin su a fagage kamar: Sheikh Umar bin Ali Al-Faruq Alfullati, Sheikh Alawi bin Abbas Al-Maliki, Sheikh Muhammadul Arabi Al-Tubbani da Sheikh Hassan bin Ibrahim Al- Sha&#8217;ir. Duk sun same shi ya isa ya mallaki takardun shaida. Haka zalika, a \u0199asar Masar, ya samu amincewar da ta dace a fagen Hadisi daga Sheikh Muhammadul Hafiz, da sauran fagagen da suka ha\u0257a da karatun Al-kur&#8217;ani daga Sheikh Mahmud Khalil Al-Husari da Sheikh Amir bin Usman Al-Sayyid.<\/p>\n\n\n\n<p>Sauran malamansa da suka ba da shaidar \u0199warewarsa a fannin Hadisi sun ha\u0257a da; Sheikh Ahmad Nur Al-Barmi daga Pakistan, Sheikh Muhammad Zakariyya bin Yahya Al-Khan Dahlawi daga Indiya, da kuma shahararren malami kuma jagoran \u018aari\u0199ar Tijjaniyya, Sheikh Ibrahim Nyass daga Senegal.<\/p>\n\n\n\n<p>Ya na iya zama abin farin ciki sanin cewa, Sheikh Ibrahim Saleh ya yi shekaru ashirin ne kacal (1944-1964) a matsayin \u0257alibi, kuma ya samu kusan dukkan horon da ya yi a Najeriya. Duk da haka, wannan ba ya na nufin cewa dukkan malamansa \u01b4an Najeriya ne ba. Amma duk da haka, ya kasance masani na gida, wadda aka samar a cikin gida ta hanyar tsarin Tsangaya.<\/p>\n\n\n\n<p>Watau, horon da ya samu a cikin tsarin karatun gida ne ya ba shi damar kasancewa mashahuri a \u0199asashen Duniya, da kuma karrama shi a matsayin \u0199wararren malami.<\/p>\n\n\n\n<p>Wa\u0257annan su ne mas&#8217;alolin da malamai suke magana a kai: nasikh wal mansukh ko asbabul nuzul. Ya na kuma iya bayar da dukkan wa\u0257annan bayanai a kan kowace ayar Al-kur&#8217;ani, (Sai dai in da raunin \u0257an Adam ya gaza).<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img decoding=\"async\" width=\"530\" height=\"300\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/10003532355843547953146290734.jpg\" alt=\"\" class=\"wp-image-2474\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/10003532355843547953146290734.jpg 530w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/10003532355843547953146290734-300x170.jpg 300w\" sizes=\"(max-width: 530px) 100vw, 530px\" \/><\/figure>\n\n\n\n<p>Bayan wa\u0257annan fagage, Sheikh Ibrahim Saleh ya bayar da muhimmanci sosai ga karatun Tauhidi da Fi\u0199ihu. Ya kuma karanta mafi yawan muhimman littattafan da ake da su a kan tauhidi. Sannan kuma ya fahimci tushe da yanayin bambance-bambance a tsakanin mazhabobi. Fi\u0199ihu na Mazhabar Malikiyya shi ma wani sarari ne a wurinsa.<\/p>\n\n\n\n<p>Sai dai kuma, Sheikh Sharif, ya ce ya fi sha&#8217;awar \u0253angaren ilimin Al-kur&#8217;ani da Hadisi kuma a nan ne ya fi \u0199warewa. Sannan ya haddace Hadisan da suke cikin Bukhari da Muslim da sauran manyan Litattafan Hadisai.<\/p>\n\n\n\n<p>Hakan kuwa ya samo asali ne sakamakon mu&#8217;amalar da yake yi da masana da mabiya sauran Mazhabobi.<\/p>\n\n\n\n<p>Wasu daga cikin ayyukansa su ne; Kafa Kwalejin Kimiyya da Ilimin Addinin Musulunci (Annahda), a shekara ta 1957.<\/p>\n\n\n\n<p>A shekarar 1963, Sheikh Ibrahim Saleh ya yi aiki wajen gudanar da ayyukan Gwamnatin Yankin Arewa, wadda ya nemi shigar da makarantun Tsangaya cikin tsarin ilimin zamani, a lardin Borno.<\/p>\n\n\n\n<p>A lokacin da Gwamnatin jihar Borno ta kafa Kwalejin Koyar da Shari\u2019a da Addinin Musulunci ta Borno (BOCOLIS), an na\u0257a shi ne domin ya taimaka wajen tsara shirye-shiryenta na ilimi.<\/p>\n\n\n\n<p>Kuma daga baya ya zama mamba na Hukumar Gudanarwa na Makarantar. Haka nan, daga 1984 zuwa 1990, ya zama Shugaban Hukumar. Amma a shekarar 1990 aka sake na\u0257a shi Shugaban Hukumar Jin Da\u0257in Alhazai ta Jiha. Ya kuma kasance a sabon ofishin nasa na kusan shekaru biyu, sannan aka mayar da shi tsohon mu\u0199aminsa na (BOCOLIS) a matsayin Shugaban Hukumar Gudanarwa.<\/p>\n\n\n\n<p>Sheikh Ibrahim Saleh, ya kuma \u0199ulla kyakkyawar ala\u0199a da gwamnatoci daban-daban tun daga 1976, a matakin Tarayya.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img decoding=\"async\" width=\"678\" height=\"452\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/10003532325910709114406722531.jpg\" alt=\"\" class=\"wp-image-2475\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/10003532325910709114406722531.jpg 678w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/10003532325910709114406722531-300x200.jpg 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/10003532325910709114406722531-600x400.jpg 600w\" sizes=\"(max-width: 678px) 100vw, 678px\" \/><\/figure>\n\n\n\n<p>Ya kasance mamba na kwamitocin da ake kafawa don ba da shawara ko jagoranci Gwamnati kan wasu manufofinta da ke da ala\u0199a da addini.<\/p>\n\n\n\n<p>Ya kuma kasance \u0257aya daga cikin wa\u0257anda gwamnatin \u0199asar ke yawan tura wa zuwa \u0199asashe a matsayin Wakilan Gwamnati ko kuma cikin wata tawaga zuwa \u0199asashe kamar; Saudi Arabiya, Iran, Masar, Turkiyya, Libiya, Morko, Malaysia, Indonesia, Pakistan, Senegal, Iraq, Sudan, da sauran su.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"530\" height=\"300\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/10003532332107231699427723031.jpg\" alt=\"\" class=\"wp-image-2476\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/10003532332107231699427723031.jpg 530w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/10003532332107231699427723031-300x170.jpg 300w\" sizes=\"(max-width: 530px) 100vw, 530px\" \/><\/figure>\n\n\n\n<p>Haka kuma an gayyace shi da dama domin gudanar da Tafsiri a gidan Gwamnati da ke Legas, a cikin watan Ramadan, daga shugabannin da suka gabata daban-daban.<\/p>\n\n\n\n<p>Ya kasance a sahun gaba wajen shirye-shiryen \u0199arfafa ha\u0257in kan Musulmi da tattaunawa tsakanin addinai domin samun zaman lafiya a Najeriya da \u0199asashen waje.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"530\" height=\"300\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/10003532306981876372749036476.jpg\" alt=\"\" class=\"wp-image-2477\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/10003532306981876372749036476.jpg 530w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/10003532306981876372749036476-300x170.jpg 300w\" sizes=\"(max-width: 530px) 100vw, 530px\" \/><\/figure>\n\n\n\n<p>A cikin wata hira (BBC Hausa) ya ce, ya kamata malamai su daina hauragiya da zage-zagen juna. &#8220;Kamata ya yi su ha\u0257a kai wajen ilimantar da al&#8217;umma.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>Sannan ya kuma koka kan yadda ya ce ake siyasa a Najeriya ba don ci gaban al&#8217;umma ba.<\/p>\n\n\n\n<p>Sheikh Ibrahim Saleh, ya na da \u0257alibai da Almajirai masu tarin yawa a fadin \u0199asashen Musulmi da na Larabawa.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"509\" height=\"603\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/10003532297197493838634174748.jpg\" alt=\"\" class=\"wp-image-2478\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/10003532297197493838634174748.jpg 509w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/10003532297197493838634174748-253x300.jpg 253w\" sizes=\"(max-width: 509px) 100vw, 509px\" \/><\/figure>\n\n\n\n<p>Haka nan, mabiyansa a kodayaushe su na tare da shi ta kowane fanni da ya shafi rayuwarsu. An kuma rubuta wasu daga cikin \u0199asidunsa da littattafansa kai-tsaye ga wasu batutuwa na Shari&#8217;a da koyarwa.<\/p>\n\n\n\n<p>A cikin babban fagagensa na sha&#8217;awar Ilimi da bincike, ya rubuta Litattafai da \u0199asidu sama 400, da kuma takardu a wajen gabatar da taro sama 100, wa\u0257anda duk a cikin harshen Larabci suke. Sun ha\u0257a da: Ilimomin Al-kur&#8217;ani, da, Hadisai, da, Tarihi, da, Falsafa, da, Fi\u0199ihun Musulunci, da, Ilimin Taurari, da, Adabin Larabci, da, Ilimin Harsuna, da, Kimiyyar Sufanci, da, Siyasar Musulunci, da, Dokokin Musulunci, da Matsayar Gado, da, Zaman Lafiya Tsakanin \u0198asashe, da, Ainihin mutuntaka da \u01b4ancin kai, da kuma sauran batutuwa daban-daban.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"607\" height=\"505\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/10003532288991518067283542494.jpg\" alt=\"\" class=\"wp-image-2480\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/10003532288991518067283542494.jpg 607w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/10003532288991518067283542494-300x250.jpg 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/10003532288991518067283542494-600x499.jpg 600w\" sizes=\"(max-width: 607px) 100vw, 607px\" \/><\/figure>\n\n\n\n<p>Baya ga \u0257imbin ayyukan koyarwa da bincike, Sheikh Ibrahim Saleh ya kuma jagoranci ko shiga cikin ayyukan \u0199ungiyoyin Musulunci na \u0199asa da na \u0199asa da \u0199asa tsawon shekaru, wadda sun ha\u0257a da;<\/p>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Shugaban Kwamitin Fatawa na Majalisar \u0198oli ta Harkokin Addinin Musulunci (SCIA) da Jama\u2019at Nasril Islam (JNI).<\/li>\n\n\n\n<li>Shugaban Majalisar Musulmi a Najeriya (AMIN).<\/li>\n\n\n\n<li>Shugaba kuma wadda ya kafa \u0199ungiyar Islamic Renaissance Organization International (IROI).<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<p>Mataimakin Babban Sakatare Janar na Jagorancin Jama&#8217;ar Musulmi na Duniya (GIWPL), har zuwa 2010.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"530\" height=\"300\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/10003532318783400890300092665.jpg\" alt=\"\" class=\"wp-image-2481\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/10003532318783400890300092665.jpg 530w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/10003532318783400890300092665-300x170.jpg 300w\" sizes=\"(max-width: 530px) 100vw, 530px\" \/><\/figure>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Mamba a Majalisar Harkokin Addini ta Najeriya (NIREC).<\/li>\n\n\n\n<li>Mamba a Vision 2010.<\/li>\n\n\n\n<li>Wadda ya kafa kuma Memba na Majalisar Malaman Addinin Musulunci ta Duniya (IFMS), Makka.<\/li>\n\n\n\n<li>Mamba a Majalisar Zartarwa ta \u0198ungiyar Malaman Musulmi ta Duniya (IUMS), Ireland (tare da hedikwata a Doha har 2010).<\/li>\n\n\n\n<li>Shugaban Kwamitin Ba da Shawarar Ku\u0257i na \u0198wararru (FRACE), na Babban Bankin Najeriya (CBN). Shi ne Shugaban Sashen Shari\u2019a na Kasuwancin Musulunci, (CBN) tun 2012.<\/li>\n\n\n\n<li>\u018aaya daga cikin wa\u0257anda suka Majalisar Dattawan Musulmi (CME) Abu Dhabi United Arab Emirates.<\/li>\n\n\n\n<li>Mamba A Cikin Kwamitin Amintattu na Hukumar Ba da Agaji ta Duniya.<\/li>\n\n\n\n<li>Mamba na Kwamitin Amintattu na \u0198ungiyar Ya\u0257a Addinin Musulunci (Sudan).<\/li>\n\n\n\n<li>Wakilin Kwamitin Amintattu Musxaf Afriqiya (sudan).<\/li>\n\n\n\n<li>Mamba Kwamitin Amintattu na Majalisar Karatun Al-kur&#8217;ani, Jihar Borno.<\/li>\n\n\n\n<li>Mamba Kwamitin Amintattu na Masallacin \u0198asa, Abuja.<\/li>\n\n\n\n<li>\u018aaya daga cikin wadda suka damar da \u0198ungiyar Malaman Musulunci a Afirka (Morocco).<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<p>Sakamakon haka, tare da jinjinawa da irin gudunmowar da ya bayar ga addinin Musulunci, da kuma ci gaba da \u0199o\u0199arin da yake yi na tabbatar da zaman lafiya a tsakanin mutane mabambantan ra\u2019ayi, Sheikh Ibrahim Saleh ya samu lambobin yabo ta \u0199asa da \u0199asa. Wa\u0257annan sun ha\u0257a da:<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"619\" height=\"495\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/10003532272456861570793112660.jpg\" alt=\"\" class=\"wp-image-2479\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/10003532272456861570793112660.jpg 619w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/10003532272456861570793112660-300x240.jpg 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/10003532272456861570793112660-600x480.jpg 600w\" sizes=\"(max-width: 619px) 100vw, 619px\" \/><\/figure>\n\n\n\n<ol class=\"wp-block-list\">\n<li>Takardar shaidar karramawa daga \u0198ungiyar \u018aalibai ta \u0198asa reshen jihar Borno, 1985.<\/li>\n\n\n\n<li>Kyautar lambar yabo ta Masarawa ta farko a fannin fasaha da kimiyya (Wisam Al-Jamhuriya), wadda shugaban Masar, Muhammad Hosni Mubarak, Jamhuriyar Larabawa ta Masar, ya bayar, 1993.<\/li>\n\n\n\n<li>Shaidar karramawa daga hannun \u018aalibai na \u0253angaren Lauyoyi, na Jami\u2019ar Midogray, 1995.<\/li>\n\n\n\n<li>Shaidar daga Karramawa daga \u018aalibai na \u0253angaren Shari\u2019ar Addinin Musulunci, 1995.<\/li>\n\n\n\n<li>Takardun Shaidar Yabo daga Sashen Agajin Gaggawa na Jama&#8217;atul Nasirul Islam Group, 1996.<\/li>\n\n\n\n<li>Takardar shaidar karramawa da lambar yabo ta Da\u2019awah ta Musulunci, wadda cibiyar Abi Alnnour Islamic Foundation da Majalisar \u0198oli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Syria, 1997 suka gabatar.<\/li>\n\n\n\n<li>Kyautar Daraja ta Farko ta Majagaba a cikin Hidimar Al&#8217;umma (Wisam Elriyada), wadda Jagoran juyin-juya halin Libiya Kanar Mu&#8217;ammar Gaddafi, Libya, 1998 ya bayar.<\/li>\n\n\n\n<li>Lambar Yabo ta (Dir&#8217;a-Daawah), wadda \u0198ungiyar Kira Zuwa Ga Addinin Musulunci ta Duniya, Libya, 1998.<\/li>\n\n\n\n<li>Lambar Yabo ta &#8220;Al-Imam Abu Ala\u2019za\u2019m&#8221; (Imam Gold Medal), Al\u0199ahira, 1998.<\/li>\n\n\n\n<li>Kyautar Daraja ta Farko a kan Rubutu (Afro-Asian Writer of the Year 2004), wadda \u0198ungiyar Afro-Asiya ta Masar ta gabatar, Al\u0199ahira, 2004.<\/li>\n\n\n\n<li>Kwamandan oda na Niger (CON), wadda shugaban \u0199asa (Umaru Musa \u01b3ar&#8217;adua) kuma babban kwamandan rundunar sojojin tarayyar Najeriya, Abuja, 2008, ya gabatar masa.<\/li>\n\n\n\n<li>Digiri na uku na Kimiyya (HNORIS COUSA) da aka ba shi, a wajen taron karo na Uku na Jami\u2019ar Turkish Nile ta Najeriya da ke Abuja, ranar Asabar, 13 ga watan Yuni, 2015.<\/li>\n<\/ol>\n\n\n\n<p>Bugu da \u0199ari, an sanyawa wani Masallaci sunansa a Jamhuriyar Nijar, (Sheikh Sharif Ibrahim Ibn Saleh Mosque, Niger).<\/p>\n\n\n\n<p>MADOGARA:<\/p>\n\n\n\n<p>1.&#8221;Highest ranking Islamic figure, Grand Imam of al-Azhar, visits Nigeria&#8221; 19 May 2016. Retrieved 2019-09-16.<\/p>\n\n\n\n<ol start=\"2\" class=\"wp-block-list\">\n<li>&#8220;The muslim 500&#8221;. Retrieved 2014-09-16.<\/li>\n\n\n\n<li>&#8220;King Mohammed VI Defense of Islam Sets &#8216;Modern&#8217; Model: African Ulema.&#8221; Morocco World News. 2017-12-09. Retrieved 2019-09-18.<\/li>\n\n\n\n<li>&#8220;Shaykh Ibrahim Ibn Saleh&#8221;. 23 October 2020.<\/li>\n\n\n\n<li>Idris Ahmed (14 January 2013). &#8220;Nigeria: CBN Inaugurates Financial Regulation Advisory Council of Experts&#8221;. allAfrica. Daily Trust. Retrieved 8 February 2023. (subscription required)<\/li>\n\n\n\n<li>&#8220;Annahada first aid group of Nigeria Maiduguri&#8221;. www.facebook.com. Retrieved 2019-09-18.[user-generated source]<\/li>\n\n\n\n<li>&#8220;General secretariat for fatwa authorities worldwide&#8221;. Retrieved 2019-09-16.[permanent dead link]<\/li>\n\n\n\n<li>&#8220;Buhari, Sultan, Saleh listed among world&#8217;s top 50 Muslim leaders&#8221;. 3 October 2015.<\/li>\n\n\n\n<li>Muhammed, Isiyaku (2019-09-27). &#8220;Jibi za a kaddamar da Gidauniyar Cibiyar Sheikh Sharif Saleh&#8221;. Aminiya (in Hausa). Archived from the original on 2019-09-30. Retrieved 2019-09-30.<\/li>\n\n\n\n<li>&#8220;Ibrahim Salih.&#8221;  <\/li>\n\n\n\n<li>University, Nile (2015-06-13). &#8220;#Sheikh Shariff Ibrahim Saleh Alhussaini giving his #acceptance #speechpic.twitter.com\/RKIUTalDLf&#8221;. @nileuni. Retrieved 2019-09-18. 4-<\/li>\n<\/ol>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya, wadda ya rubuta fiye da Littattafai 400 na addinin Musulunci. Malamin, wadda jigo ne a \u018aari\u0199ar Tijjaniyya a halin yanzu shi ne shugaban Majalisar \u0198oli ta Fatawa da Al&#8217;amuran Musulunci a Najeriya (NSCIA). Malamin ya kasance \u0257an \u0199abilar Shuwa Arab, kuma ya yi karatu a wurare da dama da [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":1828,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"inline_featured_image":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[93],"tags":[],"class_list":["post-1827","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-jiya-da-yau"],"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v27.0 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Tarihin Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Al-Hussaini CON, RTA<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"noindex, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_US\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Tarihin Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Al-Hussaini CON, RTA\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"Fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya, wadda ya rubuta fiye da Littattafai 400 na addinin Musulunci. Malamin, wadda jigo ne a \u018aari\u0199ar Tijjaniyya a halin yanzu shi ne shugaban Majalisar \u0198oli ta Fatawa da Al&#8217;amuran Musulunci a Najeriya (NSCIA). Malamin ya kasance \u0257an \u0199abilar Shuwa Arab, kuma ya yi karatu a wurare da dama da [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=1827\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"Taskar Nasaba\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2024-10-11T16:31:50+00:00\" \/>\n<meta property=\"article:modified_time\" content=\"2024-12-02T20:36:03+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/WhatsApp-Image-2024-10-11-at-9.11.21-AM.jpeg\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"679\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"564\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/jpeg\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Salahuddeen Muhammad\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"Salahuddeen Muhammad\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Est. reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"13 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\/\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=1827#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=1827\"},\"author\":{\"name\":\"Salahuddeen Muhammad\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753\"},\"headline\":\"Tarihin Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Al-Hussaini CON, RTA\",\"datePublished\":\"2024-10-11T16:31:50+00:00\",\"dateModified\":\"2024-12-02T20:36:03+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=1827\"},\"wordCount\":2549,\"commentCount\":0,\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=1827#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/WhatsApp-Image-2024-10-11-at-9.11.21-AM.jpeg\",\"articleSection\":[\"Jiya Da Yau\"],\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=1827#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=1827\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=1827\",\"name\":\"Tarihin Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Al-Hussaini CON, RTA\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=1827#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=1827#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/WhatsApp-Image-2024-10-11-at-9.11.21-AM.jpeg\",\"datePublished\":\"2024-10-11T16:31:50+00:00\",\"dateModified\":\"2024-12-02T20:36:03+00:00\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=1827#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=1827\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=1827#primaryimage\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/WhatsApp-Image-2024-10-11-at-9.11.21-AM.jpeg\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/WhatsApp-Image-2024-10-11-at-9.11.21-AM.jpeg\",\"width\":679,\"height\":564},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=1827#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Tarihin Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Al-Hussaini CON, RTA\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"description\":\"\",\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\"},\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-US\"},{\"@type\":\"Organization\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\",\"logo\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png\",\"width\":343,\"height\":345,\"caption\":\"Taskar Nasaba\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/\"}},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753\",\"name\":\"Salahuddeen Muhammad\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg\",\"caption\":\"Salahuddeen Muhammad\"},\"description\":\"\u018aanjarida, marubuci, mai manufar bun\u0199asa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.\",\"sameAs\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\"],\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?author=1\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Tarihin Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Al-Hussaini CON, RTA","robots":{"index":"noindex","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"og_locale":"en_US","og_type":"article","og_title":"Tarihin Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Al-Hussaini CON, RTA","og_description":"Fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya, wadda ya rubuta fiye da Littattafai 400 na addinin Musulunci. Malamin, wadda jigo ne a \u018aari\u0199ar Tijjaniyya a halin yanzu shi ne shugaban Majalisar \u0198oli ta Fatawa da Al&#8217;amuran Musulunci a Najeriya (NSCIA). Malamin ya kasance \u0257an \u0199abilar Shuwa Arab, kuma ya yi karatu a wurare da dama da [&hellip;]","og_url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=1827","og_site_name":"Taskar Nasaba","article_published_time":"2024-10-11T16:31:50+00:00","article_modified_time":"2024-12-02T20:36:03+00:00","og_image":[{"width":679,"height":564,"url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/WhatsApp-Image-2024-10-11-at-9.11.21-AM.jpeg","type":"image\/jpeg"}],"author":"Salahuddeen Muhammad","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"Salahuddeen Muhammad","Est. reading time":"13 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=1827#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=1827"},"author":{"name":"Salahuddeen Muhammad","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753"},"headline":"Tarihin Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Al-Hussaini CON, RTA","datePublished":"2024-10-11T16:31:50+00:00","dateModified":"2024-12-02T20:36:03+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=1827"},"wordCount":2549,"commentCount":0,"publisher":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=1827#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/WhatsApp-Image-2024-10-11-at-9.11.21-AM.jpeg","articleSection":["Jiya Da Yau"],"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=1827#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=1827","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=1827","name":"Tarihin Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Al-Hussaini CON, RTA","isPartOf":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=1827#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=1827#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/WhatsApp-Image-2024-10-11-at-9.11.21-AM.jpeg","datePublished":"2024-10-11T16:31:50+00:00","dateModified":"2024-12-02T20:36:03+00:00","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=1827#breadcrumb"},"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=1827"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=1827#primaryimage","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/WhatsApp-Image-2024-10-11-at-9.11.21-AM.jpeg","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/WhatsApp-Image-2024-10-11-at-9.11.21-AM.jpeg","width":679,"height":564},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=1827#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/taskarnasaba.com\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Tarihin Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Al-Hussaini CON, RTA"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/","name":"Taskar Nasaba","description":"","publisher":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization"},"potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-US"},{"@type":"Organization","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization","name":"Taskar Nasaba","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/","logo":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png","width":343,"height":345,"caption":"Taskar Nasaba"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/"}},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753","name":"Salahuddeen Muhammad","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/image\/","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg","caption":"Salahuddeen Muhammad"},"description":"\u018aanjarida, marubuci, mai manufar bun\u0199asa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.","sameAs":["https:\/\/taskarnasaba.com"],"url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?author=1"}]}},"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/WhatsApp-Image-2024-10-11-at-9.11.21-AM.jpeg","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/1827","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=1827"}],"version-history":[{"count":3,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/1827\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2482,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/1827\/revisions\/2482"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/1828"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=1827"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=1827"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=1827"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}