{"id":2322,"date":"2024-11-24T02:05:43","date_gmt":"2024-11-24T02:05:43","guid":{"rendered":"https:\/\/taskarnasaba.com.ng\/?p=2322"},"modified":"2024-11-24T02:08:56","modified_gmt":"2024-11-24T02:08:56","slug":"matakan-rubuta-kagaggun-labarai","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2322","title":{"rendered":"Matakan Rubuta \u0198agaggun Labarai"},"content":{"rendered":"\n<p>Idan aka ce matakan rubuta \u0199agaggun labarai, ana nufin hanyoyi ko dabaru ko wasu tubala ko kuma wasu abubuwa da ake so mai rubuta \u0199agaggun labarai ya tanada ko ya yi amfani da su a duk lokacin da ya tashi rubuta ire-iren wa\u0257annan \u0199agaggun labarai, don haka a wannan \u0253angare za mu duba ire-iren matakai ko hanyoyin ko tubala da ake amfani da su wajen rubutun.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>TUNANI<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Abu na farko da mai son rubuta \u0199agaggen Littafi na Hausa zai fara tanada shi ne; Tunani. Tunani shi ne babban abu a wajen mai rubuta \u0199agaggen Littafi don in babu tunani ko kuma in ba a yi tunanin mai ake so a rubuta ba babu rubutun Littafin gaba \u0257aya, dole ne a fara da tunanin abin da ake so a rubuta a cikin littafin.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>LABARI<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Dole ne mai son rubuta \u0199agaggen Littafi ya tanadi labari, wato abin da yake so ya rubuta, shin labarin soyayya ne ko na jarumta ko na yara ko na aljanu ko kuma wani daban? Don yin hakan shi ne zai sa ya san al\u0199iblar da ya dosa, kuma ya sami sau\u0199in isar da sa\u0199onsa, in bai tanadi labari ba akwai matsala don ko ya zauna don rubutun in bai san labarin da yake son rubutawa ba, to, abin ba zai yi wu ba.<\/p>\n\n\n\n<p>Shi kuma labarin ba sai mutum ya san komai da komai na cikinsa ba, amma dai zai fi kyau in an san daga inda aka tashi da kuma in da za a sauka, ma\u2019ana; Ka san farkon labarinka da \u0199arshensa, amma sauran abubuwan da ke cikin tsakiyar labarin sai ka zo rubutun sannan za ka same su, a lokacin da basirar rubutun take saukowa.<\/p>\n\n\n\n<p>Misali ina so zan taso daga unguwar Sabon Tasha da ke Kaduna zuwa Kwalejin Koyar da Harkokin Kasuwanci, kuma Sashen Share Fagen Shiga Jami\u2019a, a garin Dutse, don halartar taron \u0199ara wa juna sani na kwana \u0257aya, kuma na san dole zan bi ta kan titin Ahmadu Bello Way kafin in iso garin Dutse. A nan mun san ga inda na baro ga kuma inda nake son zuwa, amma abubuwan da za su faru a hanyar ban sani ba sai na taho sannan zan gani in sun faru. To haka abin yake a rubutu, sai ka zo wajen yin rubutun ne za ka ji abubuwan su na zuwar maka a \u0199wa\u0199walwa, kuma kana rattaba su a cikin takardarka ko wayarka ko na\u2019urarka ya danganta da irin abin da kake rubutun a jikinsa, Takarda ce ko Kwamfuta ko kuma Waya.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>SUNAN LITTAFI<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Ya na da kyau mai rubuta \u0199agaggen Littafi ya yi wa Littafinsa suna kafin ya fara ko kuma kafin ya gama, domin sanya wa Littafin suna ya na taimakawa mai rubutun labarinsa ya dinga tafiya da sunan Littafin. Wasu lokutan ana samun Littafi da aka gama rubutawa ba a sanya masa suna ba, sai daga baya a zo ana ta kame-kamen yadda za a sanya masa suna, wanda da an ba shi suna tun farko da ba a sami wannan matsala ba, kuma labarin zai fi tafiya da sunan sosai.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>LOKACI DA GURI<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Ya kamata mai rubuta Littafi ya lura da lokaci da kuma gurin da yake rubutun, abin da ake nufi a lura wajen sanya lokaci, kamar kwanakin wata ko shekaru don ka da a dinga samun rikicewar lissafin shekarun ko watanni, don ana iya samun rikicewarsu in ba a kula ba. Haka ma batun guri, idan kana rubuta Littafi mai bayar da labarin rayuwar Birni ko Karkara, ka tabbata abin da kake rubutawa a cikin labarin Karkara ya na faruwa a Karkara, haka abin da kake rubutawa na game da Birni ka tabbata su na wakana.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>BINCIKE<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Ya na da kyau a duk lokacin da mai rubutu ya zo yin rubutu a kan wani abu da aka san ya na bu\u0199atar bincike, to a bincika shi don ka da a rubuta shi da ka, yadda zai zo ya ru\u0257ar da mutane musamman ma wa\u0257anda ba su san shi ba. Misali abin da ya shafi Lafiya da Shari&#8217;a da Al&#8217;adu da kuma Addini.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>SINADARAI<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Har ila yau, akwai \u0199arin wasu sunadarai ko tubala wa\u0257anda idan aka ha\u0257a su yayin rubuta \u0199agaggun Littattafai musamman na soyayya sun fi da\u0257i da armashi, kamar:<\/p>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Sunayen mutanen da suka dace (Taurari)<\/li>\n\n\n\n<li>Siffanta mata masu kyan hali da kyawun halitta<\/li>\n\n\n\n<li>Bayyana ire-iren mataye ko mazajen da mafi yawan mutane suka fi so<\/li>\n\n\n\n<li>Bayyana kyawawan halaye na iyaye da \u01b4a\u01b4ansu<\/li>\n\n\n\n<li>Biyayya<\/li>\n\n\n\n<li>Fito da abubuwan da Namiji ya fi son Mace ta yi masa<\/li>\n\n\n\n<li>Fito da abubuwan da Mace ta fi son Namiji ya yi mata<\/li>\n\n\n\n<li>Fito da abubuwan da ke faruwa a rayuwa ta zahiri dangane da soyayya,<br \/>musamman a rayuwar ma\u2019aurata,<\/li>\n\n\n\n<li>Yanayin soyayya bayan ta riki\u0257e ta zama aure<\/li>\n\n\n\n<li>Amfani da kalmomin soyayya masu da\u0257i da faranta zuciya, dss.<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<p>Ko da yake wasu su na ganin a da can ba a cika rubutu kan soyayya ba saboda wasu dalilai kamar yadda a wata gabatarwar da Farfesa M.K.M. Galadanci ya yi a wani Littafi na soyayya a cikin shekarar 1992, ga abin da ya ce;<\/p>\n\n\n\n<p>\u201cMarubutan Hausa na farko ba su cika son yin rubutu kan soyayya ba, wata\u0199ila don gudun zancen Mata da amfani da kalmomin \u0199uruciya ko ma ta kai ga yin batsa saboda haka da wuya a sami da\u0257a\u0257\u0257en littafi (kai ko ma rubutacciyar wa\u0199a) kan soyayya. A \u01b4an shekarun nan marubutan zamani, matasa, sun toshe mana wannan gi\u0253i na Adabin Hausa. Wannan littafi wanda Malam Ado Ahmad Gidan Dabino ya wallafa, &#8216;Hattara Dai Masoya,&#8217; na \u0257aya daga cikin kyawawan misalan irin wannan \u0199o\u0199ari\u201d (Galadanci, M.K.M.; 1992: shafi na K).<\/p>\n\n\n\n<p>Wasu kuwa su na ganin babu wani alfanu ma kwata-kwata a cikin littatafan soyayya da ake rubutawa, su a wajen su gwara a dinga rubuce-rubuce a kan Yunwa da Fatara da Talauci da Ya\u0199e-ya\u0199e da Annobobi iri-iri, maimakon in ba kai ba sai rijiya. Sannan kuma rubuce-rubucen su na cike da kura-kuran Hausa da rabe-rabenta da kuma \u0253ata tarbiyyar matasa Maza da Mata, da kuma yin fassara daga Littattafan wasu jinsin mutane wa\u0257anda ba al\u2019adar su \u0257aya da ta Bahaushe ba.<\/p>\n\n\n\n<p>Wasu kuwa su na ganin ba labaran soyayya ne suka ishi mutane ba, a\u2019a salon ne ya ishe su in har ya ishe sun.<\/p>\n\n\n\n<p>Ko ma dai ya ya abin yake, wasu su na ganin marubuta \u0199agaggun Littattafan Hausa musamman na soyayya sun bayar da tasu gudunmawar wajen bun\u0199asa da ya\u0257a Adabin Zamani a \u0198asar Hausa da kuma Duniya baki \u0257aya, domin an samar da dubunnan Littattafai a wannan fage, kuma sanadiyyar haka an sami wa\u0257annan abubuwa;<\/p>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Riki\u0257ewar makaranta Littattafai zuwa ga rubutawa<\/li>\n\n\n\n<li>Samuwar sababbin Marubuta<\/li>\n\n\n\n<li>Samuwar makaranta Littattafai<\/li>\n\n\n\n<li>Samuwar \u0199ungiyoyin Marubuta<\/li>\n\n\n\n<li>Samuwar wa\u0257anda ba Hausawa ba a cikin rubutun Hausa<\/li>\n\n\n\n<li>Samuwar \u0198ungiyoyi Makaranta Littattafai<\/li>\n\n\n\n<li>Samuwar Kantunan sayar da Littattafai masu yawa<\/li>\n\n\n\n<li>Zuwan ba\u0199i daga wasu Jihohi da \u0199asashe don sayen Littattafai<\/li>\n\n\n\n<li>Yawaitar masu bincike a kan Littattafan soyayya (manazarta), da rubuta ta<\/li>\n\n\n\n<li>\u0198arfafa dan\u0199on zumunci (a cikin gida da waje)<\/li>\n\n\n\n<li>Cusa wa mai sauraro ko mai karatu farin ciki da gusar masa da \u0253acin rai<\/li>\n\n\n\n<li>Son karatun Hausa da bun\u0199asa Harshen<\/li>\n\n\n\n<li>Cusa sha\u2019awar yin rubutu a zu\u0199atan matasa Maza da Mata<\/li>\n\n\n\n<li>Kyautata zamantakewar Ma\u2019aurata da kuma Masoya ta hanyar karatun Littattafan<br \/>Soyayya<\/li>\n\n\n\n<li>Samar da aikin yi ga matasa Maza da Mata har da matan aure<\/li>\n\n\n\n<li>\u0198alubalantar auren dole a \u0199asar Hausa<\/li>\n\n\n\n<li>Ya\u0199ar jahilci<\/li>\n\n\n\n<li>\u0198ulla hul\u0257ar zumunci tsakanin marubuta da makarantansu, dss.<\/li>\n<\/ul>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Idan aka ce matakan rubuta \u0199agaggun labarai, ana nufin hanyoyi ko dabaru ko wasu tubala ko kuma wasu abubuwa da ake so mai rubuta \u0199agaggun labarai ya tanada ko ya yi amfani da su a duk lokacin da ya tashi rubuta ire-iren wa\u0257annan \u0199agaggun labarai, don haka a wannan \u0253angare za mu duba ire-iren matakai [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":2319,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"inline_featured_image":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[84],"tags":[],"class_list":["post-2322","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-adabi"],"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v27.0 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Matakan Rubuta \u0198agaggun Labarai<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"noindex, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_US\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Matakan Rubuta \u0198agaggun Labarai\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"Idan aka ce matakan rubuta \u0199agaggun labarai, ana nufin hanyoyi ko dabaru ko wasu tubala ko kuma wasu abubuwa da ake so mai rubuta \u0199agaggun labarai ya tanada ko ya yi amfani da su a duk lokacin da ya tashi rubuta ire-iren wa\u0257annan \u0199agaggun labarai, don haka a wannan \u0253angare za mu duba ire-iren matakai [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2322\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"Taskar Nasaba\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2024-11-24T02:05:43+00:00\" \/>\n<meta property=\"article:modified_time\" content=\"2024-11-24T02:08:56+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20241012-WA0026-2.jpg\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"350\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"232\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/jpeg\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Salahuddeen Muhammad\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"Salahuddeen Muhammad\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Est. reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"6 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\/\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2322#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2322\"},\"author\":{\"name\":\"Salahuddeen Muhammad\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753\"},\"headline\":\"Matakan Rubuta \u0198agaggun Labarai\",\"datePublished\":\"2024-11-24T02:05:43+00:00\",\"dateModified\":\"2024-11-24T02:08:56+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2322\"},\"wordCount\":1271,\"commentCount\":0,\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2322#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20241012-WA0026-2.jpg\",\"articleSection\":[\"Adabi\"],\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2322#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2322\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2322\",\"name\":\"Matakan Rubuta \u0198agaggun Labarai\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2322#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2322#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20241012-WA0026-2.jpg\",\"datePublished\":\"2024-11-24T02:05:43+00:00\",\"dateModified\":\"2024-11-24T02:08:56+00:00\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2322#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2322\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2322#primaryimage\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20241012-WA0026-2.jpg\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20241012-WA0026-2.jpg\",\"width\":350,\"height\":232},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2322#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Matakan Rubuta \u0198agaggun Labarai\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"description\":\"\",\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\"},\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-US\"},{\"@type\":\"Organization\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\",\"logo\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png\",\"width\":343,\"height\":345,\"caption\":\"Taskar Nasaba\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/\"}},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753\",\"name\":\"Salahuddeen Muhammad\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg\",\"caption\":\"Salahuddeen Muhammad\"},\"description\":\"\u018aanjarida, marubuci, mai manufar bun\u0199asa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.\",\"sameAs\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\"],\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?author=1\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Matakan Rubuta \u0198agaggun Labarai","robots":{"index":"noindex","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"og_locale":"en_US","og_type":"article","og_title":"Matakan Rubuta \u0198agaggun Labarai","og_description":"Idan aka ce matakan rubuta \u0199agaggun labarai, ana nufin hanyoyi ko dabaru ko wasu tubala ko kuma wasu abubuwa da ake so mai rubuta \u0199agaggun labarai ya tanada ko ya yi amfani da su a duk lokacin da ya tashi rubuta ire-iren wa\u0257annan \u0199agaggun labarai, don haka a wannan \u0253angare za mu duba ire-iren matakai [&hellip;]","og_url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2322","og_site_name":"Taskar Nasaba","article_published_time":"2024-11-24T02:05:43+00:00","article_modified_time":"2024-11-24T02:08:56+00:00","og_image":[{"width":350,"height":232,"url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20241012-WA0026-2.jpg","type":"image\/jpeg"}],"author":"Salahuddeen Muhammad","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"Salahuddeen Muhammad","Est. reading time":"6 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2322#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2322"},"author":{"name":"Salahuddeen Muhammad","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753"},"headline":"Matakan Rubuta \u0198agaggun Labarai","datePublished":"2024-11-24T02:05:43+00:00","dateModified":"2024-11-24T02:08:56+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2322"},"wordCount":1271,"commentCount":0,"publisher":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2322#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20241012-WA0026-2.jpg","articleSection":["Adabi"],"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2322#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2322","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2322","name":"Matakan Rubuta \u0198agaggun Labarai","isPartOf":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2322#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2322#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20241012-WA0026-2.jpg","datePublished":"2024-11-24T02:05:43+00:00","dateModified":"2024-11-24T02:08:56+00:00","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2322#breadcrumb"},"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2322"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2322#primaryimage","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20241012-WA0026-2.jpg","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20241012-WA0026-2.jpg","width":350,"height":232},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2322#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/taskarnasaba.com\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Matakan Rubuta \u0198agaggun Labarai"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/","name":"Taskar Nasaba","description":"","publisher":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization"},"potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-US"},{"@type":"Organization","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization","name":"Taskar Nasaba","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/","logo":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png","width":343,"height":345,"caption":"Taskar Nasaba"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/"}},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753","name":"Salahuddeen Muhammad","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/image\/","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg","caption":"Salahuddeen Muhammad"},"description":"\u018aanjarida, marubuci, mai manufar bun\u0199asa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.","sameAs":["https:\/\/taskarnasaba.com"],"url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?author=1"}]}},"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20241012-WA0026-2.jpg","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2322","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=2322"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2322\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2324,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2322\/revisions\/2324"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/2319"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=2322"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=2322"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=2322"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}