{"id":2425,"date":"2024-11-28T10:29:02","date_gmt":"2024-11-28T10:29:02","guid":{"rendered":"https:\/\/taskarnasaba.com.ng\/?p=2425"},"modified":"2024-12-10T00:44:29","modified_gmt":"2024-12-10T00:44:29","slug":"yadda-kirkirarriyar-basira-ta-airtificial-intelligence-za-ta-shafi-ayyuka-a-afirka","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2425","title":{"rendered":"Yadda \u0198ir\u0199irarriyar Basira ta Artificial Intelligence za ta Shafi Ayyuka a Afirka"},"content":{"rendered":"\n<p>Bankin ci gaban Afirka (Africa Development Bank) ya yi hasashen cewa kimanin Matasa Miliyan 100 da ke Nahiyar ba za su samu kowane irin sabon aiki ba, nan zuwa shekarar 2030 saboda ci gaban da ake samu ta fuskar Fasaha.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>Daga Brian Okoth<\/strong> \u270d\ufe0f<\/h2>\n\n\n\n<p>Ana ci gaba da samun rashin tabbas dangane da makomar ayyuka a Fa\u0257in Duniya kan batun \u0198ir\u0199irarriyar Basira (AI) saboda yadda za ta shafi ayyuka a nan gaba ka\u0257an.<\/p>\n\n\n\n<p>Babban tambayar da ake a yanzu ita ce ko \u0198ir\u0199irarriyar Basirar (AI) za ta jawo gagarumin rashin ayyukan yi.<\/p>\n\n\n\n<p>\u0198ungiyar Masana Kimiyya ta Turai (Europe\u2019s Scientific Foresight Unit) ta ce, \u0198ir\u0199irarriyar Basirar (AI) ta na iya nazarin muhallinta kuma ta \u0257auki matakin da ya dace \u2013 ta na da \u01b4ancin yin tunanin bisa ra\u0257in kanta \u2013 don aiwatar da aikin da ta saka a gaba.<\/p>\n\n\n\n<p>Mutembei Kariuki, ya na \u0257aya daga cikin mutanen da suka kafa wani kamfanin \u0198ir\u0199irarriyar Basirar (AI) mai suna Fastagger Inc wanda yake birnin Nairobi a \u0199asar Kenya.<\/p>\n\n\n\n<p>Ya ce, burin AI shi ne ya yi aiki mai yawa a cikin \u0199an\u0199anin lokaci da yin aiki mai kyau da nazarin bayanai cikin hazari da hasashen abubuwan da za su faruwa a harkokin kasuwanci a nan gaba da kuma rage ku\u0257in gudanar da ayyuka da kasuwanci.<\/p>\n\n\n\n<p>\u201cMutane da dama ba su fahimci fasahar \u0198ir\u0199irarriyar Basirar (AI) ba. Idan ka tambayi mutum ba shiri, mene ne AI, akwai yiwuwar zai ce maka AI ya na nufin yadda ake amfani da Robot da na&#8217;urori don yin ayyukan da dan&#8217;Adam yake yi a halin yanzu,&#8221; kamar yadda Kariuki ya shaida wa TRT Afrika.<\/p>\n\n\n\n<p>\u201cA&#8217;a, wannan ba shi ne aikin \u0198ir\u0199irarriyar Basirar (AI) ba,\u201d in ji Kariuki, ya \u0199ara da cewa Kamfanoni na amfani da fasahar ne wajen taimaka wa bincike-bincike saboda \u0257aukar matakai.<\/p>\n\n\n\n<p>\u201cA ta\u0199aice, \u0198ir\u0199irarriyar Basirar (AI) fasaha ce da take taimaka wa ma&#8217;aikata yin aikinsu cikin sauri kuma da kyau ta hanyar nazarin bayanai da hasashen wasu abubuwan da za su faruwa da taimakawa wajen gano hanyoyin samun Ku\u0257i da rage ku\u0257in da ake kashewa wajen gudanar da kasuwanci.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>\u0198ANANAN AYYUKA<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p>Fiye da shekara 10, yadda ake amfani da AI wajen yanke hukunci ya \u0199aru sosai, inda \u0253angarori kamar na ku\u0257i da tsaron \u0199asa da kiwon Lafiya da shari&#8217;ar manyan laifuka da sufuri su ma suka fara amfani da shi.<\/p>\n\n\n\n<p>Nazari iri daban-daban sun yi hasashen \u0198ir\u0199irar AI za ta maye gurbin Miliyoyin ayyuka nan da shekarar 2030, sai dai kuma a lokaci za ta samar da wasu sabbin ayyuka wa\u0257anda suke bu\u0199atar ilimin Fasaha.<\/p>\n\n\n\n<p>Wani bincike da \u0198ungiyar Tattalin Arziki ta World Economic Forum ta wallafa a ranar 30 ga watan Afrilun 2023, ya ce a\u0199alla za a rasa wasu ayyuka miliyan 14 a duk fa\u0257in Duniya nan da shekarar 2027.<\/p>\n\n\n\n<p>Nazarin ya gano cewa, yayin da ayyuka Miliyan 83 za su zama tsofaffin ya yi saboda \u0198ir\u0199irarriyar Basirar (AI), za a samu wasu sabbin damarmaki Miliyan 69, hakan ya na nufin za a samu ayyuka Miliyan 14 da za a yi asarar gurabensu nan zuwa shekarar 2027.<\/p>\n\n\n\n<p>A shekarar 2019, Bankin ci gaban Afirka na African Development Bank (ADB) ya yi hasashen cewa matasa miliyan 100 na Nahiyar ba za su iya samun wani sabon aikin yi ba nan da shekarar 2030, inda aka ala\u0199anta hakan da ci gaban fasahohin zamani.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>KOYON SABON ILIMI<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p>Kariuki ya ce, matasa da suke neman ayyuka a wannan zamani sai sun &#8220;koyi sabon ilimi&#8221; kuma su rungumi fasaha don \u0257orewarsu da ci gabansu, maimakon su ri\u0199a yi wa fasaha kallon wadda ke barazanar raba su da aikinsu.<\/p>\n\n\n\n<p>\u201cLokacin da aka fara \u0199ir\u0199iro Kwamfuta (a shekarar 1971), akwai ayyuka da dama da ta kora. Ciki har da masu aikin buga rubutu (typist) da masinja da masu tattakai bayanai a ofisoshi,&#8221; in ji Kariuki.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8221;Sai dai kuma akwai wasu sabbin ayyuka da kwamfutar ta samar. Sun ha\u0257a da ayyuka kamar haka: Graphics designer da masana Kwamfuta da masu samar da manhaja (programmers) da injiniyoyin kwamfuta da sauransu,&#8221; in ji shi.<\/p>\n\n\n\n<p>Wani rahoto da aka yi taken makomar ayyuka a Afirka ta Kudu wanda wani kamfanin \u0199asar McKinsey &amp; Company ya wallafa ya ce &#8220;ba za a iya hana&#8221; sauye-sauyen da ake samu ta fuskar ayyuka da fasaha ta kawo ba.<\/p>\n\n\n\n<p>\u201cKo da yake tasirinsu mai cutarwa, ya ce wa\u0257annan fasahohin dama ce ta ci gaba da \u0199arin ku\u0257in shiga da bun\u0199asar Tattalin Arzikin Afirka ta Kudu,&#8221; in ji rahoton.<\/p>\n\n\n\n<p>Rahoton ya ci gaba da cewa \u0198ir\u0199irarriyar Basirar (AI) da ci gaban da ake samu ta fuskar Robot za su iya samar da &#8220;miliyoyin manyan ayyuka.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>Shugaban kamfanin Massmart Holdings wani kamfanin kayayyaki a Afirka ta Kudu Kuseni Dlamini, ya bu\u0199aci kamfanoni da su ri\u0199a koyawa ma&#8217;aikatansu ilimin Fasahar Zamani don hakan zai taimaka musu wajen samun wasu sabbin ayyuka da ci gaban fasaha zai samar.<\/p>\n\n\n\n<p>\u201cYa zama dole mu yarda cewa akwai wasu ayyuka da za su kasance babu su. Saboda haka dole ne ma&#8217;aikata mayar da hankali wajen riki\u0257a don \u0199warewarsu ta dacewa da ta ayyukan da ke gaba.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;Ana bu\u0199atar ba su horo da darussa don shirya mutane sosai kan irin ayyukan da za a bu\u0199ata a gaba,&#8221; in ji Diamini.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>MAYAR DA AYYUKA A HANNUN NA&#8217;URA<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p>Rahoton McKinsey &amp; Company ya yi hasashen cewa \u0198ir\u0199irarriyar Basirar (AI) da robot da sauran ci gaban fasaha za su jawo rasa wasu ayyuka miliyan 3.3 a Afirka ta Kudu nan da shekarar 2030.<\/p>\n\n\n\n<p>Ko da yake an kuma yi hasashen cewa za a samar da wasu ayyuka Miliyan 4.5 &#8211; hakan ya na nufin an kirkiro sabbin ayyuka miliyan 1.2 ke nan.<\/p>\n\n\n\n<p>Sai dai nazarin ya ce ba a san yadda ayyukan miliyan 1.2 za su kasance ba, kodayake za su kasance ne a \u0253angaren fasaha.<\/p>\n\n\n\n<p>Fiye da sabbin ayyuka 570,000 za su kasance ne a fannin Kiwon Lafiya da jinya, sai kuma ayyuka fiye da 260,000 a \u0253angaren gine-gine, a cewar binciken.<\/p>\n\n\n\n<p>\u201cNazarin da muka yi kan ayyuka, ya nuna cewa akwai \u01b4an \u0199alilan ne da za a mayar da su kaso 100 bisa 100 a hannu na&#8217;ura.<\/p>\n\n\n\n<p>Misali, aikin tattara bayanai da jami&#8217;an da ke biyan albashin ma&#8217;aikata ke yi, kaso 72 cikin 100 na aikin ne na&#8217;ura za ta iya yi.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>Ma&#8217;aikata a wannan \u0253angare ba za a iya maye gurbinsu gaba \u0257aya da Fasahar Zamani ba, sai dai za a iya rage yawansu saboda \u0199ila mutane \u0199alilan ne ake bu\u0199ata don yin aikin.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>Nazarin da Cibiyar McKinsey Global Institute ta yi ya gano cewa kaso 60 cikin 100 na ayyuka sun \u0199unshi kaso 30 cikin 100 aikin da na&#8217;ura za ta iya yi.<\/p>\n\n\n\n<p>MUTANEN DA ABIN ZAI FI SHAFA<\/p>\n\n\n\n<p>Nazarin da aka yi a Afirka ta Kudu ya gano cewa nan da shekarar 2030, \u0198ir\u0199irarriyar Basirar da ci gaban fasaha za su share ayyuka 334,000.<\/p>\n\n\n\n<p>Daga nan sai \u0253angaren gudanarwa da shugabanci da bangaren gwamnati (ayyuka 309,000 ) da \u0253angaren masana&#8217;antu (231,000) da \u0253angaren sufuri da manyan wuraren adana kayayyaki (186,000) da \u0253angaren aikin gona da dazuka da masu sana&#8217;ar su (87,000), sai \u0253angaren samar da gidaje (20,000).<\/p>\n\n\n\n<p>An yi hasashen \u0253angaren yada labarai a Afirka ta Kudu zai rasa akalla ayyuka dubu 7,000 daga nan zuwa shekarar 2030.<\/p>\n\n\n\n<p>\u0181angarorin da ake ganin za su samu \u0199aruwa sosai na ayyuka saboda ci gaban fasahar zamani su ne kiwon lafiya (570,000 sabbin ayyuka) da gine-gine (261,000) da kuma sauran \u0253angarori masu tasowa (152,000).<\/p>\n\n\n\n<p>Haka zalika nazarin ya yi hasashen cewa akwai yiwuwar samun sabbin ayyuka a \u0253angaren kimiyya da ayyukan fasaha (ayyuka 112,000,000) da \u0253angaren ilimi (ayyuka 110,000,000) da \u0253angaren zane-zane da nisha\u0257i (ayyuka 48,000) da \u0253angaren samar da muhalli da abinci and (ayyuka 28,000) da \u0253angaren kasuwanci (ayyuka 23,000).<\/p>\n\n\n\n<p>Shugaban Jami&#8217;ar Pretoria Farfesa Tawana Kupe ya ce, &#8220;Ni ban yarda cewa Robot za su kwashe ayyukan mutane ba.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>\u201cFasaha ta na \u0257auke ayyuka da suka zamar wa mai yinsa jiki ne, ko ayyuka a ake maimaita abu guda kuma hakan zai bai wa \u0257an&#8217;Adam samun wani babban aiki da ke bu\u0199atar zurfin tunani,&#8221; in ji shi, kamar yadda aka ruwaito shi rahoton McKinsey &amp; Company.<\/p>\n\n\n\n<p>Mutembei Kariuki ya ce, \u0198ir\u0199irarriyar Basirar (AI) za ta taimakawa kusa kowane \u0253angare kuma za ta inganta ayyukan da ake yi, za ta rage lokacin da ake \u0253atawa kuma za ta sa a \u0199ara fahimtar kwastomomi da jama&#8217;a.<\/p>\n\n\n\n<p>\u201cMu \u0257auki misalin Cibiyar Nazarin Aikin Gona, za a iya amfani da AI wajen gano hanyar da za a yi noman rani da irin da zai jurewa fari da sauransu.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;Wannan zai sa a samu yalwar amfanin gona kuma zai taimaka wajen samar da ayyuka zuwa gaba,&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>\u201cA \u0253angaren nisha\u0257i, shahararren Mawa\u0199i daga Nijeriya Davido zai iya amfani da \u0198ir\u0199irarriyar Basirar (AI) wajen ya\u0257a wa\u0199o\u0199insa a kafafen sada zumunta.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;AI za ta iya yin nazarin \u0257abi&#8217;n mai sauraron wa\u0199o\u0199i kuma za ta kai wa mai \u0199aunar wa\u0199o\u0199in Davido wa\u0199ar.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;Wannan zai sa wa\u0199arsa za ta kai ga mutane masu tarin yawa idan aka kwatanta da ake ce ba a yi amfani da AI ba wajen ya\u0257a wa\u0199ar.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>Kariuki, ya \u0199ara da cewa a \u0253angaren ilimi za a samu \u0199arin guraben ayyuka, saboda za a bu\u0199aci malamai da za su ri\u0199a koyar da AI da sauransu.<\/p>\n\n\n\n<p>\u201cMasu samar da AI da masu amfani da shi za su samu damarmaki masu kyau,&#8221; in ji shi.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>SAUYIN YANAYI<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p>Joost Muller, manajan kasuwanci ne a kamfanin Hello Tractor, wani kamfani da yake amfani da AI wajen Aikin Gona, ya ce \u0198ir\u0199irarriyar Basirar (AI) za ta taimaka wajen ya\u0199i da \u0199alubalen da Sauyin Yanayi ya jawo.<\/p>\n\n\n\n<p>Muller ya ce a Afirka, kaso 80 cikin 100 na al&#8217;ummarta su na dogaro sosai ne kan noman da ya dogara da ruwan sama.<\/p>\n\n\n\n<p>Ya ce, galibi manoma su na dogaro ne da \u0199warewarsu wajen yin shuka da kuma Kiwo. &#8221;Sauyin yanayi ya na ci gaba babu \u0199a\u0199\u0199autawa, ya na da wuya mutum ya dogara a kan ruwan sama da \u0199warewa kawai.<\/p>\n\n\n\n<p>Ta hanyar amfani da \u0198ir\u0199irarriyar Basirar (AI) za a iya gano lokacin da ya fi dacewa a yi noma ta hanyar tattara hotunan tauraron \u0257an&#8217;adam,&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>Sai dai kuma akwai tsoron da wasu suke cewa bambancin da ke tsakanin Nahiyar Afirka da sauran \u0198asashe da suka ci gaba zai \u0199ara fa\u0257a\u0257a a wannan zamani na AI.<\/p>\n\n\n\n<p>Yayin da samar da fasahar AI yake da tsadar samarwa da tafiyarwa, masana su na ganin \u0199asashe da ba su da arziki sosai \u2013 kamar wa\u0257anda suke wasu \u0253angarorin Afirka da sauran yankunan \u0199asashe matalauta \u2013 za a bar su a baya idan ana maganar yin amfani da AI wajen tafiyar da ayyukan yau da kullum.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>SAUYIN CIKIN HANZARI<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p>\u201cIdan aka tambaye ni, zan ce \u0198ir\u0199irarriyar Basirar (AI) za ta ba Afirka damar kamo sauran \u0199asashen Duniya ta fuskar ci gaba.<\/p>\n\n\n\n<p>Sai dai kuma idan Afirka ba ta yi amfani da damarta ba, to gi\u0253i da ke tsakanin nahiyar da sauran \u0199asashen Duniya zai \u0199ara fa\u0257a\u0257a ne,&#8221; in ji Kariuki.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8221;Ba kamar sauye-sauyen kamar a fuskar Noma da Masana&#8217;anta ba, sauyin da \u0198ir\u0199irarriyar Basirar (AI) yake kawowa ya na faruwa ne a idon \u01b4an Afirka. Ya kamata su \u0199ar\u0253i wannan dama kuma su ci gaba da ita,&#8221; in ji shi.<\/p>\n\n\n\n<p>Kamar sauran fasahohi, akwai tsoron da ake da shi cewa AI zai \u0199ara take hakkin mutane kamar hakkin mallakar fasaha da kuma yi wa jama&#8217;a kutse.<\/p>\n\n\n\n<p>Ko da yake, wasu kamfanonin AI a Amurka su na fuskar tuhuma a kotu kan zargin yadda suke take hakkin jama&#8217;a.<\/p>\n\n\n\n<p>Dakta Carlos Lopes, tsohon Sakatare a Hukumar Tattalin Arziki ta Majalisar \u018ainkin Duniya \u0253angaren Afirka, kuma ya shaida wa TRT Afrika cewa ya dace gwamnatoci su yi dukkan mai yiwuwa wajen ganin cewa idan aka fara amfani da AI gadan-gadan, an kare bayanan jama&#8217;a.<\/p>\n\n\n\n<p>\u201cA yau, manyan kamfanoni a Duniya su na tattarawa da sarrafa bayanai jama&#8217;a. Ya kamata Afirka ta kula sosai wajen shiga yarjejeniyoyi kare bayanai da \u0199asashenta suka mallaka,&#8221; in ji shi.<\/p>\n\n\n\n<p>Shin AI zai share duka ayyukan da muke da su a yanzu a Afirka da sauran sassan Duniya? Gajeruwar amsar ita ce a&#8217;a.<\/p>\n\n\n\n<p>Kamar da Oren Etzioni, shugaban kamfanin Allen Institute for Artificial Intelligence ya ce: &#8220;Ka ce \u0198ir\u0199irarriyar Basirar (AI) za ta fara yin abin da take so don amfanin kanta, to kamar ka ce na&#8217;urar Kakuleta za ta fara lissafe-lissafe ne da kanta.&#8221;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Bankin ci gaban Afirka (Africa Development Bank) ya yi hasashen cewa kimanin Matasa Miliyan 100 da ke Nahiyar ba za su samu kowane irin sabon aiki ba, nan zuwa shekarar 2030 saboda ci gaban da ake samu ta fuskar Fasaha. Daga Brian Okoth \u270d\ufe0f Ana ci gaba da samun rashin tabbas dangane da makomar ayyuka [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":2424,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"inline_featured_image":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[103],"tags":[],"class_list":["post-2425","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-kimiyya-da-fasaha"],"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v27.0 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Yadda \u0198ir\u0199irarriyar Basira ta Artificial Intelligence za ta Shafi Ayyuka a Afirka<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"noindex, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_US\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Yadda \u0198ir\u0199irarriyar Basira ta Artificial Intelligence za ta Shafi Ayyuka a Afirka\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"Bankin ci gaban Afirka (Africa Development Bank) ya yi hasashen cewa kimanin Matasa Miliyan 100 da ke Nahiyar ba za su samu kowane irin sabon aiki ba, nan zuwa shekarar 2030 saboda ci gaban da ake samu ta fuskar Fasaha. Daga Brian Okoth \u270d\ufe0f Ana ci gaba da samun rashin tabbas dangane da makomar ayyuka [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2425\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"Taskar Nasaba\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2024-11-28T10:29:02+00:00\" \/>\n<meta property=\"article:modified_time\" content=\"2024-12-10T00:44:29+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/images-2024-11-28T113159.360.jpeg\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"650\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"472\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/jpeg\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Salahuddeen Muhammad\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"Salahuddeen Muhammad\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Est. reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"10 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\/\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2425#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2425\"},\"author\":{\"name\":\"Salahuddeen Muhammad\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753\"},\"headline\":\"Yadda \u0198ir\u0199irarriyar Basira ta Artificial Intelligence za ta Shafi Ayyuka a Afirka\",\"datePublished\":\"2024-11-28T10:29:02+00:00\",\"dateModified\":\"2024-12-10T00:44:29+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2425\"},\"wordCount\":2081,\"commentCount\":0,\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2425#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/images-2024-11-28T113159.360.jpeg\",\"articleSection\":[\"Kimiyya Da Fasaha\"],\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2425#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2425\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2425\",\"name\":\"Yadda \u0198ir\u0199irarriyar Basira ta Artificial Intelligence za ta Shafi Ayyuka a Afirka\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2425#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2425#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/images-2024-11-28T113159.360.jpeg\",\"datePublished\":\"2024-11-28T10:29:02+00:00\",\"dateModified\":\"2024-12-10T00:44:29+00:00\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2425#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2425\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2425#primaryimage\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/images-2024-11-28T113159.360.jpeg\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/images-2024-11-28T113159.360.jpeg\",\"width\":650,\"height\":472},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2425#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Yadda \u0198ir\u0199irarriyar Basira ta Artificial Intelligence za ta Shafi Ayyuka a Afirka\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"description\":\"\",\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\"},\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-US\"},{\"@type\":\"Organization\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\",\"logo\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png\",\"width\":343,\"height\":345,\"caption\":\"Taskar Nasaba\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/\"}},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753\",\"name\":\"Salahuddeen Muhammad\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg\",\"caption\":\"Salahuddeen Muhammad\"},\"description\":\"\u018aanjarida, marubuci, mai manufar bun\u0199asa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.\",\"sameAs\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\"],\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?author=1\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Yadda \u0198ir\u0199irarriyar Basira ta Artificial Intelligence za ta Shafi Ayyuka a Afirka","robots":{"index":"noindex","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"og_locale":"en_US","og_type":"article","og_title":"Yadda \u0198ir\u0199irarriyar Basira ta Artificial Intelligence za ta Shafi Ayyuka a Afirka","og_description":"Bankin ci gaban Afirka (Africa Development Bank) ya yi hasashen cewa kimanin Matasa Miliyan 100 da ke Nahiyar ba za su samu kowane irin sabon aiki ba, nan zuwa shekarar 2030 saboda ci gaban da ake samu ta fuskar Fasaha. Daga Brian Okoth \u270d\ufe0f Ana ci gaba da samun rashin tabbas dangane da makomar ayyuka [&hellip;]","og_url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2425","og_site_name":"Taskar Nasaba","article_published_time":"2024-11-28T10:29:02+00:00","article_modified_time":"2024-12-10T00:44:29+00:00","og_image":[{"width":650,"height":472,"url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/images-2024-11-28T113159.360.jpeg","type":"image\/jpeg"}],"author":"Salahuddeen Muhammad","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"Salahuddeen Muhammad","Est. reading time":"10 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2425#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2425"},"author":{"name":"Salahuddeen Muhammad","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753"},"headline":"Yadda \u0198ir\u0199irarriyar Basira ta Artificial Intelligence za ta Shafi Ayyuka a Afirka","datePublished":"2024-11-28T10:29:02+00:00","dateModified":"2024-12-10T00:44:29+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2425"},"wordCount":2081,"commentCount":0,"publisher":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2425#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/images-2024-11-28T113159.360.jpeg","articleSection":["Kimiyya Da Fasaha"],"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2425#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2425","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2425","name":"Yadda \u0198ir\u0199irarriyar Basira ta Artificial Intelligence za ta Shafi Ayyuka a Afirka","isPartOf":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2425#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2425#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/images-2024-11-28T113159.360.jpeg","datePublished":"2024-11-28T10:29:02+00:00","dateModified":"2024-12-10T00:44:29+00:00","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2425#breadcrumb"},"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2425"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2425#primaryimage","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/images-2024-11-28T113159.360.jpeg","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/images-2024-11-28T113159.360.jpeg","width":650,"height":472},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2425#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/taskarnasaba.com\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Yadda \u0198ir\u0199irarriyar Basira ta Artificial Intelligence za ta Shafi Ayyuka a Afirka"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/","name":"Taskar Nasaba","description":"","publisher":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization"},"potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-US"},{"@type":"Organization","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization","name":"Taskar Nasaba","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/","logo":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png","width":343,"height":345,"caption":"Taskar Nasaba"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/"}},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753","name":"Salahuddeen Muhammad","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/image\/","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg","caption":"Salahuddeen Muhammad"},"description":"\u018aanjarida, marubuci, mai manufar bun\u0199asa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.","sameAs":["https:\/\/taskarnasaba.com"],"url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?author=1"}]}},"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/images-2024-11-28T113159.360.jpeg","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2425","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=2425"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2425\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2719,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2425\/revisions\/2719"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/2424"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=2425"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=2425"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=2425"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}