{"id":2510,"date":"2024-12-03T02:21:42","date_gmt":"2024-12-03T02:21:42","guid":{"rendered":"https:\/\/taskarnasaba.com.ng\/?p=2510"},"modified":"2024-12-09T17:29:14","modified_gmt":"2024-12-09T17:29:14","slug":"taytu-betul-shahararriyar-sarauniyar-sarakuna","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2510","title":{"rendered":"Taytu Betul: Shahararriyar Sarauniyar Sarakuna"},"content":{"rendered":"\n<p><strong><em>Taytu Betul ta kasance sarauniyar Habasha daga 1889 zuwa 1913 kuma matar sarki Menelik na biyu. Jarumi mai tasiri wajen adawa da mulkin mallaka a \u0199arshen karni na 19 (Scramble for Africa), ita, tare da mijinta, sun kafa babban birnin Habasha na zamani, &#8216;Addis Ababa&#8217; a 1886.<\/em><\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Mahaifin <strong>Taytu<\/strong> shi ne <strong>Ras Betul Haile<\/strong> <strong>Maryam<\/strong>, ya na cikin dangin <strong>Semien<\/strong> da ke mulki da suka yi i\u0199irarin zama zuriyar <strong>Daular Annabi Sulemanu AS<\/strong> ta hannun Sarkin Sarakuna <strong>Susenyos I. Kawun Taytu<\/strong>, shi ne shahararren jarumin \u0199abilar <strong>Amhara<\/strong>, <strong>Wube Haile Maryam<\/strong>, wadda shi ne Hakimin Lardi sannan kuma mai ci kuma mai mulkin Larduna; <strong>Tsegede<\/strong>, <strong>Weilkat Tigray<\/strong> da kuma <strong>Eritrea<\/strong>. Mahaifiyar <strong>Taytu<\/strong>, <strong>Yewibdar<\/strong>, ta fito daga wani babban jigo a yankin <strong>Gonder<\/strong>.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Ilimi<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Babu wasu bayanai da suka nuna cewa, <strong>Sarauniya Taytu<\/strong> ta halarci Makaranta; Duk da haka, an koya mata karatu da rubutu cikin harshen <strong>Amharic<\/strong> da <strong>Ge&#8217;ez<\/strong>.<\/p>\n\n\n\n<p>Wannan abu ne mai wuyar gaske, ganin cewa a cikin wannan lokaci da wuya Mata su sami Ilimi. An yi imanin cewa an koyar da ita <strong>Diflomasiyya<\/strong>, <strong>Siyasa<\/strong> da <strong>Tattalin<\/strong> <strong>Arziki<\/strong>. <\/p>\n\n\n\n<p>Ana \u0257aukar <strong>Taytu Betul<\/strong> a matsayin \u0257aya daga cikin shahararrun shugabannin <strong>Habasha<\/strong>, mata ce ga Sarkin Sarakuna <strong>Menelik II.<\/strong> Ta taka rawa wajen mur\u0199ushe \u01b4an Mulkin Mallaka na <strong>Italiya<\/strong>, ita ce kuma ta kafa birnin <strong>Addis Ababa<\/strong>.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Wace ce Taytu Betul?<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p><strong>Taytu Betul<\/strong>, wata mace ce \u01b4ar \u0199asar <strong>Habasha<\/strong> mai kima da daraja wadda tare da mijinta sarkin sarakuna <strong>Menelik II<\/strong> suka yi mulkin <strong>Habasha<\/strong> daga <strong>1889<\/strong> zuwa <strong>1913<\/strong>.<\/p>\n\n\n\n<p>Ana tuna ta saboda jajircewarta da adawa da kuma nasarar da ta samu a kan Sojojin Turawan mulkin mallaka na <strong>Italiya<\/strong> da kuma \u0199arfin ikonta a kotun Sarki.<\/p>\n\n\n\n<p>Ita ce ta za\u0253i yankin da a yau ya zama babban birnin <strong>Habasha<\/strong> ta kuma sanya masa suna &#8216;<strong>Addis Ababa<\/strong>.&#8217;<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Wace ce Taytu Betul Kafin ta Zama Sarauniyar Sarakuna?<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>An haifi <strong>Taytu Betul<\/strong> cikin iyalan sarauta masu \u0199arfin tasiri wa\u0257anda ke da dangantaka da <strong>Daular Sulaimaniya<\/strong> wajen shekarar <strong>1840<\/strong> ko <strong>1851<\/strong> a cewar wasu majiyoyi a <strong>Debre Tabor<\/strong> wadda ba shi da nisa da Kogin <strong>Tana<\/strong>.<\/p>\n\n\n\n<p>An yi mata auren fari ta na yarinya \u01b4ar shekaru 10 da haihuwa, wadda ba abin mamaki ba ne ga yarinya \u01b4ar babban gida a wancan zamani.<\/p>\n\n\n\n<p>An bayyana cewa ta yi aure-aure wa\u0257anda ba ta ji da\u0257insu ba kafin daga \u0199arshe ta auri mijinta na biyar Sarkin Daular <strong>Shewa<\/strong> wadda daga baya ya zama <strong>Sarkin<\/strong> <strong>Sarakuna Menelik II<\/strong>. A lokacin aurensu ta tara dukiya da kadarori masu yawa.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Ya ya aka yi Taytu Betul ta Zama mai \u0198arfin Fa\u0257a a JI?<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Auren<strong> Taytu Betul<\/strong> da <strong>Menelik II<\/strong> ha\u0257i ne mai \u0199arfi kasancewar \u0253angarori biyu sun kawo ha\u0257aka da \u0199awance a Arewaci da Kudancin <strong>Habasha<\/strong>.<\/p>\n\n\n\n<p>Yayin da suka zama Sarkin sarakuna da Sarauniyar sarakunan sun \u0199ulla \u0199awance da sarakuna da dama na yankin wasu \u0199awancen lumana wasu kuma bayan an gwabza ya\u0199i. Sai dai kuma <strong>Taytul Betul<\/strong> ta yi \u0199o\u0199arin tabbatar da cewa ba wai ta kasance matar sarki ba kawai, amma ta zama cikin masu bada shawara da kuma cikin maya\u0199a.<\/p>\n\n\n\n<p>Masana tarihi sun ce, ana kallon ta daidai da <strong>Menelik II<\/strong> kuma a wasu lokutan ta kan zartar da \u0257aukar mataki mai tsauri fiye da mijinta.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Da me Taytu Betul ta fi Shahara<\/strong>?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Taytu Betul<\/strong> ta yi fice bisa rawar da ta taka na jagorantar ya\u0199i a kan Italiya wadda ya haifar da Ya\u0199in <strong>Adwa<\/strong>. An ce, <strong>Taytu<\/strong> ta jagoranci runduna ta Maya\u0199a <strong>5,000<\/strong> da Dawaki <strong>600<\/strong> wajen fafatawa da <strong>Italiyawa<\/strong> wa\u0257anda suke \u0199o\u0199arin yi wa <strong>Habasha<\/strong> Mulkin Mallaka.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Taytu<\/strong>, ta dage wajen yin adawa da \u0199ulla yarjejeniya da <strong>Italiya<\/strong> wadda aka yi wa la\u0199abi da yarjejeniyar &#8216;<strong>Wuchale<\/strong>&#8216; wadda a takarda ta sanya <strong>Habasha<\/strong> \u0199ar\u0199ashin ikon <strong>Italiyawa<\/strong>.<\/p>\n\n\n\n<p>A lokacin da <strong>Menelik II<\/strong> da <strong>Taytu<\/strong> suka afka ya\u0199i ga <strong>Italiyawa<\/strong>, <strong>Taytu<\/strong> ta taka muhimmiyar rawa da kuma jagorantar rundunar ta zuwa fagen daga. Ta sami gagarumar nasara a wani wuri da <strong>Italiya<\/strong> ta gina a <strong>Mekelle<\/strong> inda ta mur\u0199ushe Italiyan ta hanyar datse musu hanyoyin samun ruwa.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Shin Taytu Betul Mace ce da ta Fita Daban a Zamaninta?<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p><strong>Habasha<\/strong> ta yi shugabanni mata masu \u0199arfin iko, iyaye mata ko matan masu mulki da kuma mata da dama da suka shiga aikin soji &#8211; wata\u0199ila ba lallai su \u0257auki makamai ba, to amma sun taimaka wa Sojoji wajen girki da share-share da kuma \u0199arfafa musu guiwa. Ba kasafai mata suke jagorantar rundunar maya\u0199a ba kamar yadda <strong>Taytu<\/strong> ta yi.<\/p>\n\n\n\n<p>A wasu bayanai da suka siffanta Ya\u0199in <strong>Adwa<\/strong>, an baiyana ta a matsayin gwarzuwar ya\u0199i, sai dai babu wata shaida da ta nuna ta \u0257auki makami da kanta. Ta iya karatu da rubutu wadda hakan ya sa ta zama ta musamman. <strong>Taytu<\/strong>, na son yin wasan dara da kuma wa\u0199o\u0199i.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>ME Ya Faru Bayan Rasuwar Menelik? <\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>A <strong>1909<\/strong> Sarki <strong>Menelik<\/strong> ya sami shanyewar \u0253arin jiki. Ta kar\u0253i ragamar gudanar da yawancin ayyuka musamman gudanar da sha&#8217;anin mulki.<\/p>\n\n\n\n<p>Bayan wasu lokuta masu hamayya da ita a cikin iyalan Masarauta suka matsa mata lamba ta yi murabus. Wasu masana tarihi sun yi imanin cewar, ta zama mai matu\u0199ar \u0199arfin iko wadda ya sa wasu da dama ba sa son ta a kotun Sarki.<\/p>\n\n\n\n<p>Lokacin da <strong>Menelik<\/strong> ya rasu a <strong>1913<\/strong> aka fitar da <strong>Taytu<\/strong> daga <strong>Fada<\/strong> kuma \u0199arfin tasirinta ya shu\u0257e. Ta rasu a <strong>1917<\/strong>.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Ta ya ya Muka San Abubuwa da Yawa Game da TAYTU BETUL?<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Mun sami labari game da ita ta hanyar tarihi na baka da kuma tarihi da aka rubuta sannan kuma da bayanai na hotuna.<\/p>\n\n\n\n<p>Jama&#8217;a a kotun <strong>Habasha<\/strong> da Jakadun \u0199asashen waje da Fursunonin ya\u0199i na Italiya da kuma wasi\u0199u da Taytu ta rubuta da kanta sun yi cikakken bayani game da ita.<\/p>\n\n\n\n<p>Wani Injiniya na <strong>Switzerland<\/strong>, <strong>Alfred Ilg<\/strong> wadda ya yi hul\u0257a da Sarkin sarakuna da Sarauniyar sarakuna shi ma ya tara bayanai da hotunan sarakunan wadda ya ba da haske a kan rayuwar <strong>Fadar<\/strong>.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Madogara<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Shawarwarin kimiyya a kan wannan ma\u0199ala sun samu ne daga <strong>Farfesa Doulaye<\/strong> <strong>Konat\u00e9<\/strong>, da <strong>Dr. Lily Mafela<\/strong> da kuma <strong>Farfesa Christopher Ogbogbo.<\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Taytu Betul ta kasance sarauniyar Habasha daga 1889 zuwa 1913 kuma matar sarki Menelik na biyu. Jarumi mai tasiri wajen adawa da mulkin mallaka a \u0199arshen karni na 19 (Scramble for Africa), ita, tare da mijinta, sun kafa babban birnin Habasha na zamani, &#8216;Addis Ababa&#8217; a 1886. Mahaifin Taytu shi ne Ras Betul Haile Maryam, [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":2509,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"inline_featured_image":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[93],"tags":[],"class_list":["post-2510","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-jiya-da-yau"],"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v27.0 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Taytu Betul: Shahararriyar Sarauniyar Sarakuna<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"noindex, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_US\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Taytu Betul: Shahararriyar Sarauniyar Sarakuna\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"Taytu Betul ta kasance sarauniyar Habasha daga 1889 zuwa 1913 kuma matar sarki Menelik na biyu. Jarumi mai tasiri wajen adawa da mulkin mallaka a \u0199arshen karni na 19 (Scramble for Africa), ita, tare da mijinta, sun kafa babban birnin Habasha na zamani, &#8216;Addis Ababa&#8217; a 1886. Mahaifin Taytu shi ne Ras Betul Haile Maryam, [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2510\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"Taskar Nasaba\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2024-12-03T02:21:42+00:00\" \/>\n<meta property=\"article:modified_time\" content=\"2024-12-09T17:29:14+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-03T032254.636.jpeg\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"533\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"483\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/jpeg\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Salahuddeen Muhammad\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"Salahuddeen Muhammad\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Est. reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"5 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\/\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2510#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2510\"},\"author\":{\"name\":\"Salahuddeen Muhammad\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753\"},\"headline\":\"Taytu Betul: Shahararriyar Sarauniyar Sarakuna\",\"datePublished\":\"2024-12-03T02:21:42+00:00\",\"dateModified\":\"2024-12-09T17:29:14+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2510\"},\"wordCount\":1022,\"commentCount\":0,\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2510#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-03T032254.636.jpeg\",\"articleSection\":[\"Jiya Da Yau\"],\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2510#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2510\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2510\",\"name\":\"Taytu Betul: Shahararriyar Sarauniyar Sarakuna\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2510#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2510#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-03T032254.636.jpeg\",\"datePublished\":\"2024-12-03T02:21:42+00:00\",\"dateModified\":\"2024-12-09T17:29:14+00:00\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2510#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2510\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2510#primaryimage\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-03T032254.636.jpeg\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-03T032254.636.jpeg\",\"width\":533,\"height\":483},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2510#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Taytu Betul: Shahararriyar Sarauniyar Sarakuna\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"description\":\"\",\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\"},\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-US\"},{\"@type\":\"Organization\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\",\"logo\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png\",\"width\":343,\"height\":345,\"caption\":\"Taskar Nasaba\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/\"}},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753\",\"name\":\"Salahuddeen Muhammad\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg\",\"caption\":\"Salahuddeen Muhammad\"},\"description\":\"\u018aanjarida, marubuci, mai manufar bun\u0199asa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.\",\"sameAs\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\"],\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?author=1\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Taytu Betul: Shahararriyar Sarauniyar Sarakuna","robots":{"index":"noindex","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"og_locale":"en_US","og_type":"article","og_title":"Taytu Betul: Shahararriyar Sarauniyar Sarakuna","og_description":"Taytu Betul ta kasance sarauniyar Habasha daga 1889 zuwa 1913 kuma matar sarki Menelik na biyu. Jarumi mai tasiri wajen adawa da mulkin mallaka a \u0199arshen karni na 19 (Scramble for Africa), ita, tare da mijinta, sun kafa babban birnin Habasha na zamani, &#8216;Addis Ababa&#8217; a 1886. Mahaifin Taytu shi ne Ras Betul Haile Maryam, [&hellip;]","og_url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2510","og_site_name":"Taskar Nasaba","article_published_time":"2024-12-03T02:21:42+00:00","article_modified_time":"2024-12-09T17:29:14+00:00","og_image":[{"width":533,"height":483,"url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-03T032254.636.jpeg","type":"image\/jpeg"}],"author":"Salahuddeen Muhammad","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"Salahuddeen Muhammad","Est. reading time":"5 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2510#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2510"},"author":{"name":"Salahuddeen Muhammad","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753"},"headline":"Taytu Betul: Shahararriyar Sarauniyar Sarakuna","datePublished":"2024-12-03T02:21:42+00:00","dateModified":"2024-12-09T17:29:14+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2510"},"wordCount":1022,"commentCount":0,"publisher":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2510#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-03T032254.636.jpeg","articleSection":["Jiya Da Yau"],"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2510#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2510","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2510","name":"Taytu Betul: Shahararriyar Sarauniyar Sarakuna","isPartOf":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2510#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2510#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-03T032254.636.jpeg","datePublished":"2024-12-03T02:21:42+00:00","dateModified":"2024-12-09T17:29:14+00:00","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2510#breadcrumb"},"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2510"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2510#primaryimage","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-03T032254.636.jpeg","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-03T032254.636.jpeg","width":533,"height":483},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2510#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/taskarnasaba.com\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Taytu Betul: Shahararriyar Sarauniyar Sarakuna"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/","name":"Taskar Nasaba","description":"","publisher":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization"},"potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-US"},{"@type":"Organization","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization","name":"Taskar Nasaba","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/","logo":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png","width":343,"height":345,"caption":"Taskar Nasaba"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/"}},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753","name":"Salahuddeen Muhammad","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/image\/","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg","caption":"Salahuddeen Muhammad"},"description":"\u018aanjarida, marubuci, mai manufar bun\u0199asa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.","sameAs":["https:\/\/taskarnasaba.com"],"url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?author=1"}]}},"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-03T032254.636.jpeg","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2510","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=2510"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2510\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2716,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2510\/revisions\/2716"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/2509"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=2510"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=2510"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=2510"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}