{"id":2580,"date":"2024-12-04T15:27:26","date_gmt":"2024-12-04T15:27:26","guid":{"rendered":"https:\/\/taskarnasaba.com.ng\/?p=2580"},"modified":"2024-12-04T16:29:35","modified_gmt":"2024-12-04T16:29:35","slug":"hidimar-da-charles-henry-robinson-ya-yi-wa-harshen-hausa-i","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2580","title":{"rendered":"Hidimar da Charles Henry Robinson Ya Yi Wa Harshen Hausa I"},"content":{"rendered":"\n<p>Daga <strong>Salahuddeen Muhammad<\/strong> <\/p>\n\n\n\n<p>Shekaru 130yrs da suka gabata, a ranar Juma\u2019a, 26 ga watan Yuni, na shekara ta 1891, John Alfred Robinson, wani Bature malami a Kwalejin (Christ\u2019s College) ta Cambridge, ya mutu a garin Lokoja.<\/p>\n\n\n\n<p> Wannan Bature, wadda ya fahimci Hausa daidai gwargwado, ya na cikin mutanen da suka fara fahimtar amfanin nazarin Harshen Hausa.<\/p>\n\n\n\n<p>Watanni ka\u0257an bayan rasuwar wannan Bature, sai wasu Turawa suka ha\u0257u a wani Otal da ke birnin Landan mai suna (Charing Cross Hotel) don tattauna yadda za a ci gaba da aikin da John ya fara a kan Harshen Hausa don \u201cFara nazarin yaren a doron kimiyya da fassara littattafan addini da wasu Littattafai masu amfani, don \u0199aruwar Bahaushe.\u201d<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img fetchpriority=\"high\" decoding=\"async\" width=\"259\" height=\"400\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/97811080167281379098117659117732.jpg\" alt=\"\" class=\"wp-image-2579\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/97811080167281379098117659117732.jpg 259w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/97811080167281379098117659117732-194x300.jpg 194w\" sizes=\"(max-width: 259px) 100vw, 259px\" \/><\/figure>\n\n\n\n<p>Turawan da suka ha\u0257a wannan \u0199ungiya ta Hausa sun ha\u0257a da; Farfesa Max M\u00fcller, da Farfesa Peile, da Farfesa Margoliouth, da Farfesa Robertson Smith.<\/p>\n\n\n\n<p>Sauran sun ha\u0257a da; Mista MacGregor Laird, da Mista Francis Galton, da Mista FRS, da Manjo Darwin, da wakilin hukumar \u2018West African Enterprise\u2019 kuma gwamnan \u2018Royal Niger Company\u2019, wato Lord Abedare, da kuma mataimakinsa, Sir. George Taubman Goldie.<\/p>\n\n\n\n<p>Wa\u0257annan Turawa sun yi shawarar nemo mutumin da zai ta fi \u0199asar Hausa ya yi cu\u0257anya da Hausawa, kuma ya nazarci yarensu da al\u2019adunsu.<\/p>\n\n\n\n<p>Bayan an yi shekara ana shela a jaridu da mujallu na \u0199asar Birtaniya, kwamitin ya samu takardu daga wa\u0257anda ke sha\u2019awar wannan aiki. Amma sai dai duk wa\u0257anda suka nema, ba su samu cancantar da kwamitin ke bu\u0199ata ba.<\/p>\n\n\n\n<p>A ranar Asabar, 5 ga watan Nuwambar, 1892, wasi\u0199a ta iske Charles Henry Robinson, ya na kan aiki a garin Truro na shiyyar Cornwall da ke \u0199asar Ingila, cewa ana neman amincewar a saka sunansa a cikin wa\u0257anda za a tantance a matsayin \u0257alibin Hausa (Hausa studentship).<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img decoding=\"async\" width=\"667\" height=\"1000\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/714ovxzlmol6619049744038504019.jpg\" alt=\"\" class=\"wp-image-2577\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/714ovxzlmol6619049744038504019.jpg 667w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/714ovxzlmol6619049744038504019-200x300.jpg 200w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/714ovxzlmol6619049744038504019-600x900.jpg 600w\" sizes=\"(max-width: 667px) 100vw, 667px\" \/><\/figure>\n\n\n\n<p>Bayan da Robinson ya yi nazarin wasi\u0199ar, sai ya ga cewa, ya dace da ya \u0199arasa aikin da \u0257an\u2019uwansa ya fara. Shi Charles \u0199ani ne ga John, wancan Bature da ya rasu a Lokoja.<\/p>\n\n\n\n<p>Bayan kwamitin ya tattauna da shi don tabbatar da dacewarsa, daga bisani aka tabbatar da shi a matsayin \u0257alibin Hausa na farko.<\/p>\n\n\n\n<p>\u0198a\u2019idojin aikin sun ha\u0257a da, fara zuwa Kano da wasu manyan garuruwan \u0198asar Hausa, amma saboda yanayin rashin sabo da yanayin \u0198asar Hausa, sai aka bada shawarar ya fara zuwa birnin Tarabulus na \u0198asar Libiya ko birnin Tunis na Tunisiya, don fara koyon Hausa da Larabci a can, daga bisani sai ya zarce \u0198asar Hausa.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img decoding=\"async\" width=\"635\" height=\"483\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-04t1556114307448057270731930.jpg\" alt=\"\" class=\"wp-image-2575\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-04t1556114307448057270731930.jpg 635w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-04t1556114307448057270731930-300x228.jpg 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-04t1556114307448057270731930-600x456.jpg 600w\" sizes=\"(max-width: 635px) 100vw, 635px\" \/><figcaption class=\"wp-element-caption\"><strong>Wilnot Brooke da Alfred Robinson a \u0198asar Hausa <\/strong><\/figcaption><\/figure>\n\n\n\n<p>A ranar Lahadi, 30 ga watan Afrilu, na shekarar 1893, ya baro \u0198asar Ingila zuwa birnin Tarabulus, ya isa cikin kwanaki 40.<\/p>\n\n\n\n<p>A wancan zamanin, akwai kimanin mutane 36,000, a birnin Tarabulus, kuma daga cikin su akwai 600, da ke jin yaren Hausa.<\/p>\n\n\n\n<p>A cewar Robinson, akasarin masu jin Hausar sun zo ne a matsayin bayi ko<br \/>barori, kana kuma akwai mahajjata da hanya ta biyo da su, suka yada zango. Ya ce, akwai dubunnan Maniyyata Aikin Haji daga \u0199asar Hausa da ke yada zango a wannan gari kafin su wuce garin Suakin da ke Sudan don tsallaka tekun Maliya zuwa Jiddah.<\/p>\n\n\n\n<p>Cu\u0257anyar Robinson da irin wa\u0257annan Maniyyata ta sa ya fara koyon harshen Hausa. Amma bayan ya yi watanni shida a birnin Tarabulus, sai ya fahimci cewa ratsa Sahara don zuwa \u0198asar Hausa ba abu ne mai sau\u0199i ba.<\/p>\n\n\n\n<p>Garin Tarabulus a lokacin ya na \u0199ar\u0199ashin Daular Turkiyya, kuma Pasha (gwamnan garin) ya kar\u0253i \u2018oda\u2019 daga babban birnin Daular, wato Constantinople (wanda a yanzu ake kira Istanbul) da ka da ya bari Turawa su wuce mil 10 daga garin. Dalili kuwa shi ne, \u0199abilun da ke kan hanyar, musamman Abzinawa, su na far wa Turawa.<\/p>\n\n\n\n<p>Da Robinson ya fahimci tarna\u0199in keta Sahara ta birnin Tarabulus zuwa \u0198asar Hausa, sai ya ta fi birnin Tunis don gwadawa ta can.<\/p>\n\n\n\n<p>Saukarsa ke da wuya a garin Gabes tare da shi da Mista Harris, sai ya sa yi ra\u0199uma guda biyu. Haka ya yi makonni uku ya na zarya a wata Hamada da ke tsakanin Kudancin birnin Tunis da Aljas.<\/p>\n\n\n\n<p>Bayan da ya gama rangadin, sai ya dawo Tunis. Daga nan ne sai ya koma Ingila ya yi wata shida ya na koyon aikin Likitanci (don shirya wa zuwa \u0199asar Hausa), kana kuma ya halarci tarurruka na \u2018Hausa Association\u2019 da aka kira.<\/p>\n\n\n\n<p>Robinson, ya sake komawa dai birnin Tunis, in da su ka yi tsawon watanni shida tare da shi da Dakta. TJ Tonkin (abokin tafiyarsa zuwa Kano), su na koyon Hausa da Larabci.<\/p>\n\n\n\n<p>Da suka sake fahimtar cewa, tsallaka Sahara abu ne mai tsananin wuya, a watan Yunin, shekara ta 1894, sai suka sake dawowa Ingila don zuwa \u0199asar Hausa ta teku, zuwa Kogin Kwara. Dab da garin Turabulus, Robinson ya \u0199ara samun abokin tafiya, wato Mista John Bonner, wanda ya koyi Larabci a dalilin zamansa na shekaru biyu a Turabulus.<\/p>\n\n\n\n<p>Da ya koma Ingila, an yi taro sau biyu na \u2018Hausa Association\u2019. Taron farko an yi shi a ranar Talata, uku ga watan Yuli a \u0257akin taro na Majalisar Kasuwanci ta Landan (London Chamber of Commerce).<\/p>\n\n\n\n<p>Taron waddda Sir A. Rollit ya jagoranta, ya samu bayanai daga Mista HH Johnson, da Mista HM Stanley wa\u0257anda suka ba da bayanai a kan ha\u0257uwar su da Hausawa.<\/p>\n\n\n\n<p>Mista Johnson ya ce, \u201cA yawoce-yawocen da na yi a \u0199asashen Afrika, na fi ha\u0257uwa da Bahaushe a kan kowace \u0199abila, kuma harshen Hausa ya fi kowane harshe ya\u0257uwa a arewacin Afrika. Saboda haka, duk kuwa \u0199asar da take son mallakar \u0199waryar Afrika (Central Soudan), to kuwa dole sai ta mallaki Bahaushe. Ina fatan wata rana za a samu Farfesoshi a Jami\u2019unmu na fannin Hausa da Suwahili.\u201d<\/p>\n\n\n\n<p>Shi kuwa Mista Stanley, ya yi magana ne a kan wani Bahaushe da ya ha\u0257u da shi a \u0199asar Kwango. Ya ce fi\u0199irar Bahaushe da son Littafi daban ta ke, da yadda jahilci da camfe-camfe su ka yi wa \u0199abilun Kwango katutu.<\/p>\n\n\n\n<p>A taro na biyu, wadda aka yi a ranar Juma\u2019a, 13 ga watan Yuli, a \u0257akin taro na Liverpool Town Hall, Sir George Taubman Goldie da sauran mahalarta taron sun yi jawabai.<\/p>\n\n\n\n<p>Bayan wannan taro na biyu ne, gari na wayewa Robinson da shi da Dakta Tonkin, da Mista Bonner, da Salam (wani Balarabe mai hidimta masu) su ka hau jirgin ruwa mai suna SS Loanda don zuwa ga\u0253ar Kogin Kwara.<\/p>\n\n\n\n<p>(Wani lokaci za mu kawo labarin zuwan Robinson Kano da ha\u0257uwarsa da Sarkin Kano Alu da kuma yadda wannan Bature ya rubuta \u0199amus na Hausa zuwa Turanci na farko. Mun tsakuro wannan labari daga littafin CH Robinson mai suna \u2018Hausaland: Or 1500 Miles Through Central Soudan).<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"585\" height=\"524\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-04t1624577832519720168110422.jpg\" alt=\"\" class=\"wp-image-2578\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-04t1624577832519720168110422.jpg 585w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-04t1624577832519720168110422-300x269.jpg 300w\" sizes=\"(max-width: 585px) 100vw, 585px\" \/><\/figure>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Salahuddeen Muhammad Shekaru 130yrs da suka gabata, a ranar Juma\u2019a, 26 ga watan Yuni, na shekara ta 1891, John Alfred Robinson, wani Bature malami a Kwalejin (Christ\u2019s College) ta Cambridge, ya mutu a garin Lokoja. Wannan Bature, wadda ya fahimci Hausa daidai gwargwado, ya na cikin mutanen da suka fara fahimtar amfanin nazarin Harshen [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":2574,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"inline_featured_image":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[86],"tags":[],"class_list":["post-2580","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-harshe"],"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v27.0 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Hidimar da Charles Henry Robinson Ya Yi Wa Harshen Hausa I<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"noindex, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_US\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Hidimar da Charles Henry Robinson Ya Yi Wa Harshen Hausa I\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"Daga Salahuddeen Muhammad Shekaru 130yrs da suka gabata, a ranar Juma\u2019a, 26 ga watan Yuni, na shekara ta 1891, John Alfred Robinson, wani Bature malami a Kwalejin (Christ\u2019s College) ta Cambridge, ya mutu a garin Lokoja. Wannan Bature, wadda ya fahimci Hausa daidai gwargwado, ya na cikin mutanen da suka fara fahimtar amfanin nazarin Harshen [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2580\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"Taskar Nasaba\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2024-12-04T15:27:26+00:00\" \/>\n<meta property=\"article:modified_time\" content=\"2024-12-04T16:29:35+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-04T155601.699.jpeg\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"259\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"416\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/jpeg\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Salahuddeen Muhammad\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"Salahuddeen Muhammad\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Est. reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"6 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\/\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2580#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2580\"},\"author\":{\"name\":\"Salahuddeen Muhammad\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753\"},\"headline\":\"Hidimar da Charles Henry Robinson Ya Yi Wa Harshen Hausa I\",\"datePublished\":\"2024-12-04T15:27:26+00:00\",\"dateModified\":\"2024-12-04T16:29:35+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2580\"},\"wordCount\":1122,\"commentCount\":0,\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2580#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-04T155601.699.jpeg\",\"articleSection\":[\"Harshe\"],\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2580#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2580\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2580\",\"name\":\"Hidimar da Charles Henry Robinson Ya Yi Wa Harshen Hausa I\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2580#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2580#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-04T155601.699.jpeg\",\"datePublished\":\"2024-12-04T15:27:26+00:00\",\"dateModified\":\"2024-12-04T16:29:35+00:00\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2580#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2580\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2580#primaryimage\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-04T155601.699.jpeg\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-04T155601.699.jpeg\",\"width\":259,\"height\":416},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2580#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Hidimar da Charles Henry Robinson Ya Yi Wa Harshen Hausa I\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"description\":\"\",\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\"},\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-US\"},{\"@type\":\"Organization\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\",\"logo\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png\",\"width\":343,\"height\":345,\"caption\":\"Taskar Nasaba\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/\"}},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753\",\"name\":\"Salahuddeen Muhammad\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg\",\"caption\":\"Salahuddeen Muhammad\"},\"description\":\"\u018aanjarida, marubuci, mai manufar bun\u0199asa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.\",\"sameAs\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\"],\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?author=1\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Hidimar da Charles Henry Robinson Ya Yi Wa Harshen Hausa I","robots":{"index":"noindex","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"og_locale":"en_US","og_type":"article","og_title":"Hidimar da Charles Henry Robinson Ya Yi Wa Harshen Hausa I","og_description":"Daga Salahuddeen Muhammad Shekaru 130yrs da suka gabata, a ranar Juma\u2019a, 26 ga watan Yuni, na shekara ta 1891, John Alfred Robinson, wani Bature malami a Kwalejin (Christ\u2019s College) ta Cambridge, ya mutu a garin Lokoja. Wannan Bature, wadda ya fahimci Hausa daidai gwargwado, ya na cikin mutanen da suka fara fahimtar amfanin nazarin Harshen [&hellip;]","og_url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2580","og_site_name":"Taskar Nasaba","article_published_time":"2024-12-04T15:27:26+00:00","article_modified_time":"2024-12-04T16:29:35+00:00","og_image":[{"width":259,"height":416,"url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-04T155601.699.jpeg","type":"image\/jpeg"}],"author":"Salahuddeen Muhammad","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"Salahuddeen Muhammad","Est. reading time":"6 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2580#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2580"},"author":{"name":"Salahuddeen Muhammad","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753"},"headline":"Hidimar da Charles Henry Robinson Ya Yi Wa Harshen Hausa I","datePublished":"2024-12-04T15:27:26+00:00","dateModified":"2024-12-04T16:29:35+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2580"},"wordCount":1122,"commentCount":0,"publisher":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2580#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-04T155601.699.jpeg","articleSection":["Harshe"],"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2580#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2580","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2580","name":"Hidimar da Charles Henry Robinson Ya Yi Wa Harshen Hausa I","isPartOf":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2580#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2580#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-04T155601.699.jpeg","datePublished":"2024-12-04T15:27:26+00:00","dateModified":"2024-12-04T16:29:35+00:00","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2580#breadcrumb"},"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2580"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2580#primaryimage","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-04T155601.699.jpeg","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-04T155601.699.jpeg","width":259,"height":416},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2580#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/taskarnasaba.com\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Hidimar da Charles Henry Robinson Ya Yi Wa Harshen Hausa I"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/","name":"Taskar Nasaba","description":"","publisher":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization"},"potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-US"},{"@type":"Organization","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization","name":"Taskar Nasaba","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/","logo":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png","width":343,"height":345,"caption":"Taskar Nasaba"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/"}},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753","name":"Salahuddeen Muhammad","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/image\/","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg","caption":"Salahuddeen Muhammad"},"description":"\u018aanjarida, marubuci, mai manufar bun\u0199asa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.","sameAs":["https:\/\/taskarnasaba.com"],"url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?author=1"}]}},"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-04T155601.699.jpeg","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2580","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=2580"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2580\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2581,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2580\/revisions\/2581"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/2574"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=2580"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=2580"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=2580"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}