{"id":2583,"date":"2024-12-04T16:28:33","date_gmt":"2024-12-04T16:28:33","guid":{"rendered":"https:\/\/taskarnasaba.com.ng\/?p=2583"},"modified":"2024-12-04T17:38:33","modified_gmt":"2024-12-04T17:38:33","slug":"wani-yaki-ne-mafi-tsaho-a-tarihin-duniya","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2583","title":{"rendered":"Wani Ya\u0199i ne Mafi Tsaho a Tarihin Duniya?"},"content":{"rendered":"\n<p>Ya\u0199i Tsakanin \u0198asar Ingila da Faransa 1337 zuwa 1453, Shekaru 166 ana Gwabzawa.<\/p>\n\n\n\n<p>Daga: <strong>Salahuddeen Muhammad<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Ya\u0199in shekaru 100 ya kasance doguwar gwagwarmaya tsakanin Ingila da Faransa a kan gadon sarautar Faransa.<\/p>\n\n\n\n<p>Ya kasance daga 1337 zuwa 1453, don haka ana iya kiran shi da \u201cYa\u0199in shekaru 116yrs.\u201d<\/p>\n\n\n\n<p>Ya\u0199in ya fara ne da nasarori masu ban mamaki da dama daga \u0253angaren Birtaniya, kuma sojojin Ingila sun mamaye Faransa tsawon shekaru da dama.<\/p>\n\n\n\n<p>Ya\u0199in dai da aka yi shekaru \u0257aruruwa ana yi, shi ne ya\u0199in da aka \u0257auki tsawon lokaci ana yi ana tsagaitawa tsakanin \u0198asar Ingila da \u0198asar Faransa, tun daga shekarar 1337 zuwa 1453, wato a ta\u0199aice an shafe kusan shekaru 116 ana fafatawa.<\/p>\n\n\n\n<p>Sun shiga rikici ne kan batutuwa da dama, ciki har da ta\u0199addama kan mallakar yankin Ingilishi a Faransa da kuma halarcin gadon sarautar Faransa.<\/p>\n\n\n\n<p>Ya\u0199in Agincourt, (Oktoba 25, 1415), \u0199a\u0199\u0199arfan ya\u0199i a cikin ya\u0199in shekaru \u018aari 1337 zuwa 1453 wadda ya haifar da nasarar Ingilishi a kan Faransawa. Sojojin Ingila, \u0199ar\u0199ashin jagorancin Sarki Henry V, sun yi fice wajen samun nasara duk kuwa da fifikon adadi na abokin hamayyarsu.<\/p>\n\n\n\n<p>An fara wannan ya\u0199i ne a lokacin da sarkin ingila wadda ake kira da suna Sarki Edward na uku, ya \u0199alubalanci gadon sarautar Faransa, kuma ya mamaye yankin Arewa maso Yamma na \u0198asar ta Faransa.<\/p>\n\n\n\n<p>Sarkin da ya gaji Sarki Edward shi ne Sarki Richard na biyu, shi ma ya ci gaba da wannan ya\u0199i, haka zalika Sarki Henry na hu\u0257u wadda ya tum\u0253uke Richard daga Sarauta, shi ma ya ci gaba da gwabza ya\u0199i da Faransawa.<\/p>\n\n\n\n<p>Sarki Henry na biyar shi ne wadda ya zama Sarkin Ingila bayan Sarki Henry na hu\u0257u, shi ne kuma wadda ya ci Faransawa da ya\u0199i a ya\u0199in da ake kira da suna \u201cAgincourt\u2019\u2019 in da ya na\u0257a mu\u0199addashinsa a \u0199asar ta Faransa.<\/p>\n\n\n\n<p>Bayan shekaru da dama, Sarkin Faransa wato Charles na biyar, ya dawo da ya\u0199i sabo, in da ya koma ya\u0199ar Ingila tare da taimakon \u0199asar Scotland, kuma \u0199asar ta Faransa daga baya ta samu nasarar ya\u0199e-ya\u0199e da dama musamman ma a shekarar 1429, amma dai ba a samu wata cikakkiyar nasara ba sai a shekarar 1436, lokacin da Faransawa suka \u01b4anto birnin Paris daga \u0199ar\u0199ashin mulkin Ingila, sannan kuma a shekarar 1453, Faransa ta kori Ingila kwata-kwata daga yankinta.<\/p>\n\n\n\n<p>Ya\u0199i na biyu da yake rufawa ya\u0199in Ingila da Faransa baya, shi ne ya\u0199in Lardin Aceh, ko da yake dai akwai \u01b4ar tababa daga \u0253angaren masana tarihi game da tsayin da ake cewa, ya\u0199in na lardin Aceh ya yi, wato tsakanin al\u2019ummar Aceh na \u0199asar Indonesia da kuma al\u2019ummar \u0199asar Holland.<\/p>\n\n\n\n<p>Da farko dai, Netherlands ce ta \u0199addamar da ya\u0199i a kan al\u2019ummar lardin Aceh, a shekara ta 1873, to daga nan ne fa ya\u0199i ya ci gaba ya na yi ya na lafawa na tsawon shekaru da dama.<\/p>\n\n\n\n<p>Wasu masana tarihi sun ce, ya\u0199i ya \u0199are ne a shekarar 1903, amma dai a hukumance al\u2019ummar \u0199asar Netherlands ba su kwashe ya-nasu ya-nasu ba har sai a shekarar 1942. Saboda haka, za a iya cewa ya\u0199in lardin Aceh ya \u0257auki tsawon shekaru 30 ko kuma 69.<\/p>\n\n\n\n<p>To idan muka komo ya\u0199e-ya\u0199en da suka faru a \u0199arni na Ashirin, babu wani mutum da zai iya cewa ga ya\u0199in da ya fi tsawo, domin kuwa wa\u0257ansu har yanzu ana nan ana ci gaba da su.<\/p>\n\n\n\n<p>Misali ya\u0199in da ake yi tsakani Yahudawa da Palas\u0257inawa, ya\u0199i ne da ya samo asali tun a shekarar 1946, wato bayan ya\u0199in Duniya na biyu, lokacin da Majalisar \u018ainkin Duniya ta tsaga yankin Palas\u0257inu, in da aka bai wa Yahudawa kashi 55% da bisa 100 na Palas\u0257inu, su kuma Palas\u0257inawa aka ba su kashi 45% bisa 100, saboda haka, sai suka ce ba su yarda ba. To daga nan ne fa ya\u0199i ya fara har ya zuwa yau, kusan kimanin shekaru 75 ke nan ana cikin wannan hali.<\/p>\n\n\n\n<p>Akwai kuma rikicin \u0199asar Sudan na ya\u0199in basasa wadda aka fara tun a shekarar 1955, in da yanzu haka an \u0257auki kusan shekaru 51 ana wannan gumurzu.<\/p>\n\n\n\n<p>Haka zalika ita ma \u0199asar Guatemala ta fa\u0257a gararin ya\u0199in basasa wadda ya \u0257auki kusan shekaru 36 tun daga shekarar 1960 zuwa 1996.<\/p>\n\n\n\n<p>Kai! Babu ko shakka, abin ba\u0199in ciki ne idan aka dubi yadda tarihin Duniya ya cika da ya\u0199e-ya\u0199e masu tsawo, domin kuwa ba ya ga wa\u0257anda muka bayyana a baya, har ila yau akwai ya\u0199o\u0199i irin su ya\u0199in nan na \u0199asar Girka (Greece) mai tarihi wadda ya \u0257auki shekaru 27, da kuma ya\u0199in Vietnam wadda aka yi shekaru 18 ana yi.<\/p>\n\n\n\n<p>Ban da kuma rikicin da ya \u0199i ci ya \u0199i cinye wa fiye da shekaru 33 a yankin Northern Ireland.<\/p>\n\n\n\n<p>Wa\u0257annan ya\u0199e-ya\u0199e dukkaninsu, ya\u0199e-ya\u0199e ne masu tsawo \u0199warai da gaske.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Ya\u0199i Tsakanin \u0198asar Ingila da Faransa 1337 zuwa 1453, Shekaru 166 ana Gwabzawa. Daga: Salahuddeen Muhammad Ya\u0199in shekaru 100 ya kasance doguwar gwagwarmaya tsakanin Ingila da Faransa a kan gadon sarautar Faransa. Ya kasance daga 1337 zuwa 1453, don haka ana iya kiran shi da \u201cYa\u0199in shekaru 116yrs.\u201d Ya\u0199in ya fara ne da nasarori masu [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":2582,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"inline_featured_image":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[88],"tags":[],"class_list":["post-2583","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-tarihi"],"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v27.0 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Wani Ya\u0199i ne Mafi Tsaho a Tarihin Duniya?<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"noindex, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_US\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Wani Ya\u0199i ne Mafi Tsaho a Tarihin Duniya?\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"Ya\u0199i Tsakanin \u0198asar Ingila da Faransa 1337 zuwa 1453, Shekaru 166 ana Gwabzawa. Daga: Salahuddeen Muhammad Ya\u0199in shekaru 100 ya kasance doguwar gwagwarmaya tsakanin Ingila da Faransa a kan gadon sarautar Faransa. Ya kasance daga 1337 zuwa 1453, don haka ana iya kiran shi da \u201cYa\u0199in shekaru 116yrs.\u201d Ya\u0199in ya fara ne da nasarori masu [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2583\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"Taskar Nasaba\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2024-12-04T16:28:33+00:00\" \/>\n<meta property=\"article:modified_time\" content=\"2024-12-04T17:38:33+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-04T172733.990.jpeg\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"663\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"462\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/jpeg\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Salahuddeen Muhammad\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"Salahuddeen Muhammad\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Est. reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"4 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\/\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2583#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2583\"},\"author\":{\"name\":\"Salahuddeen Muhammad\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753\"},\"headline\":\"Wani Ya\u0199i ne Mafi Tsaho a Tarihin Duniya?\",\"datePublished\":\"2024-12-04T16:28:33+00:00\",\"dateModified\":\"2024-12-04T17:38:33+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2583\"},\"wordCount\":826,\"commentCount\":0,\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2583#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-04T172733.990.jpeg\",\"articleSection\":[\"Tarihi\"],\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2583#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2583\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2583\",\"name\":\"Wani Ya\u0199i ne Mafi Tsaho a Tarihin Duniya?\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2583#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2583#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-04T172733.990.jpeg\",\"datePublished\":\"2024-12-04T16:28:33+00:00\",\"dateModified\":\"2024-12-04T17:38:33+00:00\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2583#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2583\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2583#primaryimage\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-04T172733.990.jpeg\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-04T172733.990.jpeg\",\"width\":663,\"height\":462},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2583#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Wani Ya\u0199i ne Mafi Tsaho a Tarihin Duniya?\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"description\":\"\",\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\"},\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-US\"},{\"@type\":\"Organization\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\",\"logo\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png\",\"width\":343,\"height\":345,\"caption\":\"Taskar Nasaba\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/\"}},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753\",\"name\":\"Salahuddeen Muhammad\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg\",\"caption\":\"Salahuddeen Muhammad\"},\"description\":\"\u018aanjarida, marubuci, mai manufar bun\u0199asa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.\",\"sameAs\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\"],\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?author=1\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Wani Ya\u0199i ne Mafi Tsaho a Tarihin Duniya?","robots":{"index":"noindex","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"og_locale":"en_US","og_type":"article","og_title":"Wani Ya\u0199i ne Mafi Tsaho a Tarihin Duniya?","og_description":"Ya\u0199i Tsakanin \u0198asar Ingila da Faransa 1337 zuwa 1453, Shekaru 166 ana Gwabzawa. Daga: Salahuddeen Muhammad Ya\u0199in shekaru 100 ya kasance doguwar gwagwarmaya tsakanin Ingila da Faransa a kan gadon sarautar Faransa. Ya kasance daga 1337 zuwa 1453, don haka ana iya kiran shi da \u201cYa\u0199in shekaru 116yrs.\u201d Ya\u0199in ya fara ne da nasarori masu [&hellip;]","og_url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2583","og_site_name":"Taskar Nasaba","article_published_time":"2024-12-04T16:28:33+00:00","article_modified_time":"2024-12-04T17:38:33+00:00","og_image":[{"width":663,"height":462,"url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-04T172733.990.jpeg","type":"image\/jpeg"}],"author":"Salahuddeen Muhammad","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"Salahuddeen Muhammad","Est. reading time":"4 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2583#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2583"},"author":{"name":"Salahuddeen Muhammad","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753"},"headline":"Wani Ya\u0199i ne Mafi Tsaho a Tarihin Duniya?","datePublished":"2024-12-04T16:28:33+00:00","dateModified":"2024-12-04T17:38:33+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2583"},"wordCount":826,"commentCount":0,"publisher":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2583#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-04T172733.990.jpeg","articleSection":["Tarihi"],"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2583#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2583","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2583","name":"Wani Ya\u0199i ne Mafi Tsaho a Tarihin Duniya?","isPartOf":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2583#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2583#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-04T172733.990.jpeg","datePublished":"2024-12-04T16:28:33+00:00","dateModified":"2024-12-04T17:38:33+00:00","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2583#breadcrumb"},"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2583"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2583#primaryimage","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-04T172733.990.jpeg","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-04T172733.990.jpeg","width":663,"height":462},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2583#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/taskarnasaba.com\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Wani Ya\u0199i ne Mafi Tsaho a Tarihin Duniya?"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/","name":"Taskar Nasaba","description":"","publisher":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization"},"potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-US"},{"@type":"Organization","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization","name":"Taskar Nasaba","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/","logo":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png","width":343,"height":345,"caption":"Taskar Nasaba"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/"}},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753","name":"Salahuddeen Muhammad","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/image\/","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg","caption":"Salahuddeen Muhammad"},"description":"\u018aanjarida, marubuci, mai manufar bun\u0199asa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.","sameAs":["https:\/\/taskarnasaba.com"],"url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?author=1"}]}},"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-04T172733.990.jpeg","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2583","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=2583"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2583\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2585,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2583\/revisions\/2585"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/2582"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=2583"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=2583"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=2583"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}