{"id":2661,"date":"2024-12-09T12:16:54","date_gmt":"2024-12-09T12:16:54","guid":{"rendered":"https:\/\/taskarnasaba.com.ng\/?p=2661"},"modified":"2024-12-09T17:17:49","modified_gmt":"2024-12-09T17:17:49","slug":"rubutu-da-karatun-hausa-na-ganin-tasku-a-zamanin-yau","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2661","title":{"rendered":"Rubutu da Karatun Hausa na Ganin Tasku a Zamanin Yau"},"content":{"rendered":"\n<p><strong>Manyan \u01b4an bokon da suka fi yi wa rubutun na Hausa illa su ne \u01b4an jarida, musamman masu rubutun tallace-tallace.<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Daga; <strong>\u018aanladi Haruna<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Kasancewar Hausa Harshe ne mai sau\u0199in fahimta gami da basirar da Allah Ya yi wa \u0199abilar wajen aro wata kalmar daga wani yaren, su mayar da ita tamkar \u01b4ar asali a cikin yaren, ya sa harshen yake bun\u0199asa a dukkan fa\u0257in Duniya.<\/p>\n\n\n\n<p>A lokacin da Duniya ke kwance, duk inda Bahaushe ya je yakan fita zakka, kuma idan sun kai su dubu sai ya samu kulawa ta musamman daga masu \u2018Jan kunne\u2019 ko Larabawa.<\/p>\n\n\n\n<p>Har yanzu ma kuwa masu fita \u0199asashen wajen na shaida mana irin \u0257aukakar da suke samu alfarmar yarensu da al\u2019adunsu da addininsu.<\/p>\n\n\n\n<p>To amma fa bun\u0199asar Hausar na samun na\u0199asu ta wajen abubuwa da dama. \u018aaya daga cikinsu shi ne yadda rubutun Hausa ke cikin tsaka mai wuya.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;Idan na ce rubutun Hausa, ina nufin rubutun da aka juyar da haruffan boko zuwa Harshen Hausa, ban san yadda Ajami yake ba, watau rubutun Hausa cikin haruffan Larabci, wata\u0199ila shi ma akwai irin wa\u0257annan matsaloli da zan zayyano.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>Yanzu ya zamana cewa, duk wanda yake iya fahimtar yaren ko da ta fuskar saye da sayarwa ne, sai kurum ya hau kankanbar rubutawa, musamman irin wanda ke ta\u0199ama da ilmin Boko, ba tare da la\u2019akari da \u0199a&#8217;idojin da masana harshen suka shimfi\u0257a ba.<\/p>\n\n\n\n<p>Manyan \u01b4an bokon da suka fi yi wa rubutun na Hausa illa su ne \u01b4an jarida, musamman masu rubutun tallace-tallace.<\/p>\n\n\n\n<p>Na ci karo da wani \u0199aton Allon Talla a cikin birnin Kano an rubuta: \u201cMu na a Geyyara da Sayarawa.\u201d Wai fa nufinsu \u201cMuna gyara da sayarwa.\u201d Wani allon kuma na ga an rubuta: \u201cSan u o zuwa.\u201d Wai su na nufin: \u201cSannu da zuwa.\u201d<\/p>\n\n\n\n<p>Ha\u0199i\u0199a wannan ta\u2019addanci ne ake yi wa Harshen Hausa, maimakon a \u0257auki \u0199wararren mai fassara kamar yadda ake \u0257auka a wasu yarukan, amma ganin \u0199yashi da azar\u0253a\u0253i da rashin girmama \u0199abilar ya sa ake amfani da fassarar da aka ga dama.<\/p>\n\n\n\n<p>Na biyun masu ta\u2019addaci ga rubutun Harshen Hausar, su ne masu Gidajen Rediyo da Talabijin, musamman masu karanta labaru cikin Turanci da Hausa.<\/p>\n\n\n\n<p>Kasancewa ta mai sauraren labaran Gidajen Rediyon da ke birnin Kano, kwanaki cikin sanarwar da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (SSS) ta fitar game da binciken da ta gudanar a gidan tsohon mai ba wa Shugaban \u0198asa shawara ta fuskar tsaro, a labaran na Ingilishi sai suka ce: \u201c\u2026High calibre Rifles, several Magazines and Military related Gears were found\u2026\u201d<\/p>\n\n\n\n<p>A labaran Hausar kuma sai suka ce: \u201cAn samu manyan makamai tare da Mujallar sojoji a gidansa.\u201d<\/p>\n\n\n\n<p>Gidan Rediyo na biyu kuma suka ce: \u201cA gidan an samu wata Mujalla da ke koyar da aikin Sojoji tare da wasu manyan Bindigogi.\u201d<\/p>\n\n\n\n<p>Gidan Rediyo na uku kuma suka ce: &#8220;Tare da wata Mujalla Soja na koyar da ya\u0199i a cikinta.\u201d<\/p>\n\n\n\n<p>Gaba \u0257aya fa sun kasa fahimtar cewa, kalmar \u2018magazine\u2019 da aka fa\u0257a a sanarwar, ba ta na nufin Mujalla ba, ta na nufin Jigidar Albarusai, ko wani babban akwati mai \u0257auke da Albarusai musamman na bindigar nan mai sarrafa kanta (Machine Gun).<\/p>\n\n\n\n<p>Wannan ma babbar ta\u0253argaza ce, kuma ha\u0199i\u0199a ana cutar da Harshen Hausa bisa wannan mummunar fassara da ake yi cikin garaje.<\/p>\n\n\n\n<p>Kuma ya zama kamar raina aikin manyan Farfesoshi ne da ke hidimtawa Harshen a kullum, ba Dare ba Rana.<\/p>\n\n\n\n<p>Masu rubutu a zaurukan sada zumunci, musamman Facebook da WhatsApp da sauransu, su na gigita \u0199a&#8217;idojin rubutun Hausa.<\/p>\n\n\n\n<p>Nan ne za ka ga rubutu babu wa\u0199afi balle Aya, babu fasali balle kama, babu fasaha balle \u0199a\u2019ida. Nan ne za ka ga rubutu daga sama zuwa \u0199asa, ko daga \u0199asa zuwa sama kamar na \u01b4an \u0198asar Sin (China).<\/p>\n\n\n\n<p>Kuma wai su masu rubutun har buri suke a yi musu tsokaci, ko me za a ce da su? Oho! Ni kam ba na ko kallon rubutun nasu, domin ina gudun ka da kwamacalar da ke ciki ta sa ni amai.<\/p>\n\n\n\n<p>Da a ce ina da iko, duk wanda na samu da irin wannan baragadar rubutun, sai na ci tararsa gwargwadon \u0253arnar da ya aikata.<\/p>\n\n\n\n<p>Makarantun Firamare da Sakandare, musamman masu zaman kansu, na taka muhimmiyar rawa wajen lalata rubutun Hausa.<\/p>\n\n\n\n<p>Da yawa saboda tsumulmula ta rashin \u0257aukar \u0199wararrun malamai kamar yadda suke yi a wasu fannonin, sai su \u0257auki Ngozi ko Chinyere ko Samuel a matsayin wa\u0257anda za su koyar da Yaren Hausawa rubutun Hausa.<\/p>\n\n\n\n<p>Wannan wata mahangur\u0253a ce da ba ta haifar da da mai ido. A ganina ma ita ce ummulhaba\u2019isin faruwar ta\u0253argazojin da na ambata a sama.<\/p>\n\n\n\n<p>Don haka, ina kira ga hukumomin da abin ya shafa da su mi\u0199e tsaye su \u0199ara azama wajen kare martabar rubutun Hausa. A sanya doka mai tsanani ga duk wanda aka ga ya na rubuta gur\u0253ataccen rubutun Hausa a Allunan Talla, sannan a inganta hukumomin fassara ta yadda ba kowanne karabiti ne ke da lasisin fassara Hausa ba, sai wanda ya ke \u0199wararre.<\/p>\n\n\n\n<p>\u018aalibai kuwa, a \u0199ara himma wajen na\u0199altar hawa da saukar rubutun Hausa, ko da ba ita ce abin da kake koyo a makaranta ba, za ta zame maka abin tin\u0199aho duk inda ka je a fa\u0257in Duniya.<\/p>\n\n\n\n<p>\u0198asashen da suka ci gaba dukansu da rubutun harshen \u0199asarsu suke alfahari. Saboda haka ne ire-irenmu da ba Hausar muke karantawa a makaranta ba, amma saboda ita ce ta haife mu gaba da baya, ya sa muke nuna kishinmu game da ita.<\/p>\n\n\n\n<p>Malamai kuma ya dace su \u0199ara nutsawa fagen bincike da \u0199ir\u0199iro sabbin hanyoyin nazari da samar da tabbatattun \u0199a&#8217;idojin rubutu.<\/p>\n\n\n\n<p>Ya kuma dace su shigo harkar zamani, musamman Intanet domin su kankare kura-kurai da gangancin da ake yi wa harshen Hausa.<\/p>\n\n\n\n<p>Gwamnati kuwa da yake ita ce sha kundum, rubutun Hausa na bu\u0199atar agaji ta hanyar \u0257aukar nauyin malamai domin gudanar da bincike-bincike gami da \u0199arfafa dokokin da suka ji\u0253inci rubutun Hausa tare da inganta hanyoyin koyon rubutun, ta yadda zai zama ya tafi asin-da-asin tare da harshen ta fuskar furuci.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Manyan \u01b4an bokon da suka fi yi wa rubutun na Hausa illa su ne \u01b4an jarida, musamman masu rubutun tallace-tallace. Daga; \u018aanladi Haruna Kasancewar Hausa Harshe ne mai sau\u0199in fahimta gami da basirar da Allah Ya yi wa \u0199abilar wajen aro wata kalmar daga wani yaren, su mayar da ita tamkar \u01b4ar asali a cikin [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":2660,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"inline_featured_image":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[84],"tags":[],"class_list":["post-2661","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-adabi"],"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v27.0 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Rubutu da Karatun Hausa na Ganin Tasku a Zamanin Yau<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"noindex, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_US\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Rubutu da Karatun Hausa na Ganin Tasku a Zamanin Yau\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"Manyan \u01b4an bokon da suka fi yi wa rubutun na Hausa illa su ne \u01b4an jarida, musamman masu rubutun tallace-tallace. Daga; \u018aanladi Haruna Kasancewar Hausa Harshe ne mai sau\u0199in fahimta gami da basirar da Allah Ya yi wa \u0199abilar wajen aro wata kalmar daga wani yaren, su mayar da ita tamkar \u01b4ar asali a cikin [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2661\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"Taskar Nasaba\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2024-12-09T12:16:54+00:00\" \/>\n<meta property=\"article:modified_time\" content=\"2024-12-09T17:17:49+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-09T131802.689_1.jpeg\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"678\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"401\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/jpeg\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Taskar Nasaba\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"Taskar Nasaba\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Est. reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"5 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\/\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2661#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2661\"},\"author\":{\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/50c6fe8b25398ccbaf7fd94dee1c8456\"},\"headline\":\"Rubutu da Karatun Hausa na Ganin Tasku a Zamanin Yau\",\"datePublished\":\"2024-12-09T12:16:54+00:00\",\"dateModified\":\"2024-12-09T17:17:49+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2661\"},\"wordCount\":1037,\"commentCount\":0,\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2661#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-09T131802.689_1.jpeg\",\"articleSection\":[\"Adabi\"],\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2661#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2661\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2661\",\"name\":\"Rubutu da Karatun Hausa na Ganin Tasku a Zamanin Yau\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2661#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2661#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-09T131802.689_1.jpeg\",\"datePublished\":\"2024-12-09T12:16:54+00:00\",\"dateModified\":\"2024-12-09T17:17:49+00:00\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2661#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2661\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2661#primaryimage\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-09T131802.689_1.jpeg\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-09T131802.689_1.jpeg\",\"width\":678,\"height\":401},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2661#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Rubutu da Karatun Hausa na Ganin Tasku a Zamanin Yau\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"description\":\"\",\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\"},\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-US\"},{\"@type\":\"Organization\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\",\"logo\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png\",\"width\":343,\"height\":345,\"caption\":\"Taskar Nasaba\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/\"}},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/50c6fe8b25398ccbaf7fd94dee1c8456\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/cropped-Taskar-Nasaba-PNG-100x100.png\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/cropped-Taskar-Nasaba-PNG-100x100.png\",\"caption\":\"Taskar Nasaba\"},\"sameAs\":[\"http:\/\/www.taskarnasaba.com.ng\"],\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?author=2\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Rubutu da Karatun Hausa na Ganin Tasku a Zamanin Yau","robots":{"index":"noindex","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"og_locale":"en_US","og_type":"article","og_title":"Rubutu da Karatun Hausa na Ganin Tasku a Zamanin Yau","og_description":"Manyan \u01b4an bokon da suka fi yi wa rubutun na Hausa illa su ne \u01b4an jarida, musamman masu rubutun tallace-tallace. Daga; \u018aanladi Haruna Kasancewar Hausa Harshe ne mai sau\u0199in fahimta gami da basirar da Allah Ya yi wa \u0199abilar wajen aro wata kalmar daga wani yaren, su mayar da ita tamkar \u01b4ar asali a cikin [&hellip;]","og_url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2661","og_site_name":"Taskar Nasaba","article_published_time":"2024-12-09T12:16:54+00:00","article_modified_time":"2024-12-09T17:17:49+00:00","og_image":[{"width":678,"height":401,"url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-09T131802.689_1.jpeg","type":"image\/jpeg"}],"author":"Taskar Nasaba","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"Taskar Nasaba","Est. reading time":"5 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2661#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2661"},"author":{"name":"Taskar Nasaba","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/50c6fe8b25398ccbaf7fd94dee1c8456"},"headline":"Rubutu da Karatun Hausa na Ganin Tasku a Zamanin Yau","datePublished":"2024-12-09T12:16:54+00:00","dateModified":"2024-12-09T17:17:49+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2661"},"wordCount":1037,"commentCount":0,"publisher":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2661#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-09T131802.689_1.jpeg","articleSection":["Adabi"],"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2661#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2661","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2661","name":"Rubutu da Karatun Hausa na Ganin Tasku a Zamanin Yau","isPartOf":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2661#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2661#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-09T131802.689_1.jpeg","datePublished":"2024-12-09T12:16:54+00:00","dateModified":"2024-12-09T17:17:49+00:00","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2661#breadcrumb"},"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2661"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2661#primaryimage","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-09T131802.689_1.jpeg","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-09T131802.689_1.jpeg","width":678,"height":401},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2661#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/taskarnasaba.com\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Rubutu da Karatun Hausa na Ganin Tasku a Zamanin Yau"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/","name":"Taskar Nasaba","description":"","publisher":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization"},"potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-US"},{"@type":"Organization","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization","name":"Taskar Nasaba","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/","logo":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png","width":343,"height":345,"caption":"Taskar Nasaba"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/"}},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/50c6fe8b25398ccbaf7fd94dee1c8456","name":"Taskar Nasaba","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/image\/","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/cropped-Taskar-Nasaba-PNG-100x100.png","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/cropped-Taskar-Nasaba-PNG-100x100.png","caption":"Taskar Nasaba"},"sameAs":["http:\/\/www.taskarnasaba.com.ng"],"url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?author=2"}]}},"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-09T131802.689_1.jpeg","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2661","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=2661"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2661\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2713,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2661\/revisions\/2713"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/2660"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=2661"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=2661"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=2661"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}