{"id":2722,"date":"2024-12-10T15:52:37","date_gmt":"2024-12-10T15:52:37","guid":{"rendered":"https:\/\/taskarnasaba.com.ng\/?p=2722"},"modified":"2024-12-10T16:48:40","modified_gmt":"2024-12-10T16:48:40","slug":"tarihin-ya%c6%99in-basasar-syria","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2722","title":{"rendered":"Tarihin Ya\u0199in Basasar Syria"},"content":{"rendered":"\n<p>Ya\u0199in Basasar Syria (Sham) dai wani Ya\u0199in Basasa ne mai \u0253angarori da dama a \u0198asar Syria da ake gwabzawa tsakanin Jamhuriyar Larabawa ta Syria \u0199ar\u0199ashin jagorancin tsohon Shugaban \u0198asar Syria Bashar al-Assad da wasu dakaru na cikin gida da na waje da ke adawa da Gwamnatin Syria da kuma juna, ta fuskoki daban-daban.<\/p>\n\n\n\n<p>Fiye da shekaru 13 ke nan da Syria ta tsunduma cikin Ya\u0199in Basasa, lamarin da ya haifar da Miliyoyin \u01b4an gudun hijirar da suka rasa muhallansu, yayin da mutane a a\u0199alla Dubu 380 suka mutu a sanadiyyar rikicin \u0199asar.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img fetchpriority=\"high\" decoding=\"async\" width=\"720\" height=\"405\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-10t1646133067923351455577812.jpg\" alt=\"\" class=\"wp-image-2729\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-10t1646133067923351455577812.jpg 720w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-10t1646133067923351455577812-300x169.jpg 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-10t1646133067923351455577812-600x338.jpg 600w\" sizes=\"(max-width: 720px) 100vw, 720px\" \/><figcaption class=\"wp-element-caption\"><em>Wata uwa tare da \u01b4ayanta, a lokacin da suke \u0199aura daga muhallinsu, bayan wani hari da aka kai Birnin Aleppo. |Hoto: RFI<\/em><\/figcaption><\/figure>\n\n\n\n<p>Fage<\/p>\n\n\n\n<p>Abin da ya fara tun lokacin da zanga-zangar adawa da Gwamnatin Shugaba Assad a shekara ta 2011 ta riki\u0257e zuwa wani gaggarumin Ya\u0199i tsakanin Gwamnatin Syria da ke samun goyon bayan Rasha da Iran da kuma \u0199ungiyoyin \u01b4an tawayen da ke adawa da Gwamnati da Amurka ke marawa baya da kuma adadin kar\u0253a-kar\u0253a na \u0199awayen Amurka, da suka ha\u0257a da; Faransa, da Birtaniya, da Italiya, da Saudi Arabia, da Turkiyya, da Jordan, da kuma Ha\u0257a\u0257\u0257iyar Daular Larabawa (UAE).<\/p>\n\n\n\n<p>\u0181angarori guda uku ne ke haifar da rikicin: Yun\u0199urin ha\u0257in guiwa na fatattakar \u01b4an ta&#8217;addar da ke ikirarin kafa Daular Islama. Tashin hankali tsakanin Gwamnatin Syria da dakarun \u01b4an adawa, da kuma hare-haren soji kan \u0198urdawan Syria da dakarun Turkiyya ke yi.<\/p>\n\n\n\n<p>A shekara ta 2013 ne \u0199ungiyar IS ta fara \u0199wace iko da yankunan \u0199asar Syria. Bayan wasu hare-haren ta&#8217;addanci da \u0199ungiyar IS ta \u0257auki nauyin shiryawa a fa\u0257in nahiyar Turai a shekara ta 2015, Amurka, da Birtaniya da Faransa tare da goyon bayan Turkiyya, Saudiyya, da kuma Faransa.<\/p>\n\n\n\n<p>Sauran abokan ha\u0257in guiwa na Larabawa sun fa\u0257a\u0257a ya\u0199in da suke yi a Ira\u0199i har zuwa Syria.<\/p>\n\n\n\n<p>Tare da wa\u0257annan \u0198asashe sun kai hare-hare sama da 11,000 a kan maya\u0199an IS a Syria, yayin da \u0199awancen da Amurka ke jagoranta ke ci gaba da ba da goyon baya ga hare-haren \u0199asa da dakarun Siriyan Democratic Forces (SDF) ke yi.<\/p>\n\n\n\n<p>Tun a shekara ta 2016 ne sojojin Turkiyya suka fara kai hare-hare ta \u0199asa kan maya\u0199an IS tare da kai hare-hare kan \u0199ungiyoyin \u0198urdawa masu \u0257auke da makamai a Syria.<\/p>\n\n\n\n<p>Bisa bu\u0199atar Gwamnatin Syria a watan Satumban shekarar 2015, \u0199asar Rasha ta fara kai hare-hare ta sama kan abin da ta ce maya\u0199an IS ne, yayin da dakarun Gwamnatin Syria suka samu gagarumar nasara kan \u0199ungiyar IS, ciki har da \u0199wato birnin Palmyra.<\/p>\n\n\n\n<p>A cewar \u0199awancen da Amurka ke jagoranta na Ya\u0199i da \u0199ungiyar IS, jami&#8217;an tsaron Ira\u0199i da SDF sun \u0199wato kashi 98 cikin 100 na yankunan da \u0199ungiyar ke ri\u0199e da su a da, a Ira\u0199i da Syria ciki har da Raqqa da Deir al-Zour.<\/p>\n\n\n\n<p>Tare da goyon bayan Rasha da Iran, Gwamnatin Syria ta ci gaba da samun nasarar \u0199wace iko da yankunan daga hannun \u01b4an adawa, ciki har da tungar \u01b4an adawa a Aleppo a shekara ta 2016.<\/p>\n\n\n\n<p>An zargi Gwamnatin \u0199asar da yin amfani da makamai masu guba sau da yawa a tsawon wannan rikici, wanda ya haifar da Allah-wadai daga \u0199asashen Duniya.<\/p>\n\n\n\n<p>A 2013, 2017, da kuma 2018. Dakarun \u01b4an adawar dai na ci gaba da samun ta\u0199aitaccen iko a Idlib da ke Arewa maso Yammacin Syria da kuma kan iyakar Ira\u0199i da Syria. Sai dai kuma girgizar \u0199asar Turkiyya da Syria a shekarar 2023 ta sanya kusan ba zai yi wu a gudanar da ingantaccen mulki ba.<\/p>\n\n\n\n<p>\u0198o\u0199arin cimma matsaya ta Diflomasiyya ya ci tura. Tattaunawar zaman lafiya a Geneva kan Syria, taron da Majalisar \u018ainkin Duniya ke marawa baya na samar da sauyi a siyasance \u0199ar\u0199ashin jagorancin Manzon musamman na MDD Staffan de Mistura, bai yi nasara ba wajen cimma matsaya ta Siyasa, yayin da \u0199ungiyoyin \u01b4an adawa da jami\u2019an Gwamnatin Syria ke fafutukar samar da sharu\u0257\u0257an da za a amince da juna domin warware rikicin Syria.<\/p>\n\n\n\n<p>An fara wani sabon zagayen tattaunawar zaman lafiya a Geneva a watan Mayun 2017 tare da tawaga mai wakilai 18 daga Syria amma tun daga lokacin lamarin ya ci tura. Har ila yau, a cikin 2017, tattaunawar zaman lafiya da Rasha ta fara a birnin Astana na Kazakhstan, da Iran, Turkiyya, da mambobin Gwamnatin Syria da shugabannin \u01b4an adawa masu \u0257auke da makamai sun haifar da yarjejeniyar tsagaita wuta tare da kafa yarjejeniya.<\/p>\n\n\n\n<p>Sai dai jim ka\u0257an bayan sanar da tsagaita bu\u0257e wuta, an sake kai hare-hare daga dakarun Gwamnatin Syria kan yankunan da \u01b4an tawaye ke ri\u0199e da su a yankunan da aka wargaza.<\/p>\n\n\n\n<p>Damuwa<\/p>\n\n\n\n<p>Bisa \u0199ididdigar da \u0199ungiyar kare hakkin \u0257an&#8217;Adam ta Syria ta fitar, an kashe fiye da mutane 600,000 tun farkon ya\u0199in.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img decoding=\"async\" width=\"739\" height=\"415\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-10t1639535225114281284779303.jpg\" alt=\"\" class=\"wp-image-2728\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-10t1639535225114281284779303.jpg 739w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-10t1639535225114281284779303-300x168.jpg 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-10t1639535225114281284779303-600x337.jpg 600w\" sizes=\"(max-width: 739px) 100vw, 739px\" \/><figcaption class=\"wp-element-caption\"><em>Wasu Siriyawa a yayin da wani hari ya rutsa da su, suke neman agajin gaggawa.|Hoto: Getty Images<\/em><\/figcaption><\/figure>\n\n\n\n<p>A cikin 2023, Majalisar \u018ainkin Duniya ta ba da rahoton cewa, sama da mutane Miliyan 6.9 a lokacin suke cikin gidajensu a wuraren da abin ya shafa, in da sama da Miliyan 5.4 ke zaune a matsayin \u01b4an Gudun Hijira a \u0199asashen \u0199etare.<\/p>\n\n\n\n<p>Yawancin \u01b4an Gudun Hijirar sun yi hijira zuwa Jordan da Lebanon. sama da Siriyawa Miliyan 3.4 ne suka tsere zuwa Turkiyya, kuma da yawa sun yi yun\u0199urin neman mafaka a Turai.<\/p>\n\n\n\n<p>A \u0199ar\u0199ashin Gwamnatin Shugaba Donald J. Trump, Amurka ta fi fice daga \u0198asar Syria, in da ta bar sojojin Amurka kusan 400 a matsayin rundunonin tsaro.<\/p>\n\n\n\n<p>A ranar 16 ga watan Janairu, 2019, wani hari a Manbij wanda \u0199ungiyar mai da&#8217;awar kafa Daular Musulunci ta \u0257auki alhakin kai wa ya kashe a\u0199alla mutane 19, ciki har da Amurkawa hu\u0257u. Kafin wannan harin dai, Amurkawa biyu ne kawai aka kashe a Syria tun bayan fara ya\u0199in da Amurka ke jagoranta.<\/p>\n\n\n\n<p>Kawancen Kasa da Kasa \u0199ar\u0199ashin jagorancin Amurka na ci gaba da kai hare-haren soji kan ragowar maya\u0199an IS, da kuma wasu dakaru masu samun goyon bayan Iran.<\/p>\n\n\n\n<p>Ficewar yawancin sojojin Amurka ya \u0199ara rashin tabbas game da rawar da sauran \u0253angarorin \u0199etare ke takawa a rikicin da suka ha\u0257a da; Iran da Isra&#8217;ila da Rasha da Turkiyya da kuma makomar masu shiga tsakani. Haka nan, \u0199ara shigar da Rasha ke yi ya taimaka matu\u0199a wajen nasarar da Gwamnatin Syria ta samu na \u0199wato wasu yankuna. Yayin da Rasha ta fito fili ta bayyana cewa ta na ba da tallafin kai hari ta sama ne kawai ga Gwamnatin, ta aike da \u0199ungiyar Wagner, wata rundunar kwangilar soji mai zaman kanta, don Ya\u0199i a Siriya.<\/p>\n\n\n\n<p>Kasashen waje irin su; Iran, Isra&#8217;ila, Qatar, Rasha, Saudi Arabia, Turkiyya, da kuma \u0199awancen da Amurka ke jagoranta, su na \u0199ara gudanar da ayyukansu masu kusanci da juna, lamarin da ke dagula Ya\u0199in Basasar tare da \u0199ara nuna damuwa game da wani tashin hankali da ba a yi niyya ba. Rikicin da ke ci gaba da tashe-tashen hankula su ma sun taimaka wajen sake dawowar \u0199ungiyoyi masu tsatstsaurar ra&#8217;ayi.<\/p>\n\n\n\n<p>Ci gaba na Kwanan nan<\/p>\n\n\n\n<p>A ranar 6 ga Fabrairu, 2023, Girgizar \u0198asa mai \u0199arfin awo 7.8 da ma&#8217;aunin Girgizar \u0198asa mai \u0199arfin awo 7.5 ta afku a Kudu maso Gabashin Turkiyya da Arewa maso Yammacin Syria, wanda ke \u0257aya daga cikin bala&#8217;o&#8217;i mafi muni a wannan \u0199arni.<\/p>\n\n\n\n<p>Ya zuwa watan Mayun 2023, an \u0199iyasta adadin rayukan da aka yi asarar ya kai kusan 60,000, inda ta kashe mutane 50,700 a Turkiyya da kuma 8,400 a Syria.<\/p>\n\n\n\n<p>Rikicin Syria na shekaru 13 ya kawo cikas ga ayyukan agajin da take yi, shugaban Hukumar Samar da Abinci ta Duniya ya bayyana halin da ake ciki a matsayin wani iftila&#8217;i a kan bala\u2019i.<\/p>\n\n\n\n<p>A \u0198asar Syria ka\u0257ai, an yi \u0199iyasin Girgizar \u0198asar ta haddasa asarar Dala Biliyan 5.1.<\/p>\n\n\n\n<p>Yun\u0199urin mayar da martani ga Girgizar \u0198asa na da sar\u0199a\u0199iya saboda rarrabuwar kawuna da ya samo asali daga Ya\u0199in Basasar Syria.<\/p>\n\n\n\n<p>Yankin Arewa maso Yammacin \u0198asar Syria da Girgizar \u0198asar ta fi shafa na hannun dakarun \u01b4an tawaye a lokacin, kuma Gwamnatin Syria ta da\u0257e ta na hana shiga yankin. Don haka, dole ne Gwamnatin Turkiyya ta amince da taimakon agaji na \u0198asa da \u0198asa don wucewa ta hanyar ba da agajin jin \u0199ai \u0257aya tilo tsakanin Syria da Turkiyya, wanda aka fi sani da mashigar Bab al-Hawa.<\/p>\n\n\n\n<p>Sai dai Girgizar \u0198asar ta yi mummunar \u0253arna a hanyoyin da suka ha\u0257a Turkiyya da Syria, kuma Gwamnatin Turkiyya ta shagaltu da nata aikin agaji.<\/p>\n\n\n\n<p>A ranar Alhamis 9 ga watan Fabrairu ne ayarin Motocin Majalisar \u018ainkin Duniya na farko suka isa birnin Bab al-Hawa. A ranar Juma\u2019a 10 ga watan Fabrairu Gwamnatin Syria ta sanar da ba da izini ga \u0199ungiyoyin agaji na \u0198asa da \u0198asa don shiga yankunan da ke hannun \u01b4an tawaye a Syria, amma ba su bayar da lokacin yin hakan ba.<\/p>\n\n\n\n<p>A watan Mayun 2023, marigayi shugaban Iran Ibrahim Raisi ya gana da Shugaba Bashar al-Assad a Damascus don \u0199arfafa ha\u0257in guiwar Tattalin Arziki, wanda ke zama ziyarar farko da shugaban Iran ya kai Syria tun fara ya\u0199in.<\/p>\n\n\n\n<p>A cikin wannan watan mayun ne \u0199ungiyar \u0199asashen Larabawa ta amince da sake shigar da \u0198asar Syria bayan dakatarwar da ta yi na tsawon shekaru 12, duk kuwa da ci gaba da \u0199a\u0199aba wa Gwamnatin Shugaba Assad Takunkumi da ka iya hana \u0199asashen Larabawa masu arzikin Man Fetur zuba jari a \u0199asar ta Syria.<\/p>\n\n\n\n<p>A watan Yulin 2023, Firayim Ministan Ira\u0199i Mohammed Shi&#8217;a al-Sudan, ya tattauna batun fataucin miyagun \u0198wayoyi, dawo da \u01b4an gudun hijirar Syria, da kuma cire takunkumin da \u0198asashen Yamma suka \u0199a\u0199abawa Shugaba Assad a Damascus.<\/p>\n\n\n\n<p>Wa ke Ri\u0199e da Iko a Syria Kafin Yanzu?<\/p>\n\n\n\n<p>An shafe shekaru ana sa ran cewa ya\u0199in Syria ya zo \u0199arshe bayan gwamnatin Assad ta kar\u0253i iko a mafi yawan biranen Syria, kuma ta samu nasarar yin haka ne da taimakon Rasha da Iran da kuma \u0199ungiyoyin tawaye da Iran ke marawa baya.<\/p>\n\n\n\n<p>Gwamnatin ta yi nasarar ri\u0199e manyan wuraren da aka yi rikicin, amma mafi yawan sassan \u0199asar ba su a hannun Gwamnati.<\/p>\n\n\n\n<p>Daga cikin su akwai Arewaci da Gabashin \u0199asar da ke hannun maya\u0199an \u0199urdawa masu samun goyon bayan Amurka, da ake kira Syrian Democratic Forces (SDF).<\/p>\n\n\n\n<p>Yankunan da \u01b4an tawayen suka mamaye na \u0199arshe kafin yanzu su ne Aleppo da kuma Idlib da ke kusa da Turkiyya kuma mutane a\u0199alla miliyan hu\u0257u ke rayuwa, sai dai mafi yawan su su na zaman gudun hijira ne.<\/p>\n\n\n\n<p>Maya\u0199an HTS ne suka mamaye yankunan, amma su na ha\u0257aka da wasu \u0199ungiyoyi masu i\u0199irarin jihadi da suke zaune a yankunan.<\/p>\n\n\n\n<p>Akwai kuma wata \u0199ungiyar \u01b4an tawayen da Turkiyya ke goyon baya mai suna Syrian National Army (SNA) wadda itama ta ke ri\u0199e da wasu sassa.<\/p>\n\n\n\n<p>Su Waye \u01b3an \u0198ungiyar Hayat Tahrir al-Sham?<\/p>\n\n\n\n<p>An kafa \u0199ungiyar mai i\u0199irarin jihadi ne a 2012, inda aka ba ta suna al-Nusra, kuma bayan shekara \u0257aya kacal ta sanar da biyayyar ta ga al-Qaeda.<\/p>\n\n\n\n<p>Ana kallon Al-Nusra a matsayin \u0199ungiya mafi hatsari da ta ta\u0253a yin fito na fito da shugaba Assad. Sai dai ana ganin ta yi \u0199arfi ne saboda manufofin ta na i\u0199irarin jihadi ba saboda rajin kawo sauyi ba. Kuma a lokacin ana ganin tana da banbancin manufofi da babbar gamayyar \u01b4an tawaye ta Free Syrian Army.<\/p>\n\n\n\n<p>A 2016, Al-Nusra ta \u0253alle daga al-Qaeda kuma ta canza suna zuwa Hayat Tahrir al-Sham lokacin da ta ha\u0257e da wasu \u0199ungiyoyin tawaye.<\/p>\n\n\n\n<p>Sai dai Majalisar Dinkin Duniya da Amurka da kuma Birtaniya sun ci gaba da kallon HTS a matsayin \u0199ungiya mai biyayya ga al-Qaeda, kuma suna kiran ta da suna al-Nusra Front. Amurka ta ayyana neman shugaban \u0199ungiyar, Abu Mohammed al-Jawlani, ruwa a jallo, har ma ta sanya ladar $10m ga duk wanda ya taimaka domin kama shi bayan ta sanya shi a jerin \u01b4an ta&#8217;adda da take nema.<\/p>\n\n\n\n<p>HTS ta ci gaba da mamaye harkokin iko da birnin Idlib da kuma Aleppo, bayan ta mur\u0199ushe abokan hamayyar ta na al-Qaeda da IS. Ta kafa abin da ta kira gwamnatin \u0199wato \u01b4ancin Syria wadda kemulki da tanadin shari&#8217;ar musulumci.<\/p>\n\n\n\n<p>A wata hira da CNN, Jawlani ya ce &#8220;Manufar boren nasu ita ce kifar da gwamnatin Assad&#8221; kuma ya ce a shirye yake ya kafa gwamnatin da za ta yi mulki bisa tanadin Kundin Mulkin \u0198asa.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img decoding=\"async\" width=\"300\" height=\"169\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/da5dc690-b155-11ef-b8b4-6d288d209bd95421318598931966363-300x169.jpeg\" alt=\"\" class=\"wp-image-2725\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/da5dc690-b155-11ef-b8b4-6d288d209bd95421318598931966363-300x169.jpeg 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/da5dc690-b155-11ef-b8b4-6d288d209bd95421318598931966363-768x432.jpeg 768w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/da5dc690-b155-11ef-b8b4-6d288d209bd95421318598931966363-600x338.jpeg 600w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/da5dc690-b155-11ef-b8b4-6d288d209bd95421318598931966363.jpeg 800w\" sizes=\"(max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><figcaption class=\"wp-element-caption\"><em>HTS da \u0199awayenta sun ce sun \u0199addamar da hare-haren ne domin da\u0199ile yun\u0199urin gwamnati na kai masu samame.|Hoto: Reuters <\/em><\/figcaption><\/figure>\n\n\n\n<p><strong>Me ya sa \u01b3an Tawayen Suka \u0198addamar da Hare-Hare?<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>An shafe shekaru ana gwabza ya\u0199i a Idlib, inda dakarun gwamnatin Syria ke \u0199o\u0199arin \u0199wace iko.<\/p>\n\n\n\n<p>Amma a 2020, Turkiyya da Rasha sun ja ragamar tsagaita wuta da ta kawo \u0199arshen yun\u0199urin gwamnatin na \u0199wace birnin Idlib. Tsagaita wutar ta yi nasara duk da cewa ana samun rikicin da ke tashi a wasu wurare.<\/p>\n\n\n\n<p>A ranar 27 ga watan Nuwamba, HTS da \u0199awayen ta suka ce sun \u0199addamar da ya\u0199i domin hana a mamaye su, inda suka zargi gwamnati da \u0199ungiyoyin da Iran ke gyon baya, da kai hare-hare kan fararen hula a Arewa maso Yamma.<\/p>\n\n\n\n<p>Kuma wannan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnati ta yi fama da tsawon shekaru ana gwabza ya\u0199i, da yawan takunkumi da aka \u0199a\u0199aba mata da kuma ya\u0257uwar rashawa. Ga kuma hankalin \u0199awayenta na waje suna fama da nasu rikicin.<\/p>\n\n\n\n<p>\u0198ungiyar Hezbollah ta Lebanon da Iran ke goyon baya, ta taimaka sosai a shekarun baya, lokacin da Syria ta yi nasarar fatattakar \u01b4an tawaye, amma hare-haren Isra&#8217;ila sun hana samun irin wannan taimako a yanzu.<\/p>\n\n\n\n<p>Hare-haren Isra&#8217;ilan sun kuma kashe kwamandan sojin Iran a Syria, da kuma da\u0199ile hanyoyin da maya\u0199a masu goyon bayan gwamnati.<\/p>\n\n\n\n<p>Rasha kuma ta karkata ga ya\u0199in da take da Ukraine.<\/p>\n\n\n\n<p>Wannan gi\u0253i da aka samu ya fito da na\u0199asun dakarun Assad \u0199arara.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Yadda Aka Kawar da Gwamnatin Bashar al-Assad<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Zuri&#8217;ar Assad ta yi mulki na tsawon shekaru 53 a Siriya kafin Mulkin ya zo \u0199arshe. Shugaba Bashar al-Assad ya \u0199ar\u0253i ragamar mulki ne a 2000, bayan mahaifinsa ya yi mulkin a\u0199alla shekaru 30.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"222\" height=\"300\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/bashar_al-assad_in_may_20241312809805110513631-222x300.png\" alt=\"\" class=\"wp-image-2730\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/bashar_al-assad_in_may_20241312809805110513631-222x300.png 222w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/bashar_al-assad_in_may_20241312809805110513631.png 481w\" sizes=\"(max-width: 222px) 100vw, 222px\" \/><figcaption class=\"wp-element-caption\"><em>Ham\u0253ararren shugaban \u0198asar Syria, Bashar al-Assad.<\/em>|Hoto: Wikipedia<\/figcaption><\/figure>\n\n\n\n<p>A watan Disamba 2024 wata \u0199ungiya mai rajin Addinin Islama, Hayat Tahrir al-Sham (HTS), ta yi nasarar \u0199addamar da hari mai muni a Arewa maso Yammacin \u0199asar, bayan ta yi ha\u0257in guiwa da wasu \u0199ungiyoyin tawaye. \u01b3an tawayen sun \u0199wace birni na biyu mafi girma a Syria, Aleppo, sannan suka danna Kudanci zuwa babban birnin \u0199asar Damascus, suka kuma fi \u0199arfin dakarun Syria.<\/p>\n\n\n\n<p>\u0198ungiyar ta ci gaba da mamaya cikin sauri tamkar wutar daji, inda ta kar\u0253e iko da birnin Hama da ma wasu da dama, yayin da yankin Kudancin \u0199asar ya ku\u0253uce daga ikon Gwamnati.<\/p>\n\n\n\n<p>Assad, ya shiga cikin mummunan yanayi yayin da manyan \u0199awayensa irin su Iraq da Rasha suka gaza kai \u0257auki.<\/p>\n\n\n\n<p>A ranar lahadi 8 ga watan Disamba kwatsam! Sai aka sami labarin \u01b4an tawaye sun \u0199wace Birnin Damascus na \u0199asar, a inda Assad da iyalinsa suka gudu \u0199asar Rasha don neman mafaka.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"300\" height=\"169\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/bb0f33f0-b533-11ef-99b7-2dce9d198bc06066317982128864156-300x169.jpeg\" alt=\"\" class=\"wp-image-2724\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/bb0f33f0-b533-11ef-99b7-2dce9d198bc06066317982128864156-300x169.jpeg 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/bb0f33f0-b533-11ef-99b7-2dce9d198bc06066317982128864156-768x432.jpeg 768w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/bb0f33f0-b533-11ef-99b7-2dce9d198bc06066317982128864156-600x338.jpeg 600w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/bb0f33f0-b533-11ef-99b7-2dce9d198bc06066317982128864156.jpeg 800w\" sizes=\"(max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><figcaption class=\"wp-element-caption\"><em>\u01b3an tawayen Syria da magoya bayansu su na murnar shiga birnin Damascus ba tare da wata tirjiya ba.|Hoto: AFB<\/em><\/figcaption><\/figure>\n\n\n\n<p>Me \u0199asashen Duniya ke cewa?<\/p>\n\n\n\n<p>Fadar White House ta ce shugaban Amurka, Joe Biden da jami&#8217;ansa na bibiyar abubuwan da ke faruwa a Syria kuma tana tuntu\u0253ar masu ruwa da tsaki a \u0199asar.<\/p>\n\n\n\n<p>Siriya a Yanzu<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"300\" height=\"200\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-10t1640288493847745337922224-300x200.jpg\" alt=\"\" class=\"wp-image-2726\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-10t1640288493847745337922224-300x200.jpg 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-10t1640288493847745337922224-600x400.jpg 600w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-10t1640288493847745337922224.jpg 678w\" sizes=\"(max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><figcaption class=\"wp-element-caption\">A yayin da al&#8217;ummar Syria ke murnar kifar da gwamnatin Assad, da fatan samun kyakkyawar makoma. <\/figcaption><\/figure>\n\n\n\n<p>A yanzu haka harkokin rayuwa sun fara farfa\u0257owa bayan \u01b4an tawayen da suka mamaye Siriya sun fara tattauna kafa Gwamnatin wucin-gadi, inda Firaminista ya ci gaba da ri\u0199e madafun iko.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Ya\u0199in Basasar Syria (Sham) dai wani Ya\u0199in Basasa ne mai \u0253angarori da dama a \u0198asar Syria da ake gwabzawa tsakanin Jamhuriyar Larabawa ta Syria \u0199ar\u0199ashin jagorancin tsohon Shugaban \u0198asar Syria Bashar al-Assad da wasu dakaru na cikin gida da na waje da ke adawa da Gwamnatin Syria da kuma juna, ta fuskoki daban-daban. Fiye da [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":2727,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"inline_featured_image":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[88],"tags":[],"class_list":["post-2722","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-tarihi"],"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v27.0 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Tarihin Ya\u0199in Basasar Syria<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"noindex, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_US\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Tarihin Ya\u0199in Basasar Syria\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"Ya\u0199in Basasar Syria (Sham) dai wani Ya\u0199in Basasa ne mai \u0253angarori da dama a \u0198asar Syria da ake gwabzawa tsakanin Jamhuriyar Larabawa ta Syria \u0199ar\u0199ashin jagorancin tsohon Shugaban \u0198asar Syria Bashar al-Assad da wasu dakaru na cikin gida da na waje da ke adawa da Gwamnatin Syria da kuma juna, ta fuskoki daban-daban. Fiye da [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2722\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"Taskar Nasaba\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2024-12-10T15:52:37+00:00\" \/>\n<meta property=\"article:modified_time\" content=\"2024-12-10T16:48:40+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-10T164150.835.jpeg\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"700\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"394\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/jpeg\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Salahuddeen Muhammad\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"Salahuddeen Muhammad\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Est. reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"13 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\/\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2722#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2722\"},\"author\":{\"name\":\"Salahuddeen Muhammad\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753\"},\"headline\":\"Tarihin Ya\u0199in Basasar Syria\",\"datePublished\":\"2024-12-10T15:52:37+00:00\",\"dateModified\":\"2024-12-10T16:48:40+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2722\"},\"wordCount\":2621,\"commentCount\":0,\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2722#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-10T164150.835.jpeg\",\"articleSection\":[\"Tarihi\"],\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2722#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2722\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2722\",\"name\":\"Tarihin Ya\u0199in Basasar Syria\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2722#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2722#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-10T164150.835.jpeg\",\"datePublished\":\"2024-12-10T15:52:37+00:00\",\"dateModified\":\"2024-12-10T16:48:40+00:00\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2722#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2722\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2722#primaryimage\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-10T164150.835.jpeg\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-10T164150.835.jpeg\",\"width\":700,\"height\":394},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2722#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Tarihin Ya\u0199in Basasar Syria\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"description\":\"\",\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\"},\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-US\"},{\"@type\":\"Organization\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\",\"logo\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png\",\"width\":343,\"height\":345,\"caption\":\"Taskar Nasaba\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/\"}},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753\",\"name\":\"Salahuddeen Muhammad\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg\",\"caption\":\"Salahuddeen Muhammad\"},\"description\":\"\u018aanjarida, marubuci, mai manufar bun\u0199asa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.\",\"sameAs\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\"],\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?author=1\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Tarihin Ya\u0199in Basasar Syria","robots":{"index":"noindex","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"og_locale":"en_US","og_type":"article","og_title":"Tarihin Ya\u0199in Basasar Syria","og_description":"Ya\u0199in Basasar Syria (Sham) dai wani Ya\u0199in Basasa ne mai \u0253angarori da dama a \u0198asar Syria da ake gwabzawa tsakanin Jamhuriyar Larabawa ta Syria \u0199ar\u0199ashin jagorancin tsohon Shugaban \u0198asar Syria Bashar al-Assad da wasu dakaru na cikin gida da na waje da ke adawa da Gwamnatin Syria da kuma juna, ta fuskoki daban-daban. Fiye da [&hellip;]","og_url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2722","og_site_name":"Taskar Nasaba","article_published_time":"2024-12-10T15:52:37+00:00","article_modified_time":"2024-12-10T16:48:40+00:00","og_image":[{"width":700,"height":394,"url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-10T164150.835.jpeg","type":"image\/jpeg"}],"author":"Salahuddeen Muhammad","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"Salahuddeen Muhammad","Est. reading time":"13 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2722#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2722"},"author":{"name":"Salahuddeen Muhammad","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753"},"headline":"Tarihin Ya\u0199in Basasar Syria","datePublished":"2024-12-10T15:52:37+00:00","dateModified":"2024-12-10T16:48:40+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2722"},"wordCount":2621,"commentCount":0,"publisher":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2722#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-10T164150.835.jpeg","articleSection":["Tarihi"],"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2722#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2722","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2722","name":"Tarihin Ya\u0199in Basasar Syria","isPartOf":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2722#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2722#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-10T164150.835.jpeg","datePublished":"2024-12-10T15:52:37+00:00","dateModified":"2024-12-10T16:48:40+00:00","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2722#breadcrumb"},"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2722"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2722#primaryimage","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-10T164150.835.jpeg","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-10T164150.835.jpeg","width":700,"height":394},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2722#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/taskarnasaba.com\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Tarihin Ya\u0199in Basasar Syria"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/","name":"Taskar Nasaba","description":"","publisher":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization"},"potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-US"},{"@type":"Organization","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization","name":"Taskar Nasaba","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/","logo":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png","width":343,"height":345,"caption":"Taskar Nasaba"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/"}},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753","name":"Salahuddeen Muhammad","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/image\/","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg","caption":"Salahuddeen Muhammad"},"description":"\u018aanjarida, marubuci, mai manufar bun\u0199asa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.","sameAs":["https:\/\/taskarnasaba.com"],"url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?author=1"}]}},"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-10T164150.835.jpeg","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2722","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=2722"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2722\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2731,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2722\/revisions\/2731"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/2727"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=2722"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=2722"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=2722"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}