{"id":2744,"date":"2024-12-10T16:42:26","date_gmt":"2024-12-10T16:42:26","guid":{"rendered":"https:\/\/taskarnasaba.com.ng\/?p=2744"},"modified":"2024-12-10T16:42:57","modified_gmt":"2024-12-10T16:42:57","slug":"tarihin-rikicin-%c6%99abilar-tutsi-da-hutu-a-rwanda","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2744","title":{"rendered":"Tarihin Rikicin \u0198abilar Tutsi da Hutu a Rwanda"},"content":{"rendered":"\n<p><strong>An fara kisan kiyashi a Rwanda lokacin da aka harbo Jirgin Saman da ke \u0257auke da Shugaban Rwanda Juv\u00e9nal Habyarimana da shugaban Burundi Cyprien Ntaryamira.<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Daga: <strong>Muhammad Cisse <\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>A shekarar 1994 a cikin kwanaki 100 kacal, kisan kiyashin da aka yi a \u0198asar Ruwanda ya zama daya daga cikin manyan laifukan Ya\u0199i a Tarihin wannan zamanin.<\/p>\n\n\n\n<p>A cikin wannan kwanaki 100 tsakanin Afrilu zuwa Yuli 1994, an kashe kusan \u0198abilar Tutsi da Hutu masu matsakaicin ra&#8217;ayi kusan Miliyan \u0257aya.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img fetchpriority=\"high\" decoding=\"async\" width=\"300\" height=\"200\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-10t1732435226777308279133832-300x200.jpg\" alt=\"\" class=\"wp-image-2742\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-10t1732435226777308279133832-300x200.jpg 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-10t1732435226777308279133832-600x400.jpg 600w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-10t1732435226777308279133832.jpg 678w\" sizes=\"(max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><figcaption class=\"wp-element-caption\"><em>\u0198warangwal \u0257in Kawunan al&#8217;ummar Tutsi da Hutu wa\u0257anda suka rasa rayuwarsu a Cibiyar Tunawa da kisan kiyashin Nyamata. |Hoto: e-International Relation<\/em>s<\/figcaption><\/figure>\n\n\n\n<p>Washegari ne aka fara kisan \u0199are dangi. Sojoji, \u01b4an sanda, da \u01b4an bindiga sun kashe manyan \u01b4an Tutsi da \u01b4an Hutu masu sassaucin ra&#8217;ayi na Soja da \u01b4an Siyasa.<\/p>\n\n\n\n<p>An kafa shingayen binciken ababen hawa domin tantance duk masu ri\u0199e da katin shaidar zama \u0257ankasa ta Rwanda, wanda ke \u0257auke da shaidar nuna \u0199abilar da mutun ya fito. Hakan ya bai wa dakarun Gwamnati damar ganowa da kuma kaashe Tutsi masu tarin yawa.<\/p>\n\n\n\n<p>A Yammacin ranar 6 ga watan Afrilun shekarar 1994, aka harbo jirgin saman da ke \u0257auke da Shugaban \u0198asar Rwanda Juv\u00e9nal Habyarimana, da Shugaban \u0198asar Burundi Cyprien Ntaryamira, dukkansu \u01b4an \u0199abilar Hutu, da makami mai linzami a lokacin da yake shirin sauka a Birnin Kigali na \u0199asar Rwanda.<\/p>\n\n\n\n<p>An kashe dukkan mutane 12 da ke cikin jirgin. Kisan da aka yi ya haifar da yun\u0199urin kawar da shugabanni masu sassaucin ra&#8217;ayi na Ruwanda tare da haifar da kisan kiyashin Rwanda, daya daga cikin abubuwan da suka fi zubar da jini a \u0199arshen \u0199arni na 20.<\/p>\n\n\n\n<p>Ana ta ce-ce-ku-ce wa ke da alhakin kai harin, inda akasari aka yi zargin ko dai \u01b4an tawayen Tutsi na Rwandan Patriotic Front (RPF) a yun\u0199urinsu na kifar da Gwamnatin Habyarimana, ko kuma Hutu Power, da ke da ala\u0199a da Gwamnati, wa\u0257anda suka fuskanci rashin yiwuwar raba madafun iko da su.<\/p>\n\n\n\n<p>A shekara ta 2006, wani bincike na tsawon shekaru takwas da Al\u0199alin Faransa Jean-Louis Brugui\u00e8re ya yi, ya kammala da cewa, shugaban kasar na yanzu Paul Kagame (a wancan lokacin Kwamandan RPF) ya ba da umarnin kisan.<\/p>\n\n\n\n<p>A watan Nuwambar 2014, Emmanuel Mughisa (wanda aka fi sani da Emile Gafarita), tsohon Sojan Rwanda wanda ya ce, ya na da shaidar cewa Kagame ne ya bayar da umarnin harbo jirgin Habyarimana a Nairobi, lokacin da aka san cewa an kira shi ya ba da shaida a gaban Kwamitin binciken na Faransa.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Rikicin \u0198abilanci na Ruwanda<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>A farkon shekarun 1990, Ruwanda, wadda \u0199aramar \u0198asa ce mai \u0199arfin tattalin arzikin Noma, ta na \u0257aya daga cikin mafi yawan al&#8217;umma a Afirka. Kusan kashi 85% na al&#8217;ummarta \u01b4an Hutu ne; Sauran Tutsi ne, tare da \u01b4an tsirarun Kabilar Twa, da \u0199abilar Pygmy wa\u0257anda su ne ainihin mazauna \u0198asar Ruwanda.<\/p>\n\n\n\n<p>A Wani \u0253angare na Jamus ta Gabashin Afirka daga 1897 zuwa 1918, Ruwanda ta zama amintacciyar \u0198asar Belgium a \u0199ar\u0199ashin \u0199ungiyar (League of Nations) a bayan Ya\u0199in Duniya na \u0257aya, tare da ma\u0199wabciyarta Burundi.<\/p>\n\n\n\n<p>Zamanin Turawan Mulkin mallaka na Belgium a Ruwanda sun fifita \u01b4an \u0199abilar Tutsi tsiraru a kan \u01b4an Hutu, (don haka \u01b4an Tutsi su ne suka kasance masu Ilmin Boko tare da dafe manyan Madafun Iko), lamarin da ya \u0199ara ta\u2019azzara \u0257abi\u2019ar \u01b4an tsiraru na zaluntar mutane da dama, lamarin da ya haifar da tashin hankali da ya \u0253arke tun kafin Rwanda ta samu \u01b4ancin kai.<\/p>\n\n\n\n<p>Juyin-juya Halin Hutu a 1959 ya tilastawa Tutsi da yawansu ya kai 330,000 tserewa daga \u0198asar, abin da ya sa suka zama \u01b4an tsiraru.<\/p>\n\n\n\n<p>A farkon shekara ta 1961, Hutu masu rinjaye sun tilasta wa Sarkin Tutsi na Ruwanda Gudun Hijira tare da ayyana \u0198asar a matsayin Jamhuriya. Bayan Za\u0253en Raba Gardama na Majalisar \u018ainkin Duniya a wannan shekarar, Belgium ta ba da \u01b3ancin Kai ga Ruwanda a watan Yulin 1962.<\/p>\n\n\n\n<p>Rikicin \u0199abilanci ya ci gaba a cikin shekaru bayan samun \u01b3ancin Kai. A shekarar 1973, wata \u0199ungiyar Soji ta \u0257ora Manjo Janar Juvenal Habyarimana, \u0257an \u0199abilar Hutu masu matsakaicin ra&#8217;ayi, a kan mulki.<\/p>\n\n\n\n<p>Shi ka\u0257ai ne ya shugabanci Gwamnatin Rwanda har tsawon shekaru 20, Habyarimana ya kafa sabuwar jam&#8217;iyyar Siyasa, &#8216;National Revolutionary Movement for Development&#8217; (NRMD).<\/p>\n\n\n\n<p>An za\u0253e shi a matsayin Shugaban \u0198asa \u0199ar\u0199ashin sabon Kundin Tsarin Mulki da aka amince da shi a shekarar 1978 kuma aka sake za\u0253e a 1983 da 1988, lokacin da shi ka\u0257ai ne \u0257antakara.<\/p>\n\n\n\n<p>A shekara ta 1990, Sojojin Rwandan Patriotic Front (RPF), da suka \u0199unshi galibin \u01b4an Gudun Hijirar Tutsi, sun mamaye Rwanda daga Uganda (in da suka yi sansani), Habyarimana ya zargi \u01b4an \u0199abilar Tutsi Mazauna Rwanda (Wa\u0257anda ba su yi Gudun Hijra ba) da kasancewa \u01b4an ta&#8217;addar RPF tare da kama \u0257aruruwansu.<\/p>\n\n\n\n<p>Tsakanin 1990 zuwa 1993, Jami&#8217;an Gwamnati sun jagoranci kisan kiyashi kan \u01b4an \u0199abilar Tutsi, tare da kashe \u0257aruruwan mutane. Tsagaita wuta a cikin wa\u0257annan tashin hankalin ya haifar da tattaunawa tsakanin Gwamnati da RPF a 1992.<\/p>\n\n\n\n<p>A watan Agustan 1993, Habyarimana ya rattaba hannu kan wata yarjejeniya a Arusha, Tanzaniya, inda ya yi kira da a kafa Gwamnatin ri\u0199on \u0199warya wadda za ta ha\u0257a da RPF.<\/p>\n\n\n\n<p>Wannan yarjejeniyar raba Madafun Iko ta harzu\u0199a \u01b4an Hutu masu tsattsauran ra\u2019ayi, in da nan take ba tare da jimawa ba za su \u0257auki wani mummunan mataki na hana ta.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>An Fara Kisan Kiyashi a Ruwanda<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>A ranar 6 ga Afrilu, 1994, an harbo wani jirgin sama \u0257auke da Habyarimana da Shugaban \u0198asar Burundi Cyprien Ntaryamira a babban birnin Kigali, kuma duk sun mutu babu wanda ya tsira (Ba a gama tantance ko su wane ne masu laifin ba. Wasu na zargin \u01b4an Hutu masu tsattsauran ra&#8217;ayi, yayin da wasu ke zargin shugabannin RPF.)<\/p>\n\n\n\n<p>A cikin sa&#8217;a guda da ha\u0257arin jirgin, Sojojin Shugaban \u0198asa, tare da Mambobin Sojojin Rwandan (FAR) da kuma \u0199ungiyoyin \u01b4an tawayen Huti da aka sani da Interhamwe (Wa\u0257anda suka kai hari) da Impuzamugambi (Wa\u0257anda ke da Buri guda), sun kafa shingaye da wuraren binkice kuma suka fara kashe \u01b4an Tutsi da Hutu masu matsakaicin ra\u2019ayi ba tare da wani hukunci ba.<\/p>\n\n\n\n<p>Daga cikin wa\u0257anda kisan kiyashin na farko ya rutsa da su sun ha\u0257a da Firaminista Agathe Uwilingiyimana na Hutu mai sassaucin ra&#8217;ayi da dakarun wanzar da zaman lafiya na Belgium su 10, da aka kashe a ranar 7 ga Afrilu.<\/p>\n\n\n\n<p>Wannan tashin hankalin ya haifar da gi\u0253in siyasa, inda gwamnatin ri\u0199on \u0199warya ta shugabannin Hutu masu tsattsauran ra&#8217;ayi daga Babban Kwamandan Sojoji suka shiga cikin aikata kisa a 9 ga watan Afrilu.<\/p>\n\n\n\n<p>Kisan dakarun wanzar da zaman lafiya na Belgium, ya janyo janyewar sojojin Belgium. Kuma Majalisar \u018ainkin Duniya ta ba da umarnin cewa, dakarun wanzar da zaman lafiya su kare kansu ne kawai daga baya.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Kisan ya Ya\u0257u a Fa\u0257in \u0198asar Rwanda<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Kashe-kashen jama&#8217;a a Kigali cikin sauri ya bazu daga wannan birni zuwa sauran Ruwanda. A cikin makonni biyu na farko, masu gudanar da Mulki a Tsakiya da Kudancin Ruwanda, inda akasarin \u0199abilar Tutsi ke zaune, sun yi tir da kisan kare dangi.<\/p>\n\n\n\n<p>Bayan 18 ga Afrilu, jami&#8217;an \u0198asar sun kama da dama na masu adawa da su tare da kashe da dama daga cikinsu. Sauran abokan adawar sai suka yi shiru ko kuma suka jagoranci kisan.<\/p>\n\n\n\n<p>Jami&#8217;ai su na ba wa masu kisan gilla kyautar Abinci, abin sha, \u0199wayoyi da Ku\u0257i. Kafofin ya\u0257a labarai da Gwamnati ke \u0257aukar nauyinsu sun fara kira ga talakawan Rwanda da su kashe ma\u0199wabtansu. A cikin watanni uku, an kashe mutane 800,000.<\/p>\n\n\n\n<p>\u01b3an tawayen RPF sun sake fafatawa, kuma Ya\u0199in Basasa ya \u0253arke tare da kisan kiyashi. Ya zuwa farkon watan Yuli, dakarun RPF sun sami iko a yawancin \u0199asar, ciki har da Kigali.<\/p>\n\n\n\n<p>Dangane da hakan, fiye da mutane Miliyan 2, kusan dukkansu \u01b4an \u0199abilar Hutu ne, suka tsere daga Rwanda, su ka cunkushe a sansanonin \u01b4an gudun hijira a Kongo (wanda ake kira Zaire a lokacin) da sauran \u0199asashe ma\u0199wabta.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img decoding=\"async\" width=\"300\" height=\"196\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-10t1727445376422450921624199-300x196.jpg\" alt=\"\" class=\"wp-image-2743\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-10t1727445376422450921624199-300x196.jpg 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-10t1727445376422450921624199-600x392.jpg 600w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-10t1727445376422450921624199.jpg 685w\" sizes=\"(max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><figcaption class=\"wp-element-caption\"><em>Miliyoyin al&#8217;umma a yayin da suke gudun hijira. |Hoto: Goodreads<\/em><\/figcaption><\/figure>\n\n\n\n<p>Bayan nasarar da ta samu, jam&#8217;iyyar RPF ta kafa Gwamnatin ha\u0257in guiwa irin wadda aka amince da ita a Arusha, inda Pasteur Bizimungu \u0257an \u0199abilar Hutu ya zama Shugaban \u0198asa da Paul Kagame \u0257an Tutsi a matsayin mataimakin Shugaban \u0198asa da kuma Ministan Tsaro.<\/p>\n\n\n\n<p>An haramta jam\u2019iyyar NRMD ta Habyarimana wadda ta taka muhimmiyar rawa wajen shirya kisan kiyashi, kuma wani sabon Kundin Tsarin Mulki da aka yi a shekarar 2003 ya kawar da batun \u0199abilanci.<\/p>\n\n\n\n<p>Sabon Kundin Tsarin Mulkin ya biyo bayan za\u0253en Paul Kagame na tsawon shekaru 10 a matsayin shugaban \u0199asar Rwanda da kuma za\u0253en \u01b4an majalisar dokokin Kasar karo na farko.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Martanin Duniya<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Kamar dai yadda aka yi ta&#8217;asar da aka yi a tsohuwar Yugoslavia a lokaci guda, \u0199asashen Duniya sun kasance a gefe \u0257aya a lokacin kisan \u0199are dangi na Ruwanda. (ma&#8217;ana sun kasa kata\u0253us).<\/p>\n\n\n\n<p>\u0198uri&#8217;ar da Kwamitin Sulhu na Majalisar \u018ainkin ya yi a watan Afrilun 1994 ya kai ga janye yawancin aikin wanzar da zaman lafiya na Majalisar \u018ainkin Duniya (UNAMIR), wanda ya haifar da fa\u0257uwar da taimakawa tare da mi\u0199a mulki ga Gwamnati \u0199ar\u0199ashin yarjejeniyar Arusha.<\/p>\n\n\n\n<p>Yayin da rahotannin kisan kiyashi ke ya\u0257uwa, Kwamitin Sulhu ya ka\u0257a \u0198uri&#8217;a a tsakiyar watan Mayu don samar da \u0199arin dakaru masu \u0199arfi da suka ha\u0257a da Sojoji fiye da 5,000. A lokacin da rundunar ta isa \u0198asar amma duk da haka, an shafe watanni ana yin kisan \u0199are dangi.<\/p>\n\n\n\n<p>A wani tsoma bakin Faransa na daban da Majalisar \u018ainkin Duniya ta amince, sojojin Faransa sun shiga Rwanda daga Zaire a \u0199arshen watan Yuni. Dangane da ci gaban da RPF ke samu cikin sauri, sun ta\u0199aita tsoma bakinsu ne a kan \u201cAyyukan jin \u0199ai\u201d da aka kafa a Kudu maso Yammacin \u0198asar Ruwanda, inda suka ceci dubun-dubatan \u01b4an \u0198abilar Tutsi amma kuma sun taimaka wa wasu masu shirya kisan \u0199are dangi.<\/p>\n\n\n\n<p>Bayan kisan kiyashin da aka yi a \u0199asar Ruwanda, da dama daga cikin manyan mutane a \u0198asashen duniya sun koka da yadda \u0198asashen waje suka jahilci lamarin da kuma kasa \u0257aukar mataki domin hana aukuwar wannan ta&#8217;asa.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Shari&#8217;ar Kisan \u0198are Dangi na Rwanda<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>A cikin Oktoba 1994, Kotun \u0198asa da \u0198asa ta Ruwanda (ICTR), wacce ke Tanzaniya, an kafa ta a matsayin tsawaita Kotun Hukunta Laifukan \u0198asa da \u0198asa na tsohuwar Yugoslavia (ICTY) a Hague, kotun Kasa da Kasa ta farko tun bayan shari&#8217;ar Nuremburg na 1945-46, kuma ta farko tare da umarnin gurfanar da Masu laifin kisan \u0199are dangi.<\/p>\n\n\n\n<p>A cikin 1995, ICTR ta fara tuhuma tare da gwada wasu manyan mutane kan rawar da suka taka a kisan kiyashin Rwanda; Tsarin ya \u0199ara yin wahala saboda ba a san wa\u0257anda ake zargin da yawa ba.<\/p>\n\n\n\n<p>An ci gaba da shari&#8217;ar a cikin shekaru 10 da rabi da suka biyo baya ciki har da hukuncin 2008 da aka yanke wa wasu tsoffin manyan Jami&#8217;an Tsaro da Sojoji uku na Rwanda bisa laifin shirya kisan kiyashi.<\/p>\n\n\n\n<p>Madogarar Wannan Rubutu<\/p>\n\n\n\n<p>History Channel on YouTube<br \/>United Nations Organization<br \/>The Guardian News UK<br \/>World Vision<br \/>University Of Minnesota USA<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>An fara kisan kiyashi a Rwanda lokacin da aka harbo Jirgin Saman da ke \u0257auke da Shugaban Rwanda Juv\u00e9nal Habyarimana da shugaban Burundi Cyprien Ntaryamira. Daga: Muhammad Cisse A shekarar 1994 a cikin kwanaki 100 kacal, kisan kiyashin da aka yi a \u0198asar Ruwanda ya zama daya daga cikin manyan laifukan Ya\u0199i a Tarihin wannan [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":2741,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"inline_featured_image":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[88],"tags":[],"class_list":["post-2744","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-tarihi"],"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v27.0 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Tarihin Rikicin \u0198abilar Tutsi da Hutu a Rwanda<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"noindex, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_US\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Tarihin Rikicin \u0198abilar Tutsi da Hutu a Rwanda\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"An fara kisan kiyashi a Rwanda lokacin da aka harbo Jirgin Saman da ke \u0257auke da Shugaban Rwanda Juv\u00e9nal Habyarimana da shugaban Burundi Cyprien Ntaryamira. Daga: Muhammad Cisse A shekarar 1994 a cikin kwanaki 100 kacal, kisan kiyashin da aka yi a \u0198asar Ruwanda ya zama daya daga cikin manyan laifukan Ya\u0199i a Tarihin wannan [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2744\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"Taskar Nasaba\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2024-12-10T16:42:26+00:00\" \/>\n<meta property=\"article:modified_time\" content=\"2024-12-10T16:42:57+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-10T172937.8122.jpeg\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"630\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"418\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/jpeg\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Salahuddeen Muhammad\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"Salahuddeen Muhammad\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Est. reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"9 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\/\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2744#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2744\"},\"author\":{\"name\":\"Salahuddeen Muhammad\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753\"},\"headline\":\"Tarihin Rikicin \u0198abilar Tutsi da Hutu a Rwanda\",\"datePublished\":\"2024-12-10T16:42:26+00:00\",\"dateModified\":\"2024-12-10T16:42:57+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2744\"},\"wordCount\":1852,\"commentCount\":0,\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2744#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-10T172937.8122.jpeg\",\"articleSection\":[\"Tarihi\"],\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2744#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2744\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2744\",\"name\":\"Tarihin Rikicin \u0198abilar Tutsi da Hutu a Rwanda\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2744#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2744#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-10T172937.8122.jpeg\",\"datePublished\":\"2024-12-10T16:42:26+00:00\",\"dateModified\":\"2024-12-10T16:42:57+00:00\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2744#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2744\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2744#primaryimage\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-10T172937.8122.jpeg\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-10T172937.8122.jpeg\",\"width\":630,\"height\":418},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2744#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Tarihin Rikicin \u0198abilar Tutsi da Hutu a Rwanda\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"description\":\"\",\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\"},\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-US\"},{\"@type\":\"Organization\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\",\"logo\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png\",\"width\":343,\"height\":345,\"caption\":\"Taskar Nasaba\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/\"}},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753\",\"name\":\"Salahuddeen Muhammad\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg\",\"caption\":\"Salahuddeen Muhammad\"},\"description\":\"\u018aanjarida, marubuci, mai manufar bun\u0199asa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.\",\"sameAs\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\"],\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?author=1\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Tarihin Rikicin \u0198abilar Tutsi da Hutu a Rwanda","robots":{"index":"noindex","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"og_locale":"en_US","og_type":"article","og_title":"Tarihin Rikicin \u0198abilar Tutsi da Hutu a Rwanda","og_description":"An fara kisan kiyashi a Rwanda lokacin da aka harbo Jirgin Saman da ke \u0257auke da Shugaban Rwanda Juv\u00e9nal Habyarimana da shugaban Burundi Cyprien Ntaryamira. Daga: Muhammad Cisse A shekarar 1994 a cikin kwanaki 100 kacal, kisan kiyashin da aka yi a \u0198asar Ruwanda ya zama daya daga cikin manyan laifukan Ya\u0199i a Tarihin wannan [&hellip;]","og_url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2744","og_site_name":"Taskar Nasaba","article_published_time":"2024-12-10T16:42:26+00:00","article_modified_time":"2024-12-10T16:42:57+00:00","og_image":[{"width":630,"height":418,"url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-10T172937.8122.jpeg","type":"image\/jpeg"}],"author":"Salahuddeen Muhammad","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"Salahuddeen Muhammad","Est. reading time":"9 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2744#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2744"},"author":{"name":"Salahuddeen Muhammad","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753"},"headline":"Tarihin Rikicin \u0198abilar Tutsi da Hutu a Rwanda","datePublished":"2024-12-10T16:42:26+00:00","dateModified":"2024-12-10T16:42:57+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2744"},"wordCount":1852,"commentCount":0,"publisher":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2744#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-10T172937.8122.jpeg","articleSection":["Tarihi"],"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2744#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2744","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2744","name":"Tarihin Rikicin \u0198abilar Tutsi da Hutu a Rwanda","isPartOf":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2744#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2744#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-10T172937.8122.jpeg","datePublished":"2024-12-10T16:42:26+00:00","dateModified":"2024-12-10T16:42:57+00:00","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2744#breadcrumb"},"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2744"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2744#primaryimage","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-10T172937.8122.jpeg","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-10T172937.8122.jpeg","width":630,"height":418},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2744#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/taskarnasaba.com\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Tarihin Rikicin \u0198abilar Tutsi da Hutu a Rwanda"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/","name":"Taskar Nasaba","description":"","publisher":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization"},"potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-US"},{"@type":"Organization","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization","name":"Taskar Nasaba","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/","logo":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png","width":343,"height":345,"caption":"Taskar Nasaba"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/"}},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753","name":"Salahuddeen Muhammad","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/image\/","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg","caption":"Salahuddeen Muhammad"},"description":"\u018aanjarida, marubuci, mai manufar bun\u0199asa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.","sameAs":["https:\/\/taskarnasaba.com"],"url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?author=1"}]}},"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-2024-12-10T172937.8122.jpeg","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2744","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=2744"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2744\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2745,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2744\/revisions\/2745"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/2741"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=2744"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=2744"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=2744"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}