{"id":2786,"date":"2024-12-11T17:52:49","date_gmt":"2024-12-11T17:52:49","guid":{"rendered":"https:\/\/taskarnasaba.com.ng\/?p=2786"},"modified":"2024-12-11T17:53:57","modified_gmt":"2024-12-11T17:53:57","slug":"masarautar-katsinar-mara%c9%97i-a-jamhuriyar-nijar","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2786","title":{"rendered":"Masarautar Katsinar Mara\u0257i a Jamhuriyar Nijar"},"content":{"rendered":"\n<p><strong>Masarautar Katsinar Mara\u0257i, babbar Masarauta ce mai da\u0257a\u0257\u0257en tarihi a Jamhuriyyar Nijar inda darajar Masarautar ta tashi daga Sarki zuwa Sultan.<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Daga: <strong>Awwal Ahmad Janyau<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Mafi yawancin al&#8217;ummar Masarautar Mara\u0257i Hausawa ne da kuma wasu \u0199abilu na Nijar kuma ta \u0199unshi Musulmi da kuma wasu ka\u0257an mabiya addinin Kirista.<\/p>\n\n\n\n<p>Masarautar Mara\u0257i ta yi iyaka da yankin Damagaram daga Gabas da yankin Tawa daga Yamma da yankin Agadez daga Arewa, sannan ta yi iyaka da Najeriya daga Kudu musamman Jihohin Katsina da Zamfara da Sakkwato da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.<\/p>\n\n\n\n<p>Akan yi wa yankin Mara\u0257i kirari da gidan al&#8217;adun gargajiya na Nijar da Cibiyar ilimi kuma cibiyar ciyar da \u0199asa saboda harkokin kasuwanci da noman da ake yi a yankin.<\/p>\n\n\n\n<p>BBC ta tattauna da masana tarihi, Farfesa Ado Mahaman shugaban Jami&#8217;ar Tawa a Nijar kuma masanin wanda ya yi rubuce-rubuce da dama kan Maradi da masarautar Katsinan Maradi, da kuma Issoufou Habou Magagi malamin da ke kula da gidan tarihi na Jihar Mara\u0257i.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Kalmar Mara\u0257i<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Duk da ra&#8217;ayin manazarta ya bambanta kan asalin tushen kalmar Mara\u0257i, amma masana tarihi sun ce sunan Maradi ya samo asali ne zamanin mutumin da ya kafa garin.<\/p>\n\n\n\n<p>Malam Issoufou Magagi mai kula da gidan Tarihi na jihar Maradi ya ce, sunan Mara\u0257i ya samo asali daga kalmar &#8220;Muradi&#8221; bayan \u018aanfodiyo ya ci Katsina da ya\u0199i, lokacin da ta watse.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;Sai \u018aan \u0198asawa ya ce &#8211; mu tsaya nan kafin muradinmu ya cika mu je mu kar\u0253e birninmu na Katsina &#8211; daga kalmar Muradi aka samu sunan Mara\u0257i,&#8221; in ji shi.<\/p>\n\n\n\n<p>Ya ce, sun ci gaba da zama a wurin duk da niyyar zuwa kar\u0253o Katsina saboda sun samu \u0199asa ce mai albarka ta noma da Ruwa da Kiwo da Farauta &#8211; &#8220;Bayan sun samu \u0199asa mai albarka sai suka ci gaba da zama har suka dawwama a wurin.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>Amma a nasa \u0253angaren masanin tarihin Masarautar Katsinar Farfesa Ado Mahaman ya ce, sunan Mara\u0257i ya samo asali ne daga Sarauta na wani yanki a Katsina.<\/p>\n\n\n\n<p>Ya ce, sarautar ta na \u0199ar\u0199ashin Katsina ne kuma wanda ke ri\u0199e da sarautar shi ake kira &#8220;Mara\u0257i.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>Ya ce, akwai unguwar Mara\u0257awa da sarkin ke da ikon yankin amma kuma ya na \u0199ar\u0199ashin Katsina kafin jihadin Usman \u018aanfodiyo.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;Sarauta ce ta \u0198aramar Hukuma da ke \u0199ar\u0199ashin Sarkin Katsina na gidan Korau.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tushen Masarautar Mara\u0257i da Kafuwarta<\/strong><\/p>\n\n\n\n<div class=\"wp-block-media-text is-stacked-on-mobile\"><figure class=\"wp-block-media-text__media\"><img fetchpriority=\"high\" decoding=\"async\" width=\"300\" height=\"169\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/112893305_f803f8a3-8b24-4dc0-a6f5-dd16be0039f16316289924698998523-300x169.webp\" alt=\"\" class=\"wp-image-2780 size-full\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/112893305_f803f8a3-8b24-4dc0-a6f5-dd16be0039f16316289924698998523-300x169.webp 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/112893305_f803f8a3-8b24-4dc0-a6f5-dd16be0039f16316289924698998523-768x432.webp 768w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/112893305_f803f8a3-8b24-4dc0-a6f5-dd16be0039f16316289924698998523-600x338.webp 600w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/112893305_f803f8a3-8b24-4dc0-a6f5-dd16be0039f16316289924698998523.webp 800w\" sizes=\"(max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/figure><div class=\"wp-block-media-text__content\">\n<p><em>Hoto: Issoufou Habou Magagi<\/em><\/p>\n<\/div><\/div>\n\n\n\n<p>Masana tarihi sun ce, Masarautar Mara\u0257i ta kafu ne tsakanin shekara 1807 &#8211; Kuma Farfesa Ado da Malam Issoufou sun ce, \u018aan \u0198asawa ne ya kafa Daular Katsinar Mara\u0257i.<\/p>\n\n\n\n<p>Farfesa Ado ya ce, gidan sarautar \u018aan \u0198asawa ta samo asali ne a wajajen \u0199arni na 17 daga cikin babbar Katsina. Kuma Katsinawa ne ke Sarautar Mara\u0257i.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;Jikokin Korau ne Mara\u0257i, su suka kafa garin tun garin ya na \u0199arami suka mayar da shi babban birni da ake kira Katsinar Mara\u0257i,&#8221; in ji shi.<\/p>\n\n\n\n<p>Ya kuma ce, Gidan Korau ne suka mayar da yankin Mara\u0257i Cibiyar kasuwanci a Nijar &#8211; suka kuma tallafawa Jamhuriya ta farko har da Turawan Mallaka da ku\u0257in gudanarwa saboda noman Gya\u0257a da suke.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;Da ku\u0257in Gya\u0257a da Kiwo suka taimaka wajen tafiyar da Gwamnati har zuwa lokacin da aka samu arzikin &#8216;Uranium&#8217; a 1971.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Me ya sa ake Cewa Sarkin Katsinar Mara\u0257i?<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Kamar yadda bayani ya gabata kan tushen Mara\u0257i, Masana sun ce wa\u0257anda suka gujewa jihadin \u018aanfodiyo ne suka kafa Masarautar Mara\u0257i.<\/p>\n\n\n\n<p>Kuma duk da cewa, asalin Mara\u0257i wani yanki ne na \u0198asar Katsina ta Najeriya, amma Masarautar ta fice ne daga \u0199arni na 19.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;Wasu Katsinawan Mara\u0257i a Nijar har yanzu su na ganin Katsina ta Najeriya yanki ne na Masarautarsu,&#8221; in ji Farfesa Ado.<\/p>\n\n\n\n<p>Ya ce, tun da Katsina ta rabu biyu, sai gidan Sarautar Korau ya baro birnin Katsina ya dawo ya kafu a Mara\u0257i &#8211; &#8220;Shi ya sa ake cewa Sarkin Katsinar Mara\u0257i ko Katsina ta Arewa ko katsina ta Faransa.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>Issoufou Magagi ya ce, Korau ne ya kafa Daular Katsina ta biyu, baya ga Daular da Koma yau ya fara kafawa a \u0199arni na shida wanda ya fara kafa Daular Katsinawa a shekarar 1665.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;Muhamman Korau wanda shi ne asalin Daular Katsinan Mara\u0257i ya kafa Daularsa ne a 1348. Sannan \u018aan \u0198asawa ya kafa Daular Katsinan Mara\u0257i a 1820, wacce ita ce Daular Katsinawa ta uku,&#8221; in ji shi.<\/p>\n\n\n\n<p>Farfesa Ado ya kuma ce, Mara\u0257i ta na \u0199ar\u0199ashin Masarautar Katsina ne tun kafin Jihadi ba ma kafin zuwan Turawa ba wato kafin shekara ta 1807 lokacin da goguwar Jihadi ta ci Katsina.<\/p>\n\n\n\n<p>Kamar yadda ake cewa, &#8220;Katsinawa jikokin Korau &#8211; To \u01b4an Gidan Korau ne suka taso suka dawo Mara\u0257i.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>Don haka a cewar Farfesa Ado, Mara\u0257i wani yanki ne na Katsina &#8211; Kuma Mara\u0257i da Aguie da Madarounfa da Tessaoua da Dakoro da Korgom da Kanan Bakache duka yankuna ne na Katsina kafin goguwar Jihadi ta raba su.<\/p>\n\n\n\n<p>Sai dai ya ce, Gidan Sarautar Mara\u0257i ne ya kafa Daular Katsina a \u0199arni na 15 bayan saukar Dur\u0253awa wanda ya ba Birnin Katsina \u0199ofofinta kamar \u0198ofar \u0198waya da \u0198ofar \u0198aura da \u0198ofar Guga da \u0198ofar Marusa.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;Shi ne ya mayar da Katsina Sarkin Kasuwa, ya ba ta jami&#8217;o&#8217;inta kamar Jami&#8217;ar \u018aanmasani da ta \u018aanmarina da ta \u01b3an Doto wadda babbar Jami&#8217;a ce a Afirka duk da cewa yanzu babu ta.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>Malam Issoufou Magaji ya ce, ana cewa Katsinar Mara\u0257i don a bambanta da Katsina ta Najeriya wato Katsina ta \u0199aya da Katsina ta Mara\u0257i ta Nijar da ake kira Katsina ta laka. Amma dukkaninsu Katsinawa ne na Nijar da Najeriya.<\/p>\n\n\n\n<p>Kuma kowa mai cin gashin kansa ne babu wanda ke \u0199ar\u0199ashin wani. Amma su na hul\u0257a ta Diflomasiyya da bukukuwa tsakaninsu da kuma kuma hul\u0257ar zaman lafiya.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Sarakunan da Suka yi Mulki a Mara\u0257i<\/strong><\/p>\n\n\n\n<div class=\"wp-block-media-text is-stacked-on-mobile\"><figure class=\"wp-block-media-text__media\"><img decoding=\"async\" width=\"300\" height=\"169\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/112893306_6a3898b4-4cef-464f-b95c-ce6ae98533527653316863882628846-300x169.webp\" alt=\"\" class=\"wp-image-2781 size-full\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/112893306_6a3898b4-4cef-464f-b95c-ce6ae98533527653316863882628846-300x169.webp 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/112893306_6a3898b4-4cef-464f-b95c-ce6ae98533527653316863882628846-768x432.webp 768w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/112893306_6a3898b4-4cef-464f-b95c-ce6ae98533527653316863882628846-600x338.webp 600w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/112893306_6a3898b4-4cef-464f-b95c-ce6ae98533527653316863882628846.webp 800w\" sizes=\"(max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/figure><div class=\"wp-block-media-text__content\">\n<p><em>Elh Mahaman Sani Kure &#8211; Buzu \u018aan Zambadi &#8211; Sarkin da ya fi da\u0257ewa a Masarautar Mara\u0257in Katsina. |Hoto: Issoufou Habou Magagi<\/em><\/p>\n<\/div><\/div>\n\n\n\n<p>Sarakuna 23 ne suka yi Mulki a Mara\u0257i. Kuma \u018aan \u0198asawa ne ya fara yin Sarauta wanda ya fara kafa Masarautar.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Sarakunan Masarautar Katsinan Mara\u0257i su ne:<\/strong><\/p>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>\u018aan \u0198asawa 1807 zuwa 1830<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Rauda Magajin Haladou 1830 zuwa 1836<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>\u018aan Mari 1836 zuwa 1843\/4<\/li>\n\n\n\n<li>Binoni 1843\/4 zuwa 1848\/9<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>\u018aan Mahedi 1848\/9 zuwa 1851\/2<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>\u018aan Baura 1851\/2 zuwa 1852\/3<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Baskore Rauda 1852\/3 zuwa 1875<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Barmo \u018aan Kasawa 1875\/6 zuwa 1879<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Maza Waje \u018aan \u0198asawa 1879\/8 zuwa 1882\/3<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Malam \u018aan \u0198asawa 1882\/3 zuwa 1883\/4<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Salau \u018aan Mahedi 1883\/4 zuwa 1887\/8<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Gulbi \u018aan Kaka Rauda 1887\/8 zuwa 1889\/90<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>\u018aan Dadi Binoni 1889\/90 ya yi \u01b4an watanni<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Mijinyawa Barmo 1889\/90 zuwa 1892<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Naibo \u018aan Baura 1892 zuwa 1894<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Daci Binoni 1897 zuwa 1898<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Kure Malam 1897\/8 zuwa 1904<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Mahaman Burja \u018aan Mahedi 1920 ya yi \u01b4an watanni<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Ali \u018aan Kimale \u018aan Baura 1920 ya yi \u01b4an watanni<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>\u018aan Kulodo Malam 1920 zuwa 1944<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Mahaman \u018aan Baskore Kure 1944 zuwa 1947<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Elh Mahaman Sani Kure &#8211; Buzu \u018aan Zambadi<\/li>\n\n\n\n<li>Daga 1947 zuwa 2004<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Elh Ali Zaki &#8211; 2005 har yanzu.<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<p>Malam Issoufou Magaji ya ce, Sultan na yanzu, Alhaji Ali Zaki ya hau Karaga Mulki a ranar 1 ga watan Oktoban 2005 kuma ya hau ne bayan rasuwar Malam Sani Kure wanda ake cewa Bouzou \u018aan Zambadi wanda ya hau mulki a 1947 kuma ya rasu a 2004.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;Marigayi Buzu ya shekara 57 a kan Karagar Mulki kuma shi ne wanda ya fi da\u0257ewa a Masarautar Katsinar Mara\u0257i,&#8221; in ji shi.<\/p>\n\n\n\n<p>Zamanin Alhaji Ali Zaki ne Sarautar Katsinar Mara\u0257i ta koma Sultan tun kafa Masarautar.<\/p>\n\n\n\n<div class=\"wp-block-media-text is-stacked-on-mobile\"><figure class=\"wp-block-media-text__media\"><img decoding=\"async\" width=\"300\" height=\"92\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/112893303_7dc3aac8-77b5-4986-aabf-f4e33f5117ca710358340998746695-300x92.webp\" alt=\"\" class=\"wp-image-2782 size-full\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/112893303_7dc3aac8-77b5-4986-aabf-f4e33f5117ca710358340998746695-300x92.webp 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/112893303_7dc3aac8-77b5-4986-aabf-f4e33f5117ca710358340998746695-768x235.webp 768w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/112893303_7dc3aac8-77b5-4986-aabf-f4e33f5117ca710358340998746695-600x184.webp 600w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/112893303_7dc3aac8-77b5-4986-aabf-f4e33f5117ca710358340998746695.webp 800w\" sizes=\"(max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/figure><div class=\"wp-block-media-text__content\">\n<p><em>Sultan Katsinan Maradi Elh Ali Zaki. |Hoto: Issoufou Habou Magagi<\/em><\/p>\n<\/div><\/div>\n\n\n\n<p><strong>Ala\u0199ar Masarautar Katsinar Mara\u0257i da Daular Usmaniyya<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Masana tarihi sun ce, Masarautar Mara\u0257i ba ta da danganta da Daular Usmaniyya amma sun yi gwagwarmaya daga baya ne suka shirya dab da zuwan Turawa.<\/p>\n\n\n\n<p>Amma Malam Issoufou ya ce, Daular Mara\u0257i ta yi ala\u0199a ta ya\u0199i da Daular \u018aanfodiyo, &#8220;Ko da \u018aanfodio ya zo ya same su suna da addininsu na Musulunci.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>Ya ce, Littattafan tarihi su na nuna cewa, addinin Musulunci ya shigo yankin Mara\u0257i a \u0199arni na 11 ta hanyar kasuwanci da ke yi a yankin Sahara inda Larabawa saman Ra\u0199uma suke fatauci tun daga Hamada su ratso yankin Katsina har zuwa Kano.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;Daga lokacin ne \u0199arni na 11 ake sa ran addinin Musulunci ya shigo Daular Mara\u0257i ta hanyar Labarawan da ke zuwa fatauci.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>Malam Issoufou ya ce, lokacin da \u018aanfodio ya zo shi ya na ganin akwai kuskure kan yadda suke gudanar da addininsu wanda ya haifar da matsala tsakanin Katsinawa da Gobirawa.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;Sun yi zargin cewa, \u018aanfodio ya zo ne kawai da burin fa\u0257a\u0257a yankin shi &#8211; shi ne ya fake da Jihadi,&#8221; in ji shi.<\/p>\n\n\n\n<p>Masanin ya ce, lokacin da Usman \u018aanfodio ya tarwatsa Katsina sai ya aza Ummaru Dalaje wanda shi kuma ya tura Mani Asha zuwa yankin da yanzu ake kira Mara\u0257i.<\/p>\n\n\n\n<p>Ya ce, a lokacin Katsinawan Mara\u0257i sun zargi wakilin na \u018aanfodio da azabtar da su ta hanyar sa su aikin \u0199arfi da cin zarafi.<\/p>\n\n\n\n<p>A tarihin a cewarsa, Magaji Halidou wanda shi ne Sarki a Katsinan Mara\u0257i ya kashe kansa saboda takaicin tarwatsewar Katsina sakamakon jihadin \u018aanfodio.<\/p>\n\n\n\n<p>Wannan ya tilasta wa \u018aan \u0198asawa yin gudun hijira zuwa Damagaran, daga baya kuma ya turo maya\u0199ansa su kashe Mani Asha kafin ya zo ya kafa Daula.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;Ya tura manyan maya\u0199ansa ne guda shida suka yi masa Juyin Mulki &#8211; Suka sare kansa suka aika wa \u018aan \u0199asawa cewa, sun kashe shi kafin daga nan kuma ya dawo ya kafa Daularsa a Mara\u0257i.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Dangantakar Katsinan Maradi da Gobirawa<\/strong><\/p>\n\n\n\n<div class=\"wp-block-media-text is-stacked-on-mobile\"><figure class=\"wp-block-media-text__media\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"300\" height=\"169\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/112893304_b74c0092-cc85-462c-9ea7-645789db7ba86192704234942467698-300x169.webp\" alt=\"\" class=\"wp-image-2783 size-full\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/112893304_b74c0092-cc85-462c-9ea7-645789db7ba86192704234942467698-300x169.webp 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/112893304_b74c0092-cc85-462c-9ea7-645789db7ba86192704234942467698-768x432.webp 768w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/112893304_b74c0092-cc85-462c-9ea7-645789db7ba86192704234942467698-600x338.webp 600w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/112893304_b74c0092-cc85-462c-9ea7-645789db7ba86192704234942467698.webp 800w\" sizes=\"(max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/figure><div class=\"wp-block-media-text__content\">\n<p><em>Ma<\/em>rigayi <em>Sultan na Gobir Elh Abdou Bala Marafa. |Hoto: Issoufou Habou Maga<\/em>gi<\/p>\n<\/div><\/div>\n\n\n\n<p>Mara\u0257i ta \u0199unshi Masarautu biyu masu \u0199arfi a \u0198asar Nijar, wa\u0257anda ke da ala\u0199a ta ma\u0199wabtaka duk da sun ya\u0199i juna kafin su ha\u0257e kai su na ya\u0199ar wanda ya kawo masu farmaki.<\/p>\n\n\n\n<p>Farfesa Ado ya ce Katsinawa da Gobirawa ma\u0199wabtaka ce tsakaninsu &#8211; Su na cikin gungun manyan Sarakunan Hausawa kamar Zazzau da Kano da Daura a Hausa bakwai.<\/p>\n\n\n\n<p>Kilomita bakwai ne tsakanin Katsinar Mara\u0257i da yankin Tsibiri na Gobirawa inda Jihar Mara\u0257i ta kasance mai manyan sarakuna biyu masu girman Sultan.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;Da farko \u018aan Kasawa ne ke mulki a Katsinan Mara\u0257i -Ali \u018aan Yakouba a Tsibiri kuma dukkanin masarautun biyu yanzu Sultan ne,&#8221; in ji Malam Issoufou.<\/p>\n\n\n\n<p>Kuma a cewarsa masarautun biyu al&#8217;adunsu da addininsu da sana&#8217;arsu duka \u0257aya &#8211; ba su da wani bambanci al&#8217;adu tsakaninsu.<\/p>\n\n\n\n<p>Don haka ke nan akwai danganta ta al&#8217;ada da addini da kuma harshe da ta kasuwanci a tsakanin Katsinawa da Gobirawa.<\/p>\n\n\n\n<p>Farfesa Ado ya ce, tun can asali Gobirawa ma\u0199wabtan Katsinawa ne kuma akwai wasannin dangi tsakaninsu, amma a cewarsa dalilin sarautar Gobir ne goguwar jihadi ta taso ta ci su da ya\u0199i.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Su wa ke Na\u0257in Sabon Sarki?<\/strong><\/p>\n\n\n\n<div class=\"wp-block-media-text is-stacked-on-mobile\"><figure class=\"wp-block-media-text__media\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"300\" height=\"169\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/112833392_whatsappimage2020-06-08at035706632984481327850-300x169.webp\" alt=\"\" class=\"wp-image-2784 size-full\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/112833392_whatsappimage2020-06-08at035706632984481327850-300x169.webp 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/112833392_whatsappimage2020-06-08at035706632984481327850-768x432.webp 768w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/112833392_whatsappimage2020-06-08at035706632984481327850-600x338.webp 600w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/112833392_whatsappimage2020-06-08at035706632984481327850.webp 800w\" sizes=\"(max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/figure><div class=\"wp-block-media-text__content\">\n<p><em>A zamanin Ali Zaki sarautar Katsinar Mara\u0257i ta koma Sultan. |Hoto: Issoufou Habou Magagi<\/em><\/p>\n<\/div><\/div>\n\n\n\n<p>Masana sun ce, Sarkin Katsinar Mara\u0257i Sarki ne mai cin gashin kansa amma bisa tsarin Masarautar Katsinar Mara\u0257i mutum hu\u0257u ne ke za\u0253ar sabon Sarki; Galadima da \u01b3an\u0257akan Katsina da \u0198aura da Dur\u0253i.<\/p>\n\n\n\n<p>Yayin da wasu ke cewa, daga Katsina ta Najeriya ake na\u0257in Sarkin Katsinar Mara\u0257i, masana tarihin Masarautar sun ce, babu wata ala\u0199a tsakanin masu na\u0257a Sarki a Katsinar Mara\u0257i ta Nijar da Katsina ta Najeriya. Kowannensu mai cin gashin kansa ne babu wanda ke \u0199ar\u0199ashin wani. Amma su na hulda ta Diflomasiyya da bukukuwa tsakaninsu da kuma kuma hul\u0257ar zaman lafiya.<\/p>\n\n\n\n<p>Malam Issoufou ya ce, Galadama da \u01b3an\u0257akan Katsina a hannun damar Sarki suke yayin da \u0198aura da Dur\u0253i ke hannun hagun Sarki wadanda maya\u0199an Sarki ne.<\/p>\n\n\n\n<p>Sannan kafin za\u0253en sabon Sarki, su na la&#8217;akari da wasu muhimman abubuwa da suke duba wa idan Sarkin da ake son za\u0253a ya cika darajar da ake nema.<\/p>\n\n\n\n<p>Ana duba martabarsa da nasara; Sai an duba wanda zai fa\u0257a\u0257a Daula da samar da yalwa da wadata da hayyafa ta dabbobi da jarumtaka, duk su na cikin alamomin da ake duba wa kafin na\u0257a sabon Sarki.<\/p>\n\n\n\n<p>Hakan na nufin daga cikin \u0199a&#8217;idojin za\u0253ar Sarki sai wanda zai kawo zaman lafiya da wadata da arziki.<\/p>\n\n\n\n<p>Farfesa Ado Mahaman ya ce, idan masu na\u0257in Sarkin ba su jitu ba su na kiran Liman ya raba masu gardama. Kuma a cewarsa tun daga shekara ta 1445 suke za\u0253ar sarkin Katsinar Mara\u0257i har zuwa yanzu.<\/p>\n\n\n\n<p>Ya ce, dukkanin masu na\u0257in sabon Sarkin Katsinar Maradi su na wakiltar ko wani \u0253angare na Katsinawan Mara\u0257i daga \u0253angaren Bayi da gidan Sarauta da Sojoji da Talakawa.<\/p>\n\n\n\n<p>Sannan Farfesa ya ce, ana za\u0253ar Sarkin Mara\u0257i ba bisa kama-karya ba, &#8220;Dole sai \u0257an tsatson Gidan Korau ake za\u0253a, ba a za\u0253en wanda ba \u018aan gidansa ba.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>Masanin tarihin ya ce, akwai gwaji da ake yi bayan na\u0257in sabon Sarki kuma idan bai ci gwajin ba za a fitar da shi a saka wani.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;Gwaji na farko sai ya buga Tambura guda 12 inda ya na tsakar bugawa sai Iya ta tambaye shi wani gari ya bata? Amma idan ya kasa bugawa ya na cikin zanzana za a cire shi a sa wani.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>Za a kuma kai shi gidan Galadiman Katsina har tsawon mako \u0257aya inda za a sa shi lalle saboda Sarki mijin \u0198asa ne kuma Uban kasa ne.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;Sannan akwai gwaji na Mari da ake yi wa Sarki &#8211; Mai cin sarautar Mari ne zai kama ha\u0253ar Sarki ya na marinsa ka\u0257an-ka\u0257an.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;Ya na cewa, manta da abin ake maka kana \u0257an sarki, Manta,&#8221; in ji Farfesa Ado.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Masarautar Katsinar Mara\u0257i, babbar Masarauta ce mai da\u0257a\u0257\u0257en tarihi a Jamhuriyyar Nijar inda darajar Masarautar ta tashi daga Sarki zuwa Sultan. Daga: Awwal Ahmad Janyau Mafi yawancin al&#8217;ummar Masarautar Mara\u0257i Hausawa ne da kuma wasu \u0199abilu na Nijar kuma ta \u0199unshi Musulmi da kuma wasu ka\u0257an mabiya addinin Kirista. Masarautar Mara\u0257i ta yi iyaka da [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":2785,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"inline_featured_image":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[94],"tags":[],"class_list":["post-2786","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-masarautu"],"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v27.0 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Masarautar Katsinar Mara\u0257i a Jamhuriyar Nijar<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"noindex, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_US\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Masarautar Katsinar Mara\u0257i a Jamhuriyar Nijar\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"Masarautar Katsinar Mara\u0257i, babbar Masarauta ce mai da\u0257a\u0257\u0257en tarihi a Jamhuriyyar Nijar inda darajar Masarautar ta tashi daga Sarki zuwa Sultan. Daga: Awwal Ahmad Janyau Mafi yawancin al&#8217;ummar Masarautar Mara\u0257i Hausawa ne da kuma wasu \u0199abilu na Nijar kuma ta \u0199unshi Musulmi da kuma wasu ka\u0257an mabiya addinin Kirista. Masarautar Mara\u0257i ta yi iyaka da [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2786\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"Taskar Nasaba\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2024-12-11T17:52:49+00:00\" \/>\n<meta property=\"article:modified_time\" content=\"2024-12-11T17:53:57+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/112833211_maradi.jpg.webp\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"800\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"450\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/webp\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Taskar Nasaba\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"Taskar Nasaba\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Est. reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"11 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\/\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2786#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2786\"},\"author\":{\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/50c6fe8b25398ccbaf7fd94dee1c8456\"},\"headline\":\"Masarautar Katsinar Mara\u0257i a Jamhuriyar Nijar\",\"datePublished\":\"2024-12-11T17:52:49+00:00\",\"dateModified\":\"2024-12-11T17:53:57+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2786\"},\"wordCount\":2293,\"commentCount\":0,\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2786#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/112833211_maradi.jpg.webp\",\"articleSection\":[\"Masarautu\"],\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2786#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2786\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2786\",\"name\":\"Masarautar Katsinar Mara\u0257i a Jamhuriyar Nijar\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2786#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2786#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/112833211_maradi.jpg.webp\",\"datePublished\":\"2024-12-11T17:52:49+00:00\",\"dateModified\":\"2024-12-11T17:53:57+00:00\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2786#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2786\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2786#primaryimage\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/112833211_maradi.jpg.webp\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/112833211_maradi.jpg.webp\",\"width\":800,\"height\":450},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2786#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Masarautar Katsinar Mara\u0257i a Jamhuriyar Nijar\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"description\":\"\",\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\"},\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-US\"},{\"@type\":\"Organization\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\",\"logo\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png\",\"width\":343,\"height\":345,\"caption\":\"Taskar Nasaba\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/\"}},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/50c6fe8b25398ccbaf7fd94dee1c8456\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/cropped-Taskar-Nasaba-PNG-100x100.png\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/cropped-Taskar-Nasaba-PNG-100x100.png\",\"caption\":\"Taskar Nasaba\"},\"sameAs\":[\"http:\/\/www.taskarnasaba.com.ng\"],\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?author=2\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Masarautar Katsinar Mara\u0257i a Jamhuriyar Nijar","robots":{"index":"noindex","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"og_locale":"en_US","og_type":"article","og_title":"Masarautar Katsinar Mara\u0257i a Jamhuriyar Nijar","og_description":"Masarautar Katsinar Mara\u0257i, babbar Masarauta ce mai da\u0257a\u0257\u0257en tarihi a Jamhuriyyar Nijar inda darajar Masarautar ta tashi daga Sarki zuwa Sultan. Daga: Awwal Ahmad Janyau Mafi yawancin al&#8217;ummar Masarautar Mara\u0257i Hausawa ne da kuma wasu \u0199abilu na Nijar kuma ta \u0199unshi Musulmi da kuma wasu ka\u0257an mabiya addinin Kirista. Masarautar Mara\u0257i ta yi iyaka da [&hellip;]","og_url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2786","og_site_name":"Taskar Nasaba","article_published_time":"2024-12-11T17:52:49+00:00","article_modified_time":"2024-12-11T17:53:57+00:00","og_image":[{"width":800,"height":450,"url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/112833211_maradi.jpg.webp","type":"image\/webp"}],"author":"Taskar Nasaba","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"Taskar Nasaba","Est. reading time":"11 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2786#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2786"},"author":{"name":"Taskar Nasaba","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/50c6fe8b25398ccbaf7fd94dee1c8456"},"headline":"Masarautar Katsinar Mara\u0257i a Jamhuriyar Nijar","datePublished":"2024-12-11T17:52:49+00:00","dateModified":"2024-12-11T17:53:57+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2786"},"wordCount":2293,"commentCount":0,"publisher":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2786#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/112833211_maradi.jpg.webp","articleSection":["Masarautu"],"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2786#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2786","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2786","name":"Masarautar Katsinar Mara\u0257i a Jamhuriyar Nijar","isPartOf":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2786#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2786#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/112833211_maradi.jpg.webp","datePublished":"2024-12-11T17:52:49+00:00","dateModified":"2024-12-11T17:53:57+00:00","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2786#breadcrumb"},"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2786"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2786#primaryimage","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/112833211_maradi.jpg.webp","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/112833211_maradi.jpg.webp","width":800,"height":450},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2786#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/taskarnasaba.com\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Masarautar Katsinar Mara\u0257i a Jamhuriyar Nijar"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/","name":"Taskar Nasaba","description":"","publisher":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization"},"potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-US"},{"@type":"Organization","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization","name":"Taskar Nasaba","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/","logo":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png","width":343,"height":345,"caption":"Taskar Nasaba"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/"}},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/50c6fe8b25398ccbaf7fd94dee1c8456","name":"Taskar Nasaba","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/image\/","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/cropped-Taskar-Nasaba-PNG-100x100.png","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/cropped-Taskar-Nasaba-PNG-100x100.png","caption":"Taskar Nasaba"},"sameAs":["http:\/\/www.taskarnasaba.com.ng"],"url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?author=2"}]}},"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/112833211_maradi.jpg.webp","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2786","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=2786"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2786\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2787,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2786\/revisions\/2787"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/2785"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=2786"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=2786"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=2786"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}