{"id":2854,"date":"2024-12-18T19:35:04","date_gmt":"2024-12-18T19:35:04","guid":{"rendered":"https:\/\/taskarnasaba.com.ng\/?p=2854"},"modified":"2024-12-23T18:06:54","modified_gmt":"2024-12-23T18:06:54","slug":"yadda-ake-kiwon-kifi-a-sau%c6%99a%c6%99e","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2854","title":{"rendered":"Yadda Ake Kiwon Kifi a Sau\u0199a\u0199e"},"content":{"rendered":"\n<p>Wannan kalma ta \u2018Fishery\u2019 ta na da mabambantan ma\u2019anoni. Oxford Dictionary (2000), Encarta Dictionary (2009), Merriam-Webster Dictionary (2015), sun kalle ta a matsayin \u2018wuri ko muhallin da ake kamun Kifi\u2019.<\/p>\n\n\n\n<p>Saboda haka, za mu iya cewa ke nan wannan kalma ta \u2018Fishery\u2019 da farko ta na nufin wani yanki, ko wuri ko muhalli wanda ka iya zama wani yanki na Teku, Kogi, ko Tafki wanda Kifi ke rayuwa a wurin, kuma wurin ya zama bigiren kamun Kifi.<\/p>\n\n\n\n<p>Ke nan, duk wani yanki na Kogi ko Teku da makamantansu da Kifi ba ya rayuwa a wurin ba za a iya kiransa \u2018Fishery\u2019 ba.<\/p>\n\n\n\n<p>Sannan kuma, ta na da ma\u2019ana ta kamfanin da ke kamawa ko sayar da Kifi. Wannan kamfani zai iya kasancewa babba ko \u0199arami. Duba (Encarta Dictionary, 2009; Oxford Dictionary, 2000; Wikipedia, 2015).<\/p>\n\n\n\n<p>Har wa yau dai kuma ta na da ma\u2019ana ta dukkan wani abu da ya shafi sana\u2019ar Kifi tun daga kiwon Kifi, kamun Kifi, gyaran Kifi, da kuma sayar da kifin, da ma wurare da masa\u2019antun da ake aiwatar da wannan sana\u2019ar. Kai, har ma da dabaru ko hanyoyin kamun kifin sun shigo ciki. Wa\u0257anda suka ha\u0257u a kan haka sun ha\u0257a da (Encarta Dictionary, 2009; Wikipedia 2015).<\/p>\n\n\n\n<p>Sannan kuma akwai &#8216;Fishery&#8217;, a matsayin fannin karatu da ake koyarwa a fannin aikin Gona, wato \u2018Agriculture\u2019 da yake koyar da dukkan wani abu da ya shafi harkar Kifi kamawa tun daga sanin shi kifin a kan-kansa, kiwata shi, kama shi, gyaggyara shi, sayar da da shi da sauran dangoginsa.<\/p>\n\n\n\n<p>Wannan fanni na aikin gona (fishery), ya na bada muhimmiyar gudunmowa wajen samar da ayyukan yi, inganta harkar samar da Abinci, da kuma ha\u0253\u0253aka hanyoyin samar da ku\u0257a\u0257en shiga ga \u0257ai\u0257aikun mutane, Masana\u2019antar da kuma \u0199asashe a Duniya.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Mene ne Kiwon Kifi?<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>To da farko dai, idan muka ce Kiwon Kifi to wannan na nufin hanyar sarrafa \u0199ananan Kifaye ta hanyar ba su kulawa har su kai mizanin girma, ta yadda za su ci gaba da hayayyafa su \u0199ara yawa, wanda dama wannan shi ne babban dalilin kiwon nasu.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Yadda Ake Fara Noman Kifi<\/strong><\/p>\n\n\n\n<div class=\"wp-block-media-text is-stacked-on-mobile\"><figure class=\"wp-block-media-text__media\"><img fetchpriority=\"high\" decoding=\"async\" width=\"640\" height=\"480\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-3298873859281320642.jpeg\" alt=\"\" class=\"wp-image-2849 size-full\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-3298873859281320642.jpeg 640w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-3298873859281320642-300x225.jpeg 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-3298873859281320642-600x450.jpeg 600w\" sizes=\"(max-width: 640px) 100vw, 640px\" \/><\/figure><div class=\"wp-block-media-text__content\">\n<p><em>Wani kududdufin Kiwon Kifi<\/em><\/p>\n<\/div><\/div>\n\n\n\n<p>Noman Kifi dai iri-iri ne, akwai hanyoyi daban-daban saboda dalilan kiwonsa na \u0199ara yawa a kullum a Duniya.<\/p>\n\n\n\n<p>Akwai dalilai da dama na bun\u0199asar Noman Kifi saboda a kullum ana samun \u0199aruwar adadin mutane mabu\u0199ata Kifi da sauran albarkatun cikin ruwa wadda suke amfani da shi a matsayin Abinci ko kuma sana&#8217;a, wadda za su dogara da ita. Bayan haka, mutane na \u0199ara fahimtar muhimmancin cin Abinci mai \u0257auke da Kifi a ciki.<\/p>\n\n\n\n<p>Mutane da dama na Noman Kifi ne a bisa ra\u2019ayinsu, ko dai don a ci ko a sayarwa don samun biyan bu\u0199atar rayuwa ta yau da kullum, ko kuma saboda nisha\u0257i, wasu kuma su na Noman Kifi ne don ilmantarwa, musamman a manyan Makarantu da wasu Cibiyoyi don koyar da \u0257alibai yadda ake kiwon a aikace (Practically).<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Matakan Farko na Noman Kifi<\/strong><\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img decoding=\"async\" width=\"480\" height=\"640\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-28507623403822544696.jpeg\" alt=\"\" class=\"wp-image-2850\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-28507623403822544696.jpeg 480w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-28507623403822544696-225x300.jpeg 225w\" sizes=\"(max-width: 480px) 100vw, 480px\" \/><\/figure>\n\n\n\n<ol class=\"wp-block-list\">\n<li>A tabbatar an tantance irin Gona, wato inda za a Noma Kifin; Shin a bayan Gida ne ko kuma a Tafki ne, sa&#8217;annan ya ya wajen yake ta fuskar yanayin Zafi ko Sanyin wajen?<\/li>\n<\/ol>\n\n\n\n<p>Sa&#8217;annan dole sai an zayyana dalilin da zai sa a fara Noman Kifin wanda ta haka ne za a fi samun cikakken \u0199warin guiwa a harkar.<\/p>\n\n\n\n<p>Bayan haka dole a tantance irin nau&#8217;in Kifin da ake so ka kiwata, saboda akwai hanyoyi iri-iri wajen Noman Kifi. Saboda haka, akwai bu\u0199atar sanin wani irin Kifi ake so a Noma, da kuma rubuta tsari da manufofi na kiwon.<\/p>\n\n\n\n<p>Duk mai bu\u0199atar ya fara wannan sana&#8217;a, ya na bu\u0199atar amsa wa\u0257annan tambayoyin:<\/p>\n\n\n\n<p>a. Me za a yi da kifin bayan an Noma? Abinci za a yi da shi, sayarwa, ilmantarwa ko kuma kawai don \u0199awa (kwalliya)?<\/p>\n\n\n\n<p>b. Shin ana da nufin gina \u0257an \u0199aramin Tafkin Kifi ne, ko kuma niyyar ita ce; Kafa katafaren Kamfani domin samun riba mai yawa da shahara a wannan fanni?<\/p>\n\n\n\n<ol start=\"2\" class=\"wp-block-list\">\n<li>An tantance irin jinsin Kifin da ake so a Noma? Saboda tafkin Noman Kifin da za a gina ya danganta ne da irin kalar kifin da za a Noma.<\/li>\n<\/ol>\n\n\n\n<p>Sa&#8217;annan kuma akwai bu\u0199atar fahimtar wa\u0257annan:<\/p>\n\n\n\n<p>a. Idan har an tantance irin Kifin da ake so a Noma, to akwai bu\u0199atar tuntu\u0253ar wanda yake Noma irin wannan Kifi domin su ba da \u0199arin haske a kan yiwuwarsa da irin \u0199arfin da ake da shi.<\/p>\n\n\n\n<p>b. A rubuta kuma a tantance duk ku\u0257in da ake kashewa akan kowanne irin jinsin Kifi, kuma ya zama wajibi a san cewa, farashin kowane daga ciki ya sha bamban da kowane irin jinsin Kifi da za a Noma.<\/p>\n\n\n\n<p>c. A kuma yi la\u2019akari da irin yanayin da ake so a Noma Kifi. Akwai Kifin da ke bu\u0199atar Ruwa mai sanyi, akwai kuma mai bu\u0199atar ruwan \u0257umi, saboda haka, ana bu\u0199atar gujewa duk wani kasha-kashen ku\u0257i da ke da ala\u0199a da salon sanyayawa ko dafa ruwa.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Abubuwan da Ake Bu\u0199ata Don Bu\u0199atar Kiwon Kifi<\/strong><\/p>\n\n\n\n<div class=\"wp-block-media-text is-stacked-on-mobile\"><figure class=\"wp-block-media-text__media\"><img decoding=\"async\" width=\"639\" height=\"480\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-71447196605318389431.jpeg\" alt=\"\" class=\"wp-image-2851 size-full\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-71447196605318389431.jpeg 639w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-71447196605318389431-300x225.jpeg 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-71447196605318389431-600x451.jpeg 600w\" sizes=\"(max-width: 639px) 100vw, 639px\" \/><\/figure><div class=\"wp-block-media-text__content\">\n<p><em>Wani yanki mai yawan ruwa marasa \u0199afewa<\/em>. <\/p>\n<\/div><\/div>\n\n\n\n<p>Kafin a fara Noman Kifi, dole Manomi ya tabbatar ya tanadi wa\u0257annan abubuwan:<\/p>\n\n\n\n<ol class=\"wp-block-list\">\n<li>Tsaftataccen Ruwa mara yankewa, ko dai ta hanyar amfani da bututun zuba Ruwa ko kuma ta hanyar Rijiyar Burtsatse.<\/li>\n\n\n\n<li>Samar da lafiyayyar hanya wacce za ta sau\u0199a\u0199e shiga da fice daga Gonar.<\/li>\n\n\n\n<li>Bayan haka kuma, ya kamata a ajiye Gonar kusa da Kasuwa domin sau\u0199a\u0199e shige da fice da iya hanzarta kai Kifi Kasuwa (idan bu\u0199atar hakan ta taso) don kiyaye lalacewarsu.<\/li>\n\n\n\n<li>A tabbatar an yi Gonar a wurin da yake fili ne kuma a kiyayi yin gonar a kan Tuddai.<\/li>\n\n\n\n<li>A tabbatar da sa ido a Gonar wato ta sami cikakken kulawa.<\/li>\n\n\n\n<li>Irin Kifi da za a zuba ya kasance irin da ke da juriyar \u0199arancin iska ne kuma irin wanda ke matu\u0199ar bu\u0199ata.<\/li>\n<\/ol>\n\n\n\n<p><strong>Za\u0253en Filin Kiwon Kifi Mafi Dacewa<\/strong><\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"256\" height=\"197\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-8785319832738918142.jpeg\" alt=\"\" class=\"wp-image-2852\"\/><\/figure>\n\n\n\n<p>A nemi fili marasa Tudu, kuma a guji wuri mai yawan Tuddai da me daji-daji domin gyaransa zai haifar da \u0199aruwar ku\u0257in noman. A sau\u0199a\u0199e, za a iya gina Kududdufin kiwon a bayan Gida don samun sau\u0199in kulawa.<\/p>\n\n\n\n<ol start=\"2\" class=\"wp-block-list\">\n<li>A nemi wurin da ke da sau\u0199in shiga da abin hawa don shiga ko fita da Kifin domin hana saurin lalacewa.<\/li>\n\n\n\n<li>Dole kuma ya zama babu matsalar Ruwa a wurin don hana yawan asara.<\/li>\n<\/ol>\n\n\n\n<p><strong>Shin ko Akwai \u0198alubale a Kiwon Kifi?<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Kamar yadda muka sani bisa al&#8217;ada kusan kowace irin sana&#8217;a ta na cike da \u0199alubale da matsaloli masu \u0257imbin yawa, dole sai an yi ha\u0199uri gami da juriya musamman a lamari wanda ya shafi Kiwo.<\/p>\n\n\n\n<p>A ta\u0199aice dai, za mu iya cewa ha\u0199uri shi ne makami kuma jigon nasarar Manomi, misali; Makiyayi kullum sai ya fitar da Shanunsa zuwa Kiwo, komai Sanyi, komai Ruwa, kuma komai zafin Rana ba zai huta ba ko da na rana guda dole sai ya fita Kiwo, a haka zai ci gaba da rainonsu ya na basu kulawa shekara da shekaru har su kai \u0257aruruwa zuwa dubunnai, ba don komai ba sai don ya jure kuma yi ha\u0199uri da irin \u0199alubalen da ya fuskanta.<\/p>\n\n\n\n<p>Haka zalika mai Kiwon Kaji shi ma dole kullum sai ya tsaftace makwancinsu sa&#8217;annan ya zuba musu sabon Abinci da Safe, da Rana da Yamma ba tare da gajiyawa ba.<\/p>\n\n\n\n<p>To haka mai Kiwon Kifi wajibi ne sai ya zama mai juriya kafin ya kai ga nasara. Ha\u0199uri da bin komai sannu a hankali shi ne babban makami a sana&#8217;ar Noman Kifi.<\/p>\n\n\n\n<p>Idan mutum ba\u0199o ne a wannan fanni, to ya na bu\u0199atar samun fahimta da \u0199warewa a wannan fanni na neman \u0199arin haske daga Manoma wa\u0257anda sun da\u0257e a harkar Kifin.<\/p>\n\n\n\n<p>koda yake, alal ha\u0199i\u0199a Kiwon Kifi ba ya bu\u0199atar wani ku\u0257i mai yawa kafin fara shi. Sai dai ya danganta da \u0199arfin aljihu da kuma kwatankwacin yadda ake son a aiwatar da shi. Kamar yadda masana a fannin ke ba da shawarar farawa da \u0199aramin jari.<\/p>\n\n\n\n<p>Ba komai ya sa masanan ba da wannan shawara ba, sai dai farawa daga mataki na \u0199asa zai bayar da damar fahimta tare da \u0199warewa kafin a tsunduma ga mataki na gaba.<\/p>\n\n\n\n<p>Ko an ta\u0253a harkar, mallaka da kuma tafiyar da Gonar Kifi na bu\u0199atar ilimi mai yawa a kan yadda sana\u2019ar take.<\/p>\n\n\n\n<p>Idan kuma niyyar ita ce a mallaki sana\u2019ar, sannan a dinga lura da \u0253angaren sha&#8217;anin wannan Gona, to hakan ma ya na bukatar aa fa\u0257a\u0257a ilimi a kan sana\u2019ar, sannan a \u0257auki mutum wanda ya fi kuzari a cikin ma\u2019aikatar, domin tafiyar da wannan harka sai an sami mutum tsayayye mai juriya.<\/p>\n\n\n\n<div class=\"wp-block-media-text is-stacked-on-mobile\"><figure class=\"wp-block-media-text__media\"><img decoding=\"async\" src=\"file:\/\/\/data\/user\/0\/org.wordpress.android\/cache\/images - 2024-12-18t0005024347525226370574418.\" alt=\"\" class=\"wp-image-2198 size-full\"\/><\/figure><div class=\"wp-block-media-text__content\">\n<p><em>Tafkin Kiwon Kifi don Ado<\/em><\/p>\n<\/div><\/div>\n\n\n\n<p><strong>Wasu Hanyoyin Neman Ilimin Kiwon Kifi<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>a. a nemi aiki a Gonar da ke Noma irin jinsin kifin da ake da niyyar nomawa. Hakan zai taimaka a \u0199ara fa\u0257a\u0257a ilimi ta fannin sanin \u0257abi&#8217;ar kifayen, da kuma sanin tsarin rayuwarsu.<\/p>\n\n\n\n<p>b. A nemi ilimi a kan Intanet da Littattafan da aka buga wa\u0257anda mafi yawancin su na binciken bayanai takaimaimai akan yadda ake noman ire-iren Kifaye.<\/p>\n\n\n\n<p>c. A lazimci kasancewa Ajujuwa a Jami\u2019o&#8217;i ko makarantu musamman akan Noman Kifi. Wannan ya na da matu\u0199ar amfani idan aka yi da wuri, saboda zai fe\u0257e Biri har Wutsiya a kan wannan sana\u2019a \u0253aki \u0257ayanta.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Yadda Ake Gina Tafkin Kiwon Kifi<\/strong><\/p>\n\n\n\n<div class=\"wp-block-media-text is-stacked-on-mobile\"><figure class=\"wp-block-media-text__media\"><img decoding=\"async\" src=\"file:\/\/\/storage\/emulated\/0\/Download\/0064-01.gif\" alt=\"\" class=\"wp-image-2207 size-full\"\/><\/figure><div class=\"wp-block-media-text__content\">\n<p><em>A tabbata an cire sauwoyi da sauran ciyayi da ke wajen. <\/em><\/p>\n<\/div><\/div>\n\n\n\n<div class=\"wp-block-media-text is-stacked-on-mobile\"><figure class=\"wp-block-media-text__media\"><img decoding=\"async\" src=\"file:\/\/\/data\/user\/0\/org.wordpress.android\/cache\/screenshot_20210110-1537371585085781003370757.png\" alt=\"\" class=\"wp-image-2208 size-full\"\/><\/figure><div class=\"wp-block-media-text__content\">\n<p><em>Bayan an kammala share filin sannan an yi gwaje-gwaje, to sai a fara gina rami ana fitar da \u0199asar gefe ta yadda za a fitar da siffar ramin.<\/em><\/p>\n\n\n\n<div class=\"wp-block-media-text is-stacked-on-mobile\"><figure class=\"wp-block-media-text__media\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"300\" height=\"92\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/download4035694725740576200-300x92.png\" alt=\"\" class=\"wp-image-2858 size-full\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/download4035694725740576200-300x92.png 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/download4035694725740576200.png 405w\" sizes=\"(max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/figure><div class=\"wp-block-media-text__content\">\n<p><em>Mataki na gaba shi ne; Gwada fasalin tsayi da fa\u0257in tafkin.<\/em><\/p>\n\n\n\n<div class=\"wp-block-media-text is-stacked-on-mobile\"><figure class=\"wp-block-media-text__media\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"300\" height=\"171\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-23416678719384193414-300x171.png\" alt=\"\" class=\"wp-image-2859 size-full\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-23416678719384193414-300x171.png 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-23416678719384193414.png 350w\" sizes=\"(max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/figure><div class=\"wp-block-media-text__content\">\n<p><em>A gwada tsayi da fa\u0257in kowacce kusurwa cikin hikima.<\/em><\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"346\" height=\"163\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/0053-01.gif\" alt=\"\" class=\"wp-image-2860\"\/><\/figure>\n\n\n\n<div class=\"wp-block-media-text is-stacked-on-mobile\"><figure class=\"wp-block-media-text__media\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"307\" height=\"145\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/0072-01.gif\" alt=\"\" class=\"wp-image-2861 size-full\"\/><\/figure><div class=\"wp-block-media-text__content\">\n<p><em>A tabbatar an daidaita tudun ramin ka da ya gaza 1.5 metre.<\/em><\/p>\n\n\n\n<div class=\"wp-block-media-text is-stacked-on-mobile\"><figure class=\"wp-block-media-text__media\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"303\" height=\"137\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/0076-01.gif\" alt=\"\" class=\"wp-image-2862 size-full\"\/><\/figure><div class=\"wp-block-media-text__content\">\n<p><em>Bayan an kammala ginin tsayi da fa\u0257in ramin sai a zana magudana daga tsakiyar ramin wanda za a ri\u0199a fitar da lalataccen ruwa da sauran datti.<\/em><\/p>\n\n\n\n<div class=\"wp-block-media-text is-stacked-on-mobile\"><figure class=\"wp-block-media-text__media\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"803\" height=\"382\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-61499859922614068164.jpeg\" alt=\"\" class=\"wp-image-2863 size-full\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-61499859922614068164.jpeg 803w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-61499859922614068164-300x143.jpeg 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-61499859922614068164-768x365.jpeg 768w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-61499859922614068164-600x285.jpeg 600w\" sizes=\"(max-width: 803px) 100vw, 803px\" \/><\/figure><div class=\"wp-block-media-text__content\">\n<p><em>Sassan kammalallen kududdufin Kiwon Kifi na zamani.<\/em><\/p>\n<\/div><\/div>\n<\/div><\/div>\n<\/div><\/div>\n<\/div><\/div>\n<\/div><\/div>\n<\/div><\/div>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Wannan kalma ta \u2018Fishery\u2019 ta na da mabambantan ma\u2019anoni. Oxford Dictionary (2000), Encarta Dictionary (2009), Merriam-Webster Dictionary (2015), sun kalle ta a matsayin \u2018wuri ko muhallin da ake kamun Kifi\u2019. Saboda haka, za mu iya cewa ke nan wannan kalma ta \u2018Fishery\u2019 da farko ta na nufin wani yanki, ko wuri ko muhalli wanda ka [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":2848,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"inline_featured_image":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[102],"tags":[],"class_list":["post-2854","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-noma-da-kiwo"],"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v27.0 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Yadda Ake Kiwon Kifi a Sau\u0199a\u0199e<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"noindex, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_US\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Yadda Ake Kiwon Kifi a Sau\u0199a\u0199e\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"Wannan kalma ta \u2018Fishery\u2019 ta na da mabambantan ma\u2019anoni. Oxford Dictionary (2000), Encarta Dictionary (2009), Merriam-Webster Dictionary (2015), sun kalle ta a matsayin \u2018wuri ko muhallin da ake kamun Kifi\u2019. Saboda haka, za mu iya cewa ke nan wannan kalma ta \u2018Fishery\u2019 da farko ta na nufin wani yanki, ko wuri ko muhalli wanda ka [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2854\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"Taskar Nasaba\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2024-12-18T19:35:04+00:00\" \/>\n<meta property=\"article:modified_time\" content=\"2024-12-23T18:06:54+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-4.jpeg\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"500\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"419\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/jpeg\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Salahuddeen Muhammad\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"Salahuddeen Muhammad\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Est. reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"8 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\/\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2854#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2854\"},\"author\":{\"name\":\"Salahuddeen Muhammad\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753\"},\"headline\":\"Yadda Ake Kiwon Kifi a Sau\u0199a\u0199e\",\"datePublished\":\"2024-12-18T19:35:04+00:00\",\"dateModified\":\"2024-12-23T18:06:54+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2854\"},\"wordCount\":1711,\"commentCount\":0,\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2854#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-4.jpeg\",\"articleSection\":[\"Noma Da Kiwo\"],\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2854#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2854\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2854\",\"name\":\"Yadda Ake Kiwon Kifi a Sau\u0199a\u0199e\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2854#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2854#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-4.jpeg\",\"datePublished\":\"2024-12-18T19:35:04+00:00\",\"dateModified\":\"2024-12-23T18:06:54+00:00\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2854#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2854\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2854#primaryimage\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-4.jpeg\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-4.jpeg\",\"width\":500,\"height\":419},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2854#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Yadda Ake Kiwon Kifi a Sau\u0199a\u0199e\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"description\":\"\",\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\"},\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-US\"},{\"@type\":\"Organization\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\",\"logo\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png\",\"width\":343,\"height\":345,\"caption\":\"Taskar Nasaba\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/\"}},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753\",\"name\":\"Salahuddeen Muhammad\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg\",\"caption\":\"Salahuddeen Muhammad\"},\"description\":\"\u018aanjarida, marubuci, mai manufar bun\u0199asa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.\",\"sameAs\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\"],\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?author=1\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Yadda Ake Kiwon Kifi a Sau\u0199a\u0199e","robots":{"index":"noindex","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"og_locale":"en_US","og_type":"article","og_title":"Yadda Ake Kiwon Kifi a Sau\u0199a\u0199e","og_description":"Wannan kalma ta \u2018Fishery\u2019 ta na da mabambantan ma\u2019anoni. Oxford Dictionary (2000), Encarta Dictionary (2009), Merriam-Webster Dictionary (2015), sun kalle ta a matsayin \u2018wuri ko muhallin da ake kamun Kifi\u2019. Saboda haka, za mu iya cewa ke nan wannan kalma ta \u2018Fishery\u2019 da farko ta na nufin wani yanki, ko wuri ko muhalli wanda ka [&hellip;]","og_url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2854","og_site_name":"Taskar Nasaba","article_published_time":"2024-12-18T19:35:04+00:00","article_modified_time":"2024-12-23T18:06:54+00:00","og_image":[{"width":500,"height":419,"url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-4.jpeg","type":"image\/jpeg"}],"author":"Salahuddeen Muhammad","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"Salahuddeen Muhammad","Est. reading time":"8 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2854#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2854"},"author":{"name":"Salahuddeen Muhammad","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753"},"headline":"Yadda Ake Kiwon Kifi a Sau\u0199a\u0199e","datePublished":"2024-12-18T19:35:04+00:00","dateModified":"2024-12-23T18:06:54+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2854"},"wordCount":1711,"commentCount":0,"publisher":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2854#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-4.jpeg","articleSection":["Noma Da Kiwo"],"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2854#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2854","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2854","name":"Yadda Ake Kiwon Kifi a Sau\u0199a\u0199e","isPartOf":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2854#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2854#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-4.jpeg","datePublished":"2024-12-18T19:35:04+00:00","dateModified":"2024-12-23T18:06:54+00:00","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2854#breadcrumb"},"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2854"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2854#primaryimage","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-4.jpeg","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-4.jpeg","width":500,"height":419},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2854#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/taskarnasaba.com\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Yadda Ake Kiwon Kifi a Sau\u0199a\u0199e"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/","name":"Taskar Nasaba","description":"","publisher":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization"},"potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-US"},{"@type":"Organization","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization","name":"Taskar Nasaba","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/","logo":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png","width":343,"height":345,"caption":"Taskar Nasaba"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/"}},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753","name":"Salahuddeen Muhammad","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/image\/","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg","caption":"Salahuddeen Muhammad"},"description":"\u018aanjarida, marubuci, mai manufar bun\u0199asa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.","sameAs":["https:\/\/taskarnasaba.com"],"url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?author=1"}]}},"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/images-4.jpeg","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2854","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=2854"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2854\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2864,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2854\/revisions\/2864"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/2848"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=2854"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=2854"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=2854"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}