{"id":2872,"date":"2024-12-23T13:39:31","date_gmt":"2024-12-23T13:39:31","guid":{"rendered":"https:\/\/taskarnasaba.com.ng\/?p=2872"},"modified":"2024-12-25T01:32:25","modified_gmt":"2024-12-25T01:32:25","slug":"tatsuniya-%c6%99arya-fure-take-ba-%c6%b4a%c6%b4a","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2872","title":{"rendered":"Tatsuniya: \u0198arya Fure take ba \u01b3a\u01b4a"},"content":{"rendered":"\n<p><strong>Ga ta nan, ga ta nanku<\/strong>! <\/p>\n\n\n\n<p>An ce wata mata a wani \u0199aramin \u0198auye ta jima tare da mijinta amma ba su sami haihuwa ba. Sun nemi maganin samun haihuwa, amma ba su sami biyan bu\u0199ata ba, sai suka yi ha\u0199uri.<\/p>\n\n\n\n<p>Ana nan, wata rana matar ta je Gona ta na Noma, sai ta ji kukan Yaro a gindin wata Bishiya. Da ta matsa kusa, sai ta ga wani Jariri a cikin tsumma. Sai ta \u0257auke shi ta goya, ta kuma \u0257auki Fartanyarta, ta koma Gida.<\/p>\n\n\n\n<p>Da mijinta ya dawo sai ta \u0257auko Jariri ta kawo masa, ta ce da shi: &#8220;Da ma ina da kwantaccen ciki, shi ne yanzu ka ga na haihu a Gona.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>Mijin ya yi shiru, ya na tunani, sai ya ce: \u201cAn ya kuwa ke ce kika haifi jaririn nan?&#8221; Ta dage cewa ita ce ta haife shi. Sai ya ce: &#8220;To mun gode wa Allah.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>Suka ci gaba da renon Yaro, amma duk sanda suka je Gona da shi sai ya yi kuka ya hana su aiki. Da matar ta ga haka na faruwa kullum, sai ta je cikin danginta ta \u0257auko \u0199anwarta domin ta ri\u0199a renonsa idan sun tafi Gona ita da mijinta.<\/p>\n\n\n\n<p>Wata rana mai gida da matar suka tafi Gona suka bar yaro a hannun mai reno, mai renon ta ga yaron ya riki\u0257a, ya zama babban mutum, sai ya yi aman \u01b4an mata 12. Ya bu\u0257e Rumbu, kuma ya fito da Hatsi suka sussuka suka ni\u0199a, sai ya kwashe garin ya barbaza shi a tsakar gidan; sai kuma ya ha\u0257iye \u01b4an matan, ya riki\u0257a ya koma \u0199aramin Yaro.<\/p>\n\n\n\n<p>Can da mai gida da matar suka dawo, suka ga \u0253arnar da aka yi musu, sai matar ta kama \u0199anwarta da duka wai ta yi mata \u0253arna. Yarinya ta ce ba ita ba ce, yaron ne. Sai yayarta ta ce: &#8220;Ta ya ya wannan \u0199aramin yaro zai bu\u0257e Rumbu, ya \u0257ebo Hatsi, ya sussuka shi, ya ni\u0199e ya zubar?&#8221; Ba su dai yarda da bayanin yarinyar ba.<\/p>\n\n\n\n<p>Haka dai, kullum idan sun fita sai ya yi wata \u0253arna, kuma sai matar nan ta doka \u0199anwarta.<\/p>\n\n\n\n<p>Wata rana matar ta kama \u0199anwarta ta na duka a kan \u0253arnar da yaron ya yi, sai wata tsohuwa ta kira ta ta ce mata: &#8220;Wannan duka da kike yi wa \u0199anwarki fa ba ta da laifi. Wannan yaron da yake gidanku ba ki sani ba tsohon Aljani ne kika kawo gidan.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>Mamaki da tsoro suka kama matar, amma sai tsohuwar ta ci gaba da bayaninta ta na cewa: &#8220;Idan kina so ki tabbatar, gobe ka da ku je Gona; bayan gari ya waye ku fita ku ce za ku je Gona; sai ku zo ku \u0253uya a gidana, za ku ga komai da idanunku.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>Sai ta ce: &#8220;To. Allah ya nuna mana goben.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>Da gari ya waye mijin da matar suka shirya, kamar za su je gona. Da suka fita sai suka \u0253uya a gidan tsohuwa. Bayan wani \u0257an lokaci sai suka ga yaron ya riki\u0257a, ya zama babba, su na gani ya bu\u0257e bakinsa ya yi aman \u01b4an mata 10, nan da nan ya hau Rumbu ya bu\u0257e ya \u0257ebo Hatsi, nan take \u01b4an matan suka sussuka hatsin, suka ni\u0199e shi, suka shiga watsar da garin a cikin Gida, su na yi su na Wa\u0199a.<\/p>\n\n\n\n<p>Da matar ta ga abin da yaron ya yi sai ta gaya wa mijinta gaskiya da cewa, ai da ma ba \u0257anta ba ne, kuma a Gona ta tsince shi. Sai mijin ya ce: &#8220;Tun farko da ma na yi shakka, ga shi ta tabbata \u0199arya kika yi mini.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>Sai ta fa\u0257i ta na kuka, ta shiga hurwa ta na ba shi ha\u0199uri, ta ce: &#8220;Ai da wannan a, gara mu zauna babu.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>Da tsohuwa ta ga abin da ke gudana tsakanin mijin da matar, sai ta ce: &#8220;Yanzu abin da za ku yi domin ku rabu da wannan masifa shi ne, ku samo Akuya da \u0198wayaye guda bakwai, sai ku ce za ku je ganin Gida. Bayan kun kama hanya kun shiga Daji, sai ku sami gindin Tsamiya ku ce za ku huta. Idan kun shimfi\u0257e yaron sai ku ajiye \u0198wayaye nan bakwai a gefensa ku \u0257aure Akuyar a jikin tsamiyar. Can sai ku ce kun yi mantuwa.&#8221; Ta ce da su: &#8220;Ku na jin abin da nake fa\u0257a?&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>Suka ce: &#8220;Muna ji sarai.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>Ta ci gaba da ce wa matar: &#8220;Ki ce za ki koma Gida ki \u0257auko abin da kika manta. Daga nan ka da ki dawo. Jim ka\u0257an shi ma mijinki sai ya ce zai bi sawunki saboda kin jima. To idan kun tafi ka da ku koma; da zarar kun jima zai tashi ya tafi abinsa.&#8221; Sai suka yi wa tsohuwa godiya suka koma Gida.<\/p>\n\n\n\n<p>Da gari ya waye sai matar nan da mijinta suka ce za su je ganin gida, sai suka samo duk abubuwan da tsohuwa ta ce su nemo. Da lokacin tafiya ya yi sai suka kama hanya har suka isa gindin wata tsamiya, sai mijin ya ce ya kamata su huta a nan; suka \u0257aure Akuya a gindin Bishiya suka zauna, can sai mijin ya ce: &#8220;Kash!, mun yi mantuwa.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>Sai matar ta ce: &#8220;To bari in je in \u0257auko.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>Mijin ya ce: &#8220;To gara ki yi sauri.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>Bayan matar ta tafi, sai ya ce ta da\u0257e, bari ya bi sawunta. Shi ma ya tashi ya bar wurin. Da ya yi nisa sai ya \u0253uya. Ya na nan ya na kallon gindin Tsamiya, can sai ya ga Yaro ya riki\u0257a ya zama Tsoho tukuf da sanda; sai ya sunce Akuyar, ya ri\u0199e a hannunsa; kuma ya ga ya \u0257ebi \u0198wayayen nan bakwai ya kama hanya ya shiga \u0199ungurmin daji. Da mijin nan ya ga haka sai shi ma ya juya, ya kama hanyar Gida.<\/p>\n\n\n\n<p>Kurunkus!<\/p>\n\n\n\n<p>Abubuwan da Labarin Yake Koyarwa<\/p>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Karya da ha&#8217;inci: masifu ne da ke iya \u0253ata zaman da aka da\u0257e cikin amana.<\/li>\n\n\n\n<li>Neman afuwa da lafiya: su ne ka\u0257ai ke iya magance matsala a zaman amana.<\/li>\n\n\n\n<li>Tsintacciyar mage ba ta yin kyanwa:<\/li>\n\n\n\n<li>Karya fure take, ba ta \u01b4a\u01b4a.<\/li>\n<\/ul>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Ga ta nan, ga ta nanku! An ce wata mata a wani \u0199aramin \u0198auye ta jima tare da mijinta amma ba su sami haihuwa ba. Sun nemi maganin samun haihuwa, amma ba su sami biyan bu\u0199ata ba, sai suka yi ha\u0199uri. Ana nan, wata rana matar ta je Gona ta na Noma, sai ta ji [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":2871,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"inline_featured_image":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[97],"tags":[],"class_list":["post-2872","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-rai-dangin-goro"],"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v27.0 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Tatsuniya: \u0198arya Fure take ba \u01b3a\u01b4a<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"noindex, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_US\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Tatsuniya: \u0198arya Fure take ba \u01b3a\u01b4a\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"Ga ta nan, ga ta nanku! An ce wata mata a wani \u0199aramin \u0198auye ta jima tare da mijinta amma ba su sami haihuwa ba. Sun nemi maganin samun haihuwa, amma ba su sami biyan bu\u0199ata ba, sai suka yi ha\u0199uri. Ana nan, wata rana matar ta je Gona ta na Noma, sai ta ji [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2872\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"Taskar Nasaba\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2024-12-23T13:39:31+00:00\" \/>\n<meta property=\"article:modified_time\" content=\"2024-12-25T01:32:25+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/1734959954629.jpg\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"678\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"900\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/jpeg\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Salahuddeen Muhammad\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"Salahuddeen Muhammad\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Est. reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"5 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\/\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2872#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2872\"},\"author\":{\"name\":\"Salahuddeen Muhammad\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753\"},\"headline\":\"Tatsuniya: \u0198arya Fure take ba \u01b3a\u01b4a\",\"datePublished\":\"2024-12-23T13:39:31+00:00\",\"dateModified\":\"2024-12-25T01:32:25+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2872\"},\"wordCount\":1042,\"commentCount\":0,\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2872#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/1734959954629.jpg\",\"articleSection\":[\"Rai Dangin Goro\"],\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2872#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2872\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2872\",\"name\":\"Tatsuniya: \u0198arya Fure take ba \u01b3a\u01b4a\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2872#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2872#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/1734959954629.jpg\",\"datePublished\":\"2024-12-23T13:39:31+00:00\",\"dateModified\":\"2024-12-25T01:32:25+00:00\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2872#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2872\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2872#primaryimage\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/1734959954629.jpg\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/1734959954629.jpg\",\"width\":678,\"height\":900},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2872#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Tatsuniya: \u0198arya Fure take ba \u01b3a\u01b4a\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"description\":\"\",\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\"},\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-US\"},{\"@type\":\"Organization\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\",\"logo\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png\",\"width\":343,\"height\":345,\"caption\":\"Taskar Nasaba\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/\"}},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753\",\"name\":\"Salahuddeen Muhammad\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg\",\"caption\":\"Salahuddeen Muhammad\"},\"description\":\"\u018aanjarida, marubuci, mai manufar bun\u0199asa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.\",\"sameAs\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\"],\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?author=1\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Tatsuniya: \u0198arya Fure take ba \u01b3a\u01b4a","robots":{"index":"noindex","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"og_locale":"en_US","og_type":"article","og_title":"Tatsuniya: \u0198arya Fure take ba \u01b3a\u01b4a","og_description":"Ga ta nan, ga ta nanku! An ce wata mata a wani \u0199aramin \u0198auye ta jima tare da mijinta amma ba su sami haihuwa ba. Sun nemi maganin samun haihuwa, amma ba su sami biyan bu\u0199ata ba, sai suka yi ha\u0199uri. Ana nan, wata rana matar ta je Gona ta na Noma, sai ta ji [&hellip;]","og_url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2872","og_site_name":"Taskar Nasaba","article_published_time":"2024-12-23T13:39:31+00:00","article_modified_time":"2024-12-25T01:32:25+00:00","og_image":[{"width":678,"height":900,"url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/1734959954629.jpg","type":"image\/jpeg"}],"author":"Salahuddeen Muhammad","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"Salahuddeen Muhammad","Est. reading time":"5 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2872#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2872"},"author":{"name":"Salahuddeen Muhammad","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753"},"headline":"Tatsuniya: \u0198arya Fure take ba \u01b3a\u01b4a","datePublished":"2024-12-23T13:39:31+00:00","dateModified":"2024-12-25T01:32:25+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2872"},"wordCount":1042,"commentCount":0,"publisher":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2872#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/1734959954629.jpg","articleSection":["Rai Dangin Goro"],"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2872#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2872","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2872","name":"Tatsuniya: \u0198arya Fure take ba \u01b3a\u01b4a","isPartOf":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2872#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2872#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/1734959954629.jpg","datePublished":"2024-12-23T13:39:31+00:00","dateModified":"2024-12-25T01:32:25+00:00","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2872#breadcrumb"},"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2872"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2872#primaryimage","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/1734959954629.jpg","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/1734959954629.jpg","width":678,"height":900},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2872#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/taskarnasaba.com\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Tatsuniya: \u0198arya Fure take ba \u01b3a\u01b4a"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/","name":"Taskar Nasaba","description":"","publisher":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization"},"potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-US"},{"@type":"Organization","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization","name":"Taskar Nasaba","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/","logo":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png","width":343,"height":345,"caption":"Taskar Nasaba"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/"}},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753","name":"Salahuddeen Muhammad","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/image\/","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg","caption":"Salahuddeen Muhammad"},"description":"\u018aanjarida, marubuci, mai manufar bun\u0199asa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.","sameAs":["https:\/\/taskarnasaba.com"],"url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?author=1"}]}},"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/1734959954629.jpg","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2872","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=2872"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2872\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2931,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2872\/revisions\/2931"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/2871"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=2872"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=2872"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=2872"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}