{"id":2995,"date":"2024-12-30T00:16:06","date_gmt":"2024-12-30T00:16:06","guid":{"rendered":"https:\/\/taskarnasaba.com.ng\/?p=2995"},"modified":"2024-12-30T12:25:16","modified_gmt":"2024-12-30T12:25:16","slug":"wanne-firauna-ne-ya-yi-rayuwa-da-annabi-musa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2995","title":{"rendered":"Wanne Fir&#8217;auna ne ya yi Rayuwa da Annabi Musa?"},"content":{"rendered":"\n<p><strong>Daga: Wael Gamal (BBC News Arabic) <\/strong><\/p>\n\n\n\n<p><em><strong>Labarin asalin mutanen Masar da kuma tahirinsu ya yi \u0199asa ba a jinsa har sai lokacin da aka samu \u0253ullar Yahudawan gargajiya da ke zaune a \u0198asar Masar, wa\u0257anda aka ambata a littafin Injila, babin ficewar Banu Isra&#8217;ila daga Masar, da kuma wasu Ayoyin Al-kur&#8217;ani mai girma.<\/strong><\/em><br \/><br \/>Littattafan addini na baya su ma ba su ambato sunan wannan &#8220;Fir&#8217;aunan&#8221; ba, wanda ya mulki Masar kuma ya yi rayuwa da Annabi Musa Alaihissalam.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"bbc-1y32vyc e17g058b0\">Wannan ya janyo wasu malamai da ke da sha&#8217;awar bibiyar tarihin mutanen Masar tattara duka bayanan da tarihi ya tanada domin warware dambarwar sanin Fir&#8217;aunan da kuma gano shaidun sanin da za su warware ta\u0199addamar da ke tsakaninsu.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img fetchpriority=\"high\" decoding=\"async\" width=\"720\" height=\"405\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_17354094963143199171290165928138.png\" alt=\"\" class=\"wp-image-2994\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_17354094963143199171290165928138.png 720w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_17354094963143199171290165928138-300x169.png 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_17354094963143199171290165928138-600x338.png 600w\" sizes=\"(max-width: 720px) 100vw, 720px\" \/><figcaption class=\"wp-element-caption\"><strong>Gawar sarki Ramesses II, (c. 1297-1213 BC). <\/strong><\/figcaption><\/figure>\n\n\n\n<p class=\"bbc-1y32vyc e17g058b0\">A 1976, aka kai gawar Sarki Ramses na biyu Filin Jirgin Bourget da ke Paris babban birnin Faransa, a wani Jirgin Sojin Faransa aka kai Gidan Tarihi na Breguet.<\/p>\n\n\n\n<p>An yi wani taron biki akan gawar, wanda tawagar Shugaban Faransa na lokacin da Shugaban sojojinsu da wakilin Masar a Faransa da sauran mutane suka halarta.<br \/><br \/>An yi ka\u0257e-ka\u0257en Soji gabanin a ajiye gawar a Gidan Tarihi, da ke tsakiyar babban birnin \u0198asar, a wani shiri da ake yi na killace gawar da dawo da ita kan ganiyarta da wasu masana kimiyyar Faransa za su yi saboda cutukan da ake tsoron zai shafe su.<\/p>\n\n\n\n<div class=\"wp-block-media-text is-stacked-on-mobile\"><figure class=\"wp-block-media-text__media\"><img decoding=\"async\" width=\"300\" height=\"203\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_17354095418105050693188547384771-300x203.png\" alt=\"\" class=\"wp-image-2981 size-full\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_17354095418105050693188547384771-300x203.png 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_17354095418105050693188547384771-600x406.png 600w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_17354095418105050693188547384771.png 720w\" sizes=\"(max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/figure><div class=\"wp-block-media-text__content\">\n<p><strong>Marigayi Shugaban \u0198asar Masar Mohamed Anwar Sadat, lokacin da yake le\u0199a gawar Sarki Ramses na biyu.<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Cikin watanni bakwai na lokacin daga 26 ga watan Satumbar 1976 zuwa 10 ga watan Mayun 1977 birnin Paris ya ri\u0199a kar\u0253ar manyan \u0253aki &#8220;kamar yadda fitacciyar masaniyar kimiyyar nan Madame Christiane de Roche Noblecourt ta bayyana a littafinta na &#8220;Ramsey na biyu.<br \/><br \/>Labarin ya \u0199ara da cewa an ware wani dogon \u0257aki domin gawar ta fir&#8217;auna kawai.<br \/><br \/>Domin gane \u0199wayoyin cutar da suka shafi gawar Masaraucin, sannan a samar da wani tsari da za a kiyaye gawar, shugaban Gidan Tarihin ya samar da masu taimaka masa kimanin 120, wadanda duk suka yi al\u0199awarin za su yi aikin kyauta, cikin har da masu bincike masana kimiyya 63 a mabambantan fannoni.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Me ya sa aka kai Gawar Ramses na Biyu Birnin Paris?<\/strong><\/p>\n\n\n\n<div class=\"wp-block-media-text is-stacked-on-mobile\"><figure class=\"wp-block-media-text__media\"><img decoding=\"async\" width=\"300\" height=\"169\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_17354098756378415735180499538822-300x169.png\" alt=\"\" class=\"wp-image-2982 size-full\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_17354098756378415735180499538822-300x169.png 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_17354098756378415735180499538822-600x338.png 600w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_17354098756378415735180499538822.png 720w\" sizes=\"(max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/figure><div class=\"wp-block-media-text__content\">\n<p><strong>Madame Alice Saunier-Cit\u00e9, tare da tawagar shugaban Faransa na lokacin Val\u00e9ry Giscard d&#8217;Estaing, ta na gabatar da bayani yayin bikin gawar ta Fir&#8217;auna ko kuma Sarki Ramesses na biyu a &#8220;Bourges&#8221; da ke Rukunin Gidajen Soji tare da fitacciyar Madame Christiane de Roche Noblecourt daga hagu a tsaye.<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Akwai manufofi uku cikin aika Gawar Sarki Ramses na biyu zuwa birnin Paris. Na farko a magance wata cuta da ta kama \u0198afar Gawar, da Dunduniyarta da Kafa\u0257arta ta dama da \u0199asan Cibiyar Gawar.<br \/><br \/>Na biyu kuma a koyi wani \u0253oyayyan sirri na yadda ake ajiye gawarwakin shugabannin Masar, sannan a gano yanayin da Gawar take a yanzu, sannan a gano da wa\u0257anne irin sinadarai ake iya \u0253oye gawarwakin.<br \/><br \/>Na uku kuma shi ne yun\u0199urin gano musabbabin mutuwar sarkin: Shin mutuwa ce ta gaskiya saboda tsufa ko kuma mutuwa ce dalilin sar\u0199ewar numfashi saboda nutsewa da ya yi a ruwa?<\/p>\n\n\n\n<div class=\"wp-block-media-text is-stacked-on-mobile\"><figure class=\"wp-block-media-text__media\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"300\" height=\"169\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_17354101836264878055874457117432-300x169.png\" alt=\"\" class=\"wp-image-2983 size-full\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_17354101836264878055874457117432-300x169.png 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_17354101836264878055874457117432-600x338.png 600w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_17354101836264878055874457117432.png 720w\" sizes=\"(max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/figure><div class=\"wp-block-media-text__content\">\n<p><strong>Dakarun tsaron Faransa yayin bikin tarbar gawar Sarki Ramses na biyu a Paris.<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Masana kimiyyar na aikin gano \u0199wayoyin halitta na ciki da wajen gawar, kamar \u0181argo da Gashi da \u0198irji da kuma gefen ha\u0199ar\u0199arin gawar, sannan a yi wasu gwaje-gwaje masu yawa kan gawar.<\/p>\n\n\n\n<div class=\"wp-block-media-text is-stacked-on-mobile\"><figure class=\"wp-block-media-text__media\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"720\" height=\"475\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_17354103464335311821036089999432.png\" class=\"wp-image-3073 size-full\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_17354103464335311821036089999432.png 720w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_17354103464335311821036089999432-300x198.png 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_17354103464335311821036089999432-600x396.png 600w\" sizes=\"(max-width: 720px) 100vw, 720px\" \/><\/figure><div class=\"wp-block-media-text__content\">\n<p><strong>Gwamnatin Faransa ta samar da wani \u018aakin Gwaji da aka cika da kayan aikin na zamani a gidan tarihin domin nazari kan gawar Sarki Ramses na biyu.<\/strong><\/p>\n<\/div><\/div>\n\n\n\n<p>Tawagar na nazari kan duka wasu sassan gawar, ciki da waje, \u0198warangwal \u0257in gawar da sauran \u0199asusuwanta, ta hanyar \u0257aukar hotonta sannan suka raba gawar zuwa kashi shida da za su yi nazari a kai.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Ra\u0257a\u0257i da \u0181acin Rai Kan Sarki Ramses II<\/strong><\/p>\n\n\n\n<div class=\"wp-block-media-text is-stacked-on-mobile\"><figure class=\"wp-block-media-text__media\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"720\" height=\"479\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_17354106281808470723729534911912.png\" alt=\"\" class=\"wp-image-3074 size-full\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_17354106281808470723729534911912.png 720w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_17354106281808470723729534911912-300x200.png 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_17354106281808470723729534911912-600x399.png 600w\" sizes=\"(max-width: 720px) 100vw, 720px\" \/><\/figure><div class=\"wp-block-media-text__content\">\n<p><strong>Hoton gawar lokacin da za a duba yadda za a farfa\u0257o da jikin gawarsa a Paris. <\/strong><\/p>\n<\/div><\/div>\n<\/div><\/div>\n<\/div><\/div>\n<\/div><\/div>\n\n\n\n<p>Wani bincike kan \u0199wayoyin cutuka da aka yi a \u0253angaren \u0198afa da Dunduniyar gawar da kuma Kafa\u0257arta ta dama, ya nuna wasu \u0199wayoyin halitta sun kama gawar saboda sauyin da aka samu na yanayi tun lokacin da aka gano gawar a Deir el-Bahari &#8211; Wanda masanin kimiyya Faransa Gaston Maspero ya gano a 1881, sannan kuma aka warware na\u0257in da aka yi wa gawar a ranar 1 ga watan Janairun 1886.<br \/><br \/>Binciken masana kimiyyar ya nuna yadda \u0199ashin sama da \u0199asan ha\u0253a ke murmushewa sakamakon taruwar ruwa a wajen. Hoton masana kimiyya ya nuna yadda aka samu zaman ruwa na zama da shekaru a \u0253angaren ha\u0199ora.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"bbc-1y32vyc e17g058b0\">Sai dai binciken bai nuna an ta\u0253a yi wa sarkin aikin ha\u0199ori ba lokacin ya na raye.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"bbc-1y32vyc e17g058b0\">Bincike ya nuna kumburi a wajen ha\u0199ar\u0199arin gawar da bayan hannunta, jijiyoyin cinya da \u0199afa, \u0199ashin \u0199ugun gawar duka ya lalace ga kuma murmushewar gashin kai da yake fama da ita.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"bbc-1y32vyc e17g058b0\">Kumburin da aka gano bayan mutuwarsa an ce ya samo asali ne shekaru gabanin ya mutu a \u0199arshen shekarun rayuwarsa.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"bbc-1y32vyc e17g058b0\">Duk wa\u0257annan na nuna cewa lafiyar fir&#8217;aunan ta ta\u0253ar\u0253are, inda ya ri\u0199a fama da cutar sanyin \u0199ashi a shekaru ashirin na \u0199arshen rayuwarsa, kamar yadda nazarin Nabelcore ya nuna.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Fir&#8217;aunan da ya fi Kowanne a Tarihin Masar<\/strong><\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"720\" height=\"479\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_17354110267575641679596602378290.png\" alt=\"\" class=\"wp-image-2986\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_17354110267575641679596602378290.png 720w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_17354110267575641679596602378290-300x200.png 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_17354110267575641679596602378290-600x399.png 600w\" sizes=\"(max-width: 720px) 100vw, 720px\" \/><\/figure>\n\n\n\n<p>Sarki Ramses na biyu ana masa kallon fir&#8217;auna mafi \u0257aukaka a tarihin Masar, kuma \u0257aya daga cikin mafiya \u0257aukaka tsakanin sarakunan Duniya.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"bbc-1y32vyc e17g058b0\">Ya na \u0257aya daga cikin sarakuna \u0199alilan da suka yi mulkin dogon zamani, inda ake cewa ya kai shekaru 67 ya na jagoranci.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"bbc-1y32vyc e17g058b0\">Ya na da \u01b4a\u01b4a da dama kimanin 52 Maza ne 32 kuma mata ne, kuma shi ne mijin fitacciyar macen nan Sarauniya Nefertari.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"bbc-1y32vyc e17g058b0\">Ya sa mutane sun gina mutum-mutumi da hannu a lokacin mulkinsa masu nauyin ton dubu, yanzu su na nan a wajen bautar Ramesseum bayan fa\u0257uwar da suka yi a baya saboda girgizar \u0199asa.<\/p>\n\n\n\n<div class=\"wp-block-media-text is-stacked-on-mobile\"><figure class=\"wp-block-media-text__media\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"720\" height=\"405\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_17354113122126786666170097937360.png\" alt=\"\" class=\"wp-image-2987 size-full\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_17354113122126786666170097937360.png 720w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_17354113122126786666170097937360-300x169.png 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_17354113122126786666170097937360-600x338.png 600w\" sizes=\"(max-width: 720px) 100vw, 720px\" \/><\/figure><div class=\"wp-block-media-text__content\">\n<p><strong>Majami&#8217;ar Abu Simble da Sarki Ramses na biyu ya gina a nesa da kudancin Masar.<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Sarki Ramses na biyu ya \u0257are kujerar iko ne bayan mutuwar mahaifinsa, Sarki Seti na \u0257aya. Wasu rubutu da aka gani a majami&#8217;ar mahaifinsa a Abydos sun nuna Sarki Seti na \u0257aya ya bai wa \u0257ansa Sarki Ramses na biyu iko mai yawa tun ya na kan mulki.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Shin Ramses na biyu shi ne Fir&#8217;aunan da aka Fa\u0257a a Littafin Injila da Al-\u0198ur&#8217;ani?<\/strong><\/p>\n\n\n\n<div class=\"wp-block-media-text is-stacked-on-mobile\"><figure class=\"wp-block-media-text__media\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"720\" height=\"405\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_17354115203305802267878041698596.png\" alt=\"\" class=\"wp-image-2988 size-full\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_17354115203305802267878041698596.png 720w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_17354115203305802267878041698596-300x169.png 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_17354115203305802267878041698596-600x338.png 600w\" sizes=\"(max-width: 720px) 100vw, 720px\" \/><\/figure><div class=\"wp-block-media-text__content\">\n<p><strong>Sarki Ramses na biyu shi ne sarki guda da ya bar bajintarsa a ko&#8217;ina cikin Masar.<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"bbc-1y32vyc e17g058b0\">Malaman tarihin da ke bibiyar tarihin Masar sun ta bayyana mabambantan ra&#8217;ayi kan wannan batu.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"bbc-1y32vyc e17g058b0\">Wasu daga cikinsu, ba tare da kafa hujja da wata shaida ta masana kufai ko tarihi ba, sun yi amannar cewa banu Isra&#8217;ila wadda aka ambata a cikin ayoyin Injila da kuma Al\u0199ur&#8217;ani ta faru ne a zamanin sarakunan Huksus wa\u0257anda suka mulki Masar.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"bbc-1y32vyc e17g058b0\">Wasu ra&#8217;ayoyin kuma sun ce, sun rayu ne yayin Daular Masar ta 18, kamar yadda malaman tarihin Masar suka bayyana, musamman lokacin sarki Thutmose na uku.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"bbc-1y32vyc e17g058b0\">Wasu sun ce, an yi Banu Isra&#8217;ila lokacin Sarki Amenhotep na biyu. Yayin da ra&#8217;ayi na hu\u0257u suka ce sun yi amannar ya faru ne lokacin Sarki Amenhotep na uku.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"bbc-1y32vyc e17g058b0\">Wasu masu tarihin sun wuce gaba inda suka ce \u0199issar banu Isra&#8217;ila ta faru ne bayan mutuwar Sarki Amanhoteo na hu\u0257u &#8220;Akhenaten,&#8221; amma ra&#8217;ayin da ya fi zama mafi kar\u0253uwa a tsakanin mutane shi ne labarin Banu Isra&#8217;ila ya faru ne lokacin Sarki Ramses na biyu, kuma shi ne ra&#8217;ayin da masu shirya fim na duniya da sauran marubuta suka fi nunawa, irin shi aka nuna a shahararren fim \u0257in nan &#8220;The Ten Commandments,&#8221; wanda aka shirya a 1956 wanda Cecil B. Demille ya ba da umarni, a cikin fim \u0257in akwai \u0257an Amurkan nan Charlotte Heston (a matsayin Annabi Musa) da kuma Yul Brynner (a matsayin Fir&#8217;auna).<\/p>\n\n\n\n<div class=\"wp-block-media-text is-stacked-on-mobile\"><figure class=\"wp-block-media-text__media\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"720\" height=\"915\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_1735411853492996628253194582790.png\" alt=\"\" class=\"wp-image-2989 size-full\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_1735411853492996628253194582790.png 720w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_1735411853492996628253194582790-236x300.png 236w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_1735411853492996628253194582790-600x763.png 600w\" sizes=\"(max-width: 720px) 100vw, 720px\" \/><\/figure><div class=\"wp-block-media-text__content\">\n<p><strong>Yul Brynner a matsayin Sarki Ramesses na biyu a 1956 a fim \u0257in &#8220;The Ten Commandments.&#8221;<\/strong><\/p>\n<\/div><\/div>\n<\/div><\/div>\n<\/div><\/div>\n\n\n\n<p class=\"bbc-1y32vyc e17g058b0\">Wata marubuciya Noblecore ta ce, &#8220;Ko shakka babu zai fi dacewa a ce wannan Kissa ta faru ne tsakanin mulkin Fir&#8217;aunoni tsakanin shekara ta 10 zuwa ta 18, kamar yadda bincikenta ya nuna.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"bbc-1y32vyc e17g058b0\">&#8220;Saboda babu wasu takardun shaida daga Masar da suka yi nuni kan shekarun da lamarin ya faru.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"bbc-1y32vyc e17g058b0\">&#8220;Idan har muka dage sai mun fito da matsalolin Kissar domin mu bayyana lokacin da lamarin ya faru ba za mu iya ba, saboda akwai abubuwan da tarihi bai bayyana ba.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"bbc-1y32vyc e17g058b0\">Sunan Musa (yana nufin haihuwa) tabbas asalinsa na Misrawa ne, kuma ya yi daidai da alamun ga\u0253a ta biyu da ta uku ta sunan Ramesses.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"bbc-1y32vyc e17g058b0\">Malamar nan ta tarihi ta Faransa ta ware wata babu guda na gudun hijirar Banu Isra&#8217;ila aka bugata a littafin da Nobelcore ta wallafa, inda suka ce \u0198issar ta faru a \u0199arnin mulkinsu na 18 kafin haihuwar Annabi Isa.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"bbc-1y32vyc e17g058b0\">Ta na cewa: &#8220;Musa ya samu kariya ta musamman daga Fir&#8217;auna, kuma Sarki Horemheb wanda rikicin Banu Isra&#8217;ila ya dabaibaye.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"bbc-1y32vyc e17g058b0\">Lokacin da Musa ya kammala karatunsa sai ya koma cikin danginsa.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"bbc-1y32vyc e17g058b0\">A wannan lokacin Sarki Seti na \u0257aya ya gina wata madatsar ruwa a Delta, sannan ya gina fadarsa a Qantir wadda ta zama mazaunin Ramses na biyu.<\/p>\n\n\n\n<div class=\"wp-block-media-text is-stacked-on-mobile\"><figure class=\"wp-block-media-text__media\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"720\" height=\"385\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_17354120938781840671677892678681.png\" alt=\"\" class=\"wp-image-2990 size-full\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_17354120938781840671677892678681.png 720w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_17354120938781840671677892678681-300x160.png 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_17354120938781840671677892678681-600x321.png 600w\" sizes=\"(max-width: 720px) 100vw, 720px\" \/><\/figure><div class=\"wp-block-media-text__content\">\n<p><strong>Hoton zanen da ke nuna dakarun Fir&#8217;auna na nutsewa a ruwa lokacin hijirar Banu Isra&#8217;ila.<\/strong><\/p>\n<\/div><\/div>\n\n\n\n<p class=\"bbc-1y32vyc e17g058b0\">Musa ya cewa, Fira&#8217;auna ya zo su yi tafiya ta tsawon kwana uku a cikin sahara a matsayin sadaukarwa. Fir&#8217;auna ya \u0199i amsa kiran sai rikici ya \u0253arke.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tsaba da \u0198asa<\/strong><\/p>\n\n\n\n<div class=\"wp-block-media-text is-stacked-on-mobile\"><figure class=\"wp-block-media-text__media\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"720\" height=\"721\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_17354121269152253890979975503658.png\" alt=\"\" class=\"wp-image-3061 size-full\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_17354121269152253890979975503658.png 720w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_17354121269152253890979975503658-300x300.png 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_17354121269152253890979975503658-150x150.png 150w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_17354121269152253890979975503658-100x100.png 100w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_17354121269152253890979975503658-600x601.png 600w\" sizes=\"(max-width: 720px) 100vw, 720px\" \/><\/figure><div class=\"wp-block-media-text__content\">\n<p><strong>Wani \u0199aton zanen Sarki Ramses na biyu a jikin bangon majami&#8217;ar Abu Simbel da ke Kudancin Masar.<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"bbc-1y32vyc e17g058b0\">Wani bincikenta Nobelcore ta tattauna kan wani abu da aka gano ya kuma ja hankalin wasu mutane, wanda gawar Ramesses na biyu an samu wata shaida jikinta da za ta taimaka wajen tabbatar da abin da masana tarihi suka yi hasashe cewa, ajiye gawar na tsawon lokaci ya faru ne a yankin arewacin babban birnin.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"bbc-1y32vyc e17g058b0\">Ta ce &#8220;Mun san cewa an alkince gawar Ramesses na biyu ne a Arewacin babban birnin Masar. \u0181ur\u0253ushin \u0199asar da aka samu mai kama da ta\u0253o ta tabbatar mana da bayanan da muka tattara, wadda ta yi daidai da inda aka na\u0257e shi yankin Delta da ke nesa da kogin Nilu.<\/p>\n\n\n\n<div class=\"wp-block-media-text is-stacked-on-mobile\"><figure class=\"wp-block-media-text__media\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"664\" height=\"1006\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_17354121656843368893270862723498.png\" alt=\"\" class=\"wp-image-2992 size-full\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_17354121656843368893270862723498.png 664w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_17354121656843368893270862723498-198x300.png 198w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/watermark_17354121656843368893270862723498-600x909.png 600w\" sizes=\"(max-width: 664px) 100vw, 664px\" \/><\/figure><div class=\"wp-block-media-text__content\">\n<p><strong>Ana iya ganin fuskar gawar Fir&#8217;auna da wani \u0253ur\u0253ushi na gashinsa.<\/strong><\/p>\n<\/div><\/div>\n<\/div><\/div>\n\n\n\n<p>A cikin wani rahotonta kan tsabar \u0199asa da aka gani kan gawar, wanda ta yi wa suna da &#8220;Gawar Ramses na biyu,&#8221; Yar \u0199asar Farasa Josette Tournec ta nuna cewa, sun yi kama da \u0199asar da ke birnin Luxor na Masar, kuma \u0199asar ta shiga jikin gawar ne lokacin da ake yun\u0199urin sauya mata sabon wuri a Deir el-Bahari a \u0199arni na 20 na Daularsu.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga: Wael Gamal (BBC News Arabic) Labarin asalin mutanen Masar da kuma tahirinsu ya yi \u0199asa ba a jinsa har sai lokacin da aka samu \u0253ullar Yahudawan gargajiya da ke zaune a \u0198asar Masar, wa\u0257anda aka ambata a littafin Injila, babin ficewar Banu Isra&#8217;ila daga Masar, da kuma wasu Ayoyin Al-kur&#8217;ani mai girma. Littattafan addini [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":2993,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"inline_featured_image":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[88],"tags":[],"class_list":["post-2995","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-tarihi"],"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v27.0 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Wanne Fir&#039;auna ne ya yi Rayuwa da Annabi Musa?<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"noindex, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_US\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Wanne Fir&#039;auna ne ya yi Rayuwa da Annabi Musa?\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"Daga: Wael Gamal (BBC News Arabic) Labarin asalin mutanen Masar da kuma tahirinsu ya yi \u0199asa ba a jinsa har sai lokacin da aka samu \u0253ullar Yahudawan gargajiya da ke zaune a \u0198asar Masar, wa\u0257anda aka ambata a littafin Injila, babin ficewar Banu Isra&#8217;ila daga Masar, da kuma wasu Ayoyin Al-kur&#8217;ani mai girma. Littattafan addini [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2995\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"Taskar Nasaba\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2024-12-30T00:16:06+00:00\" \/>\n<meta property=\"article:modified_time\" content=\"2024-12-30T12:25:16+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/Watermark_1735409496314.jpg\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"720\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"405\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/jpeg\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Taskar Nasaba\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"Taskar Nasaba\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Est. reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"9 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\/\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2995#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2995\"},\"author\":{\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/50c6fe8b25398ccbaf7fd94dee1c8456\"},\"headline\":\"Wanne Fir&#8217;auna ne ya yi Rayuwa da Annabi Musa?\",\"datePublished\":\"2024-12-30T00:16:06+00:00\",\"dateModified\":\"2024-12-30T12:25:16+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2995\"},\"wordCount\":1807,\"commentCount\":0,\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2995#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/Watermark_1735409496314.jpg\",\"articleSection\":[\"Tarihi\"],\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2995#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2995\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2995\",\"name\":\"Wanne Fir'auna ne ya yi Rayuwa da Annabi Musa?\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2995#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2995#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/Watermark_1735409496314.jpg\",\"datePublished\":\"2024-12-30T00:16:06+00:00\",\"dateModified\":\"2024-12-30T12:25:16+00:00\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2995#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2995\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2995#primaryimage\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/Watermark_1735409496314.jpg\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/Watermark_1735409496314.jpg\",\"width\":720,\"height\":405},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2995#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Wanne Fir&#8217;auna ne ya yi Rayuwa da Annabi Musa?\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"description\":\"\",\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\"},\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-US\"},{\"@type\":\"Organization\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\",\"logo\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png\",\"width\":343,\"height\":345,\"caption\":\"Taskar Nasaba\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/\"}},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/50c6fe8b25398ccbaf7fd94dee1c8456\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/cropped-Taskar-Nasaba-PNG-100x100.png\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/cropped-Taskar-Nasaba-PNG-100x100.png\",\"caption\":\"Taskar Nasaba\"},\"sameAs\":[\"http:\/\/www.taskarnasaba.com.ng\"],\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?author=2\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Wanne Fir'auna ne ya yi Rayuwa da Annabi Musa?","robots":{"index":"noindex","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"og_locale":"en_US","og_type":"article","og_title":"Wanne Fir'auna ne ya yi Rayuwa da Annabi Musa?","og_description":"Daga: Wael Gamal (BBC News Arabic) Labarin asalin mutanen Masar da kuma tahirinsu ya yi \u0199asa ba a jinsa har sai lokacin da aka samu \u0253ullar Yahudawan gargajiya da ke zaune a \u0198asar Masar, wa\u0257anda aka ambata a littafin Injila, babin ficewar Banu Isra&#8217;ila daga Masar, da kuma wasu Ayoyin Al-kur&#8217;ani mai girma. Littattafan addini [&hellip;]","og_url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2995","og_site_name":"Taskar Nasaba","article_published_time":"2024-12-30T00:16:06+00:00","article_modified_time":"2024-12-30T12:25:16+00:00","og_image":[{"width":720,"height":405,"url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/Watermark_1735409496314.jpg","type":"image\/jpeg"}],"author":"Taskar Nasaba","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"Taskar Nasaba","Est. reading time":"9 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2995#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2995"},"author":{"name":"Taskar Nasaba","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/50c6fe8b25398ccbaf7fd94dee1c8456"},"headline":"Wanne Fir&#8217;auna ne ya yi Rayuwa da Annabi Musa?","datePublished":"2024-12-30T00:16:06+00:00","dateModified":"2024-12-30T12:25:16+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2995"},"wordCount":1807,"commentCount":0,"publisher":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2995#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/Watermark_1735409496314.jpg","articleSection":["Tarihi"],"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2995#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2995","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2995","name":"Wanne Fir'auna ne ya yi Rayuwa da Annabi Musa?","isPartOf":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2995#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2995#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/Watermark_1735409496314.jpg","datePublished":"2024-12-30T00:16:06+00:00","dateModified":"2024-12-30T12:25:16+00:00","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2995#breadcrumb"},"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2995"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2995#primaryimage","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/Watermark_1735409496314.jpg","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/Watermark_1735409496314.jpg","width":720,"height":405},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=2995#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/taskarnasaba.com\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Wanne Fir&#8217;auna ne ya yi Rayuwa da Annabi Musa?"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/","name":"Taskar Nasaba","description":"","publisher":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization"},"potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-US"},{"@type":"Organization","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization","name":"Taskar Nasaba","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/","logo":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png","width":343,"height":345,"caption":"Taskar Nasaba"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/"}},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/50c6fe8b25398ccbaf7fd94dee1c8456","name":"Taskar Nasaba","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/image\/","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/cropped-Taskar-Nasaba-PNG-100x100.png","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/cropped-Taskar-Nasaba-PNG-100x100.png","caption":"Taskar Nasaba"},"sameAs":["http:\/\/www.taskarnasaba.com.ng"],"url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?author=2"}]}},"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/12\/Watermark_1735409496314.jpg","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2995","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=2995"}],"version-history":[{"count":5,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2995\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3076,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2995\/revisions\/3076"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/2993"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=2995"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=2995"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=2995"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}