{"id":3080,"date":"2025-01-01T17:57:39","date_gmt":"2025-01-01T17:57:39","guid":{"rendered":"https:\/\/taskarnasaba.com.ng\/?p=3080"},"modified":"2025-01-01T17:57:39","modified_gmt":"2025-01-01T17:57:39","slug":"yau-shekaru-111-da-ha%c9%97a-najeriya-a-matsayin-dun%c6%99ulalliyar-%c6%99asa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3080","title":{"rendered":"Yau Shekaru 111 da Ha\u0257a Najeriya a Matsayin Dun\u0199ulalliyar \u0198asa"},"content":{"rendered":"\n<p><strong>A Rana mai Kamar ta Yau, 1 ga Watan Junairu aka ha\u0257a Kudanci da Arewaci a matsayin \u0198asa Najeriya (Amalgamation).<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Sir, Frederick Lugard shi ne ya taso daga \u0198asar Hong Kong ya koma Legas domin aiwatar da tunanin ofishin Mulkin Mallaka da ke Landan, inda ya yi amfanin da al\u0199alaminsa ya ha\u0257a yankunan Arewaci da Kudanci da kuma Legas suka zama \u0199asa \u0257aya mai suna Najeriya a Ranar \u0257aya ga watan Janairun shekarar 1914.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Kudi da Amfanin Gona masu Samar da Ku\u0257i<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Manoma a fa\u0257in Najeriya sun da\u0257e su na Noma Abincin da za su ci, amma da Turawan Mulkin Mallaka suka zo sai suka \u0199arfafawa Manoma guiwar Noma Amfanin Gona da za su ri\u0199a samar da Ku\u0257i domin fitar da shi zuwa Masana\u2019antun \u0198asashen Turai.<\/p>\n\n\n\n<p>Gya\u0257a da Koko da Manja da Taba da Auduga su ne suka fi daraja a lokacin. Turawan Ingila kuma sun fito da amfani da Ku\u0257i domin jin da\u0257in gudanar da harkar.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Fari da Yunwa<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>An yi fama da manyan bala\u2019o\u2019in yunwa a Najeriya lokacin Mulkin Mallaka, wa\u0257anda suka faru a shekarun 1914 da 1927 da 1942 da 1951.<\/p>\n\n\n\n<p>Hakan ya faru ne a sakamakon fari da aka yi da kuma watsi da Noman Abinci aka mayar da hankali wajen Noma Amfanin Gona mai samar da ku\u0257i kawai. Mafi munin yunwar da aka yi ita ce; \u2018\u2019Yunwar Muda\u2019\u2019 da ta mamaye yankin Arewa a tsakanin shekarar 1913 zuwa 1915.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Kafuwar Majalisa a 1922<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>An \u0199addamar da Majalisa ta farko a Najeriya a shekarar 1922 domin masu yun\u0199urin \u0199wato wa \u0198asa \u01b4anci su samu kafar Isar da matsalolinsu ga shugabannin mulkin.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Ya\u0199in Duniya na Biyu<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Da farko ba mu san dalilin da ya sanya Turawa suke ya\u0199ar junansu ba, sai a tsakanin shekarar 1940 zuwa 1945 lokacin da aka kwashi dubban matasan Najeriya da \u0199arfin-tsiya aka sanya su a Soja aka kwashe su a Jirgin Ruwa zuwa Bama domin su dakatar da \u0198asar Japan daga shiga Indiya.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Taron Tsarin Mulki a Landan<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>An gudanar da tarurruka a kan tsarin Mulki har sau uku a Landan a shekarun 1954 da 1957 a shirye-shiryen da ake yi na samar wa Najerya \u01b3ancin Kai.<\/p>\n\n\n\n<p>Sir, Ahmadu Bello, shi ne ya jagoranci wakilan yankin Arewa, Dakta Nnamdi Azikiwe kuma ya jagoranci wakilan Gabashi, shi kuma Cif Obafemi Awolawo ya jagoranci na yammacin \u0198asar nan zuwa wurin taron.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Gano Mai<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Bayan an da\u0257e ana neman Mai tun daga shekarar 1938, Kamfanin Shell sai ya gano Mai a yankin Neja Delta, inda Mai ya fara \u0253u\u0253\u0253ugowa a Rijiya ta farko a shekarar 1956 a Oloibiri da ke Jihar Ribas a halin yanzu.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Kwamitin Willink<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Taron Landan na shekarar 1957 ya amince a kafa wani kwamiti a \u0199ar\u0199ashin jagorancin tsohon Shugaban Jami\u2019ar Cambridge Harry Willink, domin ya yi nazarin tsoron da tsirarun \u0199abilu suke yi a yayin da Najeriya ta kama hanyar samun \u01b3ancin kanta, inda ya gabatar da cikakken rahoton da ya tayar da \u0199ura a karo na farko.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Samun \u01b3anci a Shekarar 1960<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Da tsakar Dare Ranar \u018aaya ga Watan Oktobar shekarar 1960 Gimbiya Alexander ta na ji, ta na gani aka sauke Tutar Ingila, wanda ke nuna cewar Mulkin Mallaka ya kawo \u0199arshen a Najeriya, inda shi kuma Firaiminista Sir, Abubakar Tafawa \u0181alewa ya zura Ido ya na kallon yadda ake \u0257aga Tutar Najeriya sama domin ta maye gurbin ta Ingila.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tsarin Mulkin Jamhuriya<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Shugabannin Jamhuriya a karo na farko sun amince a shekarar 1962, don Najeriya ya maye gurbin Sarauniyar Ingila a matsayin shugaban Najeriya, inda shugaban Jam\u2019yyar NCNC Dokta Nnamdi Azikiwe da Sarauniya ta na\u0257a shi a matsayin Gwamna Janar a shekarar 1960, ya zama Shugaban \u0198asa mara cikakken iko na farko a Ranar \u0257aya ga Watan Oktobar 1963.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Hukuncin Cin Amanar \u0198asa, 1962-1963<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>An kama Shugaban Jam&#8217;iyyar Action Group kuma jagoran \u01b4an adawa Cif Obafemi Awolawo tare da wa\u0257ansu \u01b4a\u01b4an Jam&#8217;iyyar guda 28 ana tuhumar sa da laifin yun\u0199urin kifar da Gwamnatin Tafawa \u0181alewa a shekarar 1963. Inda aka \u0257aure su, amma Gowon ya sake su a watan Agustan shekarar 1966.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Dokar Ta-\u0253aci<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Rikici ya \u0253arke a tsakanin \u0253angarori biyu na jam\u2019iyyar AG a Majalisar yankin Yammaci a watan Mayun shekarar 1962, inda magoya bayan Cif Obafemi Awolawo da Firimiya Cif Samuel Akintola suka yi ta kisan junansu. Hakan ya sanya Gwamnatin Tarayya ta ayyana dokar ta-\u0253aci a yankin.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Juyin Mulki na Farko, Janairu 1966<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Jamhuriya ta farko ta kawo \u0199arshe da \u0199arfin tsiya a shekarar 1966 lokacin da Manjo Chukwuma Nzeogwu ya jagoranci wa\u0257ansu Sojoji suka yi awon-gaba da Faraiminista Tafawa \u0181alewa da Ministan Ku\u0257i Festus Okotie-Eboh da Firimiya Ahmadu Bello da Ladoke Akintola da wa\u0257ansu Manyan Hafsoshin Soja irin su; Birgediya Zakari Maimalari da Kanar Kur Muhammad da Kanar Victor Yakubu Pam da Laftanar Kanar Abogo Largema, suka kashe su.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Dokar Mayar da Najeriya Mulukiya, May 1966<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Manjo Janar Johnson Thomas Umunnakwe Aguyi-Ironsi, wanda ya \u0199wace iko daga hannun masu Juyin Mulki ya zama Shugaban \u0198asa kuma Babban Kwamandan Rundunar Sojojin \u0198asar, ya fito da wata dokar Soja a watan Mayun 1966 da ta rushe yankunan Najeriya ta mayar da Najeriya Mulukiya mai Gwamnati a Tsakiya.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Rikicin a Raba 1966-67<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Dokar Soja da ta rushe yankuna da Ironsi ya kafa ta haifar da rikicin \u0199abilanci. Rikici ya fara \u0253arkewa ne a kasuwar Jos, nan da nan ya watsu a sauran yankunan Arewa, inda masu zanga-zanga ke kiran \u2018\u2019A raba\u2019\u2019 \u0198asar kowa ya kama gabansa.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Taron Aburi, Janairun 1967<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Gagarumin taron da aka gudanar a kan Najeriya an yi shi ne a wajen \u0198asar, inda a farkon shekarar 1967 Shugaban \u0198asar Ghana ya kar\u0253i ba\u0199uncin Majalisar \u0198oli ta Mulkin Soja da ta rabe biyu, aka gudanar da taro a Aburi ta \u0198asar Ghana domin a magance matsalolin \u0253angarorin biyu.<\/p>\n\n\n\n<p>Bayan sun dawo Najeriya kuma sai suka ci gaba da rikici dangane da shawarar da suka amince da ita a Aburi.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>\u0198ir\u0199iro Jihohi, Watan Mayu 1967<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Domin share wa \u0199ananan \u0198abilu hawayensu, Janar Gowon sai ya raba yankunan Najeriya guda hu\u0257u zuwa Jihohi 12 a Ranar 27 ga watan Mayun 1967, wanda hakan ya taka wa Gwamnan Mulkin Soja na yankin gabashi Kanar Ojukwu birki, game da burinsa.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>\u0181allewar Yankin Biafra<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>A Ranar 30 ga watan Mayun 1967 Ojukwu ya ayyana ballewar yankin gabashin kasar nan take tare da kafa kasar Biyafara mai hedkwata a Enugu. Tun da farko sai da taron dattawan yankin gabashin ya amince da yunkurin.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Ya\u0199in Basasa, 1967-1972<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Saboda kafa \u0198asar Biyafara da aka yi, ya sanya Gowon ya bayar da umarnin a nuna ba-sani, ba-sabo a yankin, wanda hakan ya haifar da Ya\u0199in Basasa da aka rasa Miliyoyin rayukan Jama\u2019a.<\/p>\n\n\n\n<p>An kawo \u0199arshen Ya\u0199in a shekarar 1970 lokacin da Ojukwu ya tsallake ya bar \u0198asar. Sojojin Biyafara sun mi\u0199a wuya, shi kuma Gowon ya ayyana cewa, babu wanda ya samu nasara kuma babu wanda aka ci galabarsa.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Mayar da Tu\u0199i Hannun Dama, Afirilu 1972<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Ranar 2 ga Afirilu 1972 da \u0199arfe 6 na safe ne ababen Hawa a Najeriya suka bar Tu\u0199i a \u0253angaren hagu suka koma amfani da \u0253angaren dama, wanda ya sanya aka kwashe shekaru Motoci masu sitiyari a dama suke \u0257auke da alamar da ke nuna cewa sitiyarinsu a dama yake.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Naira da Kobo, 1973<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Tun zamanin Mulkin Mallaka ana amfani da Ku\u0257in Fam ne da Sule da Kwabo maihuji, amma a Ranar 1 ga Janairu 1973 Kwamishinan Ku\u0257i na Tarayya Alhaji Shehu Shagari da Gwamnan Babban Bankin Najeriya Dokta Clement Isong suka fito da sabon Ku\u0257i Naira da kobo; wanda Sule yake da Kobo 10 maimakon tsohon Sule maikwabo 12.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Gara\u0253asar Odoji, 1974<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Wani Kwamitin a \u0199ar\u0199ashin jagorancin Cif Jerome Odoji, ya zauna na tsawon shekara biyu ya bayar da shawarar a \u0199ara wa Ma\u2019aikata albashinsu, saboda \u0257imbin ku\u0257in da ake samu daga Man Fetur, Gowon ba amince da shawarar kawai ya yi ba, har ma cewa ya yi a biya Ma\u2019aikata Ku\u0257in baya na shekaru biyu. Hakan ya sanya farashin kayayyaki ya yi tashin gwauron-zabi a tarihin Najeriya.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Kifar da Gwamnatin Gowon, Yuli 1975<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>An kifar da Gwamnatin Gowon a ranar 29 ga Yuli 1975, lokacin ya na halartar Taron \u0198ungiyar Ha\u0257a Kan Afirka a Kampala, \u0198asar Uganda, bayan ya kwashe shekaru tara ya na mulki.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Kashe Murtala Mohammed, Fabrairu 1976<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>A Ranar 13 ga Fabrairun 1976 ne aka ji muryar Daraktan Horar da Sojoji Motsa Jiki Kanar Bukar Suka Dimka a Rediyo ya na sanar da canjin Gwamnati, yun\u0199urin Juyin Mulkin bai yi nasara ba, amma Dimka ya kashe Shugaban Kasa Janar Murtala Mohammed.<\/p>\n\n\n\n<p>A sakamakon haka aka zartar da hukuncin kisa a kan Jami\u2019an Soja 43 da Farar Hula guda \u0257aya saboda laifin yun\u0199urin Juyin Mulki.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Sauyin \u0198ananan Hukumomi, 1976<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>A hankali Sarakunan Gargajiya su na ta rasa ikon da suke da shi a tsarin gudanar da Gwamnatin N.A da suka samu tun zamanin Mulkin Turawa. An fara rage musu iko ne a shekarar 1960, lokacin da aka \u0257auke Kotuna da \u01b4an sanda da kuma Gidajen Yari daga \u0199ar\u0199ashinsu.<\/p>\n\n\n\n<p>A shekarar 1976 kuma aka \u0199wace musu iko gaba \u0257aya, inda aka maye gurbin Gwamnatin N.A da za\u0253a\u0253\u0253un Shugabannin \u0198ananan Hukumomi.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Komawa Mulkin Farar Hula, 1979<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Tun Ranar da Gimbiya Alexander ta tsaya ta na kallo aka sauke tutar Ingila a watan Oktoba 1960, wani abu mai kama da wannan bai sake faruwa a Najeriya ba sai a Ranar 1 ga Oktobar 1979 lokacin da babban mai Shari&#8217;a na \u0198asa Atanda Fatai Williams ya rantsar da Alhaji Shehu Shagari a matsayin Shugaba mai cikakken iko na farko, inda shi kuma Shugaban Mulkin Soja Janar Olusegun Obasanjo ya ja da baya ya sara masa, wanda hakan ya nuna cewa Mulki ya tashi daga hannun Soja ya koma hannun Farar Hula.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Rikicin Maitatsine, 1980<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>An kwashe makonni biyu ana ba-ta-kashi tsakanin \u01b3ansandan kwantar da tarzoma da Almajiran Muhammadu Marwa Maitatsine, a unguwar \u01b3an Awaki da ke cikin Birnin Kano. Da al\u2019amarin ya yi \u0199amari sai aka tura Sojoji wa\u0257anda suka ragargaza unguwar, suka kashe Maitatsine tare da fatattakar dubban almajiransa.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Fa\u0257uwar Jamhuriya ta Biyu, 1983<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Kafin wannan lokacin Birgediya Sani Abacha, ba fitacce ba ne, amma sanarwar da ya yi a Rediyo na kifar da Gwamnatin Jamhuriya ta biyu ta sanya ya yi fice.<\/p>\n\n\n\n<p>A lokacin, an kama dubban \u01b4an siyasa aka tsare, tare da \u0257aure da dama daga cikinsu saboda da laifin rashawa, wa\u0257ansu ma har \u0257aurin shekaru 300 aka yankewa wasu.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Shirin Tayar da Koma\u0257ar Tattalin Arziki (SAP), 1986<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Wannan kusan za a iya cewa, shi ne shirin Gyaran Tattalin Arziki mafi ba\u0199in jini a tarihin \u0198asar, domin shirin tsuke bakin aljihu da Shagari ya fito da shi a 1981 bai yi zafin wannan shirin da Gwamnatin Babangida ta fito da shi a shekarar 1986 ba.<\/p>\n\n\n\n<p>Mutanen Najeriya da dama su na ganin an yi haka ne domin a biya wa Asusun Lamuni na Duniya (IMF) bu\u0199ata.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Kasuwar Shunku, 1986<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Kasuwar Shunku, ta na \u0257aya daga cikin jigogin tsarin shirin Tayar da Koma\u0257ar Tattalin Arziki na SAP, inda aka bar Naira ta samar wa kanta daraja.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>\u0181allewa, 1990<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>A Ranar 22 ga Afirilun 1990 Manjo Gideon Orkar ya fito da wani sabon shafi a tarihin Najeriya, inda ya ware wa\u0257ansu Jihohi ya ce ya kore su daga Najeriya, a yayin wani yun\u0199urin Juyin Mulki da ya yi. A \u0199arshe dai an zartar masa da hukuncin kisa.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Za\u0253en 12 ga Yuni<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>An yi ta shakkun shirin mi\u0199a Mulki ga Farar Hula da Janar Babangida yake tsarawa saboda kwan-gaba, kwan-bayan da shirin ke cike da shi. Al\u2019amarin ya kawo \u0199arshe a Ranar 23 ga Yuni lokacin da Gwamnati ta bayar da sanarwar soke za\u0253en Shugaban \u0198asa da aka gudanar kwanaki 11 da suka gabata, wanda Cif Moshood Abiola da ya kama hanyar lashe wa, ya tayar da \u0199ayar-baya tare da magoya bayansa. Hakan ya sanya \u2018\u2019Ranar 12 ga Yuni\u2019\u2019 ta zama muhimmiya.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Rasuwar Abacha da Abiola, Yuni 1998<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Masu lura da yadda al\u2019amura ke gudana na ganin Allah ne Ya kar\u0253i addu\u2019ar da al\u2019ummar \u0198asa suka yi domin ya samar musu da mafita, inda aka wayi gari Shugaban \u0198asa Janar Sani Abacha, wanda tsarin Tazarce ya \u0253ullo a zamaninsa, ya fa\u0257i ya mutu a Ranar 8 ga Yunin 1998.<\/p>\n\n\n\n<p>Bayan wata guda kuma babban Fursunan da ya \u0257aure Cif Abiola shi ma ya rasu, wanda ya sanya Janar Abdulsalami ya zama Shugaban \u0198asa kuma ya kafa Kwamitin mi\u0199a Mulki ga Farar Hula.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Komawa Mulkin Farar Hula, 1999<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Hannun bayar wa, hannun kar\u0253a. Lokacin da soja suka mi\u0199a Mulki a Ranar 29 ga watan Mayun shekarar 1999, wanda ya mi\u0199a a madadin Soja shekaru 30 da suka gabata ne, watau Janar (wanda yanzu ya zama) Cif Olusegun Obasanjo ya sake kar\u0253a.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Boko Haram<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Bayan Ya\u0199in Basasa \u01b3an Fashi da Makami ne suka ri\u0199a cin karensu babu babbaka, amma da \u01b3an Boko Haram suka bayyana sai al\u2019amarin \u01b3an Fashi ya zama wasan yara.<\/p>\n\n\n\n<p>Bayan an mur\u0199ushe yun\u0199urinsu a karo na farko a shekarar 2009, sai \u01b3an Boko Haram suka sake fitowa da \u0199arfi suka girgiza Najeriya ta hanyar tayar da \u0199ayar-bayan da ba a ta\u0253a ganin irinsa ba. Dubban rayuka ne suka salwanta tun daga wancan lokacin izuwa yau.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>A Rana mai Kamar ta Yau, 1 ga Watan Junairu aka ha\u0257a Kudanci da Arewaci a matsayin \u0198asa Najeriya (Amalgamation). Sir, Frederick Lugard shi ne ya taso daga \u0198asar Hong Kong ya koma Legas domin aiwatar da tunanin ofishin Mulkin Mallaka da ke Landan, inda ya yi amfanin da al\u0199alaminsa ya ha\u0257a yankunan Arewaci da [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":3079,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"inline_featured_image":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[109],"tags":[],"class_list":["post-3080","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-rana-kamar-ta-yau"],"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v27.0 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Yau Shekaru 111 da Ha\u0257a Najeriya a Matsayin Dun\u0199ulalliyar \u0198asa<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"noindex, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_US\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Yau Shekaru 111 da Ha\u0257a Najeriya a Matsayin Dun\u0199ulalliyar \u0198asa\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"A Rana mai Kamar ta Yau, 1 ga Watan Junairu aka ha\u0257a Kudanci da Arewaci a matsayin \u0198asa Najeriya (Amalgamation). Sir, Frederick Lugard shi ne ya taso daga \u0198asar Hong Kong ya koma Legas domin aiwatar da tunanin ofishin Mulkin Mallaka da ke Landan, inda ya yi amfanin da al\u0199alaminsa ya ha\u0257a yankunan Arewaci da [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3080\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"Taskar Nasaba\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2025-01-01T17:57:39+00:00\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Salahuddeen Muhammad\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"Salahuddeen Muhammad\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Est. reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"11 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\/\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3080#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3080\"},\"author\":{\"name\":\"Salahuddeen Muhammad\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753\"},\"headline\":\"Yau Shekaru 111 da Ha\u0257a Najeriya a Matsayin Dun\u0199ulalliyar \u0198asa\",\"datePublished\":\"2025-01-01T17:57:39+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3080\"},\"wordCount\":2181,\"commentCount\":0,\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3080#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/FB_IMG_1735747424057.jpg\",\"articleSection\":[\"Rana Kamar Ta Yau\"],\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3080#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3080\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3080\",\"name\":\"Yau Shekaru 111 da Ha\u0257a Najeriya a Matsayin Dun\u0199ulalliyar \u0198asa\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3080#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3080#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/FB_IMG_1735747424057.jpg\",\"datePublished\":\"2025-01-01T17:57:39+00:00\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3080#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3080\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3080#primaryimage\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/FB_IMG_1735747424057.jpg\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/FB_IMG_1735747424057.jpg\",\"width\":720,\"height\":437},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3080#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Yau Shekaru 111 da Ha\u0257a Najeriya a Matsayin Dun\u0199ulalliyar \u0198asa\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"description\":\"\",\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\"},\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-US\"},{\"@type\":\"Organization\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\",\"logo\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png\",\"width\":343,\"height\":345,\"caption\":\"Taskar Nasaba\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/\"}},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753\",\"name\":\"Salahuddeen Muhammad\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg\",\"caption\":\"Salahuddeen Muhammad\"},\"description\":\"\u018aanjarida, marubuci, mai manufar bun\u0199asa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.\",\"sameAs\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\"],\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?author=1\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Yau Shekaru 111 da Ha\u0257a Najeriya a Matsayin Dun\u0199ulalliyar \u0198asa","robots":{"index":"noindex","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"og_locale":"en_US","og_type":"article","og_title":"Yau Shekaru 111 da Ha\u0257a Najeriya a Matsayin Dun\u0199ulalliyar \u0198asa","og_description":"A Rana mai Kamar ta Yau, 1 ga Watan Junairu aka ha\u0257a Kudanci da Arewaci a matsayin \u0198asa Najeriya (Amalgamation). Sir, Frederick Lugard shi ne ya taso daga \u0198asar Hong Kong ya koma Legas domin aiwatar da tunanin ofishin Mulkin Mallaka da ke Landan, inda ya yi amfanin da al\u0199alaminsa ya ha\u0257a yankunan Arewaci da [&hellip;]","og_url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3080","og_site_name":"Taskar Nasaba","article_published_time":"2025-01-01T17:57:39+00:00","author":"Salahuddeen Muhammad","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"Salahuddeen Muhammad","Est. reading time":"11 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3080#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3080"},"author":{"name":"Salahuddeen Muhammad","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753"},"headline":"Yau Shekaru 111 da Ha\u0257a Najeriya a Matsayin Dun\u0199ulalliyar \u0198asa","datePublished":"2025-01-01T17:57:39+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3080"},"wordCount":2181,"commentCount":0,"publisher":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3080#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/FB_IMG_1735747424057.jpg","articleSection":["Rana Kamar Ta Yau"],"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3080#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3080","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3080","name":"Yau Shekaru 111 da Ha\u0257a Najeriya a Matsayin Dun\u0199ulalliyar \u0198asa","isPartOf":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3080#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3080#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/FB_IMG_1735747424057.jpg","datePublished":"2025-01-01T17:57:39+00:00","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3080#breadcrumb"},"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3080"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3080#primaryimage","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/FB_IMG_1735747424057.jpg","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/FB_IMG_1735747424057.jpg","width":720,"height":437},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3080#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/taskarnasaba.com\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Yau Shekaru 111 da Ha\u0257a Najeriya a Matsayin Dun\u0199ulalliyar \u0198asa"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/","name":"Taskar Nasaba","description":"","publisher":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization"},"potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-US"},{"@type":"Organization","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization","name":"Taskar Nasaba","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/","logo":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png","width":343,"height":345,"caption":"Taskar Nasaba"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/"}},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753","name":"Salahuddeen Muhammad","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/image\/","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg","caption":"Salahuddeen Muhammad"},"description":"\u018aanjarida, marubuci, mai manufar bun\u0199asa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.","sameAs":["https:\/\/taskarnasaba.com"],"url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?author=1"}]}},"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/FB_IMG_1735747424057.jpg","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3080","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=3080"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3080\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/3079"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=3080"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=3080"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=3080"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}