{"id":3254,"date":"2025-01-07T18:20:55","date_gmt":"2025-01-07T18:20:55","guid":{"rendered":"https:\/\/taskarnasaba.com.ng\/?p=3254"},"modified":"2026-01-10T03:32:13","modified_gmt":"2026-01-10T03:32:13","slug":"mansa-musa-sarki-mafi-arziki-a-tarihin-duniya","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3254","title":{"rendered":"Mansa Musa: Sarki Mafi Arziki a Tarihin Duniya"},"content":{"rendered":"\n<p><strong>Sarkin Daular Mali, Mansa Musa ya kasance mutum mafi \u0199arfin arziki da aka ta\u0253a samu a Duniya, wadatarsa ta ba shi damar bun\u0199asa Birnin Timbuktu<\/strong>. <\/p>\n\n\n\n<p><strong>Ya Yi Sarauta Tsakanin Shekarar 1313 zuwa 1337<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>An haifi Mansa Musa a shekara ta 1280 a garin Manden. Kodayake, ana yawan kiran shi da &#8216;Kankan Musa,&#8217; amma ainihin sunansa \u2018Kanku.\u2019 Wannan sunan Mata ne da ya samo asali daga dangin mahaifiyarsa.<\/p>\n\n\n\n<p>Wasu daga cikin manyan \u0199abilun wancan lokacin sun fi danganta Yaro da \u0253angaren Uwa, don haka, Maza ma suke \u0257aukar sunan mahaifiyarsu.<\/p>\n\n\n\n<p>A cikin shekarar 1313, bayan rasuwar yayansa Sarki Abu Bakr II, Musa ya zama Shugaban Daular Mali. A lokacin mulkinsa na tsawon shekaru da dama, ya ya\u0257a al\u2019adun Musulunci a kewayen \u0198asar Mali, kuma Daular ta zama \u0257aya daga cikin wa\u0257anda suka ci gaba a Duniya.<\/p>\n\n\n\n<p>Mansu Musa, ya fito ne daga Gidan Sarauta na Keita, wa\u0257anda suka yi mulkin Mali tsawon \u0198arni da dama.<\/p>\n\n\n\n<p>Haka nan, ya kasance Sarki mai wadata wanda ya gina Daula mai \u0199arfin fa\u0257a-a-ji, kuma wadda ta bun\u0199asa. Bisa ga bayanan al\u2019adar baka, kakansa Abu Bakr na farko, \u0199ani ne ga Sunjata Keita wanda ya kafa Daular Mali.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Sarautar Musa ta Haska Daular Mali a Duniya<\/strong><\/p>\n\n\n\n<div class=\"wp-block-media-text is-stacked-on-mobile\"><figure class=\"wp-block-media-text__media\"><img fetchpriority=\"high\" decoding=\"async\" width=\"300\" height=\"168\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-07t1644592207828006327058789-300x168.jpg\" alt=\"\" class=\"wp-image-3241 size-full\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-07t1644592207828006327058789-300x168.jpg 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-07t1644592207828006327058789-600x337.jpg 600w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-07t1644592207828006327058789.jpg 739w\" sizes=\"(max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/figure><div class=\"wp-block-media-text__content\">\n<p><em>Wannan hoton zane ne aka yi kamar yadda aka bayanna a tarihi, amma ba hoton zahiri ba ne. |Hoto: DW<\/em><\/p>\n<\/div><\/div>\n\n\n\n<p>A zamanin mulkin Musa, wata\u0199ila \u0198asar Mali ce ta kasance mai samar da Zinariya mafi girma a Duniya, kuma ana \u0257aukar Musa \u0257aya daga mutane mafi arziki a tarihi. Ko dai ya ta kasance, masu sharhi na zamani irin su: Mujallar Time, sun kammala da cewar, babu ingantacciyar hanyar da za ta \u0199ayyade arzikin Musa. Amma kuma Mujallar Marca ta ce, gaba\u0257aya, \u0199iyasin dukiyar za ta kai kusan Dala Biliyan 400.<\/p>\n\n\n\n<p>A shekarar 1324, Mansa Musa ya tafi aikin Hajji a Makka. Ayarinsa ta \u0199unshi mutum Dubu 60 da Bayi Dubu 12 da Dogarai da ke sanye da kayan \u0199awa da Sanduna na Zinariya, da kuma masu kula da Dawaki da kayansu.<\/p>\n\n\n\n<p>Wannan \u0199asaitaccen rangadin ya sa ya zama sananne, musamman a Yammacin Afirka da yankin Gabas ta Tsakiya. A cikin kowane Gari da ya yada zango, Musa ya kasance mai karamci sosai kuma ya yi ta ba da kyautar wani \u0253angare na dukiyarsa \u2013 wanda babu shakka ya yi tasiri ga tattalin arzikin yankin, da kuma labarin mulkinsa.<\/p>\n\n\n\n<div class=\"wp-block-media-text is-stacked-on-mobile\"><figure class=\"wp-block-media-text__media\"><img decoding=\"async\" width=\"300\" height=\"168\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-07t1644591676848505967603346-300x168.jpg\" alt=\"\" class=\"wp-image-3245 size-full\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-07t1644591676848505967603346-300x168.jpg 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-07t1644591676848505967603346-600x337.jpg 600w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-07t1644591676848505967603346.jpg 739w\" sizes=\"(max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/figure><div class=\"wp-block-media-text__content\">\n<p><em>Wannan hoton zane ne aka yi kamar yadda aka bayanna a tarihi, amma ba hoton zahiri ba ne. |Hoto: <\/em>DW<\/p>\n<\/div><\/div>\n\n\n\n<p>Sarki Mansa Musa (Musa Keita) ya hau kan ragamar mulki a shekarar 1312 Miladiyya, bayan rasuwar Sarki Abu Bakr na biyu. Hawansa karagar mulki ke da wuya ya fa\u0257a\u0257a iyakar Masarautarsa wacce ta faro tun daga ga\u0253ar ruwan Gambiya, har yankin \u0199asar Sudan, inda ya ha\u0257a yankin \u0198asar Hausa da ke Najeriya da \u0198asar Nijar da Senegal, Burkina Faso, Gambia, Mali, Chad da Mauritania su suka ha\u0257u suka bayar da Daular da Mansa Musa ke mulka. <\/p>\n\n\n\n<p><strong>Babban Birnin Mulki: Timbuktu Wanda ke \u0198asar Mal<\/strong>i<\/p>\n\n\n\n<p>Sarki Mansa Musa ya shimfi\u0257a mulki na \u0199asaita, ya kuma fa\u0257a\u0257a Birnin Timbuktu&nbsp;<a href=\"https:\/\/is.gd\/ISvez0\">https:\/\/is.gd\/ISvez0<\/a> ta yadda ya yi gogayya da sauran manyan biranen Duniya na wancan zamani.<\/p>\n\n\n\n<div class=\"wp-block-media-text is-stacked-on-mobile\"><figure class=\"wp-block-media-text__media\"><img decoding=\"async\" width=\"300\" height=\"201\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2024-12-06t1811361336955552690164730-300x201.jpg\" alt=\"\" class=\"wp-image-3249 size-full\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2024-12-06t1811361336955552690164730-300x201.jpg 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2024-12-06t1811361336955552690164730-600x403.jpg 600w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2024-12-06t1811361336955552690164730.jpg 612w\" sizes=\"(max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/figure><div class=\"wp-block-media-text__content\">\n<p><em>Birnin Timbuktu a tsarin ginin Gargajiya, wadda ya samo asali daga \u0199wararren magini Ishaq El Teudjin. <\/em><\/p>\n<\/div><\/div>\n\n\n\n<p>A shekarar 1324, Sarki Mansa Musa ya shirya tafiya zuwa \u0199asa mai tsarki domin sauke Farali, tafiyar da ta bar wa Duniya tarihi na ban mamaki.<\/p>\n\n\n\n<p>Lokacin da tawagar Sarki Mansa Musa ta motsa daga Birnin Timbuktu zuwa garin Makka, ya tafi da Sojoji sama da 20,000, haka zalika bayin da za su yi hidima sun haura 500. Ya kuma \u0257ebi dukiya da zummar yin Hadaya a garuruwa masu tsarki na Makka da Madina, dukiyar da ko Sarakunan Daulolin Larabawa ba su ta\u0253a mallakar irinta ba.<\/p>\n\n\n\n<p>Kamar yadda malaman tarihi suka ambato, sun ce ya tafi da Ra\u0199uma 20,000 da Dawaki 6,000 da manya-manyan mazubai cike da Zinariya da Azurfa, da Tufafi na alfarma da sauran nau\u2019ukan dukiya duk domin bayar da kyauta ga mutanen Makka da Madina.<\/p>\n\n\n\n<div class=\"wp-block-media-text is-stacked-on-mobile\"><figure class=\"wp-block-media-text__media\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"300\" height=\"168\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-07t1643505088393156007288692-300x168.jpg\" alt=\"\" class=\"wp-image-3243 size-full\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-07t1643505088393156007288692-300x168.jpg 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-07t1643505088393156007288692-600x337.jpg 600w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-07t1643505088393156007288692.jpg 739w\" sizes=\"(max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/figure><div class=\"wp-block-media-text__content\">\n<p><em>Wannan hoton zane ne aka yi kamar yadda aka bayanna a tarihi, amma ba hoton zahiri ba ne. |Hoto: <\/em>DW<\/p>\n<\/div><\/div>\n\n\n\n<p>A lokacin wannan tafiya tasa, ya tafi da wata amaryarsa wacce yake matu\u0199ar \u0199auna, wacce aka tanadar mata Bayi da Kuyangi sama da 100 wa\u0257anda aikinsu kawai yi ma ta hidima.<\/p>\n\n\n\n<p>A yayin da tawagarsa ta ratsa Hamadar Arewacin Afirka&nbsp;<a href=\"https:\/\/is.gd\/1GYvZv\">https:\/\/is.gd\/1GYvZv<\/a> bayan tafiyar watanni, sai wannan amaryar tasa ta gaji da tafiya a cikin Sahara, ta yi fatan ina ma ta samu Dausayi mai Danshi da za ta huta. Wannan bu\u0199ata da ta nuna ya sa Sarki Mansa Musa ya umarci da a share Saharar a \u0199ir\u0199irar ma ta Dausayi (Lambu) da za ta huta.<\/p>\n\n\n\n<p>A tarihin Duniya wannan shi ne lokaci na farko da aka ta\u0253a samar da dausayi a cikin Sahara.<\/p>\n\n\n\n<p>An ce, an yanka sama da Ra\u0199uma 3,000, aka yi amfani da ruwan cikinsu aka samar da wani Dausayi mai tarin ni\u2019ima da shuke-shuke masu ban sha\u2019awa. A wannan Dausayin ne amaryar tasa ta samu damar hutawa har na wasu watanni kafin daga bisani tawagar ta sake motsawa.<\/p>\n\n\n\n<p>Labarin wannan tawaga ta ratsa ko&#8217;ina a \u0199asashen Yankin Magrib. Sarakuna da dama sun ka\u0257u sun kuma firgita da \u0199arfi da kuma tarin dukiyar da suka gani ta Sarki Mansa Musa.<\/p>\n\n\n\n<div class=\"wp-block-media-text is-stacked-on-mobile\"><figure class=\"wp-block-media-text__media\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"300\" height=\"300\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-07t1643178082000208326893645-300x300.jpg\" alt=\"\" class=\"wp-image-3244 size-full\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-07t1643178082000208326893645-300x300.jpg 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-07t1643178082000208326893645-150x150.jpg 150w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-07t1643178082000208326893645-100x100.jpg 100w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-07t1643178082000208326893645.jpg 554w\" sizes=\"(max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/figure><div class=\"wp-block-media-text__content\">\n<p><em>Wannan hoton zane ne aka yi kamar yadda aka bayanna a tarihi, amma ba hoton zahiri ba ne. |Hoto: <\/em>DW<\/p>\n<\/div><\/div>\n\n\n\n<p>Lokacin da tawagar ta isa \u0198asar Misra, ya ki\u0257ima Misrawa, domin ba su ta\u0253a ganin mutum mai \u0199arfin dukiya kamar Mansa Musa ba, ta yadda har ya kusan mayar da Misirawa bayinsa saboda tarin dukiyar da suka gani.<\/p>\n\n\n\n<p>Labarin isowarsa Misira da irin dukiyar da yake \u0257auke da ita ya watsu a kowane lungu da sa\u0199o, wannan dalili ya sa mutane su ka yi ta turereniyar zuwa ganin wannan tawaga.<\/p>\n\n\n\n<p>Malaman tarihi sun ce, Mansa Musa ya yi ta raba Hadaya (Kyauta) ga mabu\u0199ata da Miskinai. Har ila yau, ya hidimtawa Malaman Misira na zamanin, ya bada Dukiya mai yawa wajen sake gina Masallatai da makarantu. Saboda kyautuka da ayyukan alheri da ya yi, ya sa aka samu hauhawar farashin kayayyaki a \u0198asar Misra.<\/p>\n\n\n\n<p>Tawagar Mansa Musa ta tashi daga Misra ta nufi Hijaz (Makka) ta Ga\u0253ar Ruwan Maliya. Tuni labarinsa da irin hidimar da ya yi wa mutanen Misra ta isa gare su. Wannan dalili ya sa ya samu kyakkyawar tarba daga mutanen Makka da Madina.<\/p>\n\n\n\n<div class=\"wp-block-media-text is-stacked-on-mobile\"><figure class=\"wp-block-media-text__media\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"300\" height=\"168\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-07t1642587797090947244368359-300x168.jpg\" alt=\"\" class=\"wp-image-3247 size-full\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-07t1642587797090947244368359-300x168.jpg 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-07t1642587797090947244368359-600x337.jpg 600w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-07t1642587797090947244368359.jpg 739w\" sizes=\"(max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/figure><div class=\"wp-block-media-text__content\">\n<p><em>Wannan hoton zane ne aka yi kamar yadda aka bayanna a tarihi, amma ba hoton zahiri ba ne. |Hoto: <\/em>DW<\/p>\n<\/div><\/div>\n\n\n\n<p>Wannan tarin Dukiya da ya taho da ita, sai ya tattara ta gaba \u0257aya ya bayar da ita Hadaya ga Haramin Makka da na Madina. Haka nan, ya bi manyan gidajen Sharifai da na zuriyar Sahabbai ya yi musu hidima ta ban mamaki. An ce Allah ne ka\u0257ai ya san iya adadin Zinariya da ya rabar.<\/p>\n\n\n\n<div class=\"wp-block-media-text is-stacked-on-mobile\"><figure class=\"wp-block-media-text__media\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"300\" height=\"169\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/54372061_9033022545633418220851-300x169.jpg\" alt=\"\" class=\"wp-image-3248 size-full\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/54372061_9033022545633418220851-300x169.jpg 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/54372061_9033022545633418220851.jpg 600w\" sizes=\"(max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/figure><div class=\"wp-block-media-text__content\">\n<p><em>Wannan hoton zane ne aka yi kamar yadda aka bayanna a tarihi, amma ba hoton zahiri ba ne. |Hoto: <\/em>DW<\/p>\n<\/div><\/div>\n\n\n\n<p><strong>Dawowarsa Daga Makka<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Bayan dawowarsa daga Makka, Mansa Musa ya taho da malamai Larabawa, da ma&#8217;aikata da masu gine-gine. Daga cikin wa\u0257anda suka tawo tare da shi har da masanin gine-gine Ishaq El Teudjin, wanda ya \u0253ullo da dabarun gine-gine ga \u0198asar Mali.<\/p>\n\n\n\n<div class=\"wp-block-media-text is-stacked-on-mobile\"><figure class=\"wp-block-media-text__media\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"640\" height=\"480\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-07t1829407770397466988893223.jpg\" class=\"wp-image-3251 size-full\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-07t1829407770397466988893223.jpg 640w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-07t1829407770397466988893223-300x225.jpg 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-07t1829407770397466988893223-600x450.jpg 600w\" sizes=\"(max-width: 640px) 100vw, 640px\" \/><\/figure><div class=\"wp-block-media-text__content\">\n<p><em>Tsohuwar Masarautar Madagou, Timbuktu, Mali.<\/em><\/p>\n<\/div><\/div>\n\n\n\n<p>Ya tsara gine-gine masu yawa ga Sarkin Sarakuna, ciki har da; sabuwar Fada mai suna &#8216;Madagou,&#8217; da Masallacin Gao, birni na biyu mafi girma a Mali, da kuma babban Masallacin Timbuktu, birni mafi girma a Cikin Daular. An sanya wa wannan Masallaci suna Djinguereber.<\/p>\n\n\n\n<div class=\"wp-block-media-text is-stacked-on-mobile\"><figure class=\"wp-block-media-text__media\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"300\" height=\"200\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/01\/images-2024-12-06t1811196319263713065831928-300x200.jpg\" class=\"wp-image-4024 size-full\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/01\/images-2024-12-06t1811196319263713065831928-300x200.jpg 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/01\/images-2024-12-06t1811196319263713065831928-600x400.jpg 600w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/01\/images-2024-12-06t1811196319263713065831928.jpg 678w\" sizes=\"(max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/figure><div class=\"wp-block-media-text__content\">\n<p><em>Masallacin Djinguereber, Timbuktu, Mali.<\/em><\/p>\n<\/div><\/div>\n\n\n\n<p>Shahararren in da El Teudjin ya gina shi ne, \u0257akin Sarki a Babban Birnin Mali na Niani.<\/p>\n\n\n\n<div class=\"wp-block-media-text is-stacked-on-mobile\"><figure class=\"wp-block-media-text__media\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"300\" height=\"300\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/01\/images28129281229900635740366762265-300x300.jpg\" class=\"wp-image-4023 size-full\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/01\/images28129281229900635740366762265-300x300.jpg 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/01\/images28129281229900635740366762265-150x150.jpg 150w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/01\/images28129281229900635740366762265-100x100.jpg 100w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/01\/images28129281229900635740366762265.jpg 554w\" sizes=\"(max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/figure><div class=\"wp-block-media-text__content\">\n<p><em>Yanzu haka, Niani \u0199auye ne a \u0198asar Guinea. Ya na cikin Lardin Kankan, a Gabashin \u0198asar. |Hoto: Wikipedia<\/em><\/p>\n<\/div><\/div>\n\n\n\n<p>Sakamakon \u0257imbin arzikin da ya mallaka, Kanku Musa ya gina wuraren Addini da na mulki da dama a shekarun 1325s. Daga cikinsu akwai; Masallatai, da Makaranta da kuma Masarauta a garuruwan Timbuktu da Gao.<\/p>\n\n\n\n<p>Masallacin Sankore da ke Timbuktu ya kasance fasaharsa da ta fi fice. Ya ba da damar musayar al\u2019adu tsakanin \u0198asar Mali da \u0199asashen Larabawa.<\/p>\n\n\n\n<p>Wasu \u0257aliban Mali sun je Misra da Maroko don kammala karatunsu, yayin da wasu malaman Masar da Moroko suka je karatu a Sankore Madrasa. A wancan lokacin ya kasance Cibiyar Ya\u0257a Kyakkyawan Al\u2019adun Musulinci a Yammacin Afirka.<\/p>\n\n\n\n<p>Mansa Musa, ya rasu a shekara ta 1337 bayan ya yi shekaru 25 bisa Karagar Mulki. \u018aansa Maghan I ne ya gaje shi.<\/p>\n\n\n\n<p>&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp; <strong>MADOGARA<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Wa\u0257anda suka yi hidima wajen ha\u0257a wannan ma\u0199ala sun ha\u0257a da; Muhammad Cisse, da Salahuddeen Muhammad, da tallafin Jaridar Blueprint Manhaja, da Mujallar Time, da Marca, da kuma sashen Hausa na DW.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Sarkin Daular Mali, Mansa Musa ya kasance mutum mafi \u0199arfin arziki da aka ta\u0253a samu a Duniya, wadatarsa ta ba shi damar bun\u0199asa Birnin Timbuktu. Ya Yi Sarauta Tsakanin Shekarar 1313 zuwa 1337 An haifi Mansa Musa a shekara ta 1280 a garin Manden. Kodayake, ana yawan kiran shi da &#8216;Kankan Musa,&#8217; amma ainihin sunansa [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":3240,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"inline_featured_image":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[93],"tags":[125],"class_list":["post-3254","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-jiya-da-yau","tag-mansa_musa-mali-timbuktu"],"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v27.0 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Mansa Musa: Sarki Mafi Arziki a Tarihin Duniya<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"noindex, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_US\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Mansa Musa: Sarki Mafi Arziki a Tarihin Duniya\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"Sarkin Daular Mali, Mansa Musa ya kasance mutum mafi \u0199arfin arziki da aka ta\u0253a samu a Duniya, wadatarsa ta ba shi damar bun\u0199asa Birnin Timbuktu. Ya Yi Sarauta Tsakanin Shekarar 1313 zuwa 1337 An haifi Mansa Musa a shekara ta 1280 a garin Manden. Kodayake, ana yawan kiran shi da &#8216;Kankan Musa,&#8217; amma ainihin sunansa [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3254\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"Taskar Nasaba\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2025-01-07T18:20:55+00:00\" \/>\n<meta property=\"article:modified_time\" content=\"2026-01-10T03:32:13+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-07T164407.463.jpeg\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"665\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"461\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/jpeg\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Salahuddeen Muhammad\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"Salahuddeen Muhammad\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Est. reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"7 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\/\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3254#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3254\"},\"author\":{\"name\":\"Salahuddeen Muhammad\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753\"},\"headline\":\"Mansa Musa: Sarki Mafi Arziki a Tarihin Duniya\",\"datePublished\":\"2025-01-07T18:20:55+00:00\",\"dateModified\":\"2026-01-10T03:32:13+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3254\"},\"wordCount\":1505,\"commentCount\":0,\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3254#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-07T164407.463.jpeg\",\"keywords\":[\"#mansa_musa #mali #timbuktu\"],\"articleSection\":[\"Jiya Da Yau\"],\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3254#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3254\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3254\",\"name\":\"Mansa Musa: Sarki Mafi Arziki a Tarihin Duniya\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3254#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3254#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-07T164407.463.jpeg\",\"datePublished\":\"2025-01-07T18:20:55+00:00\",\"dateModified\":\"2026-01-10T03:32:13+00:00\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3254#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3254\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3254#primaryimage\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-07T164407.463.jpeg\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-07T164407.463.jpeg\",\"width\":665,\"height\":461},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3254#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Mansa Musa: Sarki Mafi Arziki a Tarihin Duniya\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"description\":\"\",\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\"},\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-US\"},{\"@type\":\"Organization\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\",\"logo\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png\",\"width\":343,\"height\":345,\"caption\":\"Taskar Nasaba\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/\"}},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753\",\"name\":\"Salahuddeen Muhammad\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg\",\"caption\":\"Salahuddeen Muhammad\"},\"description\":\"\u018aanjarida, marubuci, mai manufar bun\u0199asa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.\",\"sameAs\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\"],\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?author=1\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Mansa Musa: Sarki Mafi Arziki a Tarihin Duniya","robots":{"index":"noindex","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"og_locale":"en_US","og_type":"article","og_title":"Mansa Musa: Sarki Mafi Arziki a Tarihin Duniya","og_description":"Sarkin Daular Mali, Mansa Musa ya kasance mutum mafi \u0199arfin arziki da aka ta\u0253a samu a Duniya, wadatarsa ta ba shi damar bun\u0199asa Birnin Timbuktu. Ya Yi Sarauta Tsakanin Shekarar 1313 zuwa 1337 An haifi Mansa Musa a shekara ta 1280 a garin Manden. Kodayake, ana yawan kiran shi da &#8216;Kankan Musa,&#8217; amma ainihin sunansa [&hellip;]","og_url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3254","og_site_name":"Taskar Nasaba","article_published_time":"2025-01-07T18:20:55+00:00","article_modified_time":"2026-01-10T03:32:13+00:00","og_image":[{"width":665,"height":461,"url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-07T164407.463.jpeg","type":"image\/jpeg"}],"author":"Salahuddeen Muhammad","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"Salahuddeen Muhammad","Est. reading time":"7 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3254#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3254"},"author":{"name":"Salahuddeen Muhammad","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753"},"headline":"Mansa Musa: Sarki Mafi Arziki a Tarihin Duniya","datePublished":"2025-01-07T18:20:55+00:00","dateModified":"2026-01-10T03:32:13+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3254"},"wordCount":1505,"commentCount":0,"publisher":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3254#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-07T164407.463.jpeg","keywords":["#mansa_musa #mali #timbuktu"],"articleSection":["Jiya Da Yau"],"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3254#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3254","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3254","name":"Mansa Musa: Sarki Mafi Arziki a Tarihin Duniya","isPartOf":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3254#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3254#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-07T164407.463.jpeg","datePublished":"2025-01-07T18:20:55+00:00","dateModified":"2026-01-10T03:32:13+00:00","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3254#breadcrumb"},"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3254"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3254#primaryimage","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-07T164407.463.jpeg","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-07T164407.463.jpeg","width":665,"height":461},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3254#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/taskarnasaba.com\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Mansa Musa: Sarki Mafi Arziki a Tarihin Duniya"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/","name":"Taskar Nasaba","description":"","publisher":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization"},"potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-US"},{"@type":"Organization","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization","name":"Taskar Nasaba","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/","logo":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png","width":343,"height":345,"caption":"Taskar Nasaba"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/"}},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753","name":"Salahuddeen Muhammad","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/image\/","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg","caption":"Salahuddeen Muhammad"},"description":"\u018aanjarida, marubuci, mai manufar bun\u0199asa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.","sameAs":["https:\/\/taskarnasaba.com"],"url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?author=1"}]}},"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-07T164407.463.jpeg","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3254","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=3254"}],"version-history":[{"count":3,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3254\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4025,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3254\/revisions\/4025"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/3240"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=3254"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=3254"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=3254"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}