{"id":3302,"date":"2025-01-15T20:19:46","date_gmt":"2025-01-15T20:19:46","guid":{"rendered":"https:\/\/taskarnasaba.com.ng\/?p=3302"},"modified":"2025-01-16T14:21:11","modified_gmt":"2025-01-16T14:21:11","slug":"yau-ake-cika-shekaru-59-da-juyin-mulki-na-farko-a-najeriya","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3302","title":{"rendered":"Tarihin Juyin Mulki na Farko a Najeriya"},"content":{"rendered":"\n<p><strong>A ranar 15 ga watan Janairun 1966, yayin Juyin Mulki \u0199ar\u0199ashin jagorancin Manjo Emmanuel Ifeajuna da Manjo Nzeogwu, da sauransu, inda aka \u0199ashe manyan shugabannin Siyasa da suka ha\u0257a da; Firaministan Najeriya na farko, Sir. Abubakar Tafawa \u0181alewa, da Firimiyan Jihar Arewa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato, da kuma wasu jagororin \u0198asar 22.<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Kamar yadda a Kudu maso Yammacin Najeriya, Kyatin Emmanuel Nwobosi ya jagoranci Juyin Mulki, a Yankin Arewa Manjo Chukwuma Kaduna Nzeogwu, haka ma a yankin Legas wanda take matsayin birnin Tarayyar Najeriya a wancan lokacin, Manjo Emmanuel Arinze Ifeajuna ne ya jagoranci Juyin Mulkin.<\/p>\n\n\n\n<p>Tun da farko dai, Ifeajuna, Okafor da Ademoyega (Wanda Bayarbe ne) su ne Sojojin da suka shirya dukkanin dabarun yadda za a yi a kifar da Gwamnatin Farar Hula ta Jamhuriya ta Farko.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tarihin Yadda Aka Kashe Firaministan Najeriya, Sir. Abubakar Tafawa \u0181alewa<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p><strong> <\/strong><\/p>\n\n\n\n<div class=\"wp-block-media-text is-stacked-on-mobile\"><figure class=\"wp-block-media-text__media\"><img fetchpriority=\"high\" decoding=\"async\" width=\"212\" height=\"300\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/fb_img_17369702012578403675402905698342-212x300.jpg\" alt=\"\" class=\"wp-image-3292 size-full\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/fb_img_17369702012578403675402905698342-212x300.jpg 212w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/fb_img_17369702012578403675402905698342-600x850.jpg 600w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/fb_img_17369702012578403675402905698342.jpg 720w\" sizes=\"(max-width: 212px) 100vw, 212px\" \/><\/figure><div class=\"wp-block-media-text__content\">\n<p><em>Sir. Abubakar Tafawa \u0181alewa, Firaministan N<\/em>ajeriya. <\/p>\n<\/div><\/div>\n\n\n\n<p>Tun farko, ruwayoyin Tarihi sun nuna cewar, Ministan Harkokin Cikin Gida na Jamhuriyar ta Farko, Alhaji Shehu Usman Shagari, ya sha sanarwa da Tafawa \u0181alewa shirin Sojoji na yin Juyin Mulki. Akwai ranar da ma sai da ran Firaministan ya \u0253aci sosai a kan maganar, ya ce wa Shagari, ka da ya \u0199ara tasa masa wannan maganar idan ba ya son ganin \u0253acin ransa.<\/p>\n\n\n\n<p>Daidai misalin \u0199arfe biyu da \u01b4an wasu Mintina, na Ranar 15 Ga Watan Junairu a shekarar 1966, wasu sojoji \u0199ar\u0199ashin jagorancin Manjo Ifeajuna suka dira Gidan Firaminista Sir. Abubakar Tafawa \u0181alewa da ke titin King George a birnin Legas. (A lokacin Legas ne Babban Birnin \u0198asa).<\/p>\n\n\n\n<p>Zuwan nasu ya faru ne Awanni ka\u0257an bayan Tafawa \u0181alewa ya kammala tattaunawa da wasu daga cikin Ministocinsa wa\u0257anda suka ha\u0257a da K.O. Mbadiwe ministanT Harkokin Kasuwanci, Raymond Njoku Ministan Harkokin Sadarwa, da kuma Taslim Elias Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya.<\/p>\n\n\n\n<p>A lokacin da suka shiga Gidan sun fafata da Jami\u2019an \u01b4an sanda da suke gadin Gidan, amma ba su kashe kowa ba cikin su ba. Bayan shigar su cikin Gidan babban abokin Tafawa \u0181alewa kuma sirikinsa Madakin Bauchi, na wancan lokacin, Alhaji Abubakar Garba, ya na cikin Gidan amma ba su gan shi ba.<\/p>\n\n\n\n<p>Daga baya har Madakin Bauchi yake cewa, wanda ya jagoranci far ma Gidan Tafawa \u0181alewa ba Manjo Ifeajuna bane ake fa\u0257a, Manjo Okafor ne saboda a cewar Madakin Bauchin, wadda ya kalla da idon sa wani Soja ne Fari siriri mai gashin baki, to amma dukkanin wa\u0257annan siffofin na Manjo Ifeajuna ne. Daga baya dukkanin bincike sun tabbatar da Ifeajuna ne jagoran tafiyar ba Okafor ba.<\/p>\n\n\n\n<p>Bayan Manjo Ifeajuna da tawagarsa sun shiga gidan sun yi barazanar harbe Hidimai na musamman ga Tafawa \u0181alewa, watau; ADCs \u0257insa guda biyu masu mu\u0199amin Kaftin wadda \u0257ayansu ya kasance \u0257an Arewacin Najeriya, da kuma Maxwell \u0257an \u0198abilar Ibo, idan har ba su nuna musu wurin da Tafawa \u0181alewa yake ba.<\/p>\n\n\n\n<p>Da farko sun turje sun ce, su sam ba su san inda Firaministan yake kwana ba, kuma ba su da makullan \u0257akin kwanansa. Amma daga \u0199arshe da kowanensu aka \u0257ora masa bindiga a ka ana faman matsa kunamar, sai suka wuce sama kai-tsaye wajen da Tafawa \u0181alewa yake kwana. Suka \u0199wankwasa masa \u0199ofa. Ya na bu\u0257e wa ya ga Manjo Ifeajuna tsaye ya shuno masa bindiga kai-tsaye.<\/p>\n\n\n\n<p>Da ganin Manjo Ifeajuna tsaye cikin wannan yanayin, Firaministan ya tambaya shin lafiya kuwa?<\/p>\n\n\n\n<p>Ifeajuna, ya yi masa sarawar ban girma kuma ya sanar da shi yazo ya kama shi ya tafi da shi ne.<\/p>\n\n\n\n<p>Tafawa \u0181alewa ya ce, to kafin a tafi da shi y ana ro\u0199on alfarma a ba shi dama ya yi Sallah kuma ya canja kayan jikinsa.<\/p>\n\n\n\n<p>Aka ba shi dama ya yi sallah ya saka Farar Riga da Farin Wando da kuma Takalmi Silifa.<\/p>\n\n\n\n<p>Ana \u0199o\u0199arin fita da shi hadiminsa \u0257an Arewa, Kaftan, ya ro\u0199i su Ifeajuna cewar, su taimaka ka da su tafi da Tafawa \u0181alewa saboda shi ka\u0257ai ne \u0257an mahaifiyarsa kuma ta tsufa sosai wani abu ya na faruwa da shi zuciyarta za ta iya samun matsala. Amma duk da wannan ro\u0199o ba su ji ba suka wuce da shi zuwa \u0199asa.<\/p>\n\n\n\n<p>Tafiya da Tafawa \u0181alewa, Kaftan ya biyo su har kan titin da suka ajiye motar su ya na ta ba su baki akan su fa\u0257a masa dalilin tafiya da Tafawa \u0181alewa, kuma ina za su je da shi, idan sun tafi da shi me za su yi masa?<\/p>\n\n\n\n<p>Ya ci gaba da yi musu magiya har sai da Tafawa \u0181alewa da kansa ya dakatar da shi ya kuma umarce shi cewa ya koma gida.<\/p>\n\n\n\n<p>Suka tafi da shi zuwa kan Titi suka umarce shi da ya shiga cikin motar su ta Sojoji kuma suka tabbatar masa da cewa ba za su cutar da shi ba saboda sun san dukkanin rikice-rikicen Siyasa da suke faruwa a \u0198asar musamman a yankin Kudu maso Yamma, ba laifinsa bane. Daga nan suka bi kan titin Awolowo suka tafi.<\/p>\n\n\n\n<p>Bayan tafiya da Firaministan, ma\u2019aikatan gidansa sun yi gaggawar \u0199iran Kwamishinan \u01b4an sandan birnin Legas Hamman Maiduguri, suka sanar da shi an sace Tafawa \u0181alewa. Suka sake kiran Shugaban Rundunar Sojojin Najeriya, Manjo Janar Aguyi-Ironsi, suka sanar da shi halin da ake ciki.<\/p>\n\n\n\n<p>Bayan kiran Hamman Maiduguri, shi kuma ya kira Shugaban Rundunar \u01b4an Sandan Najeriya watau; Alhaji Kam-Salim wanda shi ma yake a birnin Legas.<\/p>\n\n\n\n<p>Daga nan, tsakanin \u0199arfe 3 na Dare su biyun suka wuce ofishin mataimakin Babban Magatakardan Ma\u2019aikatar Tsaro, watau Alhaji Ahmadu Kurfi domin su sanar da shi abin da yake faruwa.<\/p>\n\n\n\n<p>A lokacin da abin ya faru ma\u2019aikatar ta tsaro ta na hannun Babban Magatakardan ta Alhaji. Suke Kolo saboda Ministan Harkokin Tsaron Alh. Inuwa Wada baya nan.<\/p>\n\n\n\n<p>Bayan labari ya fita cewar, an sace Firaminista an kuma kashe wasu daga cikin manyan Sojoji, musamman wa\u0257anda suka fito daga Arewa, Shugaban Rundunar Sojojin Najeriya, Manjo Janar Aguyi-Ironsi ya ha\u0257a Bataliya ta biyu domin su shawo kan matsalar, masu Juyin Mulkin kuma a kama su.<\/p>\n\n\n\n<p>A lokacin da suka samu labarin Aguyi-Ironsi ya na gari kuma ya shirya tsaf domin tunkarar su, daga nan sai suka fara tunanin yanda za su tsira. Tun lokacin da suka \u0257auko Tafawa \u0181alewa daga cikin gidansa, ya na cikin Motar su ta Sojoji har ya zuwa wannan lokacin ana ta zagaya wa wurare da shi. A kan idonsa an kashe Sojoji da dama.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Kisan Abubakar Tafawa \u0181alewa<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Su na cikin tafiya da Firaminista sai aka wuce Asibitin Sojoji na Yaba, domin a duba lafiyar Laftanan Ezedigbo, saboda raunuka da ya samu sakamakon arangamarsa da masu gadin gidan Janar Maimalari, lokacin da suka je kashe shi. Bayan Ifeajuna ya ajiye Ezedigbo a asibiti, sai suka wuce titin Abeokuta da Tafawa \u0181alewa a cikin Motar.<\/p>\n\n\n\n<p>Lokacin da suka hau hanyar Legas zuwa Abeokuta sai Manjo Ifeajuna ya cewa Firaminista ya sauka a Motar. Ya na fita ya harbe shi ya fa\u0257i \u0199asa. Bayan fa\u0257uwarsa sai Manjo Okafor ya je ya bincika gawar, ya tabbatar Tafawa \u0181alewa ya mutu, sai suka bu\u0257e bayan Motar su suka fito da gawar Laftanan Kanal Largema suka jefar da ita kusa da ta Firaminista, suka wuce hanyar garin Abeokuta.<\/p>\n\n\n\n<p>A kan hanyarsu ta zuwa Abeokuta suka tsaya, wasu Sojoji guda biyu suka sauka suka koma Legas. Shi kuma Manjo Ifeajuna da abokin aikinsa Okafor suka wuce garin Enugu.<\/p>\n\n\n\n<p>Su na isa garin suka je suka samu Firimiyan yankin Inyamurai watau Dr. Michael Okpara, suka yi wata \u0199warya-\u0199wayar tattaunawa da shi, wanda daga nan ne suka tafi suka \u0253uya.<\/p>\n\n\n\n<p>Daga baya Manjo Ifeajuna a hankali da taimakon abokinsa Christopher Okigbo ya sulale ya gudu \u0198asar Ghana, kuma ya samu tarba ta musamman daga Shugaban \u0198asar Ghana na wancan lokacin Kwame Nkurumah.<\/p>\n\n\n\n<p>Nkurumah, ya ba shi gida sun zauna tare da Samuel Ikoku tsohon Magatakardan Jam&#8217;iyyar AG ta Yarbawa, wanda ya gudu \u0198asar Ghana lokacin da aka yi shari\u2019ar Awolowo bisa laifin yun\u0199urin Juyin Mulki a shekarar 1962.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Gano Gawar Tafawa \u0181alewa<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Har bayan kwana uku da kashe Tafawa \u0181alewa ba a samu gawarsa da na wasu manyan Sojoji ba, hakan ya sa Aguyi Ironsi ya sanar wa \u01b4an \u0198asa cewar; har yanzu ba a san in da Firaminista yake ba, amma ana nan ana duba wa.<\/p>\n\n\n\n<p>Bayan kwana biyu da yin wannan sanarwar, wani \u018aansandan Arewa mai suna Ibrahim Babankowa mai matakin Mataimakin Sufartanda, ya je asibiti domin ganin Likita. Ya na zaune sai ya ji wasu mutane su na magana a kan wani irin mummunar wari mai \u0199arfin gaske da suke ji a kusa da inda suke rayuwa.<\/p>\n\n\n\n<p>Babankowa, ya tambaye su suka sanar masa wajen, shi ma kuma sai ya tuna akwai lokacin da ya na bakin aiki Rundunar Sojoji sun zo sun wuce ta inda yake zuwa can wajen.<\/p>\n\n\n\n<p>Babankowa ya \u0257auki Rundunar \u01b4an sanda suka tafi wajen domin duba abin da yake faruwa, wanda isar su ke da wuya suka tarar da gawarwakin mutane guda biyu har sun fara zagwanye wa.<\/p>\n\n\n\n<p>\u018aaya da kayan Sojoji wanda aka tabbatar da ko shakka babu Laftanan Kanel Largema ne; wanda aka jefar da gawarsa kusa da ta Firaministan, lokacin da aka kashe shi.<\/p>\n\n\n\n<p>\u018aaya gawar kuma ta Tafawa \u0181alewa ne, amma idan ba domin kayan da suke jikinsa ba wanda aka tabbatar su ne a jikinsa lokacin da aka tafi da shi, to da babu wanda zai iya gane gawarsa saboda yadda ta \u0253aci.<\/p>\n\n\n\n<p>Daga nan Babankowa ya umarci \u01b4an sandan da suke wajen cewar, su tsaya su kula da wajen zai je ya dawo. Lokacin da Babankowa ya tafi ya sanarwa da duk wani mai ruwa da tsaki cikin harkar tsaron Najeriya cewar an gano gawar Firaminista.<\/p>\n\n\n\n<p>Kafin ya sanarwa Shugaban Rundunar Sojojin Najeriya, Ironsi kam shi ne ma ya kira shi yake tambayar sa cikin Harshen Hausa, shin da gaske ya gano gawar Tafawa \u0181alewa? Ya ce, tabbas haka ne.<\/p>\n\n\n\n<p>Nan take suka nufo zuwa wajen da gawar take, suka samu wa\u0257annan \u01b4an sandan da Babankowa ya bari a wajen su na jira.<\/p>\n\n\n\n<p>Bayan sun iso wajen, aka fara maganar jana\u2019izar Firaministan amma babban abokinsa Madakin Bauchi ya ce, lallai Bauchi za a dawo da gawar domin a yi masa sutura.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Jana\u2019izar Tafawa \u0181alewa<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Haka kuwa aka yi, Madakin Bauchi ya bai wa Kaftan umarnin cewa, ya je ya sanarwa matan Tafawa \u0181alewa; Haj. Jummai da Haj. Laraba, abin da yake faruwa kuma su shirya tafiya Bauchi.<\/p>\n\n\n\n<p>Daga nan aka \u0257auki gawar aka wuce da ita Filin Jirgin Sama na Ikeja. Kwamishinan \u01b4an sandan Legas, Shugaban Rundunar \u01b4an sandan \u0198asa, Mataimakin Shugaban Rundunar \u01b4an sanda, Ministan Harkokin Tsaro, Madakin Bauchi da Ministan Albarkatun \u0198asa da Makamashi Alh. Yusuf Maitama Sule, su ne suka raka gawar Tafawa \u0181alewa zuwa birnin Bauchi kuma sun isa ne Ranar Bikin Sallar Azumi, saboda duk abubuwan da suka faru lokacin Juyin Mulkin, sun faru ne cikin Azumin watan Ramadan.<\/p>\n\n\n\n<p>Daga nan aka yi wa gawar sutura kamar yadda Addinin Musulunci ya tanada.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Wane Irin Kisa aka Yi Wa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato, Firimiyan Jihar Arewa?<\/strong><\/p>\n\n\n\n<div class=\"wp-block-media-text is-stacked-on-mobile\"><figure class=\"wp-block-media-text__media\"><img decoding=\"async\" width=\"300\" height=\"219\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-15t204745627939665220526882-300x219.jpg\" alt=\"\" class=\"wp-image-3293 size-full\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-15t204745627939665220526882-300x219.jpg 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-15t204745627939665220526882-600x437.jpg 600w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-15t204745627939665220526882.jpg 649w\" sizes=\"(max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/figure><div class=\"wp-block-media-text__content\">\n<p><em>Sir. Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato, Firimiyan Jihar Arewa. <\/em><\/p>\n<\/div><\/div>\n\n\n\n<p>Kisan da aka yi wa Sardauna a Gidan Gwamnatin Jihar Arewa da ke Kaduna; da yawan Mutane sun yi maganganu, wasu maganganun ma ba su da kan-gado, babu ilimi ko \u0257aya a ciki. Da yawan labaran da Mutane suke ya\u0257awa hankali ba zai \u0257auka ba.<\/p>\n\n\n\n<p>Hakan ya sa muka zurfafa bincike sosai don mu gane shin wane irin kisa aka yi wa Sardauna? Wasu Mawa\u0199an Hausa da wasu Mutane makusantar Sardauna, sun bada wasu labarai wa\u0257anda hankali ba zai \u0257auke su ba.<\/p>\n\n\n\n<p>Bincike ya tabbatar da cewa, shi wanda ya jagoranci, kisan su Sardauna Manjo Patrick Chukuma Kaduna Nzeogwu, ya da\u0257e da \u0199ullantar Sardaunan a Ransa, hakan ya sa ya fara horar da wasu Sojoji wanda mafi yawancinsu \u01b4an Arewa ne.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Nzeogwu Ya \u0198addamar da Samame<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Ya \u0199addamar da samame (Operations) masu sunaye kamar haka<\/p>\n\n\n\n<p>Damusa<br \/>Zaki<br \/>Giwa<\/p>\n\n\n\n<p>Irin wannan samamen shi Nzeogwu ya yi ta ba wa sojojin horo a kai. Su kansu Sojojin ba su san dalilin da ya sa yake ba su wannan horon ba.<\/p>\n\n\n\n<p>Kullun Dare yakan tara su, su dinga yin wannan Atisayen har Asuba. Duk da cewa, manyan Sojoji na kallon sa, su kansu ba su da masaniyar dalilin da ya sa yake ba su wannan horon ba, ya fake da cewar ya kamata a ce Sojoji na cikin shiri, kuma su ri\u0199a jiran ko-ta-kwana.<\/p>\n\n\n\n<p>Ranar 15 ga watan Janairun Daren Juma&#8217;a wurin \u0199arfe 12 na Dare, Nzeogwu ya kwaso wasu Kuratan Sojoji su 45, wasu ma suka ce su 50, \u01b4an Arewacin Najeriya.<\/p>\n\n\n\n<div class=\"wp-block-media-text is-stacked-on-mobile\"><figure class=\"wp-block-media-text__media\"><img decoding=\"async\" width=\"300\" height=\"169\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/fb_img_17369620626687076333693759942110-300x169.jpg\" alt=\"\" class=\"wp-image-3294 size-full\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/fb_img_17369620626687076333693759942110-300x169.jpg 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/fb_img_17369620626687076333693759942110-600x338.jpg 600w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/fb_img_17369620626687076333693759942110.jpg 720w\" sizes=\"(max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/figure><div class=\"wp-block-media-text__content\">\n<p><em>Hoton Sir. Ahmadu Bello Sardauna na Karshe. <\/em><br \/><br \/><em>Firimiya Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato tare da ma&#8217;aikatansa A Lemu da kuma M. Attah. Wannan ne hoto na \u0199arshe da aka \u0257auke shi kafin a kashe shi. A Ranar Juma&#8217;a 14 Ga Watan Junairu 1966. Hoto: National Achieves<\/em><\/p>\n<\/div><\/div>\n\n\n\n<p>Nzeogwu, ya kai su wani wuri inda a yanzu wata Makarantar Aikin Noma take a Mando. A wancan lokacin wurin \u0199urmumin daji ne. Daga nan ne suka taso suka nufo Gidan Sardauna.<\/p>\n\n\n\n<p>Bincike ya tabbatar da cewar, ya kashe wani Soja \u0257aya da ya nemi ya yi masa taurin Kai. Kamar yadda abun ya faru wannan Sojan ya tsananta da tambayar cewa, wane irin aiki na musamnan za su yi? A ina ne kuma za su yi wannan aikin na musamman? Kuma ya ya yanayin aikin yake?<\/p>\n\n\n\n<p>Bayan isowarsu \u0198ofar Gidan Sardauna, Nzeogwu, ya nuna wa wa\u0257annan Sojojin da ya kwaso cewar, kun san ko nan Gidan waye? Suka amsa masa da cewar, Gidan Baban duk wani \u0257an Arewa ne Sardauna.<\/p>\n\n\n\n<p>Nzeogwu ya ce musu, to mai Gidan nan shi muka fito kashe wa. Nan take wani Sargeant Bayaraben Ilori, Sajen Duru, ya ce Allah ya kiyaye shi ya sa hannu a kashe Baban shi. Bincike ya tabbatar da cewa Sajen Duru ya yi yun\u0199urin tsalake Titi ya gudu, amma nan take Nzeogwu, ya harbe shi.<\/p>\n\n\n\n<p>Makaman da Nzeogwu ya zo da su Gidan Sardauna sun fi \u0199arfin na Juyin Mulki, sai dai na Ya\u0199i da wata \u0198asa. Nan take Nzeogwu ya umarci wani kurtun Soja \u0257an asalin Jihar Kebbi Musa Manga, ya ce ya harba bindigar da ake amfani da ita wurin kakka\u0253o Jirgin Saman Ya\u0199i MM 400\u00d7 a saman rufin \u0257akin da Sardauna yake.<\/p>\n\n\n\n<p>\u0198arar wannan bindigar ta tada hankalin duk wani mutumin da ke Unguwar Shanu, da Unguwar Sarki.<\/p>\n\n\n\n<p>Wannan bindigar ita ce tasa rufin \u0257akin ya kama da wuta. Sardauna da matansa da yaran da yake ri\u0199e da su na \u01b4an&#8217;uwa da abokan arziki da duk ma&#8217;aikatan da ke gidan sun taru a farfadiyar da ake aje Mota na Gidan.<\/p>\n\n\n\n<p>Sardauna, ya tsinci kansa a wani hali na ba shi da wani mataimaki sai Allah. Ba shi da makamin da zai kare kansi balle ma ya kare iyalansa da su. Bincike ya tabbatar da cewar, a nan farfajiyar ajiye Motocin ne Nzeogwu ya samu Sardauna da matansa guda uku da Larai matar Ali Odilin Sardauna, da Ali Odili.<\/p>\n\n\n\n<p>A nan an samu mabambantan maganannu, matan Sardauna Jabbo da Goggon Bichi sun bada labari iri \u0257aya, duk da cewar ba lokaci \u0257aya aka yi hirar da su ba.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Jabbo<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Ta ce, duk kanmu muna cikin fargaba mun ru\u0257e saboda matsanancin \u0199arar harbe-harbe da muke ji, a wannan lokacin Sardauna na tsaye ne ya na jan Carbi, Hafsat uwargidansa ta na rungume da shi, dukkanmu muna kuka mun rasa inda za mu saka kanmu.<\/p>\n\n\n\n<p>Da abubuwa suka yi tsanani shi Sardauna ya ce mana, ni tawa ta \u0199are ku nake ma addu&#8217;ar Allah ya kare ku daga sharin wayannan mutanan.<\/p>\n\n\n\n<p>Hafsat, ta ri\u0199e Sardauna da \u0199arfin-tsiya, nima ina manne da jinkinsa haka Goggon Bichi. Larai matar Ali Odali na kusa da ni.<\/p>\n\n\n\n<p>Lokacin da Nzeogwu ya zo, ya zo ne da wata Fitila mai Haske irin ta Mafarauta a goshinsa, da yake Gidan akwai Duhu, babu wuta, da farin Hankici a wuyansa. Da yake muna da yawa da yara da mu matanshi mun kewaye shi a wannan lokacin.<\/p>\n\n\n\n<p>Nzeogwu, ya yi ta mana barazanar cewa idan ba mu kauce ba zai harbe mu ya kashe mu dukkan mu. Amma muka yi burus da shi. Bayan \u0199o\u0199arin sa mana \u0199arfi da ya yi, mu ka yi masa tirjya, ya sa kan bindiga ya buge ni a Goshi, Jini na ya yi tsartuwa na fa\u0257i sumammiya. Ta ce kamar yadda abubuwa suka faru, a nan ne dai Nzeogwu ya harbi Sardauna a Goshi da zuciyarsa.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Goggon Bichi<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Ta ce, lokacin da Nzeogwu ya zo da Fitila mai Haske a goshinsa, da farin Hankici a wuyansa. Mu kuma dukkanmu mun kewaye Sardauna, Hafsat ta ri\u0199e shi \u0199am-\u0199am. Jabbo ma na ri\u0199e da shi, ni ma ina manne da shi. Nzegowu ya yi barazanar zai harbe mu amma mu da yara kuka kawai muke muna Salati. Goggon Bichi ta ce ta na da ya\u0199inin cewa, kafin ma shi Nzeogwu ya harbi Sardauna Allah ya amsa ran Sardaunan. Ta kawo dalilai \u0199warara guda biyu da yake tabbatar da abun da take fa\u0257a.<\/p>\n\n\n\n<p>Abu na farko ta ce, babu yadda zaa a sa kan bindiga a bugi \u0257aya daga cikin Matansa har ta fa\u0257i ta suma ba, a ce Sardaunan bai yi magana ba, ta ce abu ne wanda ba mai yi wu ba.<\/p>\n\n\n\n<p>Goggon Bichi, ta ce ko da mai zai faru da shi kuwa, wallahi Sardauna sai ya yi magana kai sai dai bayan ransa wallahi, ba zai ta\u0253a ganin ya na raye a wula\u0199anta Matarsa ba.<\/p>\n\n\n\n<p>Dalilinta na biyu kuwa, Nzeogwu ya harbi Hafsat kafin ya harbi Sardauna, nan ma ta ce daga nan ne ma na tabbatar da cewa Sardauna ba shi da rai, wallahi ya na dai tsaye ne kawai amma Allah ya zare ransa. Ta ce har Nzeogwu ya harbe shi ba a ji ihunsa, ko \u0199ara, ko wata magana ba. Hakan ma ya \u0199ara tabbatar mana da cewa ya rasu.<\/p>\n\n\n\n<p>Jabbo da Goggon Bichi, da Larai Matar Ali Odilin Sardauna, wacce ita ma ganau ce, sun tabbatar da cewar, in ma da wani Namiji a sanda abun ya faru to Ali Odili ne.<\/p>\n\n\n\n<p>Matan na Sardauna guda biyu da Larai Matar Ali Odili sun ce, duk Mazajen da ke Gidan sun gudu. Suka ce duk wani mutum yau da ya tara \u01b4an Jaridu ya ce ya san yadda aka kashe Sardauna, ko a gabansa aka kashe Sardauna \u0199arya ya ke yi.<\/p>\n\n\n\n<p>Marigayi Sheikh Abubakar Gumi, shi ne ya yi wa Sardauna wanka ya tabbatar da cewar tabbas akwai harsashi a goshin Sardauna, a Goshi aka harbe shi.<\/p>\n\n\n\n<div class=\"wp-block-media-text is-stacked-on-mobile\"><figure class=\"wp-block-media-text__media\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"290\" height=\"300\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-15t2047186619691649909741752-290x300.jpg\" alt=\"\" class=\"wp-image-3300 size-full\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-15t2047186619691649909741752-290x300.jpg 290w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-15t2047186619691649909741752.jpg 545w\" sizes=\"(max-width: 290px) 100vw, 290px\" \/><\/figure><div class=\"wp-block-media-text__content\">\n<p><em>Firimiyan Arewa, Sir Ahmadu Bello Sardauna, tare da Sheikh Abubakar Gumi, mai taimaka masa a harkokin Addini. Hoto: Wikipedia <\/em><\/p>\n<\/div><\/div>\n\n\n\n<p><strong>\u0198arin Bayani: Ba za mu iya kawo dukkan Hikayoyin a nan ba amma za a iya neman Littafi mai suna; &#8216;Jarumar da Ba&#8217;a Rubuta ba Hafsat Ahmadu Bello,&#8217; wanda Ladi S. Adamu ta rubuta.<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p><strong>Yadda Muka Yi da Nzeogwu Bayan Ya Kashe Sardauna &#8211; Sheikh Abubakar Gumi<\/strong><\/p>\n\n\n\n<div class=\"wp-block-media-text is-stacked-on-mobile\"><figure class=\"wp-block-media-text__media\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"300\" height=\"225\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-15t2052193081788309069826644-300x225.jpg\" alt=\"\" class=\"wp-image-3295 size-full\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-15t2052193081788309069826644-300x225.jpg 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-15t2052193081788309069826644-600x450.jpg 600w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-15t2052193081788309069826644.jpg 640w\" sizes=\"(max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/figure><div class=\"wp-block-media-text__content\">\n<p><em>Sheikh Abubakar Gumi, mashawarcin Sardauna, akan harkokin da suka shafi Addinin Musulunci. Hoto: Wikipedia.<\/em><\/p>\n<\/div><\/div>\n\n\n\n<p>Kamar \u0199arfe hu\u0257u na Asuba, Ranar Juma&#8217;a aka bugo mun Waya, bayan na \u0257auka sai na ji Ministan Ilimi na Arewa Alhaji Isa Kaita, ya ce min, Sojoji fa sun yi Juyin Mulki, har an kai ma Gidan Sardauna hari, kamar yadda ya ce min, duk Manyan Jami&#8217;an Gwamnati sun \u0253uya.<\/p>\n\n\n\n<p>Ya ce min, ya yi magana da Hassan Usman Katsina, amma Hassan dai a lokacin ya ce masa babu abin da zai iya yi. Hassan ya ce masa a wannan lokacin ma, ya na ganawa ne da bijirarrun Sojojin.<\/p>\n\n\n\n<p>Isa Kaita ya ce, ya kamata ni in je Gidan Sardauna in gane ma Idanuna abin da ke faruwa.<\/p>\n\n\n\n<p>Bayan na kimtsa na yi Sallar Subahi, na kuma kama hanya na nufi Gidan Sardauna, na je na iske Gidan an yi kacha-kacha da shi, alamu sun nuna an yi amfani da manyan Makamai wurin lalata Gidan. Har lokacin da na isa Gidan haya\u0199i ne a turnu\u0199e. Sai wasu tsirarun Sojoji ne a tsaye da Bindigogi a hannunsu, ko ina tsit.<\/p>\n\n\n\n<p>Haka na wuce su na kutsa kaina cikin Gidan, ina shiga na ci karo da Gawar Firimiya a kwance a filin da ake aje Motoci na Gidan.<\/p>\n\n\n\n<p>Nan da nan, na ce a \u0257auki Gawar a kai ta Gidan Sarkin Musulmi, da ke Unguwar Sarki, Sardauna, da shi da Uwargidansa Hafsat aka kashe su.<\/p>\n\n\n\n<p>Bayan mun gama kimtsa shi, Rana ta fara \u0257agowa, ni ne na sallaci duka gawarwakin.<\/p>\n\n\n\n<p>Ina sa ne kuma da cewar, an yi babban rashin da nan kurkusa abu ne mawuyace a samu kamarsa.<\/p>\n\n\n\n<p>A kan hanyata ta dawowa gida daga wurin jana&#8217;izar Sadauna, na wuce gun-gun mutane sun taru suna ta alhinin abin da ya faru. Bayan na samu natsuwa abubuwa sun koma kamar yadda suke, Ranar komawa aiki na shirya kamar kullum na tafi wurin aikina.<\/p>\n\n\n\n<p>Ina cikin ofishina da Safe sai ga Motar Sojoji, cike da Sojoji, ta shigo harabar wurin aikina. Wasu daga cikin Sojojin suka sauko a Mota suka tambayi inda ofishina yake.<\/p>\n\n\n\n<p>Bayan sun shigo ofishina suka yi min gaisuwa irinta ta girmamawa, suka ce an turo ne su tafi da ni Maigidansu Nzeogwu, ya na son ganina.<\/p>\n\n\n\n<p>Kuma zan shiga motarsu ne, tilas su tafi da ni amma zan iya sa wani cikin ma&#8217;aikatana ya bi mu a baya shi sai ya dawo da ni.<\/p>\n\n\n\n<p>Na ta shi na bi su ban yi musu ba, na umarci Direba na ya bi ni da Mota, bayan mun gama ganawa ya dawo da ni.<\/p>\n\n\n\n<p>Bayan mun isa Bariki Sojan, in da shi Nzeogwu yake. Na ga Sojoji da yawa su na gadin Barikin, ko wane Soja sa\u0253e yake da Bindigarsa.<\/p>\n\n\n\n<p>Bayan mun yi fakin muka sauko daga Mota muka shiga cikin ofishin, cikinmu ba wanda ya yi ma wani magana tsakanina da wayannan Sojojin.<\/p>\n\n\n\n<p>Bayan sun kaini inda Nzeogwu yake, ya kuma tare ni cikin fara&#8217;arsa na kuma zauna akan kujera, sai ya fara magana cikin tattausar murya.<\/p>\n\n\n\n<p>Abin da yake son sani shi ne; ina muka \u0253oye makaman da muka sayo?<\/p>\n\n\n\n<p>Wannan tambayar tasa taba ni matu\u0199ar mamaki, na ga ni dai a rayuwata ban ma ta\u0253a ganin Nzeogwu ba, ban kuma ta\u0253a wata ala\u0199a ta rayuwa da shi ba. Ni a tunani ma shi ne ya kira ni ya yi mun ta&#8217;aziyyar rashin Sardauna, da na yi ko kuma ya nuna danasani a kan abin da ya aikata.<\/p>\n\n\n\n<p>Dama ban yi tsammanin kalamai na ba ni ha\u0199uri daga gare shi ko nadama a kan abin da ya aikata ba, tun da na lura ya na al&#8217;afari da abin da ya aikatan.<\/p>\n\n\n\n<p>Abin da kuma ya \u0199ara ba ni mamaki, wanda suka sa\u0253i Makamai suka yi Juyin mulki wai a lokacin ne suke \u0199o\u0199arin tattara hujjojinsu ko kuma dalilan ham\u0253arar da wannan gwamnatin?<\/p>\n\n\n\n<p>Sai na gama kafin in ba shi amsar tambayarsa yakamata in nemi \u0199arin bayani daga gare shi.<\/p>\n\n\n\n<p>Sai ya ce min a irin labaran da ya samu an ce masa, mun siyo Makamai masu tarin yawa, mun shigo da su cikin \u0198asa, kuma mun siyo makaman ne daga \u0198asashen Gabas ta Tsakiya. Kuma, niyyarmu ita ce; mu \u0199addamar da Jihadi a kan wa\u0257anda ba Musulmi ba, shi ya sa yake so in fa\u0257a masa inda muka \u0253oye makaman.<\/p>\n\n\n\n<p>Lokacin da na zo ba shi amsar tambayarsa, na tabbatar masa cewar ni a wurinsa ma na fara jin wannan maganar, na kuma tabbatar ina magana ne a matsayina na mashawarcin Sardauna, akan harkokin da suka shafi Addinin Musulunci. Kuma na tabbatar masa da cewa Sardauna, bai ta\u0253a zuwa wata Kasar Larabawa a matsayinsa na Firimiya ba tare da dani ba. Kuma ban ta\u0253a ji ya yi maganar Makamai ba a wata \u0198asar Larabawa, balle ma har mu siyo mu shigo da su Najeriya, da sunan wai za mu ya\u0199i wa\u0257anda da ba Musulmai ba.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Wane ne Ifeajuna wanda Ya kashe Firimiyan Najeriya?<\/strong><\/p>\n\n\n\n<div class=\"wp-block-media-text is-stacked-on-mobile\"><figure class=\"wp-block-media-text__media\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"214\" height=\"300\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/fb_img_17369599876023871494391373940048-214x300.jpg\" alt=\"\" class=\"wp-image-3296 size-full\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/fb_img_17369599876023871494391373940048-214x300.jpg 214w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/fb_img_17369599876023871494391373940048.jpg 468w\" sizes=\"(max-width: 214px) 100vw, 214px\" \/><\/figure><div class=\"wp-block-media-text__content\">\n<p><em>Emmanuel Arinze Ifeajuna, wadda ya kashe Sir. Abubakar Tafawa \u0181alewa, Firaministan Najeriya. Hoto: Muham<\/em>mad Cisse<\/p>\n<\/div><\/div>\n\n\n\n<p><strong>Daga wanda ya lashe Lambar Zinariya na Commonwealth na farko a Afirka zuwa Fuskantar hukuncin kisa a Ranar 25 ga watan Satumba na 1967.<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Emmanuel Arinze Ifeajuna (1935-1967) Hafsan Sojan Najeriya ne kuma \u0257aya daga cikin manyan jigo a Juyin Mulkin da Sojoji suka yi a Ranar 15 ga watan Janairun 1966 a Najeriya.<\/p>\n\n\n\n<p>An haife shi a Ranar 1 ga Disamba, 1935 a Onitsha, yankin Gabashin Najeriya (yanzu jihar Anambra). Ifeajuna, ya halarci Kwalejin Gwamnati da ke Umuahia daga baya kuma ya halarci Kwalejin Jami\u2019ar Ibadan, inda ya kasance Memba na Fitacciyar \u0198ungiyar Wasan Kwaikwayo ta Jami\u2019ar Ibadan (IUC).<\/p>\n\n\n\n<p>Ya kuma kasance \u0199wararren \u0257an wasa, kuma ya wakilci Najeriya a Gasar Guje-Guje da Tsalle-Tsalle a Gasar Daular Birtaniya da ta Commonwealth a shekarar 1954.<\/p>\n\n\n\n<p>Bayan kammala karatunsa a Makarantar Kimiyya, a Kwalejin Jami&#8217;ar Ibadan kuma ya shiga harkar Siyasa.<\/p>\n\n\n\n<p>Ifeajuna ya shiga Aikin Sojan Najeriya a shekarar 1959, kuma ya sami horon Aikin Soja a Najeriya da Ingila. Ya \u0199ara samun horo a Makarantar Soji ta Royal Military Academy da ke Sandhurst a \u0198asar Ingila, kuma an ba shi mu\u0199amin Hafsa a Rundunar Sojin Najeriya.<\/p>\n\n\n\n<p>Cikin \u0199an\u0199anin lokaci Ifeajuna ya haye mu\u0199ami kuma ya zama Manjo a Sojojin Najeriya.<\/p>\n\n\n\n<p>A Ranar 15 ga watan Janairun 1966, wasu gungun Matasa Hafsoshin Soja ciki har da Emmanuel Ifeajuna, suka yi Juyin Mulki a Najeriya.<\/p>\n\n\n\n<p>Wani \u0253angare na Sojojin Najeriya ne suka shirya Juyin Mulkin, wanda bai gamsu da yadda Gwamnatin \u0198asar ke zargin cin hanci da rashawa da kuma rikicin yankin Jihar Yamma da ake fama da shi a \u0198asar ba. Juyin Mulkin dai, ya yi sanadiyar kifar da Gwamnatin Firaministan Najeriya, Sir. Abubakar Tafawa \u0181alewa da kuma wasu shugabannin Siyasa da Sojoji, da ma kashe su.<\/p>\n\n\n\n<p>Sai dai, Juyin Mulkin bai cimma burin da aka sa a gaba ba, ya kuma haifar da wasu abubuwa da suka jefa Najeriya cikin wani yanayi na ta\u0253ar\u0253arewar Siyasa.<\/p>\n\n\n\n<p>Ifeajuna, ya tsere zuwa Ghana, sanye da kayan mata. Bayan watanni 20 ya dawo, ya fafata a Ya\u0199in Basasar Najeriya, inda ya shiga \u0253angaren Sojojin Biyafara.<\/p>\n\n\n\n<p>Ojukwu ya zargi Ifeajuna da wasu Jami\u2019ai uku da laifin \u0199ulla ma\u0199ar\u0199ashiya da Cin Amanar \u0198asa da fuskar taimakawa Najeriya, zargin da suka musanta, sun ce su na \u0199o\u0199arin ceto rayuka da \u0198asarsu ta hanyar tattaunawa da Gwamnatin Tarayya da kuma sake ha\u0257e Najeriya.<\/p>\n\n\n\n<p>Ojuwku ya sa an harbe su duka, a Ranar 25 ga watan Satumbar 1967.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>\u0198arin Bayani: Idan ka ta\u0253a amfani da wannan littafin tun kana yaro a makaranta a Najeriya, lura cewa hoton da ke kan bangon littafin Ifeajuna ne a lokacin a lokacin da yake wasan da ya sami lambar Zinariya da ya yi nasara a gasar Commonwealth a shekarar 1954.<\/strong><\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"482\" height=\"305\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/fb_img_17369599896631974219294613705985.jpg\" alt=\"\" class=\"wp-image-3298\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/fb_img_17369599896631974219294613705985.jpg 482w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/fb_img_17369599896631974219294613705985-300x190.jpg 300w\" sizes=\"(max-width: 482px) 100vw, 482px\" \/><\/figure>\n\n\n\n<p><strong>Jerin Sunayen Jagororin Sojojin da Suka yi Juyin Mulki na Farko a Najeriya<\/strong><\/p>\n\n\n\n<ol class=\"wp-block-list\">\n<li>Emmanuel Ifeajuna<\/li>\n\n\n\n<li>Manjo Chukuma Nzeogwu (Kaduna Nzeogwu)<\/li>\n\n\n\n<li>Timothy Onwuatuegwu<\/li>\n\n\n\n<li>Adewale Ademoyega<\/li>\n\n\n\n<li>Chris Anuforo<\/li>\n\n\n\n<li>Humphrey Chukwuka<\/li>\n\n\n\n<li>Don Okafor<\/li>\n<\/ol>\n\n\n\n<p><strong>Sunayen Wa\u0257anda aka Kashe a Juyin Mulki da Nzeogwu Kaduna Ya Jagoranta<\/strong><\/p>\n\n\n\n<div class=\"wp-block-media-text is-stacked-on-mobile\"><figure class=\"wp-block-media-text__media\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"244\" height=\"300\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-15t2113054673182219651464729-244x300.jpg\" alt=\"\" class=\"wp-image-3299 size-full\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-15t2113054673182219651464729-244x300.jpg 244w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-15t2113054673182219651464729.jpg 480w\" sizes=\"(max-width: 244px) 100vw, 244px\" \/><\/figure><div class=\"wp-block-media-text__content\">\n<p><em>Manjo Chukuma Nzeogwu, wadda ya jagoranci kashe Firimiyan Arewa, Ahmadu Bello Sardauna da sauran wasu jigajigan \u01b4an Siyasa. Hoto: African Pan Achieves<\/em><\/p>\n<\/div><\/div>\n\n\n\n<p>Farar Hula<\/p>\n\n\n\n<ol class=\"wp-block-list\">\n<li>Firaminista Abubakar Tafawa \u0181alewa<\/li>\n\n\n\n<li>Firimiya Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato<\/li>\n\n\n\n<li>Firimiya Samuel Ladoke Akintola<\/li>\n\n\n\n<li>Ministan Ku\u0257i Festus Okotie-Eboh<\/li>\n\n\n\n<li>Ahmed Ben Musa (Babban Mataimakin Sakataren Tsaro na Sardauna Ahmadu Bello)<\/li>\n\n\n\n<li>Hafsatu Bello (Matar Sardauna \u01b3ar Sarkin Musulmi Abubakar na Uku)<\/li>\n\n\n\n<li>Madam Latifat Ademulegun<\/li>\n\n\n\n<li>Zarumi Sardauna,<\/li>\n\n\n\n<li>Ahmed Fatigi (Direban Sardauna Ahmadu Bello)<\/li>\n<\/ol>\n\n\n\n<p>Sojoji da \u01b3ansanda<\/p>\n\n\n\n<ol class=\"wp-block-list\">\n<li>Brig. Samuel Ademulegun<\/li>\n\n\n\n<li>Brig. Zakariya Maimalari<\/li>\n\n\n\n<li>Col. Ralph Shodeinde<\/li>\n\n\n\n<li>Col. Kur Mohammed<\/li>\n\n\n\n<li>Laftanar Kanal Abogo Largema<\/li>\n\n\n\n<li>Lt. Col. James Pam<\/li>\n\n\n\n<li>Lt. Col. Arthur Unegbe<\/li>\n\n\n\n<li>Sajan Daramola Oyegoke (Ya taimaka wa Nzeogwu a harin da aka kai Gidan Sardauna kuma a cewar rahoton \u01b4an sanda, Nzeogwu ne ya kashe shi)<\/li>\n\n\n\n<li>PC Yohanna Garkawa<\/li>\n\n\n\n<li>Lance Kofur Musa Nimzo<\/li>\n\n\n\n<li>PC Akpan Anduka<\/li>\n\n\n\n<li>PC Hagai Lai<\/li>\n\n\n\n<li>Philip Lewande.<\/li>\n<\/ol>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>A ranar 15 ga watan Janairun 1966, yayin Juyin Mulki \u0199ar\u0199ashin jagorancin Manjo Emmanuel Ifeajuna da Manjo Nzeogwu, da sauransu, inda aka \u0199ashe manyan shugabannin Siyasa da suka ha\u0257a da; Firaministan Najeriya na farko, Sir. Abubakar Tafawa \u0181alewa, da Firimiyan Jihar Arewa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato, da kuma wasu jagororin \u0198asar 22. Kamar yadda a [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":3303,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"inline_featured_image":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[88],"tags":[],"class_list":["post-3302","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-tarihi"],"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v27.0 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Tarihin Juyin Mulki na Farko a Najeriya<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"noindex, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_US\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Tarihin Juyin Mulki na Farko a Najeriya\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"A ranar 15 ga watan Janairun 1966, yayin Juyin Mulki \u0199ar\u0199ashin jagorancin Manjo Emmanuel Ifeajuna da Manjo Nzeogwu, da sauransu, inda aka \u0199ashe manyan shugabannin Siyasa da suka ha\u0257a da; Firaministan Najeriya na farko, Sir. Abubakar Tafawa \u0181alewa, da Firimiyan Jihar Arewa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato, da kuma wasu jagororin \u0198asar 22. Kamar yadda a [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3302\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"Taskar Nasaba\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2025-01-15T20:19:46+00:00\" \/>\n<meta property=\"article:modified_time\" content=\"2025-01-16T14:21:11+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/FB_IMG_1736961896425.jpg\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"720\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"301\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/jpeg\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Salahuddeen Muhammad\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"Salahuddeen Muhammad\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Est. reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"23 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\/\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3302#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3302\"},\"author\":{\"name\":\"Salahuddeen Muhammad\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753\"},\"headline\":\"Tarihin Juyin Mulki na Farko a Najeriya\",\"datePublished\":\"2025-01-15T20:19:46+00:00\",\"dateModified\":\"2025-01-16T14:21:11+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3302\"},\"wordCount\":4655,\"commentCount\":0,\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3302#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/FB_IMG_1736961896425.jpg\",\"articleSection\":[\"Tarihi\"],\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3302#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3302\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3302\",\"name\":\"Tarihin Juyin Mulki na Farko a Najeriya\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3302#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3302#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/FB_IMG_1736961896425.jpg\",\"datePublished\":\"2025-01-15T20:19:46+00:00\",\"dateModified\":\"2025-01-16T14:21:11+00:00\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3302#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3302\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3302#primaryimage\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/FB_IMG_1736961896425.jpg\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/FB_IMG_1736961896425.jpg\",\"width\":720,\"height\":301},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3302#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Tarihin Juyin Mulki na Farko a Najeriya\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"description\":\"\",\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\"},\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-US\"},{\"@type\":\"Organization\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\",\"logo\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png\",\"width\":343,\"height\":345,\"caption\":\"Taskar Nasaba\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/\"}},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753\",\"name\":\"Salahuddeen Muhammad\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg\",\"caption\":\"Salahuddeen Muhammad\"},\"description\":\"\u018aanjarida, marubuci, mai manufar bun\u0199asa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.\",\"sameAs\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\"],\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?author=1\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Tarihin Juyin Mulki na Farko a Najeriya","robots":{"index":"noindex","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"og_locale":"en_US","og_type":"article","og_title":"Tarihin Juyin Mulki na Farko a Najeriya","og_description":"A ranar 15 ga watan Janairun 1966, yayin Juyin Mulki \u0199ar\u0199ashin jagorancin Manjo Emmanuel Ifeajuna da Manjo Nzeogwu, da sauransu, inda aka \u0199ashe manyan shugabannin Siyasa da suka ha\u0257a da; Firaministan Najeriya na farko, Sir. Abubakar Tafawa \u0181alewa, da Firimiyan Jihar Arewa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato, da kuma wasu jagororin \u0198asar 22. Kamar yadda a [&hellip;]","og_url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3302","og_site_name":"Taskar Nasaba","article_published_time":"2025-01-15T20:19:46+00:00","article_modified_time":"2025-01-16T14:21:11+00:00","og_image":[{"width":720,"height":301,"url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/FB_IMG_1736961896425.jpg","type":"image\/jpeg"}],"author":"Salahuddeen Muhammad","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"Salahuddeen Muhammad","Est. reading time":"23 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3302#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3302"},"author":{"name":"Salahuddeen Muhammad","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753"},"headline":"Tarihin Juyin Mulki na Farko a Najeriya","datePublished":"2025-01-15T20:19:46+00:00","dateModified":"2025-01-16T14:21:11+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3302"},"wordCount":4655,"commentCount":0,"publisher":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3302#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/FB_IMG_1736961896425.jpg","articleSection":["Tarihi"],"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3302#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3302","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3302","name":"Tarihin Juyin Mulki na Farko a Najeriya","isPartOf":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3302#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3302#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/FB_IMG_1736961896425.jpg","datePublished":"2025-01-15T20:19:46+00:00","dateModified":"2025-01-16T14:21:11+00:00","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3302#breadcrumb"},"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3302"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3302#primaryimage","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/FB_IMG_1736961896425.jpg","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/FB_IMG_1736961896425.jpg","width":720,"height":301},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3302#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/taskarnasaba.com\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Tarihin Juyin Mulki na Farko a Najeriya"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/","name":"Taskar Nasaba","description":"","publisher":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization"},"potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-US"},{"@type":"Organization","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization","name":"Taskar Nasaba","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/","logo":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png","width":343,"height":345,"caption":"Taskar Nasaba"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/"}},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753","name":"Salahuddeen Muhammad","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/image\/","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg","caption":"Salahuddeen Muhammad"},"description":"\u018aanjarida, marubuci, mai manufar bun\u0199asa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.","sameAs":["https:\/\/taskarnasaba.com"],"url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?author=1"}]}},"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/FB_IMG_1736961896425.jpg","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3302","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=3302"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3302\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3305,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3302\/revisions\/3305"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/3303"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=3302"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=3302"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=3302"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}