{"id":3308,"date":"2025-01-17T18:30:15","date_gmt":"2025-01-17T18:30:15","guid":{"rendered":"https:\/\/taskarnasaba.com.ng\/?p=3308"},"modified":"2025-01-17T18:30:15","modified_gmt":"2025-01-17T18:30:15","slug":"shaka-zulu-tushen-alummar-zulu","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3308","title":{"rendered":"Shaka Zulu: Tushen al&#8217;ummar Zulu"},"content":{"rendered":"\n<p><strong>Shaka kaSenzangakhona, shi ne Sarkin Masarautar Zulu daga 1816 zuwa 1828. \u018aaya daga cikin mafi tasiri na Monalu Zulu, ya ba da umarnin yin gyare-gyare mai fa&#8217;ida wanda ya sake tsara sojojinsa suka zama gagarabadau.<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p><strong>Sunan Shaka Zulu na da Nasaba da Ya\u0199i<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Dakarunsa kan tarwatsa duk wanda ya sha masa gaba. DW ta yi hira da masanin tarihi Maxwell Shamase wanda yake ganin an gur\u0253ata tarihin Shaka.<\/p>\n\n\n\n<p>An fa\u0257i abubuwa da dama game da Shaka Zulu. Idan ana batun bambance gaskiya da \u0199agaggen labari, Maxwell Zakhele Shamase mashahuri ne. Shi da Mthandeni Patrick Mbatha, masanin tarihi daga Jami&#8217;ar Zululand a yanzu haka su na rubuta wani Littafi a kan mutumin da ke zama Gwarzon tarihi.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Me Ya Sa Za Ku Rubuta Tarihi Game da Shaka Zulu?<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Maxwell Shamase: Ba a yi wani rubutu mai yawa a game da Sarki Shaka ba musamman daga mahanga ta Afrika ba. Wasu daga cikin abubuwa wa\u0257anda mutanen da ba \u01b4an Afirka ba suka rubuta, an gur\u0253ata gaskiyar lamura a cikinsu. Muna so mu bayar da labarin daga mahanga ta \u01b4an Afrika.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Ya Ya Za Ka Bayyana Sarki Shaka?<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Kafin a haifi Shaka, wata Bokanya mai suna Sithayi, ta ba da labarin cewa za a haifi wani yaro wanda zai kawo sabon sauyi da kuma sabuwar \u0198asa. Ya kasance Soja \u0257anbaiwa a Afirka. Mutum ne wanda ya gina \u0198asa ba mai son kisa da zubar da jini ba. Kuma ba mutum ne mara tausayi \u0257an ina da da kisa ba.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Yaushe ne Kuma a Ina aka Haifi Shaka?<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>An haife shi a watan Juli na shekarar 1787 a cikin al&#8217;ummar Langeni inda mahaifiyarsa ta fito.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Ina Shaka Zulu Ya Samo Sunansa?<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Mahaifinsa mutum ne mai aiki da hankali (Senzangakhona). Mahaifiyarsa \u01b4ar Sarkin Nandi ce a Gidan Sarautar Mhlongo wanda ya rayu a wurin da ake kira &#8216;Langeni.&#8217; <\/p>\n\n\n\n<p>Sunan Shaka, ya samo asali ne daga wata cuta da ake kira &#8216;Ishaka.&#8217; Wannan cuta na sanya jikin Mata ya ri\u0199a ciwo da kasala da kuma kumburi. A lokacin da mahaifiyarsa wacce a wancan lokaci ba ta yi aure ba ta samu ciki, mutane sun yi tsammanin ta na fama ne da cutar Ishaka; yadda Shaka ya sami wannan sunan ke nan.<\/p>\n\n\n\n<p>Saboda haka ya kasance Shaka \u0257an Senzangakhona. A wancan lokaci sunan mahaifinka shi ne sunanka na biyu. Kuma sunan kakan Shaka shi ne Zulu.<\/p>\n\n\n\n<p>Lokacin da Zulu ya zama Sarki, sai Shaka ya ce, ya kamata mu sami al&#8217;adarmu mu kira kanmu mutanen Zulu. Shi ne na farko da ya kira jama&#8217;arsa mutanen Zulu, shi ya sa aka san shi a matsayin wanda ya kafa \u0198asar Zulu duk da cewa ya gaji Sarautar da ta da\u0257e tsawon zamani.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Shin Mahaifin Shaka, Senzangakhona, ya Amince \u018aansa ne?<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Ya yi ta \u0199o\u0199arin musantawa saboda ya na tsaron mahaifinsa, Sarki Zulu. Ga Yarima mai jiran Gadon Sarauta kamar Senzangakhona ya yi wa yarinya ciki kafin aure abin kunya ne wanda ka iya kai wa ga hukunci mai tsanani, ciki har da yiwuwar rasa damar yin Sarauta.<\/p>\n\n\n\n<p>Daga baya iyayensa suka amince kuma Senzangakhona ya biya ku\u0257in Sadaki wanda ya bai wa Nandi damar tare wa cikin iyalan Senzangakhona. Daga baya, an fitar da Nandi da Shaka daga Gidan Senzangakhona,<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Shin Ya Ya Aka Yi Haka ta Faru?<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Nandi, Mace ce mai \u0257agawa da saurin fushi da so a kullum ta ri\u0199a bai wa mutane umarni. A saboda haka, dangantakarsu ta kasance cike da rigingimu. Shi kuwa Senzangakhona, ba zai iya jurewa ba. Ya kore ta tare da Shaka. Sun yi ta watangaririya. <\/p>\n\n\n\n<p>Nandi ta ha\u0257u da Ngwati. Suka fara soyayya su ka ci gaba da zama tare inda ta haifi \u0199anwar Shaka. Bayan da aka kashe Ngwati, Sarkin Mthethwa Dingiswayo ya kar\u0253i \u01b4a\u01b4anta biyu.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Ya Ya aka Yi Shaka ya Shiga Cikin Rundunar Sojin Mthethewa?<\/strong><\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img fetchpriority=\"high\" decoding=\"async\" width=\"739\" height=\"415\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-17t1731277144666201618292217.jpg\" alt=\"\" class=\"wp-image-3307\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-17t1731277144666201618292217.jpg 739w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-17t1731277144666201618292217-300x168.jpg 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-17t1731277144666201618292217-600x337.jpg 600w\" sizes=\"(max-width: 739px) 100vw, 739px\" \/><\/figure>\n\n\n\n<p>Ya zama babban yaron Sarki Dingiswayo a lokacin da ya ke \u0257an shekaru 16 da haihuwa. Wannan kuwa ya kasance ne saboda basirarsa da kuma \u0199arfin zuciya. Ba a jima ba aka \u0257auke shi a matsayin maya\u0199i aka sa shi cikin Rundunar Izicwe.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Wane Tasiri Shaka Zulu Ya Yi a Rundunar Sojin Mthethwa?<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>A matsayin Kwamanda, ya hana maya\u0199an sanya Takalmi Fade, ya kuma umarce su, su ri\u0199a tafiya babu Takalmi. Haka kuma, ya hana amfani da dogon Mashi wanda maya\u0199a za su harbi abokin-gaba da shi.<\/p>\n\n\n\n<p>Maimakon haka, ya \u0253ullo da gajeren Mashi \u2018Iklwa&#8217; domin fa\u0257a dab da dab da abokin-gaba. Wannan ya tilasta wa maya\u0199ansa su matso kusa su sari abokin-gaba sannan su juya su sari wani da makami \u0257aya. Ya kuma \u0253ullo da dabarar raba maya\u0199a dama da hagu domin yi wa abokan gaba \u0199ofar rago.<\/p>\n\n\n\n<p>Tsarin ya yi kama da yanayin kahuna biyu na Karkanda. Ya zama mutumin da ake matu\u0199ar jin tsoronsa wanda kuma ya yi fice hatta a sauran \u0199abilu da Masarautu, a kan haka ne ma ya sami sunan &#8216;Nodumehleli&#8217; (wanda daga zaune ya ke sa Duniyata girgiza).<\/p>\n\n\n\n<p>Maya\u0199in Mthethwa shi ne wanda a \u0199arshe Shaka ya dam\u0199a wa Sarautar Senzangakhona.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Shin Babu Wanda Ya \u0198alubalanci Wannan Mataki?<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>A lokacin da mahaifinsa Senzangakhona ya rasu, Sarki Dingiswayo ya taimaka masa dawo wa wajen al&#8217;ummar mahaifinsa, inda ya ba shi maya\u0199a biyu su taimaka masa kar\u0253e ragamar mulki. Sai dai Senzangakhona ya fa\u0257a wa babban Wazirinsa cewa, \u0257ayan \u0257an nasa Sigujana shi ne Yarimansu mai jiran gado amma ba Shaka ba.<\/p>\n\n\n\n<p>Da isarsa sai ya kashe Sigujana kuma ya \u0199ar\u0253i Karagar Mulki a shekarar 1816 a matsayin Sarki. Bayan mutuwar Sarki Dingiswayo, Shaka Ya shigar da mutanen Mthethwa \u0199ar\u0199ashin Daularsa, sannan ya sa \u0199abilar da Dingiswayo ya ci da ya\u0199i cikin sojojin da ke \u0199ar\u0199ashin jagorancin Shaka. Ya kuma ci gaba da cin sauran \u0199abilu da ya\u0199i ya kuma mulke su.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Shaka Na da Mummuna Tunani Kan Aure, Inda Har ta Kai Wasu Mutane na Cewa Mai Yiwuwa \u018aanluwa\u0257i ne shi. Mene ne Dalilin Haka?<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Mummunan tunaninsa ga Aure ya faru ne sakamakon yadda ya ga aka yi wa mahaifiyarsa. Sannan an ci zalinsa matu\u0199a sakamakon tasowa da ya yi ba cikin danginsa ba kuma ba tare da mahaifinsa ba. Babu shakka ya na yin Jima&#8217;i da Mata to amma da zarar sun sami ciki sai ya mi\u0199a su ga \u0257an&#8217;uwansa, Mpande wanda ake gani a matsayin rauni.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Gaskiya ne Cewa, Shaka Zulu Ya na Kashe Matan da Ya Yi wa Ciki, Kamar Yadda Aka Yi Ta Ra\u0257e-ra\u0257i?<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Wannan ba gaskiya ba ne. Mun dai san cewar, akwai wani lokaci da wasu \u01b4an kasuwa farar fata suka farfa\u0257o da wata Mata da ta suma saboda zazza\u0253i mai zafi. Shaka da mutanensa sun yi tsammanin ta mutu. Sun ba ta magani su ka farfa\u0257o da ita. Shaka ya za\u0199u ya na so ya tabbatar ko da gaske ne \u01b4an kasuwar sun tayar da matacce.<\/p>\n\n\n\n<p>Ya bada umarnin a kashe wata Mata sannan ya umarci \u01b4an kasuwar su nuna ikonsu su tayar da ita wanda ko shakka babu ba su iya yin hakan ba. A wasu lokuta saboda son ganin \u0199wa\u0199waf, an shaida mana cewa, ya fe\u0257e cikin wata Mace mai ciki domin ganin yadda jariri ya ke girma a cikin ciki.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Mun ji Cewa, Shaka ya Kashe Mutane Kusan Miliyan \u018aaya, Wasu Daga Cikinsu Haka Kawai ko Kuma Wai Saboda Sun yi Gajarta. Shin Gaskiya ne?<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Wannan tunani ne na \u0198asashen Yamma, kuma ba gaskiya ba ne. Ku tuna mutane Miliyan 50 suka mutu a Ya\u0199in Duniya na biyu baya ga wasu Miliyoyi da suka rasa rayukansu a Ya\u0199in Duniya na \u0257aya. A saboda haka, wane ne ya fi rashin imani tsakanin Shaka da wa\u0257annan Turawa da suka haddasa Ya\u0199in Duniya na \u0257aya da na biyu? To amma ya kamata a \u0257auki kisan da aka aikata a wannan hali a yanayi na lokaci. Abu ne da mutane s ka saba da shi a wancan lokaci.<\/p>\n\n\n\n<p>Zai ba da dalilai da su ka sa aka aikata kisan. Alal misali, wa\u0257anda aka tabbatar da cewa Mayu ne an kashe su. Sarakuna a wancan zamani sun \u0257ore ta hanyar kashe abokan hamayyarsu.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Wata Hanya aka Kashe Shaka Zulu?<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>An kashe shi a cikin watan Satumba na shekarar 1828. Akwai wani makirci da aka shirya bisa jagorancin goggonsa. Babban dalili shi ne bayan mutuwar mahaifiyarsa Nandi, Shaka ya samu ta\u0253in hankali inda ya kashe mutane da dama ba tare da yin tunani ba, inda ya fake da jimamin mutuwar mahaifiyarsa.<\/p>\n\n\n\n<p>Wasu ya kashe su ne saboda sun ci zalinsa a lokacin da yake \u0257an yaro, yayin da wasu kuma aka kashe su saboda ba su nuna alhini sosai game da rasuwar mahaifisarsa ba.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Shin Matsala ce a Kira Shaka \u2018Ba\u0199i ko kuma Napoleon \u0257in Afirka?<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Gwarzon Soja ne \u0257anbaiwa na Afirka ba ba\u0199in Napoleon ba.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Me ya sa Ba Za a Ce da Napoleon Farin Shaka Ba?<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Bai ta\u0253a zuwa Turai ba kuma babu wani Bature da ya koyar da shi abubuwan da ya yi a fagen ya\u0199i. Sun fito ne daga baiwar da yake da ita.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Ko har Yanzu Shaka Zulu Ya na da Tasiri a Yau?<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Shi ne jigon ha\u0257in kan Zulu. Jam&#8217;iyyar Inkatha Freedom Party, wadda ta mamaye Kwazulu Natal ta danganta kanta da Sarki Shaka a matsayin tushenta. Sarakunan Zulu da al&#8217;ummarsu su na yin mubaya&#8217;a ga Sarautar Sarki Shaka har zuwa yau.<\/p>\n\n\n\n<p>Maxwell Zakhele Shamase, \u0199wararren masanin tarihin Zulu ya na da digirin-digirgir a tarihi da siyasar wannan zamani da kuma tarihin al&#8217;ummar Zulu. A yanzu haka ya na rubuta wani Littafi a kan Sarki Shaka. H Shamase shi ma Malami ne kuma Shugaban Tsangayar Koyar da Tarihi a Jami&#8217;ar Zululand wanda har ila yau ake kira &#8216;Unizulu.&#8217;<\/p>\n\n\n\n<p><strong>MADOGARA<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Shawarwari da suka danganci kimiyya a wannan \u0199asidar, an same su ne daga masana tarihi Farfesa Doulaye Konat\u00e9, da Dr. Lily Mafela, da Farfesa Christopher Ogbogbo, da DW, da kuma Gidauniyar Gerda Henkel.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Shaka kaSenzangakhona, shi ne Sarkin Masarautar Zulu daga 1816 zuwa 1828. \u018aaya daga cikin mafi tasiri na Monalu Zulu, ya ba da umarnin yin gyare-gyare mai fa&#8217;ida wanda ya sake tsara sojojinsa suka zama gagarabadau. Sunan Shaka Zulu na da Nasaba da Ya\u0199i Dakarunsa kan tarwatsa duk wanda ya sha masa gaba. DW ta yi [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":3306,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"inline_featured_image":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[93],"tags":[],"class_list":["post-3308","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-jiya-da-yau"],"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v27.0 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Shaka Zulu: Tushen al&#039;ummar Zulu<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"noindex, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_US\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Shaka Zulu: Tushen al&#039;ummar Zulu\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"Shaka kaSenzangakhona, shi ne Sarkin Masarautar Zulu daga 1816 zuwa 1828. \u018aaya daga cikin mafi tasiri na Monalu Zulu, ya ba da umarnin yin gyare-gyare mai fa&#8217;ida wanda ya sake tsara sojojinsa suka zama gagarabadau. Sunan Shaka Zulu na da Nasaba da Ya\u0199i Dakarunsa kan tarwatsa duk wanda ya sha masa gaba. DW ta yi [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3308\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"Taskar Nasaba\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2025-01-17T18:30:15+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-17t1731277144666201618292217.jpg\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"739\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"415\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/jpeg\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Salahuddeen Muhammad\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"Salahuddeen Muhammad\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Est. reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"8 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\/\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3308#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3308\"},\"author\":{\"name\":\"Salahuddeen Muhammad\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753\"},\"headline\":\"Shaka Zulu: Tushen al&#8217;ummar Zulu\",\"datePublished\":\"2025-01-17T18:30:15+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3308\"},\"wordCount\":1680,\"commentCount\":0,\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3308#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/52196437_803.png\",\"articleSection\":[\"Jiya Da Yau\"],\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3308#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3308\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3308\",\"name\":\"Shaka Zulu: Tushen al'ummar Zulu\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3308#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3308#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/52196437_803.png\",\"datePublished\":\"2025-01-17T18:30:15+00:00\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3308#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3308\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3308#primaryimage\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/52196437_803.png\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/52196437_803.png\",\"width\":575,\"height\":575},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3308#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Shaka Zulu: Tushen al&#8217;ummar Zulu\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"description\":\"\",\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\"},\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-US\"},{\"@type\":\"Organization\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\",\"logo\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png\",\"width\":343,\"height\":345,\"caption\":\"Taskar Nasaba\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/\"}},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753\",\"name\":\"Salahuddeen Muhammad\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg\",\"caption\":\"Salahuddeen Muhammad\"},\"description\":\"\u018aanjarida, marubuci, mai manufar bun\u0199asa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.\",\"sameAs\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\"],\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?author=1\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Shaka Zulu: Tushen al'ummar Zulu","robots":{"index":"noindex","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"og_locale":"en_US","og_type":"article","og_title":"Shaka Zulu: Tushen al'ummar Zulu","og_description":"Shaka kaSenzangakhona, shi ne Sarkin Masarautar Zulu daga 1816 zuwa 1828. \u018aaya daga cikin mafi tasiri na Monalu Zulu, ya ba da umarnin yin gyare-gyare mai fa&#8217;ida wanda ya sake tsara sojojinsa suka zama gagarabadau. Sunan Shaka Zulu na da Nasaba da Ya\u0199i Dakarunsa kan tarwatsa duk wanda ya sha masa gaba. DW ta yi [&hellip;]","og_url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3308","og_site_name":"Taskar Nasaba","article_published_time":"2025-01-17T18:30:15+00:00","og_image":[{"width":739,"height":415,"url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/images-2025-01-17t1731277144666201618292217.jpg","type":"image\/jpeg"}],"author":"Salahuddeen Muhammad","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"Salahuddeen Muhammad","Est. reading time":"8 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3308#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3308"},"author":{"name":"Salahuddeen Muhammad","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753"},"headline":"Shaka Zulu: Tushen al&#8217;ummar Zulu","datePublished":"2025-01-17T18:30:15+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3308"},"wordCount":1680,"commentCount":0,"publisher":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3308#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/52196437_803.png","articleSection":["Jiya Da Yau"],"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3308#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3308","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3308","name":"Shaka Zulu: Tushen al'ummar Zulu","isPartOf":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3308#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3308#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/52196437_803.png","datePublished":"2025-01-17T18:30:15+00:00","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3308#breadcrumb"},"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3308"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3308#primaryimage","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/52196437_803.png","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/52196437_803.png","width":575,"height":575},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3308#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/taskarnasaba.com\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Shaka Zulu: Tushen al&#8217;ummar Zulu"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/","name":"Taskar Nasaba","description":"","publisher":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization"},"potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-US"},{"@type":"Organization","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization","name":"Taskar Nasaba","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/","logo":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png","width":343,"height":345,"caption":"Taskar Nasaba"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/"}},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753","name":"Salahuddeen Muhammad","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/image\/","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg","caption":"Salahuddeen Muhammad"},"description":"\u018aanjarida, marubuci, mai manufar bun\u0199asa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.","sameAs":["https:\/\/taskarnasaba.com"],"url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?author=1"}]}},"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/52196437_803.png","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3308","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=3308"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3308\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/3306"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=3308"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=3308"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=3308"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}