{"id":3543,"date":"2025-02-11T02:16:32","date_gmt":"2025-02-11T02:16:32","guid":{"rendered":"https:\/\/taskarnasaba.com.ng\/?p=3543"},"modified":"2025-02-11T02:16:32","modified_gmt":"2025-02-11T02:16:32","slug":"dr-sivaramakrishna-iyer-padmavati-mace-ta-farko-da-ta-kasance-likitan-zuciya-a-indiya","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3543","title":{"rendered":"Dr. Sivaramakrishna Iyer Padmavati: Mace ta Farko da ta Kasance Likitan Zuciya a Indiya"},"content":{"rendered":"\n<p><strong>Ta na yin aiki na sa\u2019o\u2019i goma sha biyu (12hrs) a Rana, da kwanaki biyar a Mako, a Cibiyar Kula da Zuciya ta \u0198asa da ke Delhi, har sai da ta yi Ritaya ta na da shekaru 98 a Duniya, a shekarar 2015.<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Bugu da \u0199ari, har zuwa lokacin ritayarta, ta na ziyartar cibiyar sau \u0257aya ko sau biyu a Mako don ganin wasu tsoffin Majinyata, har zuwa Ranar da ta Mutu, a Ranar 29 ga watan Agusta, 2020, sakamakon Annobar COVID-19.<\/p>\n\n\n\n<p>Dr. Sivaramakrishna Iyer Padmavati, Likitar Zuciya ce a \u0198asar Indiya.<\/p>\n\n\n\n<p>Ta kasance Daraktan Cibiyar Kula da Zuciya ta \u0198asa, da ke Delhi, kuma ita ce shugabar Cibiyar Zuciya ta \u201cAll India Heart Foundation.\u201d Cibiyar ta na ha\u0257in guiwa tare da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) wajen horar da \u0257alibai kan ilimin Cututtukan Zuciya.<\/p>\n\n\n\n<p>Dr. Padmavati, ta sami Lambar Yabo na biyu Mafi Girma na Indiya, watau; \u201cPadma Bhushan\u201d a cikin shekara ta 1992.<\/p>\n\n\n\n<p>Ta kuma sami, Lambar Yabo na uku Mafi Girma na Indiya a 1967, \u201cPadma Vibhushan Riband,\u201d babbar daraja ta farar hula na biyu ta Indiya a 1992.<\/p>\n\n\n\n<p>Dr. Padmavati, ta kasance za\u0253a\u0253\u0253iya ta musamman a Kwalejin Kimiyyar Kiwon Lafiya ta \u0198asa, ita ce Mace ta farko da ta kasance \u0199wararriyar Likitar Zuciya a Indiya, kuma ta kafa Asibitin Zuciya na farko da \u0257akin bincike na Zuciya a \u0198asar.<\/p>\n\n\n\n<p>An haifi Padmavati a Burma, \u0198asar Myanmar ta yau, a Ranar 20 ga watan Yuni, 1917. Ta na da \u01b4an\u2019uwa wadda sun kasance Maza uku da Mata biyu.<\/p>\n\n\n\n<p>Ta sami shaidar Digiri na MBBS daga Rangoon Medical College, daga baya ta koma Landan a 1949, in da ta sami shahadar FRCP daga Royal College of Physicians, sannan FRCPE daga Royal College of Physicians na Edinburgh.<\/p>\n\n\n\n<p>A lokacinta a Birtaniya, ta yi aiki a Asibitin Zuciya, da Asibitin Kirji, da Asibitin \u0198asa, na Queen Square, da ke Landan.<\/p>\n\n\n\n<p>Daga baya, bayan kammala FRCP \u0257in ta, ta koma \u0198asar Sweden na tsawon Watanni uku, in da ta yi kwasa-kwasan ilimin Zuciya a asibitin Kudancin \u0198asar.<\/p>\n\n\n\n<p>A wane lokaci, ta nemi ha\u0257in guiwa a Asibitin Johns Hopkins, Baltimore, wani \u0253angare na Jami\u2019ar Johns Hopkins, kuma an za\u0253e ta, kuma ta ci gaba da yin karatu tare da sanannen Likitan Zuciya Helen Taussig.<\/p>\n\n\n\n<p>A cikin 1952, ta shiga Makarantar Kiwon Lafiya ta Harvard (Jami\u2019ar Harvard), in da ta yi karatu a \u0199ar\u0199ashin Paul Dudley White, majagaba a cikin ilimin Zuciya na zamani.<\/p>\n\n\n\n<p>A Indiya, ta fara aikinta a 1953, a matsayin Malama a Kwalejin Kiwon Lafiya ta Lady Hardinge, Delhi, in da ta bu\u0257e Asibitin Zuciya.<\/p>\n\n\n\n<p>A cikin 1954, ta kasance cikin \u01b4an Likitocin Mata na farko a Indiya, daga baya a matsayin mai jarabawa tare da Majalisar Likita ta Indiya, ta fara DM ta farko a cikin ilimin Zuciya a Indiya.<\/p>\n\n\n\n<p>Ta kafa Gidauniyar All India Heart Foundation (AIHF) a cikin 1962, tare da \u0199ungiyar Likitoci da Masana\u2019antu Ashok Jain na Bennett, Coleman &amp; Co. Ltd.<\/p>\n\n\n\n<p>Ta shiga Kwalejin Kiwon Lafiya ta Maulana Azad, Delhi a cikin 1967, kuma Gwamnatin Indiya ta ba ta Lambar Yabo ta \u201cPadma Bhushan\u201d a wannan shekarar.<\/p>\n\n\n\n<p>Ta kafa \u0257aya daga cikin sassan farko na ilimin Zuciya, a Asibitin G.B. Pant, wadda ke cikin harabar Kwaleji.<\/p>\n\n\n\n<p>Ta kasance Sakatare-Janar na Majalisar \u018ainkin Duniya ta \u201c5th World Congress of Cardiology, New Delhi\u201d a 1966.<\/p>\n\n\n\n<p>A cikin shekarun 1970s, ta kasance Shugabar Gudanarwa na Manyan Cibiyoyi uku a lokaci guda, a Kwalejin Kiwon Lafiya ta Maulana Azad, da Asibitin Lok Nayak, da asibitin G.B. Pant.<\/p>\n\n\n\n<p>Ta yi ritaya a matsayin Darakta (Principal) na Kwalejin Likitanci Maulana Azad, a cikin 1978.<\/p>\n\n\n\n<p>Bayan ta yi ritaya, ta kafa Cibiyar Kula da Zuciya ta \u0198asa (NHI) a \u0199ar\u0199ashin AIHF, a Kudancin Delhi, a cikin 1981, wadda ta fa\u0257a\u0257a cikin shekaru masu zuwa ta ha\u0257a da kula da Marasa Lafiya na manyan Makarantu, bincike da wayar da kan jama\u2019a, kuma in da ta ci gaba da aiki.<\/p>\n\n\n\n<p>Har ila yau, ta kasance Farfesar Farfesoshi (Emeritus Professor) na Likitanci da Ilimin Zuciya na Jami\u2019ar Delhi.<\/p>\n\n\n\n<p>Padmavati, ta zama \u0257aya daga cikin masu fa\u0257a a ji na Reshen kula da maganin da ke Magance Cututtuka da rashin daidaituwar Zuciya ta Turai, (European Society Of Cardiology) a lokacin ta na da shekaru 90, wadda ya ba ta damar kasancewa Jami\u2019a Mafi shekaru a reshen.<\/p>\n\n\n\n<p>A Ranar 29 ga watan Agusta, 2020, ta mutu sakamakon Annobar COVID-19, a Indiya a Cibiyar Zuciya ta \u0198asa da ke New Delhi.<\/p>\n\n\n\n<p>Ta na da shekaru 103 a lokacin mutuwarta, kuma ita ce Likita Mafi Tsufa a Indiya. An \u0199ona gawarta a wani wuri na musamman da ake \u0199one wadda cutar COVID-19 ta hallaka, a Punjabi Bagh a New Delhi.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>MADOGARA<\/strong><\/p>\n\n\n\n<ol class=\"wp-block-list\">\n<li>Dr. S. Padmavati: Chief Consultant In Cardiology Archived 14 July 2011 at the Wayback Machine NHI website.<\/li>\n\n\n\n<li>Expert Profile: Dr S Padmavati Archived 14 July 2011 at the Wayback Machine NDTV.<\/li>\n\n\n\n<li>WHO Collaborating Centres in India: Non-Communicable Diseases &amp; Mental Health Archived 12 June 2010 at the Wayback Machine WHO India.<\/li>\n\n\n\n<li>&#8220;Padma Awards&#8221;. Ministry of Communications and Information Technology. Archived from the original on 10 July 2011. Retrieved 13 April 2010.<\/li>\n\n\n\n<li>&#8220;List of Fellows \u2014 NAMS&#8221; (PDF). National Academy of Medical Sciences. 2016. Archived (PDF) from the original on 4 March 2016. Retrieved 19 March 2016.<\/li>\n\n\n\n<li>&#8220;Feature \u2014 Against the Tide: Been there, done that&#8221;. Express Healthcare (Indian Express). March 2007. Archived from the original on 22 November 2010. Retrieved 13 April 2010.<\/li>\n\n\n\n<li>&#8220;Sivaramakrishna Iyer Padmavati&#8221;. the-women-of-hopkins. Archived from the original on 1 September 2020. Retrieved 31 August 2020.<\/li>\n\n\n\n<li>&#8220;Matters Of Heart&#8221;. The Financial Express. 29 September 2002. Archived from the original on 1 September 2020. Retrieved 31 August 2020.<\/li>\n\n\n\n<li>&#8220;Eminent Cardiologist Dr S Padmavati Dies Of COVID-19 At 103&#8221;. NDTV.com. Archived from the original on 31 August 2020. Retrieved 31 August 2020.<\/li>\n\n\n\n<li>Prominent doctors honoured with the Wockhardt Medical Excellence Awards Archived 11 June 2015 at the Wayback Machine 17 February 2003.<\/li>\n\n\n\n<li>Development of Cardiac surgery in India Archived 14 July 2011 at the Wayback Machine<\/li>\n\n\n\n<li>&#8220;Awareness on cardiac health vital&#8221;. The Hindu. 24 December 2009. Archived from the original on 28 December 2009. Retrieved 4 August 2010.<\/li>\n\n\n\n<li>&#8220;SI Padmavati: India&#8217;s 1st female cardiologist dies of Covid at 103 | India News &#8211; Times of India&#8221;. The Times of India. TNN. 31 August 2020. Archived from the original on 31 August 2020. Retrieved 31 August 2020.<\/li>\n\n\n\n<li>Dr O. P. Yadava (31 August 2020). &#8220;The heart doctor with a big heart passes away | India News &#8211; Times of India&#8221;. The Times of India. Archived from the original on 1 September 2020. Retrieved 31 August 2020.<\/li>\n\n\n\n<li>&#8220;Fifth World Congress of Cardiology&#8221; (PDF). British Medical Journal. Archived (PDF) from the original on 26 April 2019. Retrieved 30 August 2020.<\/li>\n\n\n\n<li>National Award winners Archived 21 July 2011 at the Wayback Machine Maulana Azad Medical College website.<\/li>\n\n\n\n<li>&#8220;A Centenarian Fellow&#8221;. www.escardio.org. Archived from the original on 1 September 2020. Retrieved 31 August 2020.<\/li>\n<\/ol>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Ta na yin aiki na sa\u2019o\u2019i goma sha biyu (12hrs) a Rana, da kwanaki biyar a Mako, a Cibiyar Kula da Zuciya ta \u0198asa da ke Delhi, har sai da ta yi Ritaya ta na da shekaru 98 a Duniya, a shekarar 2015. Bugu da \u0199ari, har zuwa lokacin ritayarta, ta na ziyartar cibiyar sau [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":3542,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"inline_featured_image":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[93],"tags":[],"class_list":["post-3543","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-jiya-da-yau"],"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v27.0 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Dr. Sivaramakrishna Iyer Padmavati: Mace ta Farko da ta Kasance Likitan Zuciya a Indiya<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"noindex, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_US\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Dr. Sivaramakrishna Iyer Padmavati: Mace ta Farko da ta Kasance Likitan Zuciya a Indiya\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"Ta na yin aiki na sa\u2019o\u2019i goma sha biyu (12hrs) a Rana, da kwanaki biyar a Mako, a Cibiyar Kula da Zuciya ta \u0198asa da ke Delhi, har sai da ta yi Ritaya ta na da shekaru 98 a Duniya, a shekarar 2015. Bugu da \u0199ari, har zuwa lokacin ritayarta, ta na ziyartar cibiyar sau [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3543\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"Taskar Nasaba\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2025-02-11T02:16:32+00:00\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Salahuddeen Muhammad\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"Salahuddeen Muhammad\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Est. reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"5 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\/\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3543#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3543\"},\"author\":{\"name\":\"Salahuddeen Muhammad\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753\"},\"headline\":\"Dr. Sivaramakrishna Iyer Padmavati: Mace ta Farko da ta Kasance Likitan Zuciya a Indiya\",\"datePublished\":\"2025-02-11T02:16:32+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3543\"},\"wordCount\":1087,\"commentCount\":0,\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3543#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/02\/images-2025-02-11T031803.433.jpeg\",\"articleSection\":[\"Jiya Da Yau\"],\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3543#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3543\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3543\",\"name\":\"Dr. Sivaramakrishna Iyer Padmavati: Mace ta Farko da ta Kasance Likitan Zuciya a Indiya\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3543#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3543#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/02\/images-2025-02-11T031803.433.jpeg\",\"datePublished\":\"2025-02-11T02:16:32+00:00\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3543#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3543\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3543#primaryimage\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/02\/images-2025-02-11T031803.433.jpeg\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/02\/images-2025-02-11T031803.433.jpeg\",\"width\":640,\"height\":480},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3543#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Dr. Sivaramakrishna Iyer Padmavati: Mace ta Farko da ta Kasance Likitan Zuciya a Indiya\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"description\":\"\",\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\"},\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-US\"},{\"@type\":\"Organization\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\",\"logo\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png\",\"width\":343,\"height\":345,\"caption\":\"Taskar Nasaba\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/\"}},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753\",\"name\":\"Salahuddeen Muhammad\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg\",\"caption\":\"Salahuddeen Muhammad\"},\"description\":\"\u018aanjarida, marubuci, mai manufar bun\u0199asa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.\",\"sameAs\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\"],\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?author=1\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Dr. Sivaramakrishna Iyer Padmavati: Mace ta Farko da ta Kasance Likitan Zuciya a Indiya","robots":{"index":"noindex","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"og_locale":"en_US","og_type":"article","og_title":"Dr. Sivaramakrishna Iyer Padmavati: Mace ta Farko da ta Kasance Likitan Zuciya a Indiya","og_description":"Ta na yin aiki na sa\u2019o\u2019i goma sha biyu (12hrs) a Rana, da kwanaki biyar a Mako, a Cibiyar Kula da Zuciya ta \u0198asa da ke Delhi, har sai da ta yi Ritaya ta na da shekaru 98 a Duniya, a shekarar 2015. Bugu da \u0199ari, har zuwa lokacin ritayarta, ta na ziyartar cibiyar sau [&hellip;]","og_url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3543","og_site_name":"Taskar Nasaba","article_published_time":"2025-02-11T02:16:32+00:00","author":"Salahuddeen Muhammad","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"Salahuddeen Muhammad","Est. reading time":"5 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3543#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3543"},"author":{"name":"Salahuddeen Muhammad","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753"},"headline":"Dr. Sivaramakrishna Iyer Padmavati: Mace ta Farko da ta Kasance Likitan Zuciya a Indiya","datePublished":"2025-02-11T02:16:32+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3543"},"wordCount":1087,"commentCount":0,"publisher":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3543#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/02\/images-2025-02-11T031803.433.jpeg","articleSection":["Jiya Da Yau"],"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3543#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3543","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3543","name":"Dr. Sivaramakrishna Iyer Padmavati: Mace ta Farko da ta Kasance Likitan Zuciya a Indiya","isPartOf":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3543#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3543#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/02\/images-2025-02-11T031803.433.jpeg","datePublished":"2025-02-11T02:16:32+00:00","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3543#breadcrumb"},"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3543"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3543#primaryimage","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/02\/images-2025-02-11T031803.433.jpeg","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/02\/images-2025-02-11T031803.433.jpeg","width":640,"height":480},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3543#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/taskarnasaba.com\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Dr. Sivaramakrishna Iyer Padmavati: Mace ta Farko da ta Kasance Likitan Zuciya a Indiya"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/","name":"Taskar Nasaba","description":"","publisher":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization"},"potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-US"},{"@type":"Organization","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization","name":"Taskar Nasaba","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/","logo":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png","width":343,"height":345,"caption":"Taskar Nasaba"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/"}},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753","name":"Salahuddeen Muhammad","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/image\/","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg","caption":"Salahuddeen Muhammad"},"description":"\u018aanjarida, marubuci, mai manufar bun\u0199asa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.","sameAs":["https:\/\/taskarnasaba.com"],"url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?author=1"}]}},"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/02\/images-2025-02-11T031803.433.jpeg","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3543","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=3543"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3543\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/3542"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=3543"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=3543"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=3543"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}