{"id":3593,"date":"2025-02-20T17:15:15","date_gmt":"2025-02-20T17:15:15","guid":{"rendered":"https:\/\/taskarnasaba.com.ng\/?p=3593"},"modified":"2025-02-20T17:17:24","modified_gmt":"2025-02-20T17:17:24","slug":"tarihin-bikin-ranar-masoya-ta-duniya","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3593","title":{"rendered":"Bikin Ranar Masoya ta Duniya"},"content":{"rendered":"\n<p><strong>Ranar Masoya, wadda kuma ake kira &#8216;Saint Valentine&#8217;s Day&#8217; ko kuma idin Saint Valentine, ana bikin kowace shekara a Ranar 14 ga Watan Fabrairu. Al&#8217;adar, ta zama gagarumar Bikin al&#8217;adu, addini, da kasuwanci da kuma soyayya a yankuna da dama na Duniya.<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Akwai wata al&#8217;adar cewa, Paparoma Gelasius I, ya kafa ta a shekara ta 496AD don yin bikin Ranar 14 ga Fabrairu, don girmama Saint Valentine na Rome, wanda ya rasu a wannan Ranar, a AD 269.<\/p>\n\n\n\n<p>Ranar Masoya ba Ranar hutu ce ta jama&#8217;a a kowace \u0198asa ba, kodayake, Ranar Biki ce a hukumance a cikin ha\u0257in guiwar Anglican da Cocin Lutheran.<\/p>\n\n\n\n<p>Yawancin sassan Cocin Orthodox na Gabas kuma su na bikin Ranar Valentine a Ranar shida ga watan Yuli, don girmama shugaban Roman Saint Valentine, da kuma Ranar 30 ga Yuli don girmama Hieromartyr Valentine, Bishop na Interamna (Terni ta zamani).<\/p>\n\n\n\n<p>Asalin Bikin Ranar Masoya na daga bukukuwan Romawa a lokacin da suke kan Addinin Maguzanci fiye da \u0198arni 17 da suka gabta. Haka nan, bikin ya samo asali ne daga a\u0199idar Romawa, cewa; wai wata Macen Kyarkeci ta ta\u0253a shayar da Romulus, wanda ya assasa Garin Rome, Nono, kuma hakan ya ba shi \u0199arfin gaske da kuma Hikima ta musamman.<\/p>\n\n\n\n<p>Romawa sun ri\u0199a yin gagarumin bikin murnar zagayowar wannan Rana a tsakiyar Watan Fabrairun kowace shekara.<\/p>\n\n\n\n<p>A lokacin bikin, ana yanka Kare da Akuya, a inda \u0199artin Matasa (majiya \u0199arfi) za su shafe jikinsu da jinin, sannan, su wanke jinin da Madara. Daga nan, sai su jagoranci faretin zagaya Gari a kan tituna, su na ri\u0199e da fatun da za su bugi duk wanda ya fa\u0257o masu. Matan Romawa su na afkawa wa\u0257annan Matasa don a buge su, kuma hakan ya na faranta masu rai saboda imanin da suka yi cewa, ya na maganin matsalar rashin haihuwa.<\/p>\n\n\n\n<p>An ce, Valentine sunan wani malamin Kiristoci ne wanda ya mutu a dalilin cutarwar Claudius, shugaban Gothic a shekarar 296 CE.<\/p>\n\n\n\n<div class=\"wp-block-media-text is-stacked-on-mobile\"><figure class=\"wp-block-media-text__media\"><img fetchpriority=\"high\" decoding=\"async\" width=\"204\" height=\"300\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/02\/images-2025-02-20t1812058014369053134166448-204x300.jpg\" alt=\"\" class=\"wp-image-3592 size-full\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/02\/images-2025-02-20t1812058014369053134166448-204x300.jpg 204w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/02\/images-2025-02-20t1812058014369053134166448.jpg 456w\" sizes=\"(max-width: 204px) 100vw, 204px\" \/><\/figure><div class=\"wp-block-media-text__content\">\n<p><em>Saint Valentine. Hoto: Brittanca<\/em><\/p>\n<\/div><\/div>\n\n\n\n<p>A shekarar 350 CE, an gina Coci a wurin da ya mutu, domin a ri\u0199a tunawa da shi. Da Romawa suka shiga cikin Kiristanci, sun ci gaba da bikin Soyayya, illa iyaka, sun canja shi daga bikin Soyayyar Ruhi irin na Muguzanci zuwa bikin Shahidan Soyayya don tunawa da Valentine, kasancewar a cewar su, ya ya\u0257a \u0199auna da Soyayya da da zaman lafiya, abin da kuma ya kai shi ga rasa ransa.<\/p>\n\n\n\n<p>A wani \u0199aulin kuma, an ce Bikin Ranar Valentine ya samo asali ne daga lokacin da Romawa suka shiga cikin Kiristanci. Sarkin Rome, Claudius II ya sanya dokar hana Sojoji yin Aure a \u0199arni na uku bisa hujjar cewa, aure zai shagaltar da su, kuma ya kau da tunaninsu daga ya\u0199i.<\/p>\n\n\n\n<p>Valentine ya bijire wa wannan doka, kuma ya ci gaba da \u0257aurawa Sojoji aure a \u0253oye. Da Sarkin ya gano, sai ya jefa shi cikin Kurkuku, kuma ya yanke masa hukuncin kisa. Ya na cikin Kurkuku ne ya kamu da ciwon son \u01b4ar-sarkin, amma a \u0253oye, duk da cewa haramun ne ya so wata Mace ko kuma ya yi Aure, a matsayinsa na babban malamin Kirista, kasancewar dokokin Kiristanci sun hana.<\/p>\n\n\n\n<p>An ce, daga baya Sarkin Romawa ya nemi Valentine ya bar Kiristanci, ya bauta wa Gunkin Romawa, shi kuma zai mai da shi \u0257aya daga cikin makusantansa kuma ya aurar masa da \u01b4arsa.<\/p>\n\n\n\n<p>Kasancewar Valentine ya \u0199i yarda da haka, an kashe shi a Ranar 14 ga Fabrairun 270 CE, a Daren 15 ga watan Fabrairu da aka saba yin bikin &#8216;Lupercalis.&#8217;<\/p>\n\n\n\n<p>Daga nan aka canja sunan bikin ya koma Ranar tunawa da Valentine, ko dai saboda dagewar da ya yi a kan Kiristanci, ko kuma saboda goyon bayan da ya nuna wa sojojin da suka fa\u0257a cikin soyayya, har hakan ya kai shi ga rasa ransa.<\/p>\n\n\n\n<p>Daga nan, sai Pope, Shugaban Kiristocin da ya gaji Saint Peter, ya mai da Ranar 14 ga Fabrairun 270 CE a matsayin Ranar Bikin Soyayya, kuma ya shar\u2019anta wa dukkan Kiristoci murnar zagayowar wannan Rana a kowace shekara.<\/p>\n\n\n\n<p>Da ma Allah (Ma\u0257aukaki) Ya ba da labarin yadda Kiristoci ke \u0257aukar malamansu a matsayin abin bauta, da yadda su ke bin abubuwan da suka halarta ko suka haramta masu sau da kafa, ba tare da neman dalili a cikin littafinsu ba.<\/p>\n\n\n\n<p>Abubuwan Lura Dangane da Ranar Valentine<\/p>\n\n\n\n<p>Asalin Bikin Ranar Valentine daga Romawa ne wa\u0257anda ke bin a\u0199idar Maguzanci. A wajensu, biki ne da ke nuna soyayyar da su ke wa gunkinsu mai suna &#8216;Ubangijin Soyayya.&#8217;<\/p>\n\n\n\n<p>Tarihin wannan biki a wajen Romawa ya \u0199unshi Tatsuniya da Surkullen da duk wani mai hankali zai \u0199aryata, ballantana kuma Musulmin da ya san abin da ya ke yi. Hatta ma a wajen Kiristoci, akwai sa\u0253ani mai yawan gaske a tsakanin malamansu dangane da gaskiyar ala\u0199ar Valentine da wannan biki.<\/p>\n\n\n\n<p>Biki ne da ya \u0199unshi kamanceceniya da mushirikan Romawa da kuma tarayya da kiristoci. Yin kamanceceniya da Kafirai ko tarayya da su a cikin addininsu ko a\u0199idarsu ko ibadarsu ko wata al\u2019ada da ta ke\u0253anta da su, haramun ne kamar yadda manyan malaman Musulunci suka bayyana.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Ranar Masoya, wadda kuma ake kira &#8216;Saint Valentine&#8217;s Day&#8217; ko kuma idin Saint Valentine, ana bikin kowace shekara a Ranar 14 ga Watan Fabrairu. Al&#8217;adar, ta zama gagarumar Bikin al&#8217;adu, addini, da kasuwanci da kuma soyayya a yankuna da dama na Duniya. Akwai wata al&#8217;adar cewa, Paparoma Gelasius I, ya kafa ta a shekara ta [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":3591,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"inline_featured_image":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[85],"tags":[],"class_list":["post-3593","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-alada"],"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v27.0 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Bikin Ranar Masoya ta Duniya<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"noindex, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_US\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Bikin Ranar Masoya ta Duniya\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"Ranar Masoya, wadda kuma ake kira &#8216;Saint Valentine&#8217;s Day&#8217; ko kuma idin Saint Valentine, ana bikin kowace shekara a Ranar 14 ga Watan Fabrairu. Al&#8217;adar, ta zama gagarumar Bikin al&#8217;adu, addini, da kasuwanci da kuma soyayya a yankuna da dama na Duniya. Akwai wata al&#8217;adar cewa, Paparoma Gelasius I, ya kafa ta a shekara ta [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3593\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"Taskar Nasaba\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2025-02-20T17:15:15+00:00\" \/>\n<meta property=\"article:modified_time\" content=\"2025-02-20T17:17:24+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/02\/images-2025-02-20T181231.549.jpeg\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"672\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"457\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/jpeg\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Salahuddeen Muhammad\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"Salahuddeen Muhammad\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Est. reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"4 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\/\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3593#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3593\"},\"author\":{\"name\":\"Salahuddeen Muhammad\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753\"},\"headline\":\"Bikin Ranar Masoya ta Duniya\",\"datePublished\":\"2025-02-20T17:15:15+00:00\",\"dateModified\":\"2025-02-20T17:17:24+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3593\"},\"wordCount\":856,\"commentCount\":0,\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3593#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/02\/images-2025-02-20T181231.549.jpeg\",\"articleSection\":[\"Al'ada\"],\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3593#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3593\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3593\",\"name\":\"Bikin Ranar Masoya ta Duniya\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3593#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3593#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/02\/images-2025-02-20T181231.549.jpeg\",\"datePublished\":\"2025-02-20T17:15:15+00:00\",\"dateModified\":\"2025-02-20T17:17:24+00:00\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3593#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3593\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3593#primaryimage\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/02\/images-2025-02-20T181231.549.jpeg\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/02\/images-2025-02-20T181231.549.jpeg\",\"width\":672,\"height\":457},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3593#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Bikin Ranar Masoya ta Duniya\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"description\":\"\",\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\"},\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-US\"},{\"@type\":\"Organization\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\",\"logo\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png\",\"width\":343,\"height\":345,\"caption\":\"Taskar Nasaba\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/\"}},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753\",\"name\":\"Salahuddeen Muhammad\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg\",\"caption\":\"Salahuddeen Muhammad\"},\"description\":\"\u018aanjarida, marubuci, mai manufar bun\u0199asa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.\",\"sameAs\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\"],\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?author=1\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Bikin Ranar Masoya ta Duniya","robots":{"index":"noindex","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"og_locale":"en_US","og_type":"article","og_title":"Bikin Ranar Masoya ta Duniya","og_description":"Ranar Masoya, wadda kuma ake kira &#8216;Saint Valentine&#8217;s Day&#8217; ko kuma idin Saint Valentine, ana bikin kowace shekara a Ranar 14 ga Watan Fabrairu. Al&#8217;adar, ta zama gagarumar Bikin al&#8217;adu, addini, da kasuwanci da kuma soyayya a yankuna da dama na Duniya. Akwai wata al&#8217;adar cewa, Paparoma Gelasius I, ya kafa ta a shekara ta [&hellip;]","og_url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3593","og_site_name":"Taskar Nasaba","article_published_time":"2025-02-20T17:15:15+00:00","article_modified_time":"2025-02-20T17:17:24+00:00","og_image":[{"width":672,"height":457,"url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/02\/images-2025-02-20T181231.549.jpeg","type":"image\/jpeg"}],"author":"Salahuddeen Muhammad","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"Salahuddeen Muhammad","Est. reading time":"4 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3593#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3593"},"author":{"name":"Salahuddeen Muhammad","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753"},"headline":"Bikin Ranar Masoya ta Duniya","datePublished":"2025-02-20T17:15:15+00:00","dateModified":"2025-02-20T17:17:24+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3593"},"wordCount":856,"commentCount":0,"publisher":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3593#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/02\/images-2025-02-20T181231.549.jpeg","articleSection":["Al'ada"],"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3593#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3593","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3593","name":"Bikin Ranar Masoya ta Duniya","isPartOf":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3593#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3593#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/02\/images-2025-02-20T181231.549.jpeg","datePublished":"2025-02-20T17:15:15+00:00","dateModified":"2025-02-20T17:17:24+00:00","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3593#breadcrumb"},"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3593"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3593#primaryimage","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/02\/images-2025-02-20T181231.549.jpeg","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/02\/images-2025-02-20T181231.549.jpeg","width":672,"height":457},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3593#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/taskarnasaba.com\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Bikin Ranar Masoya ta Duniya"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/","name":"Taskar Nasaba","description":"","publisher":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization"},"potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-US"},{"@type":"Organization","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization","name":"Taskar Nasaba","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/","logo":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png","width":343,"height":345,"caption":"Taskar Nasaba"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/"}},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753","name":"Salahuddeen Muhammad","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/image\/","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg","caption":"Salahuddeen Muhammad"},"description":"\u018aanjarida, marubuci, mai manufar bun\u0199asa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.","sameAs":["https:\/\/taskarnasaba.com"],"url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?author=1"}]}},"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/02\/images-2025-02-20T181231.549.jpeg","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3593","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=3593"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3593\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3594,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3593\/revisions\/3594"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/3591"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=3593"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=3593"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=3593"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}