{"id":3658,"date":"2025-03-02T22:58:22","date_gmt":"2025-03-02T22:58:22","guid":{"rendered":"https:\/\/taskarnasaba.com.ng\/?p=3658"},"modified":"2025-03-02T22:58:22","modified_gmt":"2025-03-02T22:58:22","slug":"wane-ne-aristotle-shahararren-masanin-falsafa-na-duniya","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3658","title":{"rendered":"Wane ne Aristotle Shahararren Masanin Falsafa na Duniya?"},"content":{"rendered":"\n<p><strong>Aristotle ya kawo gagarumin sauyi a rayuwar al&#8217;ummar Duniya, kuma ana ganin tasirinsa a fannonin Siyasa da Kimiyya da fagen rubuce-rubuce.<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Shin a iya cewa Aristotle ne mutumin da ya fi tasiri da aka ta\u0253a gani a doron-\u0199asa? Wani fitaccen malamin falsafa \u0257an Birtaniya, John Sellars na ganin haka.<\/p>\n\n\n\n<p>Ya ce, ana iya ganin tasirin masanin falsafar \u0257an asalin Girka a fagage da dama da irin yadda ya taimaka da tunaninsa a fannoni daban-daban na rayuwa.<\/p>\n\n\n\n<p>Kama daga fagen Siyasa da Kimiyya, rubuce-rubuce zuwa tunani da dabaru, ana iya ganin tasirin Aristotle a ko&#8217;ina.<\/p>\n\n\n\n<p>Ya yi nazarin ilimin halittun cikin ruwa, wani abu da ya haifar da ilimin &#8216;Biology.&#8217;<\/p>\n\n\n\n<p>Ya kuma yi bayanin fannonin tsarin mulki daban-daban, wani abu da ya haifar da ilimin kimiyyar siyasa.<\/p>\n\n\n\n<p>Haka kuma sharhinsa kan iya bayar da labari a cikin Wa\u0199o\u0199i ya taimaka wajen samar da tsarin Sinima a yau.<\/p>\n\n\n\n<p>Sannan a fannin tunani, dabarunsa a fannin bayar da hujja ya taimaka a kowane fanni kama daga ilimin falsafa zuwa shekarun fasahar zamani.<\/p>\n\n\n\n<p>Farfesa Sellars na Jamai&#8217;ar Royal Holloway, da ke Landan, ya sani cewa maganarsa na da \u0199arfi. Amma ya dage cewa; tasirin Aristotle ya zarce a yi maganarsa. &#8221;Ya gyara yadda muke tunani&#8221;, in ji shi.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Babban I\u0199irari<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>A wata Mu\u0199ala da ya wallafa a Mujallar Antigone, Sellars ya yi wani i\u0199irari da ya ja hankali game da masanin falsafar, in da ya ce, &#8220;Aristotle ba kawai babban masanin falsafa ne da ba a ta\u0253a ganin irinsa ba &#8211; Shi ne ma mutum mafi muhimmanci da aka ta\u0253a yi a Duniya.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>Wannan babban i\u0199irari ne, kuma wanda ya fa\u0257a\u0257a a littafinsa mai suna &#8216;Aristotle: Understanding the World&#8217;s Greatest Philosopher.&#8217;<\/p>\n\n\n\n<div class=\"wp-block-media-text is-stacked-on-mobile\"><figure class=\"wp-block-media-text__media\"><img fetchpriority=\"high\" decoding=\"async\" width=\"246\" height=\"300\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/eaad6ee0-d9d9-11ef-bc01-8f2c83dad2173636425784292276410-246x300.jpg\" class=\"wp-image-3653 size-full\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/eaad6ee0-d9d9-11ef-bc01-8f2c83dad2173636425784292276410-246x300.jpg 246w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/eaad6ee0-d9d9-11ef-bc01-8f2c83dad2173636425784292276410-768x937.jpg 768w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/eaad6ee0-d9d9-11ef-bc01-8f2c83dad2173636425784292276410-600x732.jpg 600w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/eaad6ee0-d9d9-11ef-bc01-8f2c83dad2173636425784292276410.jpg 800w\" sizes=\"(max-width: 246px) 100vw, 246px\" \/><\/figure><div class=\"wp-block-media-text__content\">\n<p>&#8220;Plato ne abokina, amma gaskiya ce babbar \u0199awata,&#8221; a cewar Aristotle. Hoto: Getty Images<\/p>\n<\/div><\/div>\n\n\n\n<p>&#8220;A lokacin da na fara nazarin falsafa, na fahimci cewa, Aristotle ya na da muhimmanci, amma kamar ya na da tsoro,&#8221; a cewar Sellars.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;Duk lokacin da na yi \u0199o\u0199ari na karanta rubuce-rubucensa, sai nan da nan abubuwa su \u0253ace min.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>Sai dai bayan lokaci mai tsawo ya fahimci cewa, karantar rubuce-rubucen Aristotle na bu\u0199atar ha\u0199uri da juriya. &#8221;Kana bu\u0199atar sanin yadda za ka karanta rubutunsa,&#8221; kamar yadda ya bayyana.<\/p>\n\n\n\n<p>Ya rubuta littafin nasa da nufin taimaka wa masu karatu su san hikimomin Aristotle tare da nuna irin tasirin fitaccen malamin falsafar.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Rayuwar Neman Ilimi<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Aristotle da Socrates da Plato ne suka gina babban fagen ilimin Falsafa a Duniya.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img decoding=\"async\" width=\"738\" height=\"416\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/images-2025-03-02t2354342332156261304643864.jpg\" alt=\"\" class=\"wp-image-3654\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/images-2025-03-02t2354342332156261304643864.jpg 738w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/images-2025-03-02t2354342332156261304643864-300x169.jpg 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/images-2025-03-02t2354342332156261304643864-600x338.jpg 600w\" sizes=\"(max-width: 738px) 100vw, 738px\" \/><\/figure>\n\n\n\n<p>An haifi Aristotle a Arewacin Girka, ya na da shekaru 18 ya koma Athens inda ya yi karatu a Makarantar Plato, ya kuma shafe shekaru 20 a matsayin \u018aalibi da kuma Malami a Makarantar.<\/p>\n\n\n\n<p>Duk da girmama Plato, Aristotle ya gina nasa ra&#8217;ayoyin. Bayan mutuwar malamin nasa, ya bar Athens zuwa tsibirin Lesbos don karantar yanayi. Ya yi fice a fannin, inda daga baya aka za\u0253e shi a matsayin malamin \u0257an Sarkin Macedon, wanda ke matsayin Yarima mai jiran-gado, wato Alexander the Great.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img decoding=\"async\" width=\"800\" height=\"727\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/0cd0a400-d9db-11ef-902e-cf9b84dc13574518182114479885735.jpg\" alt=\"\" class=\"wp-image-3655\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/0cd0a400-d9db-11ef-902e-cf9b84dc13574518182114479885735.jpg 800w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/0cd0a400-d9db-11ef-902e-cf9b84dc13574518182114479885735-300x273.jpg 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/0cd0a400-d9db-11ef-902e-cf9b84dc13574518182114479885735-768x698.jpg 768w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/0cd0a400-d9db-11ef-902e-cf9b84dc13574518182114479885735-600x545.jpg 600w\" sizes=\"(max-width: 800px) 100vw, 800px\" \/><\/figure>\n\n\n\n<p>A lokacin da Alexander ya fara mulkinsa, Aristotle ya koma Athens inda ya kafa tasa makarantar, mai suna &#8216;The Lyceum.&#8217;<\/p>\n\n\n\n<p>Ya kwashe shekarun \u0199arshe na rayuwarsa ya na koyarwa, da rubuce-rubuce da bincike kafin rasuwarsa a lokacin ya na da shekaru 62.<\/p>\n\n\n\n<p>Duk da cewa ka\u0257an ne daga cikin ayyukansa suka samu wanzuwa, har yanzu su na tasiri, musamman a fagen tunani.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>\u0198wararren Masanin Kimiyya<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Ba a ilimin falsafa kawai Aristotle ya yi fice ba, ya kasance \u0257aya daga cikin masana ilimin kimiyya na farko-farko.<\/p>\n\n\n\n<p>Da jimawa kafin bayyanar na&#8217;urorin Microscopes da ilimin Halittu, Aristotle ya nazarci halittun Duniya, inda ya karkasa Dabbobi da Tsirrai a wani mataki da ya bayar da damar samar da fagen ilimin Biology.<\/p>\n\n\n\n<p>Wasu binciken nasa, daga baya ilimi ya tabbatar da kuskure a cikinsu. Amma Sellars ya ce babbar asarar Aristotle ita ce dabarar da ya bi, ya na mai cewa, bincike da hujja suke taimaka wa fahimta.<\/p>\n\n\n\n<p>Kuma wa\u0257annan dabaru har yanzu su ne zuciyar Kimiyya.<\/p>\n\n\n\n<div class=\"wp-block-media-text is-stacked-on-mobile\"><figure class=\"wp-block-media-text__media\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"294\" height=\"300\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/8a6cb520-d9db-11ef-bc01-8f2c83dad2176639189079866957626-294x300.jpg\" class=\"wp-image-3656 size-full\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/8a6cb520-d9db-11ef-bc01-8f2c83dad2176639189079866957626-294x300.jpg 294w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/8a6cb520-d9db-11ef-bc01-8f2c83dad2176639189079866957626-768x782.jpg 768w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/8a6cb520-d9db-11ef-bc01-8f2c83dad2176639189079866957626-600x611.jpg 600w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/8a6cb520-d9db-11ef-bc01-8f2c83dad2176639189079866957626.jpg 800w\" sizes=\"(max-width: 294px) 100vw, 294px\" \/><\/figure><div class=\"wp-block-media-text__content\">\n<p>Makarantar Lyceum ta Aristotle, ta bayar da Leccoci masu yawa ga jama&#8217;a kuma a kyauta, sa\u0253anin Makarantar Plato. Hoto: Getty Images<\/p>\n<\/div><\/div>\n\n\n\n<p><strong>Gudunmowa a Siyasa da Rubuce-Rubuce<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Aristotle ya sanya wasu dabarun ilimi da tunani cikin Siyasa<\/p>\n\n\n\n<p>Ya tattara tare da kwatanta Kundayen Tsarin Mulki na Birane da \u0198asashe daban-daban domin fahimtar dalilin da ya sa wasu \u0198asashen suka ci gaba, wasu kuma suka zama koma-baya.<\/p>\n\n\n\n<p>Wannan hanya da aka tsara bisa doron hujja maimakon ra&#8217;ayi, ita ce ta bayar da damar samar da Ilimin Kimiyyar Zamantakewa, wato &#8216;Social Sciences.&#8217;<\/p>\n\n\n\n<p>Haka ma tasirinsa a fannin rubuce-rubuce ba zai misaltu ba. Baya ga Wa\u0199o\u0199i ya kuma yi nazarin wasannin Girka, tare da karkasa labarai zuwa sassa daban-daban, farko da tsakiya da kuma \u0199arshe, wata dabara da masu rubuta Littattafai da masu shirya Fina-finai na yanzu ke amfani da ita.<\/p>\n\n\n\n<div class=\"wp-block-media-text is-stacked-on-mobile\"><figure class=\"wp-block-media-text__media\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"735\" height=\"1025\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/d706d870-d9db-11ef-902e-cf9b84dc13574637168971886979769-735x1025.jpg\" class=\"wp-image-3657 size-full\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/d706d870-d9db-11ef-902e-cf9b84dc13574637168971886979769-735x1025.jpg 735w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/d706d870-d9db-11ef-902e-cf9b84dc13574637168971886979769-215x300.jpg 215w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/d706d870-d9db-11ef-902e-cf9b84dc13574637168971886979769-768x1071.jpg 768w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/d706d870-d9db-11ef-902e-cf9b84dc13574637168971886979769-600x837.jpg 600w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/d706d870-d9db-11ef-902e-cf9b84dc13574637168971886979769.jpg 800w\" sizes=\"(max-width: 735px) 100vw, 735px\" \/><\/figure><div class=\"wp-block-media-text__content\">\n<p>Ana kallon Aristotle a matsayin \u0257aya daga cikin mutanen da suka fi tasiri a tarihin Falsafar Musulunci. Hoto: Getty Images<\/p>\n<\/div><\/div>\n\n\n\n<p><strong>Masanin Dabaru da Falsafa<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Ayyukan Aristotle a fagen dabaru na \u0257aya daga cikin gagarumar gudunmowar da ya bayar.<\/p>\n\n\n\n<p>Ya \u0253ullo da \u0199a&#8217;idar cewa, kowace magana ka iya zama gaskiya ko \u0199arya &#8211; abin da a yanzu ake kira &#8216;Law of the Excluded Middle.&#8217;<\/p>\n\n\n\n<p>Aristotle ya kuma tunkari manyan tambayoyin rayuwa na: Ta ya ya muke rayuwa?<\/p>\n\n\n\n<p>A cikin littafin \u018aa&#8217;a na Nicomachean, ya bayar da hujjar cewa; Mutane na fama a lokacin da suka daidaita hujja da ala\u0199ar zamantakewa da sha&#8217;awar \u0199wa\u0199\u0199wafi game da hankali.<\/p>\n\n\n\n<p>Rayuwa mai kyau, ita ce inda muke samun iko da kanmu, mu shiga cikin al&#8217;ummominmu, don neman ilimi.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tasirin da ba mu Ta\u0253a Gani ba<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Sellars, ya yi imanin cewa, fasahohin Aristotle sun zurfafa cikin fasahohin zamani duk da cewa ba za mu iya tantance su duka ba.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;Dabarunsa sun shiga ko&#8217;ina, amma muna \u0257aukarsu yanzu tamkar namu.&#8221; a cewarsa.<\/p>\n\n\n\n<p>Don haka ma iya cewa, Aristotle ne mutumin da ya fi muhimmanci a Tarihi?<\/p>\n\n\n\n<p>Sellars ya ce a \u0199arshe, ya rage ga mai karatu ya yanke shawara &#8211; shin Aristotle babban mai tunani ne kawai, ko kuwa, kamar yadda Sellars ya yi jayayya, \u0257an&#8217;Adam mafi mahimmancin tarihi?<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Aristotle ya kawo gagarumin sauyi a rayuwar al&#8217;ummar Duniya, kuma ana ganin tasirinsa a fannonin Siyasa da Kimiyya da fagen rubuce-rubuce. Shin a iya cewa Aristotle ne mutumin da ya fi tasiri da aka ta\u0253a gani a doron-\u0199asa? Wani fitaccen malamin falsafa \u0257an Birtaniya, John Sellars na ganin haka. Ya ce, ana iya ganin tasirin [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":3652,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"inline_featured_image":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[93],"tags":[],"class_list":["post-3658","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-jiya-da-yau"],"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v27.0 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Wane ne Aristotle Shahararren Masanin Falsafa na Duniya?<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"noindex, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_US\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Wane ne Aristotle Shahararren Masanin Falsafa na Duniya?\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"Aristotle ya kawo gagarumin sauyi a rayuwar al&#8217;ummar Duniya, kuma ana ganin tasirinsa a fannonin Siyasa da Kimiyya da fagen rubuce-rubuce. Shin a iya cewa Aristotle ne mutumin da ya fi tasiri da aka ta\u0253a gani a doron-\u0199asa? Wani fitaccen malamin falsafa \u0257an Birtaniya, John Sellars na ganin haka. Ya ce, ana iya ganin tasirin [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3658\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"Taskar Nasaba\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2025-03-02T22:58:22+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/eaad6ee0-d9d9-11ef-bc01-8f2c83dad2173636425784292276410.jpg\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"800\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"976\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/jpeg\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Taskar Nasaba\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"Taskar Nasaba\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Est. reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"5 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\/\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3658#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3658\"},\"author\":{\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/50c6fe8b25398ccbaf7fd94dee1c8456\"},\"headline\":\"Wane ne Aristotle Shahararren Masanin Falsafa na Duniya?\",\"datePublished\":\"2025-03-02T22:58:22+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3658\"},\"wordCount\":1039,\"commentCount\":0,\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3658#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/1126c9a0-d9d9-11ef-bc01-8f2c83dad217.jpg.webp\",\"articleSection\":[\"Jiya Da Yau\"],\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3658#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3658\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3658\",\"name\":\"Wane ne Aristotle Shahararren Masanin Falsafa na Duniya?\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3658#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3658#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/1126c9a0-d9d9-11ef-bc01-8f2c83dad217.jpg.webp\",\"datePublished\":\"2025-03-02T22:58:22+00:00\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3658#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3658\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3658#primaryimage\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/1126c9a0-d9d9-11ef-bc01-8f2c83dad217.jpg.webp\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/1126c9a0-d9d9-11ef-bc01-8f2c83dad217.jpg.webp\",\"width\":800,\"height\":460},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3658#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Wane ne Aristotle Shahararren Masanin Falsafa na Duniya?\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"description\":\"\",\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\"},\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-US\"},{\"@type\":\"Organization\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\",\"logo\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png\",\"width\":343,\"height\":345,\"caption\":\"Taskar Nasaba\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/\"}},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/50c6fe8b25398ccbaf7fd94dee1c8456\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/cropped-Taskar-Nasaba-PNG-100x100.png\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/cropped-Taskar-Nasaba-PNG-100x100.png\",\"caption\":\"Taskar Nasaba\"},\"sameAs\":[\"http:\/\/www.taskarnasaba.com.ng\"],\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?author=2\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Wane ne Aristotle Shahararren Masanin Falsafa na Duniya?","robots":{"index":"noindex","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"og_locale":"en_US","og_type":"article","og_title":"Wane ne Aristotle Shahararren Masanin Falsafa na Duniya?","og_description":"Aristotle ya kawo gagarumin sauyi a rayuwar al&#8217;ummar Duniya, kuma ana ganin tasirinsa a fannonin Siyasa da Kimiyya da fagen rubuce-rubuce. Shin a iya cewa Aristotle ne mutumin da ya fi tasiri da aka ta\u0253a gani a doron-\u0199asa? Wani fitaccen malamin falsafa \u0257an Birtaniya, John Sellars na ganin haka. Ya ce, ana iya ganin tasirin [&hellip;]","og_url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3658","og_site_name":"Taskar Nasaba","article_published_time":"2025-03-02T22:58:22+00:00","og_image":[{"width":800,"height":976,"url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/eaad6ee0-d9d9-11ef-bc01-8f2c83dad2173636425784292276410.jpg","type":"image\/jpeg"}],"author":"Taskar Nasaba","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"Taskar Nasaba","Est. reading time":"5 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3658#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3658"},"author":{"name":"Taskar Nasaba","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/50c6fe8b25398ccbaf7fd94dee1c8456"},"headline":"Wane ne Aristotle Shahararren Masanin Falsafa na Duniya?","datePublished":"2025-03-02T22:58:22+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3658"},"wordCount":1039,"commentCount":0,"publisher":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3658#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/1126c9a0-d9d9-11ef-bc01-8f2c83dad217.jpg.webp","articleSection":["Jiya Da Yau"],"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3658#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3658","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3658","name":"Wane ne Aristotle Shahararren Masanin Falsafa na Duniya?","isPartOf":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3658#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3658#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/1126c9a0-d9d9-11ef-bc01-8f2c83dad217.jpg.webp","datePublished":"2025-03-02T22:58:22+00:00","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3658#breadcrumb"},"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3658"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3658#primaryimage","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/1126c9a0-d9d9-11ef-bc01-8f2c83dad217.jpg.webp","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/1126c9a0-d9d9-11ef-bc01-8f2c83dad217.jpg.webp","width":800,"height":460},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3658#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/taskarnasaba.com\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Wane ne Aristotle Shahararren Masanin Falsafa na Duniya?"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/","name":"Taskar Nasaba","description":"","publisher":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization"},"potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-US"},{"@type":"Organization","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization","name":"Taskar Nasaba","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/","logo":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png","width":343,"height":345,"caption":"Taskar Nasaba"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/"}},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/50c6fe8b25398ccbaf7fd94dee1c8456","name":"Taskar Nasaba","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/image\/","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/cropped-Taskar-Nasaba-PNG-100x100.png","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/cropped-Taskar-Nasaba-PNG-100x100.png","caption":"Taskar Nasaba"},"sameAs":["http:\/\/www.taskarnasaba.com.ng"],"url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?author=2"}]}},"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/1126c9a0-d9d9-11ef-bc01-8f2c83dad217.jpg.webp","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3658","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=3658"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3658\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/3652"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=3658"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=3658"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=3658"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}