{"id":3893,"date":"2025-08-17T21:43:38","date_gmt":"2025-08-17T21:43:38","guid":{"rendered":"https:\/\/taskarnasaba.com.ng\/?p=3893"},"modified":"2025-08-17T21:47:41","modified_gmt":"2025-08-17T21:47:41","slug":"me-ya-sa-misirawa-suka-ri%c6%99a-gina-manya-manyan-dala","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3893","title":{"rendered":"Me ya sa Misirawa suka ri\u0199a gina manya-manyan Dala?"},"content":{"rendered":"\n<p>Ginin Dalar Masar ta zamanin da ba abu ba ne da kawai aka yi shi haka ba, ba tare da wasu dalilai ba, ko rashin ma&#8217;ana ko kuma an yi wannan katafaren gini na Dutse ne a matsayin Kabari ko hubbaren sarakuna domin girmama sarakunan na zamanin da ba.<\/p>\n\n\n\n<p>Aiki ne da ya \u0199unshi dalilai da dama kama daga jin-\u0199ai da addini da kuma falsafa wa\u0257anda ta hanyarsu al&#8217;ummar ta Masar ke bayyana irin a\u0199idarsu ta addini da kuma yadda suka yi amanna da rayuwa bayan mutuwa.<\/p>\n\n\n\n<p>Gina wannan Dala ba wai kawai nuni ne na \u0199warewa a fagen gini ba, abu ne da ya \u0199unshi dalilai da dama, kamar yadda bayani ya gabata &#8211; rayuwar Duniya da addini da rayuwa bayan mutuwa.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img fetchpriority=\"high\" decoding=\"async\" width=\"720\" height=\"405\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/watermark_17554652888964830374661246491114.png\" alt=\"\" class=\"wp-image-3883\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/watermark_17554652888964830374661246491114.png 720w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/watermark_17554652888964830374661246491114-300x169.png 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/watermark_17554652888964830374661246491114-600x338.png 600w\" sizes=\"(max-width: 720px) 100vw, 720px\" \/><figcaption class=\"wp-element-caption\"><em><strong>Dalar Giza, daga Daula ta hu\u0257u. <\/strong><\/em><\/figcaption><\/figure>\n\n\n\n<p>Wa\u0257annan gine-gine da dalilin yin su sun \u0257auki hankalin mutane da dama tsawon \u0199arni da dama. Wannan ne ma ya sa har ake ganin abin ya wuce tunani &#8211; inda ake danganta aiki da labarai iri daban-daban kan yadda aka samar da wa\u0257annan dala-dala a Masar.<\/p>\n\n\n\n<p>Wannan ne ya kai mu ga neman amsar wasu tambayoyi game da wa\u0257annan abubuwan ban mamaki : Me ya sa Misirawa suka yi wannan gini da wannan siffa ta Dala domin adana gawarwakin sarakunansu? Mene ne amfanin wa\u0257annan gine-gine ta fuskar addini da falsafa?<\/p>\n\n\n\n<p>Shin ana amfani da Dalar ne a matsayin Kabari ko kuma su na da wata ma&#8217;ana ko dalili da ya shafi jana&#8217;iza?<\/p>\n\n\n\n<p>Mutanen Masar \u0257in ne ka\u0257ai ko kuma akwai wasu mutanen da ke da hannu a aikin?<\/p>\n\n\n\n<p>Sannan a \u0199arshe an gina su ne ta hanyar aikin tilas ko kuma gwale-gwale, kamar yadda wasu ke i\u0199irari.<\/p>\n\n\n\n<p>Bari mu yi nazarin wasu daga cikin dalilan gine-ginen dalar:<\/p>\n\n\n\n<p>&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp; <strong>\u0198o\u0199arin kai wa ga Rana<\/strong><\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img decoding=\"async\" width=\"720\" height=\"404\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/watermark_17554653277117951304626183952239.png\" alt=\"\" class=\"wp-image-3884\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/watermark_17554653277117951304626183952239.png 720w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/watermark_17554653277117951304626183952239-300x168.png 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/watermark_17554653277117951304626183952239-600x337.png 600w\" sizes=\"(max-width: 720px) 100vw, 720px\" \/><figcaption class=\"wp-element-caption\"><strong>Hoton Dalar Sarki Khafre na Daula ta hu\u0257u, wanda ya yi zamani daga 2437-2414 kafin haihuwar Annabi Isa (AS)<\/strong><\/figcaption><\/figure>\n\n\n\n<p>Akan yi tambaya galibi cewa &#8211; Me ya sa sarakunan Masar na zamanin da suke son gina kaburburansu a siffar dala?<\/p>\n\n\n\n<p>Ana ganin su na yin hakan ne domin nuna yadda suka yi amanna da bautar rana &#8211; wadda ita ce jigon bauta a zamanin da a Masar.<\/p>\n\n\n\n<p>Su na yin wannan siffa ne musamman ma \u0199oli-\u0199olin Dalar &#8211; yadda yake da tsini &#8211; alama ce ta yadda hasken yake tunkaro Duniya. Saboda haka suke son binne sarakunansu a kabarin da yake da siffar yanayin hasken Rana, wadda suke fatan tashi zuwa gare ta a ranar tashin \u0199iyama &#8211; kamar yadda tarihinsu addinin Masar \u0257in na zamanin da ya nuna.<\/p>\n\n\n\n<p>&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp; <strong>Hanyar zuwa Aljanna<\/strong><\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img decoding=\"async\" width=\"720\" height=\"405\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/watermark_17554653726899163059473672584760.png\" alt=\"\" class=\"wp-image-3885\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/watermark_17554653726899163059473672584760.png 720w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/watermark_17554653726899163059473672584760-300x169.png 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/watermark_17554653726899163059473672584760-600x338.png 600w\" sizes=\"(max-width: 720px) 100vw, 720px\" \/><figcaption class=\"wp-element-caption\"><em><strong>\u0198wararrun injiniyoyin Sarki Sneferu sun yi nasarar gina hubbarensa a siffar Dala &#8211; wadda ake kira &#8216;Jar Dala&#8217; (Red Pyramid) da ke yankin Dahshur. <\/strong><\/em><\/figcaption><\/figure>\n\n\n\n<p>Mutanen Masar su na kiran Dala &#8220;Mer&#8221; a harshensu na zamanin da &#8211; wanda hakan ke nufin wajen da za a tashi sama.<\/p>\n\n\n\n<p>Wannan na nuna \u0199arara abin da suka yi amanna da shi a lokacin cewa ta wannan Dala ne ruhin sarkinsu zai tashi ya tafi sama &#8211; Aljanna in da zai ha\u0257u da Ubangiji Ra.<\/p>\n\n\n\n<p>Mutanen Masar na zamanin da na \u0257aukar Dala a matsayin hanyar zuwa rayuwa ta gaba &#8211; sama ko Aljanna &#8211; ga sarakunansu.<\/p>\n\n\n\n<p>Saboda kamar su mutanen Masar na zaman da sun yi amanna cewa, Mutuwa ba ita ce \u0199arshen rayuwa ba, sai ma dai farkon wata sabuwar rayuwa kuma hanyar tafiyar Ruhi zuwa ga Aljanna.<\/p>\n\n\n\n<p>A don haka, su na \u0257aukar Dala a matsayin wata matattakala ta kai wa ga sama &#8211; Aljanna.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"720\" height=\"404\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/watermark_17554654054668203057812924697017.png\" alt=\"\" class=\"wp-image-3886\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/watermark_17554654054668203057812924697017.png 720w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/watermark_17554654054668203057812924697017-300x168.png 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/watermark_17554654054668203057812924697017-600x337.png 600w\" sizes=\"(max-width: 720px) 100vw, 720px\" \/><figcaption class=\"wp-element-caption\"><em><strong>Dala mai matattakala ta Sarki Geser na Daula ta Uku da kuma hubbarensa a Saqqara &#8211; ya yi mulki daga shekara 2584-2565 kafin zuwan Annabi Isa (AS).<\/strong><\/em><em> <\/em><\/figcaption><\/figure>\n\n\n\n<p>Wasu masana sun yi amanna cewa, bayan alamtata da hasken Rana ita Dala wata alama ce ta \u0199arfin da ke da nasaba da ubangiji &#8211; wanda wannan \u0199arfi ne suka yi amanna zai \u0257aga ruhin sarkinsu bayan ya rasu zuwa Aljanna.<\/p>\n\n\n\n<p>Bayan rasuwarsa shi sarkinsu ya na zama abin da suke kira &#8216;Osiris&#8217; &#8211; wato ubangijin bayan mutuwa &#8211; wanda ta hakan ya zama wanda ba zai mutu ba kuma kamar ubangiji, kuma abokin tafiya a tafiye-tafiyensa na yau da kullum a sama &#8211; Aljanna &#8211; saboda haka ne siffar Dala take haka.<\/p>\n\n\n\n<p>Wannan ne ya sa a lokacin da su mutanen Masar suke gina Dala suke tsara ta, ta yadda za ta zama wajen ajiye gawar sarkin da ya mutu ba tare da wata matsala ba &#8211; domin kare ruhinsa ta yadda zai ci gaba da rayuwa da ba ta da \u0199arshe.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"720\" height=\"404\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/watermark_17554654390375460436705732437025.png\" alt=\"\" class=\"wp-image-3887\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/watermark_17554654390375460436705732437025.png 720w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/watermark_17554654390375460436705732437025-300x168.png 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/watermark_17554654390375460436705732437025-600x337.png 600w\" sizes=\"(max-width: 720px) 100vw, 720px\" \/><figcaption class=\"wp-element-caption\"><em><strong>Zanen sashen inda ake binne Sarki a cikin Dalar Sarki Khufu na Daula ta Hu\u0257u &#8211; ya yi Mulki daga 2470-2447 kafin zuwan Annabi Isa (AS). <\/strong><\/em><\/figcaption><\/figure>\n\n\n\n<p>A wajen al&#8217;ummar Masar ta wancan zamanin na da ruhi da kuma abokin tafiyarsa (Ba da Ka) ba za su iya tafiya zuwa rayuwa ta gaba da wadda ba ta da \u0199arshe, ba tare da wajen adana jikin mutumin da ya mutu ba yadda zai kasance \u0199alau ba tare da wani abu ya same shi ba.<\/p>\n\n\n\n<p>Saboda haka ne suke yin wannan Dala su yi waje mai kyau da tsaro su tanadi kayayyakin da Sarki ya saba rayuwa da su a Duniya a ajiye masa a cikin wannan Dala da aka binne shi tare da adana gawarsa yadda ita ma ba za ta lalace ba ko a sace ta.<\/p>\n\n\n\n<p>Su na yin hakan ne bisa amannar cewa, ruhin sarkin zai koma ya shiga jikinsa a lokacin da zai yi tafiya ta sama ko Aljanna wadda ba sauran mutuwa.<\/p>\n\n\n\n<p>Akwai kuma wani tunanin cewa, in da ake danganta Dalar ta Masar da wata alamar ta Addini &#8211; wadda ke cewa, kafin a halicci \u0257an&#8217;Adam da sauran halittu, Duniya Kogi ce da wani Tsauni a cikinsa.<\/p>\n\n\n\n<p>Nazariyya ta ce, daga cikin wannan Tsauni ne Ubangijin Rana (Ra) kamar yadda suka yi imani ya halicci kansa da kuma sauran Duniya.<\/p>\n\n\n\n<p>Bisa wannan ne suka yi amanna cewa, Dala alama ce ta wannan Tsauni na ainahi, saboda haka Misirawa na zamanin da suke \u0257aukar Dala da tsarki da muhimmanci.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"720\" height=\"404\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/watermark_17554654777881356658342653390126.png\" alt=\"\" class=\"wp-image-3888\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/watermark_17554654777881356658342653390126.png 720w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/watermark_17554654777881356658342653390126-300x168.png 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/watermark_17554654777881356658342653390126-600x337.png 600w\" sizes=\"(max-width: 720px) 100vw, 720px\" \/><figcaption class=\"wp-element-caption\"><em><strong>An yi rubuce-rubucen addini da suka fi da\u0257ewa a Duniya ne a Dalar Unas da ke Saqqara daga Daula ta Biyar &#8211; wadda ta kasance daga 2312-2282 kafin zuwan Annabi Isa (AS). <\/strong><\/em><\/figcaption><\/figure>\n\n\n\n<p>A nazarin da ta yi mai suna, &#8220;The Pharaohs in the Time of the God-Kings,&#8221; malamar Jami&#8217;a Claire Lalouette, \u01b4ar Faransa ta bayar da shaida da wasu daga cikin rubuce-rubucen a kan tashin da sarkin ya yi zuwa Aljanna.<\/p>\n\n\n\n<p>Ginin zuwa Aljanna<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"720\" height=\"405\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/watermark_17554655178195435324801050633265.png\" alt=\"\" class=\"wp-image-3889\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/watermark_17554655178195435324801050633265.png 720w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/watermark_17554655178195435324801050633265-300x169.png 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/watermark_17554655178195435324801050633265-600x338.png 600w\" sizes=\"(max-width: 720px) 100vw, 720px\" \/><figcaption class=\"wp-element-caption\"><em><strong>\u0181angaren Dalar Sarki Sneferu a Dahshur, da ya \u0253a\u0253\u0253angare &#8211; Daula ta Uku (2584-2117 kafin zuwan Annabi Isa (AS). <\/strong><\/em><\/figcaption><\/figure>\n\n\n\n<p>A rubutunsa na tarihin Masar ta zamanin da (&#8220;Ancient Egyptian History,&#8221; ) Ramadan Abdo ya yi ammana cewa hubbaren sarakunan lokacin ta zama haka ne &#8211; dala saboda abu biyu:<\/p>\n\n\n\n<p>&#8221;Na farko domin girmamawa da tsarkake sarki &#8211; wanda saboda matsayinsa sai an gina masa \u0199aton waje in da daga nan ne zai ri\u0199a sanya ido a kan abin da ke faruwa a Duniya &#8211; kamar yadda yake yi a lokacin ya na raye a wannan duniyar.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8221;Abu na biyu kuma shi ne, sha&#8217;awar da al&#8217;ummar Masar na lokacin suke da ita ta yin abubuwa na al&#8217;ada na \u0199awa &#8211; wannan ya sa su nemo wata hanya ta bajinta ta gina hubbare.<\/p>\n\n\n\n<p>Sarakunan Masar sun gina Dala ne ta hanyar bautar da Mutane?<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"720\" height=\"404\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/watermark_17554655574474019388080407065016.png\" alt=\"\" class=\"wp-image-3890\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/watermark_17554655574474019388080407065016.png 720w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/watermark_17554655574474019388080407065016-300x168.png 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/watermark_17554655574474019388080407065016-600x337.png 600w\" sizes=\"(max-width: 720px) 100vw, 720px\" \/><\/figure>\n\n\n\n<p>Wasu masana na \u0199asashen Yammacin Duniya sun da\u0257e su na i\u0199irarin cewa, Bayi ne suka gina dala-dalar Masar &#8211; i\u0199irarin da ke nuna cewa, an ci zarafin Mutane a aikin gina dala-dalar da ta kasance gini mai \u0257aukar hankali na ban mamaki a tarihin Duniya.<\/p>\n\n\n\n<p>Sai dai kuma, wasu kayayyakin Tarihi da aka tono kwanan nan da wasu rubuce-rubuce da aka samu sun sa\u0253a da wannan ra&#8217;ayi.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"720\" height=\"451\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/watermark_17554655964028027724436753411701.png\" alt=\"\" class=\"wp-image-3891\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/watermark_17554655964028027724436753411701.png 720w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/watermark_17554655964028027724436753411701-300x188.png 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/watermark_17554655964028027724436753411701-600x376.png 600w\" sizes=\"(max-width: 720px) 100vw, 720px\" \/><\/figure>\n\n\n\n<p>Kayayyakin sun nuna cewa al&#8217;ummar da aka santa da tsari da kuma \u0199warewa wadda kuma ke samar wa ma&#8217;aikatan manyan ayyuka irin su; Dala da tsari na kare rayuwarsu da kuma jin da\u0257in abin da ke nuna an damu da jin da\u0257insu sosai.<\/p>\n\n\n\n<p>Ga al&#8217;ummar Masar wannan dala-dala da kakanninsu suka gina a zamanin da, ba kawai manyan gine-gine ba ne a tsakiyar Sahara a wajen birnin.<\/p>\n\n\n\n<p>Alamu ne na ci gaba da kuma tsabar kishin addini &#8211; da ke zaman hubbare, wajen ibada sannan kuma hanyar zuwa sama &#8211; Aljanna.<\/p>\n\n\n\n<p>Har ila yau, sun kasance wurin yawon bude ido, in da al&#8217;umma daga sassa daban-daban na Duniya ke ziyarta.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"750\" height=\"409\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/images-2025-08-17t2209563256889462255712886.jpg\" alt=\"\" class=\"wp-image-3892\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/images-2025-08-17t2209563256889462255712886.jpg 750w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/images-2025-08-17t2209563256889462255712886-300x164.jpg 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/images-2025-08-17t2209563256889462255712886-600x327.jpg 600w\" sizes=\"(max-width: 750px) 100vw, 750px\" \/><\/figure>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Ginin Dalar Masar ta zamanin da ba abu ba ne da kawai aka yi shi haka ba, ba tare da wasu dalilai ba, ko rashin ma&#8217;ana ko kuma an yi wannan katafaren gini na Dutse ne a matsayin Kabari ko hubbaren sarakuna domin girmama sarakunan na zamanin da ba. Aiki ne da ya \u0199unshi dalilai [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":3882,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"inline_featured_image":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[88],"tags":[116],"class_list":["post-3893","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-tarihi","tag-taskarnasaba-unesco-giza"],"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v27.0 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Me ya sa Misirawa suka ri\u0199a gina manya-manyan Dala?<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"noindex, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_US\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Me ya sa Misirawa suka ri\u0199a gina manya-manyan Dala?\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"Ginin Dalar Masar ta zamanin da ba abu ba ne da kawai aka yi shi haka ba, ba tare da wasu dalilai ba, ko rashin ma&#8217;ana ko kuma an yi wannan katafaren gini na Dutse ne a matsayin Kabari ko hubbaren sarakuna domin girmama sarakunan na zamanin da ba. Aiki ne da ya \u0199unshi dalilai [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3893\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"Taskar Nasaba\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2025-08-17T21:43:38+00:00\" \/>\n<meta property=\"article:modified_time\" content=\"2025-08-17T21:47:41+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/Watermark_1755465660858.jpg\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"720\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"660\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/jpeg\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Taskar Nasaba\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"Taskar Nasaba\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Est. reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"7 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\/\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3893#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3893\"},\"author\":{\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/50c6fe8b25398ccbaf7fd94dee1c8456\"},\"headline\":\"Me ya sa Misirawa suka ri\u0199a gina manya-manyan Dala?\",\"datePublished\":\"2025-08-17T21:43:38+00:00\",\"dateModified\":\"2025-08-17T21:47:41+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3893\"},\"wordCount\":1447,\"commentCount\":0,\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3893#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/Watermark_1755465660858.jpg\",\"keywords\":[\"#taskarnasaba #UNESCO #giza\"],\"articleSection\":[\"Tarihi\"],\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3893#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3893\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3893\",\"name\":\"Me ya sa Misirawa suka ri\u0199a gina manya-manyan Dala?\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3893#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3893#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/Watermark_1755465660858.jpg\",\"datePublished\":\"2025-08-17T21:43:38+00:00\",\"dateModified\":\"2025-08-17T21:47:41+00:00\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3893#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3893\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3893#primaryimage\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/Watermark_1755465660858.jpg\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/Watermark_1755465660858.jpg\",\"width\":720,\"height\":660},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3893#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Me ya sa Misirawa suka ri\u0199a gina manya-manyan Dala?\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"description\":\"\",\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\"},\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-US\"},{\"@type\":\"Organization\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\",\"logo\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png\",\"width\":343,\"height\":345,\"caption\":\"Taskar Nasaba\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/\"}},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/50c6fe8b25398ccbaf7fd94dee1c8456\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/cropped-Taskar-Nasaba-PNG-100x100.png\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/cropped-Taskar-Nasaba-PNG-100x100.png\",\"caption\":\"Taskar Nasaba\"},\"sameAs\":[\"http:\/\/www.taskarnasaba.com.ng\"],\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?author=2\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Me ya sa Misirawa suka ri\u0199a gina manya-manyan Dala?","robots":{"index":"noindex","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"og_locale":"en_US","og_type":"article","og_title":"Me ya sa Misirawa suka ri\u0199a gina manya-manyan Dala?","og_description":"Ginin Dalar Masar ta zamanin da ba abu ba ne da kawai aka yi shi haka ba, ba tare da wasu dalilai ba, ko rashin ma&#8217;ana ko kuma an yi wannan katafaren gini na Dutse ne a matsayin Kabari ko hubbaren sarakuna domin girmama sarakunan na zamanin da ba. Aiki ne da ya \u0199unshi dalilai [&hellip;]","og_url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3893","og_site_name":"Taskar Nasaba","article_published_time":"2025-08-17T21:43:38+00:00","article_modified_time":"2025-08-17T21:47:41+00:00","og_image":[{"width":720,"height":660,"url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/Watermark_1755465660858.jpg","type":"image\/jpeg"}],"author":"Taskar Nasaba","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"Taskar Nasaba","Est. reading time":"7 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3893#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3893"},"author":{"name":"Taskar Nasaba","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/50c6fe8b25398ccbaf7fd94dee1c8456"},"headline":"Me ya sa Misirawa suka ri\u0199a gina manya-manyan Dala?","datePublished":"2025-08-17T21:43:38+00:00","dateModified":"2025-08-17T21:47:41+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3893"},"wordCount":1447,"commentCount":0,"publisher":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3893#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/Watermark_1755465660858.jpg","keywords":["#taskarnasaba #UNESCO #giza"],"articleSection":["Tarihi"],"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3893#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3893","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3893","name":"Me ya sa Misirawa suka ri\u0199a gina manya-manyan Dala?","isPartOf":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3893#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3893#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/Watermark_1755465660858.jpg","datePublished":"2025-08-17T21:43:38+00:00","dateModified":"2025-08-17T21:47:41+00:00","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3893#breadcrumb"},"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3893"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3893#primaryimage","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/Watermark_1755465660858.jpg","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/Watermark_1755465660858.jpg","width":720,"height":660},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3893#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/taskarnasaba.com\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Me ya sa Misirawa suka ri\u0199a gina manya-manyan Dala?"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/","name":"Taskar Nasaba","description":"","publisher":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization"},"potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-US"},{"@type":"Organization","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization","name":"Taskar Nasaba","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/","logo":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png","width":343,"height":345,"caption":"Taskar Nasaba"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/"}},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/50c6fe8b25398ccbaf7fd94dee1c8456","name":"Taskar Nasaba","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/image\/","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/cropped-Taskar-Nasaba-PNG-100x100.png","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/cropped-Taskar-Nasaba-PNG-100x100.png","caption":"Taskar Nasaba"},"sameAs":["http:\/\/www.taskarnasaba.com.ng"],"url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?author=2"}]}},"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/Watermark_1755465660858.jpg","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3893","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=3893"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3893\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3894,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3893\/revisions\/3894"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/3882"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=3893"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=3893"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=3893"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}