{"id":3898,"date":"2025-08-17T21:59:03","date_gmt":"2025-08-17T21:59:03","guid":{"rendered":"https:\/\/taskarnasaba.com.ng\/?p=3898"},"modified":"2025-08-17T21:59:03","modified_gmt":"2025-08-17T21:59:03","slug":"wace-ce-nana-asmau-%c6%b4ar-shehu-usmanu-%c9%97anfodiyo","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3898","title":{"rendered":"Wace ce Nana Asma&#8217;u, \u01b4ar Shehu Usmanu \u018aanfodiyo"},"content":{"rendered":"\n<p><strong>Daga: A&#8217;isha Aliyu Ja&#8217;afar<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p><em>Nana Asma&#8217;u \u0257iya ce daga cikin \u01b4a\u01b4a 23 na Shehu Usmanu \u018aanfodio, mujaddadin da ya jaddada addinin Musulunci a \u0199arni na 17, a Arewacin Najeriya<\/em>.<\/p>\n\n\n\n<p><em>Kasancewarta \u01b4an biyu &#8211; an haifi Asma&#8217;u tare da Hassan \u0257inta a shekarar 1793, shekaru 11 kafin kafa Daular Usmaniyya kuma ta rasu a 1865 ta na da shekaru 72<\/em><strong><em>.<\/em><\/strong><\/p>\n\n\n\n<p><em>Duk da cewa Nana Asma&#8217;u, ba ita ka\u0257ai ce \u01b4a mace ga Shehu Usmanu ba, amma sunanta ya fi shahara a kan na \u01b4an uwanta da suka ha\u0257a da Aisha da Maryam da Fatima da kuma Hauwa&#8217;u<\/em><strong><em>.<\/em><\/strong><\/p>\n\n\n\n<p><em>Ana yi wa Nana la\u0199abi da sunaye kamar Asma&#8217;u Uwar Daje, ko Nana ko kuma Ma&#8217;u.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><strong>Iyalin Asma&#8217;u<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>A shekarar 1807 ne Nana Asma&#8217;u ta auri maigidanta Usman Gi\u0257a\u0257o wanda \u0257aya ne daga cikin manyan almajiran mahaifinta, Shehu Usmanu \u018aanfodiyo da suka zauna da shi, kuma \u0257aya daga cikin malaman da suka taimaka masa wajen gina Daular Usmaniyya.<\/p>\n\n\n\n<p>\u01b3a\u01b4an Nana Asma&#8217;u guda biyar ne kuma dukkanninsu maza ne kamar yadda Jean Boyd da Beverly B. Mack suka rubuta:<\/p>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Abdul\u0199adir<\/li>\n\n\n\n<li>Ahmad<\/li>\n\n\n\n<li>Usman<\/li>\n\n\n\n<li>Abdullahi Bayero<\/li>\n\n\n\n<li>Muhammad Laima<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<p><strong>Ilimantarwa<\/strong><\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img fetchpriority=\"high\" decoding=\"async\" width=\"720\" height=\"720\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/watermark_17554675539286815303065087527083.png\" alt=\"\" class=\"wp-image-3896\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/watermark_17554675539286815303065087527083.png 720w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/watermark_17554675539286815303065087527083-300x300.png 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/watermark_17554675539286815303065087527083-150x150.png 150w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/watermark_17554675539286815303065087527083-100x100.png 100w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/watermark_17554675539286815303065087527083-600x600.png 600w\" sizes=\"(max-width: 720px) 100vw, 720px\" \/><\/figure>\n\n\n\n<p>Nana Uwar Daji, ta shahara a fagen ilimantarwa musamman ga \u01b4an uwanta Mata, inda ta bai wa mahaifinta gagarumar gudunmowar sake wa Mata tunani a sabuwar Daular Musulunci dangane da yadda za su gudanar da ibadunsu na yau da kullum.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;Ta yi karatu mai zurfi a wurin mahaifinta, kuma masana tarihi sun ce ta na da gogewa a manyan harsuna uku &#8211; Larabci da Hausa da kuma Mashek (yaran Buzaye).<\/p>\n\n\n\n<p>Hakazalika, ta \u0199ware a Fulantanci wanda kuma ta na rubutu da dukkan harsunan. Amma ta fi rubutu a Hausa da Larabci da kuma Fulatanci.&#8221; In ji dakta Abdullahi Hamisu Shehu, Malami a Tsangayar Tarihi da ke Jami&#8217;ar Bayero ta Kano.<\/p>\n\n\n\n<p>Wani salo da Nana Asma&#8217;u ta yi amfani da shi wajen ilimantar da Mata a lokacin shi ne; ta hanyar Wa\u0199e, kamar dai yadda mahaifinta ya yi wajen jan hankulan al&#8217;umma ba tare da tsaurarawa ba.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;Galibin rubutunta a Wa\u0199e ta yi su, saboda Wa\u0199a na da hikima da saurin isar da sa\u0199o musamman idan ana rerawa.<\/p>\n\n\n\n<p>Idan ana yi, Yara da Mata na haddacewa cikin \u0199an\u0199anin lokaci, ba kamar rubutun zube ba,&#8221; in ji Dakta Abdullahi.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Makarantar Matan Aure na Farko<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Kasancewar a zamanin babu ajujuwan koyarwa kamar na yau, amma tun a lokacin Nana Asma&#8217;u na da majalisai na koyarwa a cikin Gida, wanda za a iya cewa ita ta assasa abin da ake kira a yanzu, &#8216;Makarantar Matan Aure,&#8217; saboda cikin almajiranta akwai Matan Aure da kuma \u01b4anmata.<\/p>\n\n\n\n<p>Kuma hakan ne ya sa ta samu kar\u0253uwa sannan abin da ta koyar ya yi naso.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;Abubuwan da take koyarwa sun yi naso, saboda har wa\u0257anda ba sa zuwa makarantarta su na samun ilimin daga iyayensu ko \u01b4a\u01b4a,&#8221; in ji Dakta Hamisu.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8221;A wannan lokacin babu kamarta wajen koyar da Mata, hakan ya ba ta kima da tasiri na musamman saboda gudunmowar da ta bayar wurin ilimantarwa.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>Idan aka cire Shehu Usmanu \u018aanfodiyo, da \u0257an&#8217;uwansa Sheikh Abdullahi bin Fodiyo da kuma \u0257ansa Muhammadu Bello, wa\u0257anda za a ce sun bayar da gudunmowa kuma an tasirantu da su ta fuskar ilimantarwa a lokacinsu da lokacin baya, Nana Asma&#8217;u ce,&#8221; a cewar Dakta Hamisu.<\/p>\n\n\n\n<p>Nana Asma&#8217;u ta yi tsawon rai inda ta rasu a lokacin ta na da shekaru 75 wanda ya \u0199ara mata tasiri sosai a zukatan mutane musamman Mata.<\/p>\n\n\n\n<p>Sa\u0253anin tunanin da ake yi wa Mata na gaza yin bautar Ubangiji kamar Maza, Nana Asma&#8217;u ta kasance Mace mai \u0199o\u0199arin ibada da ta sallama rayuwarta wajen bautata wa Ubangiji tare da yi wa addinin Musulunci hidima.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8221;Tarihinta ya nuna ba ta da aiki sai ibada, da koyo da koyarwa, kuma saliha ce,&#8221; in ji Dakta Abdullahi.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Rubuce-rubucen Nana Asma&#8217;u<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Ba a san iya yawan rubuce-rubucen Nana Asma&#8217;u ba kasancewar wasu sun \u0253ata, wasu sun lalace kafin a juya su zuwa tsarin rubutu na yanzu.<\/p>\n\n\n\n<p>Sai dai an samu guda 66 da ke cikin gafakarta ta adana rubuce-rubucenta wadda take a gidanta.<\/p>\n\n\n\n<p>Nana Asma&#8217;u ta rubuta su ne da harshen Larabci da Fulatanci da Hausa amma a salon Ajami.<\/p>\n\n\n\n<p>Mafi yawancin rubuce-rubucen nata wa\u0257anda a salon wa\u0199e ne sun \u0199unshi Tarihi da alhinin magabata da wa&#8217;azi da garga\u0257i wa\u0257anda su ne suka zama ginshi\u0199in da ya taimaka wajen ri\u0199e Daular ta Usmaniyya.<\/p>\n\n\n\n<p>Ga jerin wasu daga cikin rubuce-rubucen Nana Asma&#8217;u da ake yi la\u0199abi da Uwar Daji na muka na\u0199alto daga littafin &#8220;Collected Works of Nana Asma&#8217;u, Daughter of Usmanu \u018aanfodiyo (1793-1864) wanda Jean Boyd da Beverly B. Mack suka rubuta.<\/p>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Tabbat Hakika<\/li>\n\n\n\n<li>Tawassuli ga Mata Masu Albarka<\/li>\n\n\n\n<li>Wa\u0199ar Fadanci da Surorin Alkur&#8217;ani<\/li>\n\n\n\n<li>Wa\u0199ar Ahmada<\/li>\n\n\n\n<li>Wa\u0199ar Gewaye<\/li>\n\n\n\n<li>Godaben Gaskiya<\/li>\n\n\n\n<li>Muma Kan Nasara Ya\u0199i<\/li>\n\n\n\n<li>Alhinin Mutuwa<\/li>\n\n\n\n<li>Wa&#8217;azu<\/li>\n\n\n\n<li>Ro\u0199on Ruwa<\/li>\n\n\n\n<li>Tsorace-Tsoracen Tsayin Al-Kiyama<\/li>\n\n\n\n<li>Dalilin Samuwar Allah<\/li>\n\n\n\n<li>Labaran Shehu<\/li>\n\n\n\n<li>Alhinin Mutuwar Modibbo \u018aan Ali<\/li>\n\n\n\n<li>Begore (Yabon Allah)<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<p>Masana na ganin cewa, wa\u0199en da Nana Asma&#8217;u ta yi su ne suka zama \u0257an-ba na \u0199arfafa wa matan Daular Usmaniyya, watau; matan Arewacin Najeriya a yau \u0257in nan guiwar yin Wa\u0199e.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Nazari kan rayuwarta da Ayyukanta<\/strong><\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img decoding=\"async\" width=\"522\" height=\"588\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/images-2025-08-17t2250314158438204051116381.jpg\" alt=\"\" class=\"wp-image-3897\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/images-2025-08-17t2250314158438204051116381.jpg 522w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/images-2025-08-17t2250314158438204051116381-266x300.jpg 266w\" sizes=\"(max-width: 522px) 100vw, 522px\" \/><\/figure>\n\n\n\n<p>Dakta Abdullahi Hamisu ya ce, Malaman Tarihi da dama daga wurare daban-daban sun yi bincike tare da nazari kan ayyukanta da abubuwan da ta fa\u0257i kamar; darussan ibada, da na zamantakewa, da yadda za a kyautata rayuwa mai kyau, kusan duk abin da ya shafi addinin Musulunci ta yi rubutu a kai.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8221;Wannan ya sa aka yi ayyuka da yawa kan rubutunta na Larabci da Fulatanci da kuma Hausa, musamman fasalin rubutunta da sa\u0199onnin da suke \u0199unshe a ciki, inda aka taskace su aka kuma adana su,&#8221; in ji shi.<\/p>\n\n\n\n<p>Ya kuma ce ko a shekarar 2019 tsohon Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya amince da kafa wata Jami&#8217;a ta koyar da aikin Likitanci da aka sanya wa sunan Nana Asma&#8217;u domin a ci gaba da tunawa da ita da ayyukanta da kuma gudunmowar da ta bai wa Musulmai a Arewacin Najeriya.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga: A&#8217;isha Aliyu Ja&#8217;afar Nana Asma&#8217;u \u0257iya ce daga cikin \u01b4a\u01b4a 23 na Shehu Usmanu \u018aanfodio, mujaddadin da ya jaddada addinin Musulunci a \u0199arni na 17, a Arewacin Najeriya. Kasancewarta \u01b4an biyu &#8211; an haifi Asma&#8217;u tare da Hassan \u0257inta a shekarar 1793, shekaru 11 kafin kafa Daular Usmaniyya kuma ta rasu a 1865 ta [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":3895,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"inline_featured_image":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[93],"tags":[117],"class_list":["post-3898","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-jiya-da-yau","tag-taskarnasaba-nanaasmau-anfodiyo"],"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v27.0 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Wace ce Nana Asma&#039;u, \u01b4ar Shehu Usmanu \u018aanfodiyo<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"noindex, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_US\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Wace ce Nana Asma&#039;u, \u01b4ar Shehu Usmanu \u018aanfodiyo\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"Daga: A&#8217;isha Aliyu Ja&#8217;afar Nana Asma&#8217;u \u0257iya ce daga cikin \u01b4a\u01b4a 23 na Shehu Usmanu \u018aanfodio, mujaddadin da ya jaddada addinin Musulunci a \u0199arni na 17, a Arewacin Najeriya. Kasancewarta \u01b4an biyu &#8211; an haifi Asma&#8217;u tare da Hassan \u0257inta a shekarar 1793, shekaru 11 kafin kafa Daular Usmaniyya kuma ta rasu a 1865 ta [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3898\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"Taskar Nasaba\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2025-08-17T21:59:03+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/watermark_17554675539286815303065087527083.png\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"720\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"720\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/png\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Taskar Nasaba\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"Taskar Nasaba\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Est. reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"5 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\/\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3898#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3898\"},\"author\":{\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/50c6fe8b25398ccbaf7fd94dee1c8456\"},\"headline\":\"Wace ce Nana Asma&#8217;u, \u01b4ar Shehu Usmanu \u018aanfodiyo\",\"datePublished\":\"2025-08-17T21:59:03+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3898\"},\"wordCount\":1041,\"commentCount\":0,\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3898#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/Watermark_1755467611600.jpg\",\"keywords\":[\"#taskarnasaba #nanaasma'u #\u018aanfodiyo\"],\"articleSection\":[\"Jiya Da Yau\"],\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3898#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3898\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3898\",\"name\":\"Wace ce Nana Asma'u, \u01b4ar Shehu Usmanu \u018aanfodiyo\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3898#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3898#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/Watermark_1755467611600.jpg\",\"datePublished\":\"2025-08-17T21:59:03+00:00\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3898#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3898\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3898#primaryimage\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/Watermark_1755467611600.jpg\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/Watermark_1755467611600.jpg\",\"width\":720,\"height\":422},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3898#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Wace ce Nana Asma&#8217;u, \u01b4ar Shehu Usmanu \u018aanfodiyo\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"description\":\"\",\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\"},\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-US\"},{\"@type\":\"Organization\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\",\"logo\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png\",\"width\":343,\"height\":345,\"caption\":\"Taskar Nasaba\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/\"}},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/50c6fe8b25398ccbaf7fd94dee1c8456\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/cropped-Taskar-Nasaba-PNG-100x100.png\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/cropped-Taskar-Nasaba-PNG-100x100.png\",\"caption\":\"Taskar Nasaba\"},\"sameAs\":[\"http:\/\/www.taskarnasaba.com.ng\"],\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?author=2\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Wace ce Nana Asma'u, \u01b4ar Shehu Usmanu \u018aanfodiyo","robots":{"index":"noindex","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"og_locale":"en_US","og_type":"article","og_title":"Wace ce Nana Asma'u, \u01b4ar Shehu Usmanu \u018aanfodiyo","og_description":"Daga: A&#8217;isha Aliyu Ja&#8217;afar Nana Asma&#8217;u \u0257iya ce daga cikin \u01b4a\u01b4a 23 na Shehu Usmanu \u018aanfodio, mujaddadin da ya jaddada addinin Musulunci a \u0199arni na 17, a Arewacin Najeriya. Kasancewarta \u01b4an biyu &#8211; an haifi Asma&#8217;u tare da Hassan \u0257inta a shekarar 1793, shekaru 11 kafin kafa Daular Usmaniyya kuma ta rasu a 1865 ta [&hellip;]","og_url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3898","og_site_name":"Taskar Nasaba","article_published_time":"2025-08-17T21:59:03+00:00","og_image":[{"width":720,"height":720,"url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/watermark_17554675539286815303065087527083.png","type":"image\/png"}],"author":"Taskar Nasaba","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"Taskar Nasaba","Est. reading time":"5 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3898#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3898"},"author":{"name":"Taskar Nasaba","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/50c6fe8b25398ccbaf7fd94dee1c8456"},"headline":"Wace ce Nana Asma&#8217;u, \u01b4ar Shehu Usmanu \u018aanfodiyo","datePublished":"2025-08-17T21:59:03+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3898"},"wordCount":1041,"commentCount":0,"publisher":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3898#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/Watermark_1755467611600.jpg","keywords":["#taskarnasaba #nanaasma'u #\u018aanfodiyo"],"articleSection":["Jiya Da Yau"],"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3898#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3898","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3898","name":"Wace ce Nana Asma'u, \u01b4ar Shehu Usmanu \u018aanfodiyo","isPartOf":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3898#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3898#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/Watermark_1755467611600.jpg","datePublished":"2025-08-17T21:59:03+00:00","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3898#breadcrumb"},"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3898"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3898#primaryimage","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/Watermark_1755467611600.jpg","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/Watermark_1755467611600.jpg","width":720,"height":422},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3898#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/taskarnasaba.com\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Wace ce Nana Asma&#8217;u, \u01b4ar Shehu Usmanu \u018aanfodiyo"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/","name":"Taskar Nasaba","description":"","publisher":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization"},"potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-US"},{"@type":"Organization","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization","name":"Taskar Nasaba","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/","logo":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png","width":343,"height":345,"caption":"Taskar Nasaba"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/"}},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/50c6fe8b25398ccbaf7fd94dee1c8456","name":"Taskar Nasaba","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/image\/","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/cropped-Taskar-Nasaba-PNG-100x100.png","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/10\/cropped-Taskar-Nasaba-PNG-100x100.png","caption":"Taskar Nasaba"},"sameAs":["http:\/\/www.taskarnasaba.com.ng"],"url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?author=2"}]}},"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/Watermark_1755467611600.jpg","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3898","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=3898"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3898\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/3895"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=3898"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=3898"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=3898"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}