{"id":3924,"date":"2025-09-02T00:39:05","date_gmt":"2025-09-02T00:39:05","guid":{"rendered":"https:\/\/taskarnasaba.com.ng\/?p=3924"},"modified":"2025-09-02T00:39:05","modified_gmt":"2025-09-02T00:39:05","slug":"lina-medina-uwa-mafi-%c6%99an%c6%99antar-shekaru-a-duniya","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3924","title":{"rendered":"Lina Medina: Uwa mafi \u0199an\u0199antar shekaru a Duniya"},"content":{"rendered":"\n<p><em>A tarihin bil\u2019adama akwai labaran da suka \u0199unshi mamaki, wasu kuma su na \u0257auke da darussa masu zurfi. Labarin Lina Medina, yarinya daga \u0199asar Peru, na \u0257aya daga cikin wa\u0257annan abubuwa da ba a manta da su ba.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><strong>Farkon Rayuwa da Samuwar Ciki<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>An haifi Lina Medina a shekara ta 1933 a \u0199auyen Ticrapo, cikin gundumar Castrovirreyna Province a \u0199asar Peru. Mahaifinta, Tiburelo Medina, ya kasance mai sana\u2019ar sarrafa Azurfa, yayin da mahaifiyarta ita ce Victoria Losea. Lina ta kasance \u0257aya daga cikin \u01b4a\u01b4a tara a cikin iyalin iyayenta.<\/p>\n\n\n\n<p>Lokacin da take da shekaru biyar, iyayenta suka kai ta Asibiti a garin Pisco, saboda ciki ya fara fitowa a jikinta. A farko Likitoci sun \u0257auka cutar ciwon \u0199ari (tumor) ce, amma daga \u0199arshe suka gano ta na da ciki, har ma cikin ya kai wata bakwai. Likita Dr. Gerardo Lozada, wanda daga baya ya kula da ita, ya tabbatar da hakan tare da sauran \u0199wararru daga Lima.<\/p>\n\n\n\n<p>Lamarin ya jawo hankalin Duniya. Jaridar San Antonio Light ta Amurka ta wallafa a ranar 16 ga watan Yuli, 1939, cewa \u0199ungiyar Likitoci a Peru ta bu\u0199aci a kai Lina Cibiyar Haihuwa ta \u0198asa. Har ma aka rawaito cewa, wani kamfanin shirya Fina-finai daga Amurka ya ba da tayin Dala 5,000 domin ya samu damar yin Fim \u0257in lamarin, amma iyayenta suka \u0199i amincewa.<\/p>\n\n\n\n<p>Likita Lozada da kansa ya yi rikodin Fim \u0257in haihuwar don amfani a fannin binciken kimiyya, in da ya gabatar da shi a gaban Majalisar Likitocin Peru.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Haihuwa da Abubuwan Mamaki<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Bayan makonni shida da gano ta na da ciki, a ranar 14 ga Mayu, 1939, Lina ta haihu ta hanyar aikin tiyata (caesarean section) saboda \u0199ananan \u0199ashin \u0199ugunta ba zai iya ba ta damar haihuwa ta hanyar \u0257abi\u2019a ba. Tiyatar ta gudana ne a hannun Dr. Lozada da Dr. Busalleu, tare da Dr. Colareta a matsayin mai bada maganin sa Barci.<\/p>\n\n\n\n<p>An haifi jariri Namiji mai nauyin Kilo 2.7, aka kuma saka masa suna &#8220;<strong>Gerardo<\/strong>,&#8221; (sunan likitan da ya kula da lamarin). Likitoci sun tabbatar cewa Lina ta ri ga ta sami cikakken tsarin ga\u0253o\u0253in Mace saboda abin da ake kira &#8216;precocious puberty&#8217; (balaga tun da wuri).<\/p>\n\n\n\n<div class=\"wp-block-media-text is-stacked-on-mobile\"><figure class=\"wp-block-media-text__media\"><img fetchpriority=\"high\" decoding=\"async\" width=\"300\" height=\"226\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/images-2025-09-02t0126265228087204808568479-300x226.jpg\" class=\"wp-image-3920 size-full\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/images-2025-09-02t0126265228087204808568479-300x226.jpg 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/images-2025-09-02t0126265228087204808568479-600x451.jpg 600w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/images-2025-09-02t0126265228087204808568479.jpg 638w\" sizes=\"(max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/figure><div class=\"wp-block-media-text__content\">\n<p><em>Lokacin da Lina Medina ta haifi \u0257anta, ta na \u01b4ar shekaru biyar.<\/em> <\/p>\n<\/div><\/div>\n\n\n\n<p>Likita Edmundo Escomel ya wallafa rahoton nata a cikin Mujallar likitanci ta Faransa, &#8216;La Presse M\u00e9dicale,&#8217; in da ya bayyana cewa, al\u2019adarta ta farko ta zo tun ta na watanni takwas, sa\u0253anin rahotannin baya da suka nuna wai ta fara al\u2019ada tun ta na shekaru biyu da rabi ko uku.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Rayuwar Gerardo<\/strong><\/p>\n\n\n\n<div class=\"wp-block-media-text is-stacked-on-mobile\"><figure class=\"wp-block-media-text__media\"><img decoding=\"async\" width=\"300\" height=\"200\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/images-2025-09-02t0131402369647804101751575-300x200.jpg\" class=\"wp-image-3922 size-full\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/images-2025-09-02t0131402369647804101751575-300x200.jpg 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/images-2025-09-02t0131402369647804101751575-600x400.jpg 600w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/images-2025-09-02t0131402369647804101751575.jpg 678w\" sizes=\"(max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/figure><div class=\"wp-block-media-text__content\">\n<p><em>Lina Medina tare da \u0257anta Gerardo. <\/em><\/p>\n<\/div><\/div>\n\n\n\n<p>Da farko an shaidawa Gerardo cewa, Lina \u01b4ar&#8217;uwarsa ce, amma daga baya, lokacin da ya kai shekaru goma, ya gano cewa ita ce mahaifiyarsa. Bayan wani lokaci, Likita Lozada ya \u0257auki nauyin tarbiyyar Gerardo a gidansa a Lima, in da ya kuma ba da damar Lina ta zauna da yin aiki a asibitinsa. Duk da haka, ba ta samun damar ganin \u0257anta akai-akai.<\/p>\n\n\n\n<div class=\"wp-block-media-text is-stacked-on-mobile\"><figure class=\"wp-block-media-text__media\"><img decoding=\"async\" width=\"197\" height=\"300\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/images-2025-09-02t0137361645669453662857879-197x300.jpg\" class=\"wp-image-3923 size-full\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/images-2025-09-02t0137361645669453662857879-197x300.jpg 197w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/images-2025-09-02t0137361645669453662857879.jpg 449w\" sizes=\"(max-width: 197px) 100vw, 197px\" \/><\/figure><div class=\"wp-block-media-text__content\">\n<p><em>Lina Medina tare da \u0257anta Gerardo. <\/em><\/p>\n<\/div><\/div>\n\n\n\n<p>Gerardo ya tashi cikin \u0199oshin lafiya, amma daga baya ya rasu a shekara ta 1979, ya na da shekaru 40, sakamakon cutar \u0199ashi (bone marrow disease).<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Batun Mahaifin Jariri<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>A bisa dokar \u0199asar Peru, kasancewar Lina ta \u0257auki ciki a wannan \u0199an\u0199antar shekaru ya nuna cewa ta fuskanci cin zarafi. Duk da haka, har zuwa yau ba a san asalin mahaifin jaririn ba.<\/p>\n\n\n\n<p>Lina ba ta ta\u0253a bayyana yadda lamarin ya faru da ita ba, kuma wasu sun ce; wata\u0199ila ma ba ta sani ba saboda \u0199arancin shekarunta a wancan lokacin.<\/p>\n\n\n\n<p>Mahaifinta, an kama shi bisa zargin cin zarafi, amma daga baya aka sake shi saboda rashin shaida da hujja.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Rayuwa daga Baya<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Bayan wannan lamari, Lina ta ci gaba da rayuwa cikin natsuwa da \u0253oye sirri. A lokacin samartaka, ta yi aiki a matsayin Sakatariya a Asibitin Dr. Lozada a Lima, abin da ya ba ta damar samun ilimi da kuma tallafawa \u0257anta ya yi karatu har zuwa Sakandire.<\/p>\n\n\n\n<p>A shekara ta 1972, ta yi aure kuma ta haifi \u0257a na biyu. Amma duk da shaharar da ta samu a Duniya, ta \u0199i bayyana cikakkun bayanai game da abin da ya faru da ita.<\/p>\n\n\n\n<div class=\"wp-block-media-text is-stacked-on-mobile\"><figure class=\"wp-block-media-text__media\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"300\" height=\"168\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/images-2025-09-02t013301863180382216218876-300x168.jpg\" class=\"wp-image-3921 size-full\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/images-2025-09-02t013301863180382216218876-300x168.jpg 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/images-2025-09-02t013301863180382216218876-600x336.jpg 600w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/images-2025-09-02t013301863180382216218876.jpg 740w\" sizes=\"(max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/figure><div class=\"wp-block-media-text__content\">\n<p><em>Lina Medina lokacin da ta yi aure<\/em>. <\/p>\n<\/div><\/div>\n\n\n\n<p>A shekara ta 2002, ta \u0199i ba da bayani ga Kamfanin Dillanci Labarai na Reuters, kamar yadda ta saba \u0199in amsa tambayoyin manema labarai tun a baya.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Darasin Tarihi ga Al\u2019umma<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Labarin Lina Medina ya koya mana darussa masu yawa:<\/p>\n\n\n\n<p><strong><em>\u0198addara<\/em><\/strong>: A wasu lokuta abubuwan da ba mu zato ko tsammani ba ne suke faruwa a rayuwarmu.<\/p>\n\n\n\n<p><strong><em>Kare Yara<\/em><\/strong>: Ya na nuna muhimmancin tsare lafiyar yara da kare su daga cin zarafi.<\/p>\n\n\n\n<p><strong><em>Kimiyya<\/em><\/strong>: Ya na bayyana yadda ilimin Likitanci ke iya fassara abin da ake \u0257auka a matsayin al\u2019ajabi, amma har yanzu akwai \u0253angaren rayuwa da ya wuce iyakokin fahimtar \u018aan&#8217;Adam.<\/p>\n\n\n\n<p><strong><em>Sirri da natsuwa<\/em><\/strong>: Duk da wannan shahara, Lina ta za\u0253i rayuwa cikin sau\u0199i da \u0253oye sirri, abin da ke koya mana darasin mutuntaka da muhimmanci adana sirri.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>A tarihin bil\u2019adama akwai labaran da suka \u0199unshi mamaki, wasu kuma su na \u0257auke da darussa masu zurfi. Labarin Lina Medina, yarinya daga \u0199asar Peru, na \u0257aya daga cikin wa\u0257annan abubuwa da ba a manta da su ba. Farkon Rayuwa da Samuwar Ciki An haifi Lina Medina a shekara ta 1933 a \u0199auyen Ticrapo, cikin [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":3919,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"inline_featured_image":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[93],"tags":[120],"class_list":["post-3924","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-jiya-da-yau","tag-taskarnasaba-lina-medina"],"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v27.0 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Lina Medina: Uwa mafi \u0199an\u0199antar shekaru a Duniya<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"noindex, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_US\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Lina Medina: Uwa mafi \u0199an\u0199antar shekaru a Duniya\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"A tarihin bil\u2019adama akwai labaran da suka \u0199unshi mamaki, wasu kuma su na \u0257auke da darussa masu zurfi. Labarin Lina Medina, yarinya daga \u0199asar Peru, na \u0257aya daga cikin wa\u0257annan abubuwa da ba a manta da su ba. Farkon Rayuwa da Samuwar Ciki An haifi Lina Medina a shekara ta 1933 a \u0199auyen Ticrapo, cikin [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3924\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"Taskar Nasaba\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2025-09-02T00:39:05+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/images-2025-09-02t0126265228087204808568479.jpg\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"638\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"480\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/jpeg\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Salahuddeen Muhammad\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"Salahuddeen Muhammad\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Est. reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"4 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\/\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3924#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3924\"},\"author\":{\"name\":\"Salahuddeen Muhammad\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753\"},\"headline\":\"Lina Medina: Uwa mafi \u0199an\u0199antar shekaru a Duniya\",\"datePublished\":\"2025-09-02T00:39:05+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3924\"},\"wordCount\":847,\"commentCount\":0,\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3924#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/Lina_Medina.jpg\",\"keywords\":[\"#taskarnasaba #lina-medina\"],\"articleSection\":[\"Jiya Da Yau\"],\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3924#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3924\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3924\",\"name\":\"Lina Medina: Uwa mafi \u0199an\u0199antar shekaru a Duniya\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3924#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3924#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/Lina_Medina.jpg\",\"datePublished\":\"2025-09-02T00:39:05+00:00\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3924#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3924\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3924#primaryimage\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/Lina_Medina.jpg\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/Lina_Medina.jpg\",\"width\":414,\"height\":276},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3924#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Lina Medina: Uwa mafi \u0199an\u0199antar shekaru a Duniya\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"description\":\"\",\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\"},\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-US\"},{\"@type\":\"Organization\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\",\"logo\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png\",\"width\":343,\"height\":345,\"caption\":\"Taskar Nasaba\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/\"}},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753\",\"name\":\"Salahuddeen Muhammad\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg\",\"caption\":\"Salahuddeen Muhammad\"},\"description\":\"\u018aanjarida, marubuci, mai manufar bun\u0199asa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.\",\"sameAs\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\"],\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?author=1\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Lina Medina: Uwa mafi \u0199an\u0199antar shekaru a Duniya","robots":{"index":"noindex","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"og_locale":"en_US","og_type":"article","og_title":"Lina Medina: Uwa mafi \u0199an\u0199antar shekaru a Duniya","og_description":"A tarihin bil\u2019adama akwai labaran da suka \u0199unshi mamaki, wasu kuma su na \u0257auke da darussa masu zurfi. Labarin Lina Medina, yarinya daga \u0199asar Peru, na \u0257aya daga cikin wa\u0257annan abubuwa da ba a manta da su ba. Farkon Rayuwa da Samuwar Ciki An haifi Lina Medina a shekara ta 1933 a \u0199auyen Ticrapo, cikin [&hellip;]","og_url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3924","og_site_name":"Taskar Nasaba","article_published_time":"2025-09-02T00:39:05+00:00","og_image":[{"width":638,"height":480,"url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/images-2025-09-02t0126265228087204808568479.jpg","type":"image\/jpeg"}],"author":"Salahuddeen Muhammad","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"Salahuddeen Muhammad","Est. reading time":"4 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3924#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3924"},"author":{"name":"Salahuddeen Muhammad","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753"},"headline":"Lina Medina: Uwa mafi \u0199an\u0199antar shekaru a Duniya","datePublished":"2025-09-02T00:39:05+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3924"},"wordCount":847,"commentCount":0,"publisher":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3924#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/Lina_Medina.jpg","keywords":["#taskarnasaba #lina-medina"],"articleSection":["Jiya Da Yau"],"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3924#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3924","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3924","name":"Lina Medina: Uwa mafi \u0199an\u0199antar shekaru a Duniya","isPartOf":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3924#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3924#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/Lina_Medina.jpg","datePublished":"2025-09-02T00:39:05+00:00","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3924#breadcrumb"},"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3924"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3924#primaryimage","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/Lina_Medina.jpg","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/Lina_Medina.jpg","width":414,"height":276},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=3924#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/taskarnasaba.com\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Lina Medina: Uwa mafi \u0199an\u0199antar shekaru a Duniya"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/","name":"Taskar Nasaba","description":"","publisher":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization"},"potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-US"},{"@type":"Organization","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization","name":"Taskar Nasaba","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/","logo":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png","width":343,"height":345,"caption":"Taskar Nasaba"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/"}},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753","name":"Salahuddeen Muhammad","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/image\/","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg","caption":"Salahuddeen Muhammad"},"description":"\u018aanjarida, marubuci, mai manufar bun\u0199asa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.","sameAs":["https:\/\/taskarnasaba.com"],"url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?author=1"}]}},"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/Lina_Medina.jpg","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3924","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=3924"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3924\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/3919"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=3924"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=3924"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=3924"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}