{"id":4417,"date":"2026-03-06T23:50:08","date_gmt":"2026-03-06T23:50:08","guid":{"rendered":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4417"},"modified":"2026-03-06T23:50:08","modified_gmt":"2026-03-06T23:50:08","slug":"behanzin-sarkin-afirka-da-tarihin-duniya-ba-zai-manta-da-shi-ba","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4417","title":{"rendered":"B\u00e9hanzin: Sarkin Afirka da Tarihin Duniya ba Zai Manta da Shi ba"},"content":{"rendered":"\n<p><em><strong>Isidore Kouwonou<\/strong><\/em><br><em><strong>BBC News Afrique, Dakar<\/strong><\/em><\/p>\n\n\n\n<p>Rayuwarsa ta zama abar koyi ga \u0257imbin Mutane, in da har masu shirya Fina-finai da dama suka shirya Fim kan tarihinsa, musamman kan assasa Rundunar Soji ta mata a masarautarsa da ake kira &#8220;Agodji\u00e9&#8221; ko &#8220;Amazon&#8217;s.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>A Fina-finai irin su &#8220;Black Panther&#8221; da &#8220;The Woman King,&#8221; an nuna irin \u0199wazo da jajircewar dakarun matan nan a wajen ya\u0199i.<\/p>\n\n\n\n<p>Fina-finan nan ba wai Tarihi ba ne ka\u0257ai, labari ne kan nahiyar Afirka na shekaru aru-aru, da ala\u0199ar nahiyar da Turai, musamman Faransa, wadda ta sha fama da Sarki B\u00e9hanzin kan \u01b4ancin masarautarsa ta Dahomey a tsakanin 1889 zuwa 1906.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;B\u00e9hanzin ya bar Tarihi mai kyau na jajircewa. Sarki ne wanda ya \u0199i bayar da kansa bori ya hau a lokacin da Turawa suka kutsa yankinsa. Sarki ne wanda ya sadaukar da rayuwarsa saboda mutanensa da \u0199asarsa da masarautarsa,&#8221; in ji Farfesa Romuald Michozounou, na Sashen Nazarin Tarihi a Jami&#8217;ar Abomey-Calavi da ke \u200b\u200bBenin.<\/p>\n\n\n\n<p>A ranar 10 ga Disamba ne Jamhuriyar Benin ta yi bikin cika shekara 119 da mutuwar Behanzin.<\/p>\n\n\n\n<p>Sarki B\u00e9hanzin ya na da matu\u0199ar mutunci da daraja sosai a fa\u0257in Afirka baki \u0257aya, ba ma Benin ka\u0257ai ba.<\/p>\n\n\n\n<p>A matsayin Sarkin Dahomey, B\u00e9hanzin ya kasance babban Sarki mai \u0199arfin iko da ya \u0257are karagar mulki a 1889, wanda ya \u0199e\u0199ashe \u0199asa ya \u0199i mi\u0199a wa Faransa wuya cikin sau\u0199i. Ya na cikin sarakunan da suka yi gwagwarmaya da Turawan Mulkin Mallaka.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>\u0198in Mi\u0199a Wuya ga Turawa<\/strong><\/p>\n\n\n\n<div class=\"wp-block-media-text is-stacked-on-mobile\"><figure class=\"wp-block-media-text__media\"><img fetchpriority=\"high\" decoding=\"async\" width=\"655\" height=\"1025\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/4bfc9c40-fd2c-11f0-b7e1-afb6d0884c181258400570126232954-655x1025.jpg\" class=\"wp-image-4412 size-full\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/4bfc9c40-fd2c-11f0-b7e1-afb6d0884c181258400570126232954-655x1025.jpg 655w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/4bfc9c40-fd2c-11f0-b7e1-afb6d0884c181258400570126232954-192x300.jpg 192w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/4bfc9c40-fd2c-11f0-b7e1-afb6d0884c181258400570126232954-768x1202.jpg 768w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/4bfc9c40-fd2c-11f0-b7e1-afb6d0884c181258400570126232954.jpg 773w\" sizes=\"(max-width: 655px) 100vw, 655px\" \/><\/figure><div class=\"wp-block-media-text__content\">\n<p><em>Turawan Faransa sun yi yun\u0199urin \u0199wace wani \u0253angare na ga\u0253ar Tekun Cotonou, babban birnin Jamhuriyar Benin. |Hoto: Getty Images<\/em> <\/p>\n<\/div><\/div>\n\n\n\n<p>Dahomey babbar Masarauta ce, kuma sarkin ya kasance ya na mulki a birnin Abomey, garin da ake matu\u0199ar tsoro.<\/p>\n\n\n\n<p>Bayan rasuwar Sarki Gl\u00e8l\u00e8, sai \u0257ansa Yarima Kondo, ya hau karagar mulki a 1889, sai ya koma amsa sunan Sarki B\u00e9hanzin.<\/p>\n\n\n\n<p>A cewar Gidan Adana Tarihi na Jamhuriyar Benin, har zuwa watan Yulin 1976, ya kasance babban Sarki mai \u0199arfin fa\u0257a a ji, wanda mutanensa ke matu\u0199ar \u0199auna.<\/p>\n\n\n\n<p>Ya sadaukar da kansa wajen kare masarautarsa daga farmakin mahara, musamman ma Turawa.<\/p>\n\n\n\n<p>Ya gwabza ya\u0199i da turawan Faransa wa\u0257anda suka yi yun\u0199urin \u0199wace wani \u0253angare na masarautarsa.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;Muna fata za ka turo mana wani Hafsa domin tattauna wannan matsalar. Amma maganar Cotonou, ban samu wasiyya daga mahaifina ba kan mi\u0199a ta ga \u0199asar Faransa, don haka nima ba zan amince ba,&#8221; kamar yadda Sarki B\u00e9hanzin ya rubuta zuwa ga Shugaban Faransa a ranar 30 ga watan Afrilun 1890, kamar yadda tarihin ya nuna.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;Sarki B\u00e9hanzin ya \u0257are karagar mulki a rubu&#8217;i na \u0199arshe na \u0199arni na 19 a lokacin da Masarautar ke tsaka mai wuya saboda Turawan Mulkin Mallaka sun ri ga sun kutsa Afirka.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;Za a iya cewa ya fara mulki ne a ranar ga Janairun 1890 bayan rasuwar mahaifinsa Gl\u00e8l\u00e8. A lokacin kuma Faransa ta ri ga ta fara yun\u0199urin \u0199wace wani \u0253angare na Cotonou, amma ya \u0199i saboda mahaifinsa ma bai amince ba,&#8221; in ji Farfesa Romuald Michozounou.<\/p>\n\n\n\n<p>Faransa ta so \u0199wace wani sashe na Cotonou, wanda a yanzu ya zama babban birnin Benin domin samun hanyar ratsewa zuwa \u0199asar.<\/p>\n\n\n\n<p>Sarkin ya yi watsi da yun\u0199urin sayar da yankin ga Faransa, wanda a cewarsa ya sa\u0253a da al&#8217;ada.<\/p>\n\n\n\n<p>Sarki B\u00e9hanzin ya gwabza ya\u0199i ne da Faransa da dakaru Mata a rundunar Agodji\u00e9 (Amazons), in da ya samu nasara a ya\u0199in da aka fafata 1890 kafin aka shiga yarjejeniyar tsagaita wuta da Faransa.<\/p>\n\n\n\n<p>Amma ya\u0199in ya koma \u0257anye bayan shekara \u0257aya, in da aka yi asarar rayuka da dama a dukkan \u0253angarorin.<\/p>\n\n\n\n<p>A kusa da \u0199arshen shekarar 1892 ne Faransa ta samu nasarar kama masarautar Dahomey, in da Sarki B\u00e9hanzin ya \u0199one Masarautar, sannan ya mi\u0199a wuya a ranar 25 ga Janairun 1894.<\/p>\n\n\n\n<p>\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0 <strong>Yadda Ya Rasu<\/strong><\/p>\n\n\n\n<div class=\"wp-block-media-text is-stacked-on-mobile\"><figure class=\"wp-block-media-text__media\"><img decoding=\"async\" width=\"300\" height=\"119\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/cdeee820-fd2c-11f0-9972-d3f265c101c6502913633283625238-300x119.jpg\" class=\"wp-image-4413 size-full\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/cdeee820-fd2c-11f0-9972-d3f265c101c6502913633283625238-300x119.jpg 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/cdeee820-fd2c-11f0-9972-d3f265c101c6502913633283625238.jpg 769w\" sizes=\"(max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/figure><div class=\"wp-block-media-text__content\">\n<p><em>A shekarar 1906 ne aka mayar da B\u00e9hanzin Aljeriya, in da ya rasu a Blida a ranar 10 ga watan Disamban shekarar. |Hoto: Getty Images<\/em><\/p>\n<\/div><\/div>\n\n\n\n<p>Masana tarihin Benin sun ce, dama asali Faransa ta ri ga ta fara shirye-shiryen kai hari a Dahomey da nufin kutsawa har zuwa Tekun Niger, don haka a cewarsu, B\u00e9hanzin ya kar\u0253i mulki ne cikin tsaka mai wuya, in da bai ma samu lokacin kafa masarautarsa da kyau ba.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;A \u0199arshen rubu&#8217;i na farko na mulkinsa ne fara takun-sa\u0199a da sojojin Faransa, in da ya yi ta fama da su na kusan shekara hu\u0257u. Ya yi sarauta ne a lokacin da Turawan Mulkin Mallaka suke ta kutsawa Afirka.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>A ranar 30 ga watan Maris na shekarar 1894 ne aka mayar da tsigaggen sarkin zuwa garin Fort-de-France da ke Martinique.<\/p>\n\n\n\n<p>A Littafin tarihinsa da \u0257ansa wanda yake tare da shi a duk lokacin da ake tum\u0253uke shi ya rubuta, ya ruwaito mahaifin na cewa Janar Dodds, wanda ya jagoranci dakarun Faransa ne ya gayyace shi.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;Duk da alamun samun nasarar da dakarun Faransa a kansa, sai Sarkin ya bu\u0199aci Janar Dodds ya shirya masa zama da shugaban Faransa domin su tattauna yarjejeniyar zaman lafiya, saboda ya na ganin a matsayinsa na Sarki, bai kamata ya tattauna da Soja ba. Lokacin ne maimakon Janar \u0257in ya kai shi wajen shugaban \u0199asar, sai ya \u0199i mayar da shi Martinique,&#8221; in ji Farfesa Michozounou.<\/p>\n\n\n\n<p>B\u00e9hanzin bai samu ganawa da shugaban Faransa ba, in da aka mayar da shi can ya ri\u0199a rayuwa daga shi sai \u0257ansa.<\/p>\n\n\n\n<p>A 1906 ne aka mayar da B\u00e9hanzin zuwa Algeria, in da ya rasu a Blida a ranar 10 ga watan Disamban shekarar, sannan aka mayar da gawarsa zuwa tsohuwar masarautarsa a shekarar 1928, in da aka yi masa jana&#8217;izar ban-girma.<\/p>\n\n\n\n<p>\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0 <strong>Mutum Mai Daraja<\/strong><\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img decoding=\"async\" width=\"800\" height=\"450\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/6ff16ed0-1570-11f1-95f1-2d2dc214ddf64779646763205433185.jpg\" alt=\"\" class=\"wp-image-4414\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/6ff16ed0-1570-11f1-95f1-2d2dc214ddf64779646763205433185.jpg 800w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/6ff16ed0-1570-11f1-95f1-2d2dc214ddf64779646763205433185-300x169.jpg 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/6ff16ed0-1570-11f1-95f1-2d2dc214ddf64779646763205433185-768x432.jpg 768w\" sizes=\"(max-width: 800px) 100vw, 800px\" \/><figcaption class=\"wp-element-caption\"><em>Hoto: Getty Images <\/em><\/figcaption><\/figure>\n\n\n\n<p>B\u00e9hanzin mutum ne mai daraja sosai a tarihin Jamhuriyar Benin. \u01b3an \u0199asar na son shi kuma su na girmama shi saboda gwagwarmayar da ya sha da Turawan Mulkin Mallaka.<\/p>\n\n\n\n<p>An gina mutum-mutuminsa a dandalin Goho da ke garin Abomey, daidai mashigar Cotonou, in da ya yi zama na \u0199arshe da Janar Dodd a shekarar 1890.<\/p>\n\n\n\n<p>A tsakankanin shekarun 1970 ne Shugaban \u0198asa Mathieu K\u00e9r\u00e9kou ya \u0257aga dajarsa a tarihi zuwa matakin &#8220;Gwarzon \u0198asa.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>Sai kuma aka sanya wa Makarantar Sakandaren farko a \u0198asar, wadda aka gina a babban birnin Dahomey.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;Lokacin bikin \u01b4ancin kai, wa\u0257anda suka yi fafutikar samun \u01b4ancin \u0199asar sai suka canja sunan makarantar Victor Ballot High School zuwa B\u00e9hanzin High School, in da har yanzu sunan makarantar ke nan. Kuma yawancin shugabannin \u0199asar a makarantar suka yi karatu.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Ala\u0199arsa da Tarihi da Al&#8217;adun Benin<\/strong><\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"706\" height=\"397\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/7b31ae90-1570-11f1-95f1-2d2dc214ddf67643749785026303710.jpg\" alt=\"\" class=\"wp-image-4415\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/7b31ae90-1570-11f1-95f1-2d2dc214ddf67643749785026303710.jpg 706w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/7b31ae90-1570-11f1-95f1-2d2dc214ddf67643749785026303710-300x169.jpg 300w\" sizes=\"(max-width: 706px) 100vw, 706px\" \/><figcaption class=\"wp-element-caption\">Dubban masu yawon bu\u0257e ido ne suke zuwa \u0199asar Benin domin gane wa idonsu tarihi da al&#8217;adun mutanen \u0199asar wadda a baya ake kira da Jamhuriyar Dahomey. |Hoto: Getty Images. <\/figcaption><\/figure>\n\n\n\n<p>Yawancin al&#8217;adun \u0199asar na da ala\u0199a da Masarautar Dahomey. Har yanzu akwai Masarautar, amma ta koma \u0199arama.<\/p>\n\n\n\n<p>A cewar Kundin Tsarin Mulkin \u0199asar na 1990, Sarakunan Gargajiya sun zama iyayen \u0199asa, wa\u0257anda masu mulki za su ri\u0199a neman shawararwarinsu, musamman a lokacin za\u0253e.<\/p>\n\n\n\n<p>Idan Jamhuriyar Benin, wadda ba ta da ma&#8217;adinai sosai ta samu nasarar kafa kanta a Duniya, al&#8217;adunta za su taka muhimmiyar rawa, kuma yawancin al&#8217;adun su na da ala\u0199a da Masarautar da ma Sarki B\u00e9hanzin.<\/p>\n\n\n\n<p>Yanzu, a sabuwar Gidan Adana Tarihin \u0199asar da ake kira &#8220;Museum of the Kings and Amazons of Dahomey&#8221; B\u00e9hanzin na da waje na musamman a cikin Sarakuna 12 da suka mulki Masarautar.<\/p>\n\n\n\n<p>Ana tuna shi ne a matsayin jajirtacce, wanda ya \u0199i mi\u0199a wuya, sannan ya yi duk abin da zai iya yi domin kare martabar \u0199asarsa da mutanensa.<\/p>\n\n\n\n<p>Bayan Gidan Adana Tarihin, tsohuwar Fadar B\u00e9hanzin, wadda bai samu damar kammalawa ba saboda ya\u0199i da Faransa, za a sabunta ta kamar sauran wurare irin su: Gl\u00e8l\u00e8 da Gu\u00e9zo da na sauran masarautun.<\/p>\n\n\n\n<p>Bayan mur\u0199ushe B\u00e9hanzin, Kanal Dodds sai ya \u0199wace Masarautar da sauran kayayyakin tarihi, wa\u0257anda aka tura Faransa.<\/p>\n\n\n\n<p>Wa\u0257annan kayayyakin tarihin da aka sace daga Dahomey, an fara ajiye su ne a Gidan Adana Tarihi Mus\u00e9e de l&#8217;Homme, kafin daga bisani aka mayar da su Gidan Tarihin Mus\u00e9e du Quai Branly Jacques Chirac.<\/p>\n\n\n\n<p>Kayayyakin tarihi guda 26 ne aka kwashe aka kai Faransa, in da Benin ta ci gaba da gwagwarmayar \u0199wato su. A shekarar 2021 ne aka mayar musu da kayayyakin, in da yanzu suka ajiye su a Gidan tarihin B\u00e9hanzin Museum da ke Cotonou.<\/p>\n\n\n\n<p>\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0\u00a0 <strong>Abin Koyi ga \u01b3an \u0198asar<\/strong><\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"720\" height=\"901\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/72c8ee70-fd2a-11f0-9972-d3f265c101c65027902841220224498.jpg\" alt=\"\" class=\"wp-image-4416\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/72c8ee70-fd2a-11f0-9972-d3f265c101c65027902841220224498.jpg 720w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/72c8ee70-fd2a-11f0-9972-d3f265c101c65027902841220224498-240x300.jpg 240w\" sizes=\"(max-width: 720px) 100vw, 720px\" \/><figcaption class=\"wp-element-caption\">Sarki B\u00e9hanzin ya na da daraja ba a Benin ka\u0257ai ba, har a sauran \u0199asashen Afirka. |Hoto: Archives nationales de la R\u00e9publique populaire du B\u00e9nin. <\/figcaption><\/figure>\n\n\n\n<p>Farfesan tarihi a Jami&#8217;ar Abomey-Calavi ya ce, tarihin Masarautar Dahomey da mulkin B\u00e9hanzin na cikin muhimman tarihin da aka koyar da \u0257alibai tun daga Firamare zuwa Jami&#8217;a, &#8220;kuma haka ya kamata a bar tsarin.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>Ya \u0199ara da cewa, masu tasowa su na bu\u0199atar sanin tarihin domin su yi koyi da shi, musamman jajircewarsa da sadaukar da rayuwarsa domin \u0199asar da mutanenta.<\/p>\n\n\n\n<p>Shi kuma Farfesa Michozounou cewa, ya yi B\u00e9hanzin Sarki ne da ya kamata \u0199asashen Afirka su nazarta domin zama abin koyi ga masu tasowa a \u0198asar.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Isidore KouwonouBBC News Afrique, Dakar Rayuwarsa ta zama abar koyi ga \u0257imbin Mutane, in da har masu shirya Fina-finai da dama suka shirya Fim kan tarihinsa, musamman kan assasa Rundunar Soji ta mata a masarautarsa da ake kira &#8220;Agodji\u00e9&#8221; ko &#8220;Amazon&#8217;s.&#8221; A Fina-finai irin su &#8220;Black Panther&#8221; da &#8220;The Woman King,&#8221; an nuna irin \u0199wazo [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":4411,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"inline_featured_image":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[93],"tags":[143],"class_list":["post-4417","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-jiya-da-yau","tag-behanzin-benin-dahomey"],"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v27.0 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>B\u00e9hanzin: Sarkin Afirka da Tarihin Duniya ba Zai Manta da Shi ba<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"noindex, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_US\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"B\u00e9hanzin: Sarkin Afirka da Tarihin Duniya ba Zai Manta da Shi ba\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"Isidore KouwonouBBC News Afrique, Dakar Rayuwarsa ta zama abar koyi ga \u0257imbin Mutane, in da har masu shirya Fina-finai da dama suka shirya Fim kan tarihinsa, musamman kan assasa Rundunar Soji ta mata a masarautarsa da ake kira &#8220;Agodji\u00e9&#8221; ko &#8220;Amazon&#8217;s.&#8221; A Fina-finai irin su &#8220;Black Panther&#8221; da &#8220;The Woman King,&#8221; an nuna irin \u0199wazo [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4417\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"Taskar Nasaba\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2026-03-06T23:50:08+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/4bfc9c40-fd2c-11f0-b7e1-afb6d0884c181258400570126232954.jpg\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"773\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"1210\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/jpeg\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Salahuddeen Muhammad\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"Salahuddeen Muhammad\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Est. reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"8 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\/\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4417#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4417\"},\"author\":{\"name\":\"Salahuddeen Muhammad\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753\"},\"headline\":\"B\u00e9hanzin: Sarkin Afirka da Tarihin Duniya ba Zai Manta da Shi ba\",\"datePublished\":\"2026-03-06T23:50:08+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4417\"},\"wordCount\":1550,\"commentCount\":0,\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4417#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/72c8ee70-fd2a-11f0-9972-d3f265c101c6.jpg.webp\",\"keywords\":[\"B\u00e9hanzin #Benin #Dahomey\"],\"articleSection\":[\"Jiya Da Yau\"],\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4417#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4417\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4417\",\"name\":\"B\u00e9hanzin: Sarkin Afirka da Tarihin Duniya ba Zai Manta da Shi ba\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4417#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4417#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/72c8ee70-fd2a-11f0-9972-d3f265c101c6.jpg.webp\",\"datePublished\":\"2026-03-06T23:50:08+00:00\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4417#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4417\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4417#primaryimage\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/72c8ee70-fd2a-11f0-9972-d3f265c101c6.jpg.webp\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/72c8ee70-fd2a-11f0-9972-d3f265c101c6.jpg.webp\",\"width\":720,\"height\":901},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4417#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"B\u00e9hanzin: Sarkin Afirka da Tarihin Duniya ba Zai Manta da Shi ba\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"description\":\"\",\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\"},\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-US\"},{\"@type\":\"Organization\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\",\"logo\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png\",\"width\":343,\"height\":345,\"caption\":\"Taskar Nasaba\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/\"}},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753\",\"name\":\"Salahuddeen Muhammad\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg\",\"caption\":\"Salahuddeen Muhammad\"},\"description\":\"\u018aanjarida, marubuci, mai manufar bun\u0199asa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.\",\"sameAs\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\"],\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?author=1\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"B\u00e9hanzin: Sarkin Afirka da Tarihin Duniya ba Zai Manta da Shi ba","robots":{"index":"noindex","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"og_locale":"en_US","og_type":"article","og_title":"B\u00e9hanzin: Sarkin Afirka da Tarihin Duniya ba Zai Manta da Shi ba","og_description":"Isidore KouwonouBBC News Afrique, Dakar Rayuwarsa ta zama abar koyi ga \u0257imbin Mutane, in da har masu shirya Fina-finai da dama suka shirya Fim kan tarihinsa, musamman kan assasa Rundunar Soji ta mata a masarautarsa da ake kira &#8220;Agodji\u00e9&#8221; ko &#8220;Amazon&#8217;s.&#8221; A Fina-finai irin su &#8220;Black Panther&#8221; da &#8220;The Woman King,&#8221; an nuna irin \u0199wazo [&hellip;]","og_url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4417","og_site_name":"Taskar Nasaba","article_published_time":"2026-03-06T23:50:08+00:00","og_image":[{"width":773,"height":1210,"url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/4bfc9c40-fd2c-11f0-b7e1-afb6d0884c181258400570126232954.jpg","type":"image\/jpeg"}],"author":"Salahuddeen Muhammad","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"Salahuddeen Muhammad","Est. reading time":"8 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4417#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4417"},"author":{"name":"Salahuddeen Muhammad","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753"},"headline":"B\u00e9hanzin: Sarkin Afirka da Tarihin Duniya ba Zai Manta da Shi ba","datePublished":"2026-03-06T23:50:08+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4417"},"wordCount":1550,"commentCount":0,"publisher":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4417#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/72c8ee70-fd2a-11f0-9972-d3f265c101c6.jpg.webp","keywords":["B\u00e9hanzin #Benin #Dahomey"],"articleSection":["Jiya Da Yau"],"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4417#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4417","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4417","name":"B\u00e9hanzin: Sarkin Afirka da Tarihin Duniya ba Zai Manta da Shi ba","isPartOf":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4417#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4417#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/72c8ee70-fd2a-11f0-9972-d3f265c101c6.jpg.webp","datePublished":"2026-03-06T23:50:08+00:00","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4417#breadcrumb"},"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4417"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4417#primaryimage","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/72c8ee70-fd2a-11f0-9972-d3f265c101c6.jpg.webp","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/72c8ee70-fd2a-11f0-9972-d3f265c101c6.jpg.webp","width":720,"height":901},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4417#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/taskarnasaba.com\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"B\u00e9hanzin: Sarkin Afirka da Tarihin Duniya ba Zai Manta da Shi ba"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/","name":"Taskar Nasaba","description":"","publisher":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization"},"potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-US"},{"@type":"Organization","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization","name":"Taskar Nasaba","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/","logo":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png","width":343,"height":345,"caption":"Taskar Nasaba"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/"}},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753","name":"Salahuddeen Muhammad","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/image\/","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg","caption":"Salahuddeen Muhammad"},"description":"\u018aanjarida, marubuci, mai manufar bun\u0199asa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.","sameAs":["https:\/\/taskarnasaba.com"],"url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?author=1"}]}},"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/72c8ee70-fd2a-11f0-9972-d3f265c101c6.jpg.webp","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4417","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=4417"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4417\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/4411"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=4417"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=4417"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=4417"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}