{"id":4430,"date":"2026-03-07T00:57:53","date_gmt":"2026-03-07T00:57:53","guid":{"rendered":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4430"},"modified":"2026-03-07T00:57:53","modified_gmt":"2026-03-07T00:57:53","slug":"turawa-biyar-da-suka-bai-wa-harshen-hausa-gudunmowa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4430","title":{"rendered":"Turawa Biyar da suka bai wa Harshen Hausa Gudunmowa"},"content":{"rendered":"\n<p><em>A duk lokacin da aka yi maganar ci gaban harshen Hausa dole ne a yi batun rubutu da karatu a cikin harshen.<\/em><br \/><br \/><em>A yanzu haka harshen Hausa na cikin manyan Harsunan Duniya da ake amfani da su a kafafen ya\u0257a labarai a Duniya da shafukan sada zumunta.<\/em><br \/><br \/><em>An fara karatu da rubutu irin na Boko a cikin Harshen Hausa tun a \u0199arni na 19, kamar yadda tarihi ya nuna.<\/em><br \/><br \/><em>Akwai Turawa da dama da suka bai wa Harshen Hausa gudunmowa wajen ha\u0253akarsa ta hanyar karatu da rubutu.<\/em><br \/><br \/><em>Wasu daga cikinsu sun ta\u0253a zuwa \u0198asar Hausa, in da suka yi rayuwa da Hausawa, suka fahimci al&#8217;adu da \u0257abi&#8217;unsu.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>A wannan ma\u0199ala mun rarrayo muku wasu Turawa biyar da suka bayar da gudunmowarsu wajen ha\u0253aka harshen Hausa a Duniya.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><strong>Paul Newman (Masanin Harshe)<\/strong><\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img fetchpriority=\"high\" decoding=\"async\" width=\"527\" height=\"360\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/newman7088541540885637412.jpg\" alt=\"\" class=\"wp-image-4429\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/newman7088541540885637412.jpg 527w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/newman7088541540885637412-300x205.jpg 300w\" sizes=\"(max-width: 527px) 100vw, 527px\" \/><\/figure>\n\n\n\n<p>An haifi Paul Newman &#8211; wanda Ba&#8217;amurke ne masanin Harsunan Afirka &#8211; a shekarar 1933.<br \/><br \/>Ya koyar a Jami&#8217;ar Yale da ke Leiden a Amurka.<\/p>\n\n\n\n<p>A yanzu haka Newman shi ne babban Farfesa a Sashen Kimiyyar Harsuna na Jami&#8217;ar Indiyana ta Amurka, bayan da ya jagorancin sashen na tsawon wa&#8217;adi biyu.<br \/><br \/>Newman ya taka muhimmiyar rawa wajen ha\u0253aka hanyar Harshen Hausa da ma wasu Harsunan Afirka ta hanyar rubuce-rubucensa.<br \/><br \/>Ya ta\u0253a zuwa \u0198asar Hausa, in da har ya ta\u0253a koyarwa a Sashen Nazarin Harsunan Najeriya a Jami&#8217;ar Bayero da ke Kano, kamar yadda Farfesa Aliyu Muhammad Bunza na Jami&#8217;ar Danfodio da ke Sakkwato ya bayyana.<br \/><br \/>&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp; <strong>Ayyukansa<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p><em>Wasu daga cikin rubuce-rubucen da ya yi a Harshen Hausa sun ha\u0257a da:<\/em> <\/p>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>1977. Sabon \u0199amus Na Hausa Zuwa Turanci<\/li>\n\n\n\n<li>2000. The Hausa Language: An Encyclopedic Reference Grammar. New Haven.<\/li>\n\n\n\n<li>2002. Chadic and Hausa Linguistics: Selected Papers of Paul Newman, with Commentaries<\/li>\n\n\n\n<li>2007. A Hausa\u2013English Dictionary. New Haven<\/li>\n\n\n\n<li>2022. A History of the Hausa Language. Reconstruction and Pathways to the Present<\/li>\n\n\n\n<li>2004. Klingenheben&#8217;s Law in Hausa. K\u00f6ln: Rudiger K\u00f6ppe Verlag.<\/li>\n\n\n\n<li>The Hausa Negative markers&#8217;, Great Vowel Tone classes and Exention in The Hausa verbal System.<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<p>Dakta Sani Dauda Ibrahim wani Masanin Kimiyyar Harshe a Kano ya shaida cewa, Paul Newman ya bayar da gagarumar gudunmowa wajen ha\u0253aka Harshen Hausa.<br \/><br \/>Ya ce, Littafin da ya rubuta a 2018 mai suna &#8216;The Comprehensive Bibliography of Chadic and Hausa Linguistics&#8217;, ya kasance jigo a fagen ilimin Nazarin Harsuna.<br \/><br \/>Dakta Sani ya ce, abin da Littafin ya \u0199unsa shi ne; ya tattaro duka ayyukan da aka yi cikin Harsunan gidan Chadi da Hausa tun daga 1790 zuwa 2018.<br \/><br \/>&#8221;Wani abin mamaki shi ne an tattara ma\u0199aloli da littafai da ayyukan bincike na digiri na \u0257aya da na biyu da na uku da aka yi sama da 3,500, amma daga ciki kusan 2,000 duk a kan Harshen Hausa aka yi su&#8221;, a cewar Dakta Sani Dauda.<br \/><br \/>Bayan ya tattara wa\u0257annan bayanan sai kuma ya sake rubuta wani Littafi a 2022 mai suna &#8221;A History of the Hausa Language. Reconstruction and Pathways to the Present.&#8221;<br \/><br \/>Dakta Sani ya ce, abin da ya sa Newman ya rubuta wannan littafi shi ne har yanzu babu wani littafi da aka rubuta da ya bibiyi tarihin harshen Hausa a shekarun da suka wuce, ya yi bayani, da halin da Harshe ke ciki a yanzu, matsayinsa da darajarsa da tasirinsa ya kuma bayyana inda harshen ya nufa a yanzu.<br \/><br \/>&#8221;Ya faro ne tun daga Haruffan Hausa da ginin jimla da darajarsa a yau da kuma inda ya nufa&#8221;, in Dakta Sani Dauda Ibrahim.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading css-1szm4ix emoh99e1\" id=\"G-P-Bargery\">G P Bargery<\/h2>\n\n\n\n<p class=\"css-tmqcq9 e1yuyadm0\">An haifi George Percy Bargery ranar 1 ga Oktoban 1876, wanda fitaccen masanin harshe ne kuma Baturen Mishan \u0257an asalin Ingila.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"css-tmqcq9 e1yuyadm0\">Bayan ya kammala Jami&#8217;ar Landan, Bargery ya fara aiki da cocin \u01b4anmishan a 1899.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"css-tmqcq9 e1yuyadm0\">Ya shiga jerin mishan da ke aiki da turawan mulkin mallaka, in da aka tura shi Arewacin Najeriya, in da ya yi aiki har zuwa 1910.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"css-tmqcq9 e1yuyadm0\">A tsawon lokacin da ya \u0257auka a Arewacin Najeriya ya koyi Harshen Hausa &#8211; wanda shi ne Harshen da aka fi magana da shi a yankin &#8211; har ma ya yi rubuce-rubuce a cikinsa a matakin karatunsa na Digiri na uku.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"css-tmqcq9 e1yuyadm0\">Ya koma Ingila da zama na dindindin a shekarar 1957, in da Daular Birtaniya ta karrama shi da lambar yabo ta OBE.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"css-tmqcq9 e1yuyadm0\">&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp; <strong>Ayyukansa<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"css-tmqcq9 e1yuyadm0\">Bargery ya kasance \u0257aya daga cikin Turawan da suka hidimta wa Harshen Hausa.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"css-tmqcq9 e1yuyadm0\">Ya rubuta \u0199amusan Hausa zuwa Turanci a shekarar 1934, in da ya fassara kalmomin Hausa masu yawa zuwa Harshen Turancin.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"css-tmqcq9 e1yuyadm0\">&#8221;Wannan \u0199amusun na da kalmomi fiye da 30,000&#8221;, in ji Farfesa Bunza.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"css-tmqcq9 e1yuyadm0\">\u0198amusun ya yi fice sosai tare da samun \u0199ar\u0253uwa, lamarin da ya kai ga har sai da Jami&#8217;ar Landan ta ba shi digirin girmamawa a 1937.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"css-tmqcq9 e1yuyadm0\">Bargery ya ci gaba da koyar da Harshen Hausa a Jami&#8217;ar Landan, in da har ya zama farfesa a harshen Hausa.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"css-tmqcq9 e1yuyadm0\">Baturen ya rubuta ma\u0199aloli masu yawa cikin Harshen Hausa da aka tattara a Jami&#8217;ar ta Landan.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Graham Furniss<\/strong><\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img decoding=\"async\" width=\"200\" height=\"276\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/graham_furniss7341476486135291947.jpg\" alt=\"\" class=\"wp-image-4428\"\/><\/figure>\n\n\n\n<p>Ya ta\u0253a ri\u0199e shugaban Hausa a Jami&#8217;ar Landan, ana kuma yi masa la\u0199abi da &#8221;Uban Hausa&#8221;, kamar yadda Farfesa Bunza ya bayyana.<br \/><br \/>An haifi Graham a Indiya, ya kuma kasance malamin Ingilishi a yankin Casamance da ke kudancinY Senegal, kafin ya yi digirinsa na farko a 1968.<br \/><br \/>Bayan kammala digirinsa na farko kan Harshen Hausa da tarihin zamantakewar Hausawa, ya tafi zuwa Kano domin yin digirinsa na uku kan wa\u0199o\u0199in al&#8217;umomin garin, wanda ke Arewacin Najeriya.<br \/><br \/>Yayin da yake digirinsa na uku, a kwalejin Abdullahi Bayero da Kano &#8211; wadda daga baya ta koma Jami&#8217;ar Bayero &#8211; ya ri\u0199a koyar da \u0257aliban digirin farko na wucin-gadi.<br \/><br \/>Bayan kammala digirinsa na ukun, ya fara koyarwa a Sashen Nazarin Harsuna da Kimiyyar Harshe na jami&#8217;ar Maiduguri da ke Arewa Maso Gabashin Najeriya.<br \/><br \/>Ya koma Landan a 1979 in da ya ri\u0199a koyar da Hausa a Jami&#8217;ar Landan, musamman fannonin Furuci da rubutun Adabi da kuma Al&#8217;ada, wa\u0257anda su ya fi \u0199warewa a kai.<br \/><br \/>Ya ri\u0199e mu\u0199aman Shugaban Sashen Nazarin Afirka da Shugaban Sashen Harsuna, sannan Shugaban Cibiyar Nazarin Harsuna duka a Jami&#8217;ar ta Landan.<br \/><br \/>&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp; <strong>Ayyukansa<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Furniss ya yi rubuce-rubuce masu yawa a Harshen Hausa da suka \u0199unshi Wa\u0199o\u0199in Zube da Wasannin Kwaikwayo.<br \/><br \/>An kuma wallafa rubuce-rubucen nasa a sigar Tatsuniyoyi da rubutattun Wa\u0199o\u0199i, da ma\u0199aloli, yayin da wasu Wasannin \u0198wakwayon da ya rubuta aka shirya tare da gabatar da su a Gidan Talabijin.<br \/><br \/><strong>Philip J. Jagga<\/strong>r<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img decoding=\"async\" width=\"1025\" height=\"939\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/newjager6229660659226659301-1025x939.jpg\" alt=\"\" class=\"wp-image-4427\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/newjager6229660659226659301-1025x939.jpg 1025w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/newjager6229660659226659301-300x275.jpg 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/newjager6229660659226659301-768x703.jpg 768w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/newjager6229660659226659301.jpg 1153w\" sizes=\"(max-width: 1025px) 100vw, 1025px\" \/><\/figure>\n\n\n\n<p>Philip Jaggar, Farfesa ne masanin kimiyyar Harshe a Jami&#8217;ar Landan, kuma wanda ake \u0257auka matsayin Shakundum Harshen Hausa.<br \/><br \/>Ya kwashe wata biyu ya na koyar da Harshen Hausa da sauran Harasa dangin Harsunan Gidan Chadi kuma masanin Harsunan Afirka.<br \/><br \/>Baturen ya samu digirinsa na biyu da na uku a Jami&#8217;ar California da ke Amurka a 1985.<br \/><br \/>&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp; <strong>Ayyukansa<\/strong><br \/><br \/>Philip J. Jagger ya kwashe shekaru masu yawa, ya na koyar da Harshen Hausa da Kimiyyar Harshe a kwalejin Abdullahi Bayero da ke Kano (Wadda daga baya koma Jami&#8217;ar Bayero).<br \/><br \/>Haka kuma ya koyar da Harshen Hausa a jami&#8217;o&#8217;in Hamburg da ke Jamus da Jami&#8217;ar UCLA ta Amurka, da kuma Jami&#8217;ar Landan.<br \/><br \/>Farfesa Aliyu Muhammad Bunza ya ce, Philip J. Jagger ya rubuta wani littafin Nahawun Hausa da ya ce har yanzu babu kamarsa a fannin Nahawun Hausa.<br \/><br \/>&#8221;Ya kuma rubuta wani Littafi kan Hausawa Ma\u0199era&#8221;, in ji Farfesa Bunza.<br \/><br \/><strong>A.H.M Kirk-Greene<\/strong><\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"640\" height=\"400\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/images28129283029174646555530968588.jpg\" alt=\"\" class=\"wp-image-4426\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/images28129283029174646555530968588.jpg 640w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/images28129283029174646555530968588-300x188.jpg 300w\" sizes=\"(max-width: 640px) 100vw, 640px\" \/><\/figure>\n\n\n\n<p>An haifi Anthony Hamilton Millard Kirk-Greene a Tunbridge Wells a Kent da ke Ingila a ranar 16 ga watan Mayun 1925.<br \/><br \/>Ya ta\u0253a aiki a matsayin matu\u0199in Jirgi a rundunar sojin Indiya daga 1943 zuwa 1947 lokacin Ya\u0199in Duniya na biyu.<br \/><br \/>Daga baya ya koma jami&#8217;ar Cambridge da ke Ingila, inda ya yi digiransa na farko da na biyu, kafin ya yi wani digirin na biyu a Jami&#8217;ar Oxford.<br \/><br \/>Kirk-Greene ya shiga ayyukan Turawan Mulkin Mallaka a matsayin jami&#8217;in mulki, in da har ya zama babban Kwamishinan Gunduma a Arewacin Najeriya.<br \/><br \/>A wannan lokaci ne ya soma sha&#8217;awar rayuwa da al&#8217;adun Hausawa da ma harshensu har ya koya ya kuma \u0199ware a kai.<br \/><br \/>Bayan samun \u01b3ancin kan Najeriya, Kirk-Greene ya zama babban malami a Jami&#8217;ar Ahmadu Bello da ke Zariya a jihar Kaduna daga 1961 zuwa 1965.<br \/><br \/>Farfesa Bunza ya ce, Baturen &#8211; wanda daga baya ya koma Jami&#8217;ar Oxford &#8211; ya yi rubuce-rubuce masu yawa da suka taimaki Harshen Hausa.<br \/><br \/>&#8221;La\u0199abin da ake yi masa a Jami&#8217;ar Oxford shi ne Nigerianist (\u018aan Najeriya), saboda duk abin da ya shafi Najeriya babu abin da bai sani ba,&#8221; a cewar Farfesa Bunza.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>A duk lokacin da aka yi maganar ci gaban harshen Hausa dole ne a yi batun rubutu da karatu a cikin harshen. A yanzu haka harshen Hausa na cikin manyan Harsunan Duniya da ake amfani da su a kafafen ya\u0257a labarai a Duniya da shafukan sada zumunta. An fara karatu da rubutu irin na Boko [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":4425,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"inline_featured_image":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[86],"tags":[145],"class_list":["post-4430","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-harshe","tag-harshen-hausa"],"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v27.0 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Turawa Biyar da suka bai wa Harshen Hausa Gudunmowa<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"noindex, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_US\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Turawa Biyar da suka bai wa Harshen Hausa Gudunmowa\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"A duk lokacin da aka yi maganar ci gaban harshen Hausa dole ne a yi batun rubutu da karatu a cikin harshen. A yanzu haka harshen Hausa na cikin manyan Harsunan Duniya da ake amfani da su a kafafen ya\u0257a labarai a Duniya da shafukan sada zumunta. An fara karatu da rubutu irin na Boko [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4430\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"Taskar Nasaba\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2026-03-07T00:57:53+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/newman7088541540885637412.jpg\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"527\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"360\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/jpeg\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Salahuddeen Muhammad\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"Salahuddeen Muhammad\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Est. reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"7 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\/\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4430#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4430\"},\"author\":{\"name\":\"Salahuddeen Muhammad\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753\"},\"headline\":\"Turawa Biyar da suka bai wa Harshen Hausa Gudunmowa\",\"datePublished\":\"2026-03-07T00:57:53+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4430\"},\"wordCount\":1498,\"commentCount\":0,\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4430#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/c91dff90-82a0-11f0-ab3e-bd52082cd0ae.png.webp\",\"keywords\":[\"#Harshen Hausa\"],\"articleSection\":[\"Harshe\"],\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4430#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4430\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4430\",\"name\":\"Turawa Biyar da suka bai wa Harshen Hausa Gudunmowa\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4430#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4430#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/c91dff90-82a0-11f0-ab3e-bd52082cd0ae.png.webp\",\"datePublished\":\"2026-03-07T00:57:53+00:00\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4430#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4430\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4430#primaryimage\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/c91dff90-82a0-11f0-ab3e-bd52082cd0ae.png.webp\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/c91dff90-82a0-11f0-ab3e-bd52082cd0ae.png.webp\",\"width\":800,\"height\":450},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4430#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Turawa Biyar da suka bai wa Harshen Hausa Gudunmowa\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"description\":\"\",\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\"},\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-US\"},{\"@type\":\"Organization\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\",\"logo\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png\",\"width\":343,\"height\":345,\"caption\":\"Taskar Nasaba\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/\"}},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753\",\"name\":\"Salahuddeen Muhammad\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg\",\"caption\":\"Salahuddeen Muhammad\"},\"description\":\"\u018aanjarida, marubuci, mai manufar bun\u0199asa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.\",\"sameAs\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\"],\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?author=1\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Turawa Biyar da suka bai wa Harshen Hausa Gudunmowa","robots":{"index":"noindex","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"og_locale":"en_US","og_type":"article","og_title":"Turawa Biyar da suka bai wa Harshen Hausa Gudunmowa","og_description":"A duk lokacin da aka yi maganar ci gaban harshen Hausa dole ne a yi batun rubutu da karatu a cikin harshen. A yanzu haka harshen Hausa na cikin manyan Harsunan Duniya da ake amfani da su a kafafen ya\u0257a labarai a Duniya da shafukan sada zumunta. An fara karatu da rubutu irin na Boko [&hellip;]","og_url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4430","og_site_name":"Taskar Nasaba","article_published_time":"2026-03-07T00:57:53+00:00","og_image":[{"width":527,"height":360,"url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/newman7088541540885637412.jpg","type":"image\/jpeg"}],"author":"Salahuddeen Muhammad","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"Salahuddeen Muhammad","Est. reading time":"7 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4430#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4430"},"author":{"name":"Salahuddeen Muhammad","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753"},"headline":"Turawa Biyar da suka bai wa Harshen Hausa Gudunmowa","datePublished":"2026-03-07T00:57:53+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4430"},"wordCount":1498,"commentCount":0,"publisher":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4430#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/c91dff90-82a0-11f0-ab3e-bd52082cd0ae.png.webp","keywords":["#Harshen Hausa"],"articleSection":["Harshe"],"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4430#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4430","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4430","name":"Turawa Biyar da suka bai wa Harshen Hausa Gudunmowa","isPartOf":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4430#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4430#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/c91dff90-82a0-11f0-ab3e-bd52082cd0ae.png.webp","datePublished":"2026-03-07T00:57:53+00:00","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4430#breadcrumb"},"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4430"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4430#primaryimage","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/c91dff90-82a0-11f0-ab3e-bd52082cd0ae.png.webp","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/c91dff90-82a0-11f0-ab3e-bd52082cd0ae.png.webp","width":800,"height":450},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4430#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/taskarnasaba.com\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Turawa Biyar da suka bai wa Harshen Hausa Gudunmowa"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/","name":"Taskar Nasaba","description":"","publisher":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization"},"potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-US"},{"@type":"Organization","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization","name":"Taskar Nasaba","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/","logo":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png","width":343,"height":345,"caption":"Taskar Nasaba"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/"}},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753","name":"Salahuddeen Muhammad","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/image\/","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg","caption":"Salahuddeen Muhammad"},"description":"\u018aanjarida, marubuci, mai manufar bun\u0199asa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.","sameAs":["https:\/\/taskarnasaba.com"],"url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?author=1"}]}},"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/c91dff90-82a0-11f0-ab3e-bd52082cd0ae.png.webp","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4430","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=4430"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4430\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/4425"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=4430"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=4430"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=4430"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}