{"id":4442,"date":"2026-03-09T13:57:35","date_gmt":"2026-03-09T13:57:35","guid":{"rendered":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4442"},"modified":"2026-03-09T22:53:52","modified_gmt":"2026-03-09T22:53:52","slug":"yadda-aka-kafa-israila-a-tsakiyar-larabawa-da-tsagin-yankin-palas%c9%97inawa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4442","title":{"rendered":"Yadda aka kafa Isra&#8217;ila a tsakiyar Larabawa da Tsagin Yankin Palas\u0257inawa"},"content":{"rendered":"\n<p class=\"css-tmqcq9 eea635z0\">Duk da cewa rikici tsakanin Isra&#8217;ila da Pala\u0257inawa a Gabas ta Tsakiya ya shafe tsawon shekaru ana fama da shi, har yanzu damuwa kawai ake nunawa ba tare da samar da mafita ba.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"css-tmqcq9 eea635z0\">Isra&#8217;ila, wadda aka kafa shekaru 75 da suka wuce ta zamo mai \u0199arfin fa\u0257a a ji, a yankin, yayin da Falas\u0257inawa ke ci gaba da neman mafaka a \u0199asashen waje kuma sun kasa kafa tasu \u0199asar mai zaman kanta.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"css-tmqcq9 eea635z0\">Ya\u0199in da Isra&#8217;ila ke yi da Hamas bayan harin da \u0199ungiyar ta kai mata ya \u0199ara ruruta wahalar da Palas\u0257inawa ke ciki da kuma \u0199ara jefa su cikin barazanar iya kawar da su a doron-\u0199asa.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"css-tmqcq9 eea635z0\">Akwai kuma tsoron cewa, matakin hukumomin Isra&#8217;ila na neman \u0199wace iko a Gaza da kuma fa\u0257a\u0257a mamayar Yahudawa a ga\u0253ar yamma da kogin Jordan zai \u0199ara tarwatsa Palas\u0257inawa da jefa rayuwar su cikin hatsari.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"css-tmqcq9 eea635z0\">Ta ya ya aka raba \u0199asar Falas\u0257inawa zuwa gida biyu, Isra&#8217;ila da Falas\u0257inu? Ta ya ya aka kafa \u0199asar Yahudawa ta Isra&#8217;ila?<\/p>\n\n\n\n<p>A ranar 14 ga watan Mayun 1984 da \u0199arfe 10 na safe \u0257aruruwan Yahudawa suka taru a \u0199ofar shiga gidan tarihi na Tel Aviv.<br \/><br \/>David Ben-Gurion na cikin gidan tarihin, in da ya ke gabatar da jawabin da ya zamo mai canza tarihin yankin Gabas ta Tsakiya.<br \/><br \/>A cikin jawabin ne David Ben-Gurion, shugaban \u0199ungiyar &#8216;Palestine Liberation Organization,&#8217; ya sanar da bayar da \u01b4ancin \u0199asar Isra&#8217;ila. Bayan \u01b4an sa&#8217;o&#8217;i kafin nan kuma dakarun Birtaniya suka fice daga yankin.<\/p>\n\n\n\n<p>Rana ce da Yahudawa ke tunawa suna murna da farin ciki, yayin da Larabawa ke tuna ta a matsayin ranar annoba.<br \/><br \/>Yadda aka kafa Isra&#8217;ila kenan, \u0199asar da a yanzu ta zamo mai \u0199arfin soji da tattalin arziki da kuma fasahar \u0199ere-\u0199ere.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img fetchpriority=\"high\" decoding=\"async\" width=\"800\" height=\"450\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/c188e6e0-80c6-11f0-a477-db87ce9e1d947403958519141769825.jpg\" alt=\"\" class=\"wp-image-4437\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/c188e6e0-80c6-11f0-a477-db87ce9e1d947403958519141769825.jpg 800w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/c188e6e0-80c6-11f0-a477-db87ce9e1d947403958519141769825-300x169.jpg 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/c188e6e0-80c6-11f0-a477-db87ce9e1d947403958519141769825-768x432.jpg 768w\" sizes=\"(max-width: 800px) 100vw, 800px\" \/><figcaption class=\"wp-element-caption\">Albert Einstein da Firaministan Isra&#8217;ila na farko David Ben-Gurion |Hoto: Getty Images<\/figcaption><\/figure>\n\n\n\n<p><strong>Fafutukar Kafa \u0198asar Isra&#8217;ila (Zionism) <\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>A shekarun1880, yankin Palas\u0257inawa na cikin Daular Ottoman wadda aka fi sani da &#8220;Greater Syria.&#8221;<br \/><br \/>Musulmai ne suka fi yawa a cikin Falas\u0257inawa, amma akwai tsirarun Kiristoci da kuma Yahudawa. An yi hasashen yawan Yahudawan zai kai kashi biyar cikin \u0257ari na Palas\u0257inawan.<br \/><br \/>Yahudawa da suka warwatsu a sassan Duniya sun nemi kafa \u0199asarsu ta kansu, kuma burinsu shi ne, kafa ta a Gabas ta Tsakiya.<br \/><br \/>Daga nan ne Yahudawa suka fara tururuwa zuwa Palas\u0257inu in da suke wa kallon wani waje da za su iya cika burin nasu na kafa \u0199asa, kuma lokacin yankin yana a \u0199ar\u0199ashin Daular Ottoman.<br \/><br \/>Mafi yawan Yahudawan \u01b4an asalin Rasha ne. Lokacin da suke a Rasha, da daman su su na cikin wa\u0257anda aka yanke wa hukunci bayan samun su da hannu a kisan Sarki Tsar Alexander II.<br \/><br \/>Yahudawan da suka isa Palas\u0257inu a wancan lokacin sun fara ne da \u0199ananan ayyukan noma ta hanyar kafa gonakinsu da kuma \u0199ananan \u0199auyuka. Ana kiran su da suna &#8216;kibbutzim&#8217;.<br \/><br \/>Yahudawan da suka fara sauka Palas\u0257inu sun samu goyon bayan masu fafutukar kafa \u0199asar Isra&#8217;ila da aka fi sani da masu akidar kishin Yahudawa, wani gangami da ya samu kar\u0253uwa sosai a tsakanin Yahudawa.<br \/><br \/>Theodor Herzl shi ne jagoran masu wannan a\u0199ida, kuma fitaccen \u0257anjarida.<br \/><br \/>Masanin tarihi Jorge Ramos, ya ce Herzl &#8220;Ya gamsu cewa \u0199alubalen da Yahudawa ke fuskanta a Turai ba batun addini ba ne, kawai batu ne na rashin asali. Abin da a\u0199idar Zionism ta yi shi ne samar da wata \u0199asa da Yahudawa za su kira tasu, kuma Duniya ta amince cewa suna da asali.&#8221;<br \/><br \/>Manyan \u0199asashen duniya sun goyi bayan wannan a\u0199ida a wancan lokacin, don haka sun ri\u0199a neman wajen da za a kafa \u0199asar Yahudawa. Sun yi nazari daga Argentina zuwa Uganda, daga Madagaascar zuwa Rasha da kuma gabas ta tsakiya.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img decoding=\"async\" width=\"594\" height=\"441\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/fb039760-80c3-11f0-ab3e-bd52082cd0ae7807309089488914687.jpg\" alt=\"\" class=\"wp-image-4438\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/fb039760-80c3-11f0-ab3e-bd52082cd0ae7807309089488914687.jpg 594w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/fb039760-80c3-11f0-ab3e-bd52082cd0ae7807309089488914687-300x223.jpg 300w\" sizes=\"(max-width: 594px) 100vw, 594px\" \/><figcaption class=\"wp-element-caption\">Yahudawa \u01b4an gudun hijira da ya\u0199i ya \u0257ai\u0257aita daga Turai, lokacin da suka isa ga\u0253ar tekun Haiifa a 1947. |Hoto: Getty Images <\/figcaption><\/figure>\n\n\n\n<p><strong>Kwace Falas\u0257inu daga Daular Ottoman da mi\u0199a ta ga Birtaniya<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Gabas ta Tsakiya ta ja hankalin Duniya sosai a lokacin ya\u0199in Duniya na farko, wanda ya faru a Turai tsakanin 1914 da 1918, inda aka tafka asarar miliyoyin mutane.<br \/><br \/>Birtaniya wadda ke adawa da daular Ottoman, ta sha alwashin \u0199wace yankunan da a baya Daular ta mamaye. A wancan lokacin, Birtaniya ta mamaye Suez Canal, wajen da ya zamo hanyar samun haraji ga Birtaniyar.<br \/><br \/>&#8220;Birtaniya ta yi yun\u0199urin karya Daular Ottoman a lokacin Ya\u0199in Duniya na farko, ta hanyar tunzura yi wa hukumomin Daular bore,&#8221; in ji Jorge Ramos.<br \/><br \/>Saboda haka Birtaniya ta mayar da hankali kan Larabawa, ta na cewa za ta goyi bayan kafa gagarumar \u0199asar Larabawa a yankin.<br \/><br \/>Wannan batu yana cikin yarjejeniyar da aka cimma tsakanin sarkin Makka Hussein bin Ali, da jakadan Birtaniya a birnin Al\u0199hahira, Henry MacMahon, a 1915 da kuma 1916.<br \/><br \/>A lokaci guda kuma Palas\u0257inawa da sauran Larabawa suka fara yi wa dakarun Daular Ottoman bore, duk da cewa dakarun sun shafe gomman shekaru su na iko da yankin.<br \/><br \/>Birtaniya ta kuma rubuta wata wasi\u0199a tana goyon bayan Yahudawa a \u0199o\u0199arin kafa \u0199asar su.<br \/><br \/>A 1917 Birtaniya ta rubuta wasika tana bayyana goyon bayan ta ga kafa \u0199asar Yahudawa a cikin Palas\u0257inu. Amma ta bayyana cewa tsarin zai mutunta \u01b4ancin sauran mutanen da ba Yahudawa ba.<br \/><br \/>Ana cikin tattaunawa tsakanin Yahudawa da Larabawa, sai Birtaniya ta bi bayan fage ta sanya hannu kan yarjejeniyar Sykes-Picot a asirce tsakanin ta da Faransa, in da suka amince da yadda za su mamaye Daular Ottoman.<br \/><br \/>A bisa wannan yarjejeniya ne kuma aka tarwatsa daular a 1918, bayan \u0199asashen Birtaniya da Faransa sun yi nasara a ya\u0199in.<br \/><br \/>Da farko Palas\u0257inu ta kasance a \u0199ar\u0199ashin kulawar \u0199asashen Duniya, amma daga baya Birtaniya ta sanar da sha&#8217;awar mallakar yankin.<br \/><br \/>A 1920, sabuwar \u0199ungiyar \u0199asashen Duniya ta League of Nations, wadda ta riki\u0257e ta koma Majalisar Dinkin Duniya daga baya, ta amince da bu\u0199atar Birtaniya ta ri\u0199e madafun iko a Palas\u0257inu.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img decoding=\"async\" src=\"file:\/\/\/data\/user\/0\/org.wordpress.android\/cache\/4a9de500-6e31-11f0-91e6-fdb094521f8b1848867884241057447.webp\" alt=\"\" class=\"wp-image-1509\"\/><figcaption class=\"wp-element-caption\">Birtaniya ta kawo \u0199arshen mulkin mallakarta a Palas\u0257inu a 1948. |Hoto: Getty Images<\/figcaption><\/figure>\n\n\n\n<p>&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp; <strong>Bore da Jajircewa<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Aikin \u0199idayar da aka yi a Palas\u0257inu a 1931 ya nuna cewa Yahudawa na \u0199ara yawa, inda suka kai kashi 16 cikin \u0257ari.<br \/><br \/>Yawan da suke \u0199arawa kuma ya zamo wani abu da ke ruruta zaman \u0257ar\u0257ar a tsakanin Yahudawa da Larabawa a yankin.<br \/><br \/>A 1936 Larabawa suka yi wa Birtaniya bore a Palas\u0257inu. Boren nasu ya shafe tsawon watanni shida, inda suke neman bai wa Larabawa \u01b4anci da kuma kawo \u0199arshen yawaitar Yahudawa \u01b4an-kama-wuri-zauna a yankin.<br \/><br \/>Amma boren bai yi nasara ba domin kuwa ya kai ga kisan dubban mutane, kuma ya yi sanadiyyar karya guiwar gangamin neman kafa \u0199asar Palas\u0257inawa.<br \/><br \/>Yayin ya\u0199in duniya na biyu, Yahudawa sun ci gaba da tururuwa zuwa Palas\u0257inu, musamman bayan tarwatsa sansanin da Nazi ke tsare da Yahudawan.<br \/><br \/>Daga baya Birtaniya ta fuskanci \u0199arin bore daga Larabawa da kuma Yahudawa masu neman ta fice daga yankin.<br \/><br \/>Wannan bore ya kai ga wasu sun kai wa ofishin da gwamnatin yankin ta Birtaniya ke tafiyar da mulki hari a ranar 22 ga watan Yulin 1946.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img decoding=\"async\" width=\"800\" height=\"481\" src=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/f80efd90-80c5-11f0-a34f-318be3fb048129581709070715216.jpg\" alt=\"\" class=\"wp-image-4440\" srcset=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/f80efd90-80c5-11f0-a34f-318be3fb048129581709070715216.jpg 800w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/f80efd90-80c5-11f0-a34f-318be3fb048129581709070715216-300x180.jpg 300w, https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/f80efd90-80c5-11f0-a34f-318be3fb048129581709070715216-768x462.jpg 768w\" sizes=\"(max-width: 800px) 100vw, 800px\" \/><figcaption class=\"wp-element-caption\">Bayan kafa Isra&#8217;ila, an tilastawa Palas\u0257inawa da dama yin hijira. Wannan hoton Palas\u0257iwa \u01b4an gudun hijira ne da Jirgin Ruwa ya kai su Masar. |Hoto: Getty Images<\/figcaption><\/figure>\n\n\n\n<p><strong>Rarraba yankin Palas\u0257inawa<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>\u0198aruwar rikici a yankin ya sa Birtaniya ta gabatar da batun ga Majalisar \u018ainkin Duniya. Hakan ya sa aka kafa wani kwamiti na musamman kan Falas\u0257inu wanda ya \u0199unshi \u0199asashe 11.<br \/><br \/>Kwamitin ya bayar da shawarar samar da \u0199asashe biyu masu \u01b4ancin kansu, \u0257aya ta Larabawa, \u0257aya kuma ta Yahudawa. Dukkan su za su mallaki yankuna uku, tare da ware birnin \u0198udus wanda zai ci gaba da zama a \u0199ar\u0199ashin ikon \u0199asashen Duniya.<br \/><br \/>\u0198udirin da aka yi wa la\u0199abi da &#8216;Proposition 181&#8217; ya bai wa Yahudawa kashi 55 na yankin sannan ya bai wa Larabawa kashi 45. A wancan lokacin yawan Yahudawan bai wuce kashi \u0257aya cikin uku na jimillar jama&#8217;ar yankin ba.<br \/><br \/>A ranar 29 ga watan Nuwamban 1947 aka gabatar da \u0199udirin a zauren Majalisar \u018ainkin Duniya, inda aka ka\u0257a \u0199uri&#8217;a.<br \/><br \/>Osvaldo Aranha, shugaban zauren na wancan lokacin ya sanar da sakamakon za\u0253en da aka yi, inda aka samu \u0199uri&#8217;u 33 masu goyon baya da 13 masu adawa da kuma 10 da suka \u0199i ka\u0257a \u0199uri&#8217;a.<br \/><br \/>Mafi yawan \u0199asashen Turai da Latin Amurka, ciki har da Amurka da Tarayyar Sobiya sun goyi bayan samar da \u0199asashe biyu masu cin gashin kansu, na Yahudawa da kuma Larabawa.<br \/><br \/>\u0198asashen Larabawa ciki har da Masar sun yi adawa da matakin. Wasu \u0199asashen 10 kuma ciki har da Habasha (Ethiopia) da Birtaniya da kuma Sin (China) suka \u0199i ka\u0257a \u0199uri&#8217;a.<br \/><br \/>Yahudawa sun yi maraba da matakin, yayin da Larabawa suka koka.<br \/><br \/>Wannan mataki ne kuma ya haifar da \u0199asar Isra&#8217;ila wadda aka kafa a ranar 14 ga watan Mayun 1948, a gidan tarihi na Tel Aviv.<br \/><br \/>A ranar, dakarun Birtaniya suka fice daga Falas\u0257inu da misalin \u0199arfe 5 na asuba, lamarin da ya kawo \u0199arshen mulkin Birtaniya a yankin.<br \/><br \/>Sa&#8217;oi biyar bayan nan kuma Firaministan Isra&#8217;ila na farko, David Ben-Gurion, ya sanar da kafa Isra&#8217;ila a matsayin \u0199asar Yahudawa a Gabas ta Tsakiya.<br \/><br \/>Shekaru 75 bayan nan, yayin da Isra&#8217;ila ta yi \u0199wari kuma ta shiga jerin \u0199asashe masu \u0199arfin soji da fasahar \u0199ere-\u0199ere, har yanzu Palas\u0257inawa na fa\u0257i tashin neman duniya ta amince da su a matsayin \u0199asa mai \u01b4ancin kai.<br \/><br \/>Yayin wannan fafutuka, yankin ya zamo wajen da ake fama da rikici daga lokaci zuwa lokaci, inda aka kashe dubun-dubatan mutane, aka kuma tilasta wa wasu miliyoyi yin hijira.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Duk da cewa rikici tsakanin Isra&#8217;ila da Pala\u0257inawa a Gabas ta Tsakiya ya shafe tsawon shekaru ana fama da shi, har yanzu damuwa kawai ake nunawa ba tare da samar da mafita ba. Isra&#8217;ila, wadda aka kafa shekaru 75 da suka wuce ta zamo mai \u0199arfin fa\u0257a a ji, a yankin, yayin da Falas\u0257inawa ke [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":4441,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"inline_featured_image":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[88],"tags":[147],"class_list":["post-4442","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-tarihi","tag-palasinawa-israila"],"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v27.0 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Yadda aka kafa Isra&#039;ila a tsakiyar Larabawa da Tsagin Yankin Palas\u0257inawa<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"noindex, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_US\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Yadda aka kafa Isra&#039;ila a tsakiyar Larabawa da Tsagin Yankin Palas\u0257inawa\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"Duk da cewa rikici tsakanin Isra&#8217;ila da Pala\u0257inawa a Gabas ta Tsakiya ya shafe tsawon shekaru ana fama da shi, har yanzu damuwa kawai ake nunawa ba tare da samar da mafita ba. Isra&#8217;ila, wadda aka kafa shekaru 75 da suka wuce ta zamo mai \u0199arfin fa\u0257a a ji, a yankin, yayin da Falas\u0257inawa ke [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4442\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"Taskar Nasaba\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2026-03-09T13:57:35+00:00\" \/>\n<meta property=\"article:modified_time\" content=\"2026-03-09T22:53:52+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/4368fc90-80c2-11f0-90fb-178351e5b841.jpg.webp\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"592\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"333\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/webp\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Salahuddeen Muhammad\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"Salahuddeen Muhammad\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Est. reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"8 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\/\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4442#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4442\"},\"author\":{\"name\":\"Salahuddeen Muhammad\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753\"},\"headline\":\"Yadda aka kafa Isra&#8217;ila a tsakiyar Larabawa da Tsagin Yankin Palas\u0257inawa\",\"datePublished\":\"2026-03-09T13:57:35+00:00\",\"dateModified\":\"2026-03-09T22:53:52+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4442\"},\"wordCount\":1640,\"commentCount\":0,\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4442#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/4368fc90-80c2-11f0-90fb-178351e5b841.jpg.webp\",\"keywords\":[\"#Palas\u0257inawa #Isra'ila\"],\"articleSection\":[\"Tarihi\"],\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4442#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4442\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4442\",\"name\":\"Yadda aka kafa Isra'ila a tsakiyar Larabawa da Tsagin Yankin Palas\u0257inawa\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4442#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4442#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/4368fc90-80c2-11f0-90fb-178351e5b841.jpg.webp\",\"datePublished\":\"2026-03-09T13:57:35+00:00\",\"dateModified\":\"2026-03-09T22:53:52+00:00\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4442#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4442\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4442#primaryimage\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/4368fc90-80c2-11f0-90fb-178351e5b841.jpg.webp\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/4368fc90-80c2-11f0-90fb-178351e5b841.jpg.webp\",\"width\":592,\"height\":333},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4442#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Yadda aka kafa Isra&#8217;ila a tsakiyar Larabawa da Tsagin Yankin Palas\u0257inawa\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"description\":\"\",\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\"},\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-US\"},{\"@type\":\"Organization\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization\",\"name\":\"Taskar Nasaba\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/\",\"logo\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png\",\"width\":343,\"height\":345,\"caption\":\"Taskar Nasaba\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/\"}},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753\",\"name\":\"Salahuddeen Muhammad\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg\",\"contentUrl\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg\",\"caption\":\"Salahuddeen Muhammad\"},\"description\":\"\u018aanjarida, marubuci, mai manufar bun\u0199asa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.\",\"sameAs\":[\"https:\/\/taskarnasaba.com\"],\"url\":\"https:\/\/taskarnasaba.com\/?author=1\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Yadda aka kafa Isra'ila a tsakiyar Larabawa da Tsagin Yankin Palas\u0257inawa","robots":{"index":"noindex","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"og_locale":"en_US","og_type":"article","og_title":"Yadda aka kafa Isra'ila a tsakiyar Larabawa da Tsagin Yankin Palas\u0257inawa","og_description":"Duk da cewa rikici tsakanin Isra&#8217;ila da Pala\u0257inawa a Gabas ta Tsakiya ya shafe tsawon shekaru ana fama da shi, har yanzu damuwa kawai ake nunawa ba tare da samar da mafita ba. Isra&#8217;ila, wadda aka kafa shekaru 75 da suka wuce ta zamo mai \u0199arfin fa\u0257a a ji, a yankin, yayin da Falas\u0257inawa ke [&hellip;]","og_url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4442","og_site_name":"Taskar Nasaba","article_published_time":"2026-03-09T13:57:35+00:00","article_modified_time":"2026-03-09T22:53:52+00:00","og_image":[{"width":592,"height":333,"url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/4368fc90-80c2-11f0-90fb-178351e5b841.jpg.webp","type":"image\/webp"}],"author":"Salahuddeen Muhammad","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"Salahuddeen Muhammad","Est. reading time":"8 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4442#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4442"},"author":{"name":"Salahuddeen Muhammad","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753"},"headline":"Yadda aka kafa Isra&#8217;ila a tsakiyar Larabawa da Tsagin Yankin Palas\u0257inawa","datePublished":"2026-03-09T13:57:35+00:00","dateModified":"2026-03-09T22:53:52+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4442"},"wordCount":1640,"commentCount":0,"publisher":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4442#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/4368fc90-80c2-11f0-90fb-178351e5b841.jpg.webp","keywords":["#Palas\u0257inawa #Isra'ila"],"articleSection":["Tarihi"],"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4442#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4442","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4442","name":"Yadda aka kafa Isra'ila a tsakiyar Larabawa da Tsagin Yankin Palas\u0257inawa","isPartOf":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4442#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4442#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/4368fc90-80c2-11f0-90fb-178351e5b841.jpg.webp","datePublished":"2026-03-09T13:57:35+00:00","dateModified":"2026-03-09T22:53:52+00:00","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4442#breadcrumb"},"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4442"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4442#primaryimage","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/4368fc90-80c2-11f0-90fb-178351e5b841.jpg.webp","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/4368fc90-80c2-11f0-90fb-178351e5b841.jpg.webp","width":592,"height":333},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?p=4442#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/taskarnasaba.com\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Yadda aka kafa Isra&#8217;ila a tsakiyar Larabawa da Tsagin Yankin Palas\u0257inawa"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#website","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/","name":"Taskar Nasaba","description":"","publisher":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization"},"potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-US"},{"@type":"Organization","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#organization","name":"Taskar Nasaba","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/","logo":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/cropped-TN_WHITE.jpg-removebg-preview.png","width":343,"height":345,"caption":"Taskar Nasaba"},"image":{"@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/logo\/image\/"}},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/44e1eb0350c3f1b57f525e9d3ebe4753","name":"Salahuddeen Muhammad","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/taskarnasaba.com\/#\/schema\/person\/image\/","url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg","contentUrl":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20191129-WA0036-100x100.jpg","caption":"Salahuddeen Muhammad"},"description":"\u018aanjarida, marubuci, mai manufar bun\u0199asa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.","sameAs":["https:\/\/taskarnasaba.com"],"url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/?author=1"}]}},"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/taskarnasaba.com\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/4368fc90-80c2-11f0-90fb-178351e5b841.jpg.webp","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4442","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=4442"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4442\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4449,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4442\/revisions\/4449"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/4441"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=4442"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=4442"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/taskarnasaba.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=4442"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}