Sabon tsarin tantancewar zai inganta kiwo, kasuwanci da kare Raƙuma a Ƙasar.
Ƙasar Saudiyya, ta sanar da shirin fara bai wa raƙuma fasfo na musamman, wani tsari da aka tsara domin tantancewa, kula da lafiya da kuma daidaita kasuwancin raƙuma a faɗin Ƙasar.
A cewar hukumomin da ke da alhakin kula da harkokin kiwon Dabbobi, wannan Fasfo zai zama takardar shaida da ke ɗauke da cikakkun bayanai game da kowanne Raƙumi, domin sauƙaƙa gane shi da kuma bin sahihin tarihinsa.

A shekarar 2024, Gwamnatin Saudiya ta ƙiyasta cewa, akwai kimanin Raƙuma Miliyan 2.2 a faɗin Ƙasar. — Reuters file
Mene ne Fasfon Raƙuma?
Fasfon Raƙuma takardar tantancewa ce ta zamani da za a bai wa kowanne Raƙumi. Takardar za ta ƙunshi muhimman bayanai kamar lambar tantancewa (Microchip), sunan Raƙumi, shekarunsa, jinsinsa, launinsa da kuma bayanan lafiyarsa da rigakafi.
Ana sa ran wannan tsari zai taimaka wajen samun sahihan bayanai a duk lokacin da ake buƙatar canja wuri, sayarwa ko binciken lafiyar Raƙuma.
Dalilin Ƙaddamar da Tsarin
Gwamnatin Saudiyya ta bayyana cewa, an ƙaddamar da wannan tsari ne domin:
- Inganta tsarin kiwo na zamani,
- Daidaita kasuwanci da zirga-zirgar Raƙuma,
- Rage satar Dabbobi da ruɗani,
- Kare haƙƙin masu Raƙuma,
- Da kuma adana bayanan tarihi da na al’adu da suka shafi Raƙuma.
Raƙuma na da matsayi na musamman a al’adu da tarihin Larabawa, kuma su na taka muhimmiyar rawa a rayuwar al’umma tun ƙarni da dama.
Raƙuma da Muhimmancinsu a Tarihi
A tarihi, Raƙuma sun kasance ginshiƙin rayuwa a yankunan hamada. Su ne manyan hanyoyin sufuri, tushen hanyoyin samun abinci da kuma muhimmin abin kasuwanci. Har zuwa yau, Raƙuma na ci gaba da zama alama ta al’ada da martabar Larabawa.
Sabon tsarin bai wa raƙuma fasfo ya na nuna yadda Saudiyya ke ƙoƙarin haɗa fasahar zamani da kare gadon al’adu, domin tabbatar da cewa wannan muhimmiyar dabba ba ta rasa kulawa a wannan zamani na ci gaba ba.
Bai wa Raƙuma Fasfo wata muhimmiyar hanya ce ta kawo tsari, sahihanci da ci gaba a harkar kiwo da kasuwanci. Haka kuma, ya na ƙara tabbatar da matsayin Raƙuma a matsayin wani muhimmin ɓangare na tarihi da al’adun Ƙasar Saudiyya.

