Ku Kasance Tare da Mu!

Yi rijista don samun sabbin labaranmu nan take!

Tsimi Da Tanadi

Kuɗaɗen Duniya Mafi Ƙarfi – Janairu 2026

Ƙarfi ko rauni na kuɗi ya na nuna tsayayyen tattalin arziki, kyakkyawan tsarin kuɗi, da amincewar masu zuba jari.

A duniya, wasu Ƙasashe sun kiyaye ƙarfin kuɗinsu sosai idan aka kwatanta da Dalar Amurka, sakamakon kyakkyawan shugabanci, manufofi masu inganci, da ci gaban tattalin arziki mai ɗorewa.

A cewar Forbes Currency Calculator, ga kuɗaɗen Duniya mafi ƙarfi guda 10:

1. Kuwait – Kuwaiti Dinar (KWD)

    • 0.31 KWD = 1 USD
      Dinar ɗin Kuwait shi ne kuɗin Duniya mafi ƙarfi. Ƙarfinsa ya na samuwa ne sakamakon babban ajiyar Mai, tsayayyen tattalin arziki, da kula da hauhawar farashi.

    2. Bahrain – Bahraini Dinar (BHD)

      • 0.38 BHD = 1 USD
        Dinar ɗin Bahrain ya na da ƙarfi sosai saboda Man Fetur da tattalin arziki mai daidaito, tare da tsayayyen tsarin kuɗi.

      3. Oman – Omani Rial (OMR)

        • 0.39 OMR = 1 USD
          Rial ɗin Oman ya na da ƙarfi saboda Man Fetur mai yawa, kyakkyawan shugabanci, da tsayayyen tsarin kuɗi.

        4. Jordan – Jordanian Dinar (JOD)

          • 0.71 JOD = 1 USD
            Dinar ɗin Jordan ya na da ƙarfi duk da ƙarancin albarkatun ƙasa. Wannan ya samo asali ne daga tsayayyen tsarin kuɗi, manufofin tattalin arziki masu kyau, da tallafin ƙasashen waje.

          5. Gibraltar – Gibraltar Pound (GIP)

            • 0.79 GIP = 1 USD
              Pound ɗin Gibraltar ya na da ƙarfi saboda daidaiton tsarin kuɗi da tattalin arzikin ƙaramar ƙasa mai dogaro kan kasuwanci da yawon shaƙatawa.

            6. Cayman Islands – Cayman Islands Dollar (KYD)

              • 0.82 KYD = 1 USD
                Dollar ɗin Cayman Islands ya na ƙarfi saboda kasuwancin bankuna na Duniya, tattalin arziki mai ƙarfi, da daidaitaccen tsarin kuɗi.

              7. British Pound – Pound Sterling (GBP)

                • 0.87 GBP = 1 USD
                  Pound Sterling ya na daga cikin kuɗaɗen Duniya mafi ƙarfi, ya na da tarihi mai ƙarfi da tattalin arziki mai ɗorewa, da kuma karfin kasuwanci da masana’antu.

                8. Euro – EUR

                  • 0.94 EUR = 1 USD
                    Euro ya na da ƙarfi saboda tsayayyen tattalin arziki na ƙasashen Turai, haɗin guiwar EU, da tsayayyen tsarin kuɗi.

                  9. Swiss Franc – CHF

                    • 1.01 CHF = 1 USD
                      Franc ɗin Switzerland ya na da ƙarfi saboda tsayayyen tsarin kuɗi, babban tattalin arziki mai daidaito, da tsaron kuɗi.

                    10. US Dollar – USD

                    • 1 USD = 1 USD
                      Dalar Amurka, duk da cewa ita ce ma’aunin Duniya, ta na cikin jerin kuɗaɗen da ake amfani da su sosai saboda karfin tattalin arziki, tsayayyen tsarin kuɗi, da amincewar ƙasashen Duniya.
                    Salahuddeen Muhammad

                    Salahuddeen Muhammad

                    About Author

                    Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

                    Leave a comment

                    Your email address will not be published. Required fields are marked *

                    Labarai Masu Alaƙa

                    Tsimi Da Tanadi

                    Sharhi: Tattalin Arziki

                    Tattalin Arziƙi (Economy) ya dogara ne a kan samar da Abinci, Sutura, Ayyuka, Kiwon Lafiya, Ilimi, Gine-Gine da sauransu, da
                    Tsimi Da Tanadi

                    Dabino na Samun Tagomashi a Saudiyya

                    Kasuwar Dabino a Saudiyya na bunƙasa, yayin da aka samu ƙaruwar riba da kashi 14% a shekarar da ta gabata