Kasar Sin ta sanar da wani shiri mai faɗi na cire Haraji (zero-tariff) kan duk kayayyakin da ake shigo da su daga ƙasashen Africa guda 53 da take da alaƙar Diflomasiyya da su, wanda za a fara aiwatarwa daga 1ga watan Mayu, 2026, a cewar rahotannin Jaridun Duniya.
Wannan mataki ya na ƙara faɗaɗa manufofin da aka fara aiwatarwa a baya, in da Sin ta ri ga ta ba da damar shigo da kayayyaki ba tare da biyan Haraji daga wasu ƙasashe – musamman ƙasashen da suke a matakin tattalin arziki na ƙarshe (LDCs) – amma yanzu ya shafi kusan dukkan ƙasashen da ke da alaƙar Siyasa da Beijing.
Sai dai kuma, Ƙasa ɗaya tilo a Afirka wato Eswatini kadai ce ba ta cikin wannan tsari; saboda ta na da dangantakar Diflomasiyya da Taiwan, wanda Sin ke ganin a matsayin wani yanki na kanta.
Shirin na zuwa ne a lokacin da kasuwannin Duniya ke fuskantar sauye-sauye, ciki har da sabunta dokokin ciniki a Turai da Amurka.
Sin ta bayyana cewa, wannan mataki zai taimaka wajen ƙara damar fitar da kayayyaki daga Afirka zuwa kasuwannin Duniya da kuma ƙarfafa haɗin guiwa a fannin tattalin arziki. Haka kuma, ta na shirin ƙarin inganta hanyoyin da za su sa kayayyakin Afirka su shiga kasuwarta da sauri ta hanyar tsarin da ake kira “Green channel.”

Yawancin masana da shugabannin Afirka sun yi maraba da wannan yunƙuri a matsayin wata dama ta bunƙasa fitar kayayyaki da samun ƙarin kuɗaɗen shiga.

