Rahoton da Ƙungiyar Global Improvement of Less Privileged Persons Initiative (GIOPPINI) ta fitar cewa, sama da Yara Miliyan Biyu na gararamba da kwana a wurare marasa tsafta da tsaro a Kano ya buɗe babbar muhawara da tattaunawa kan makomar Yara da tsarin zamantakewa a Arewacin Najeriya.

Tushen Matsalar
Nazari ya nuna cewar, rayuwar Yara a Titi ba ta samo asali daga dalili guda ba. Akwai haɗuwar abubuwa kamar:
- Talaucin Iyali da rashin abin dogaro
- Hijirar Yara daga ƙauyuka zuwa birane da sunan neman ilimi ko sana’a
- Giɓin kulawa da tsarin ilimin Almajirai
- Rashin ingantattun tsare-tsaren jin daɗin Yara a matakin Jiha da Ƙasa
Wannan na nuni da cewar, matsalar ta fi ƙarfin ɗaukar matakan agaji da jin ƙai kaɗai — ta na buƙatar tsari mai ɗorewa.
Illolin Zamani
Idan Yara suka taso a muhalli mara kulawa:
- Su na fuskantar haɗarin cin zarafi da kamuwa da cututtuka
- Su na iya faɗawa aikata laifuka na ta’adda ko kasancewa ababen amfani ga masu aikata laifuka
- Al’umma na rasa jarin ɗan Adam (human capital) da zai iya zama ginshiƙin ci gaba
Wannan ya mayar da matsalar ba ta jin ƙai kaɗai ba, har ma ta tsaro da tattalin arziki.
Ina Mafita?
Masana ci gaban al’umma na jaddada cewa, mafita mai ɗorewa ta haɗa da:
- Gyaran tsarin ilimin Almajirai da daidaita shi da na zamani
- Tallafin kai-tsaye ga Iyalai masu rauni
- Tsare-tsaren kula da zirga-zirgar Yara tsakanin Jihohi
- Haɗin kai tsakanin Gwamnati, Malamai, Iyaye da ƙungiyoyin Farar Hula
Babban Darasi
Abin tambaya shi ne: Shin muna kallon Yaran titi a matsayin matsala, ko kuma a matsayin alamar gazawar tsarin da ya kamata ya kula da su?
Domin duk Yaro da yake kwana a Titi, akwai labarin dalilin haka — talauci, sakaci ko rashin tsari.
Idan ba a magance tushen matsalar ba, ƙididdiga za ta ci gaba da ƙaruwa, matsaloli na ƙara fantsama cikin al’umma.


