Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III, wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA), ya umarci al’ummar Musulmi da su fara duban jinjirin watan Ramadan bayan faɗuwar Rana a ranar Talata, 17 ga Fabrairu, 2026, wanda ya yi daidai da 29 Sha’aban 1447 A.H.
Sanarwar da Babban Sakataren Majalisar, Farfesa Is-haq Oloyede, ya sanya wa hannu ta bayyana cewa, za a dogara ne kawai da sahihiyar shaidar ganin wata kafin a ayyana fara Azumi. Majalisar ta kuma ce, Kwamitin Duban Wata na Ƙasa, tare da haɗin guiwar Hukumomin Lura da Sararin Samaniya, sun tanadi kayan aiki domin tabbatar da ingantacciyar shaida.
Idan aka ga jinjirin a daren Talata, Laraba 18 ga Fabrairu za ta zama ranar farko ta Ramadan 1447 A.H. Idan kuma ba a gani ba, Alhamis 19 ga Fabrairu za ta kasance 1 ga Ramadan.
Baya ga batun watan Azumi, Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya, ta nuna damuwa kan abin da ta kira ƙaruwar yaɗa labaran ƙyamar Musulunci a ƙasar cikin shekarar da ta gabata, ta na mai cewa ana ƙoƙarin ɗora wa Musulmi laifuffukan da ba su aikata ba, duk da cewa su ma su na cikin waɗanda hare-haren ta’addanci da fashi da makami suka shafa.
Haka kuma, Majalisar ta ce, ta samu koke-koke dangane da shirya wasu zaɓuɓɓuka a cikin watan Ramadan, tare da bayyana cewa ta na sa ido kan lamarin kuma ta na fatan za a sake nazari kan jadawalin.
A ƙarshe, ta buƙaci al’ummar Musulmi da su kasance masu haƙuri, jajircewa da riƙon kyawawan halaye, tare da addu’ar Allah Ya ba su ikon shaida da kammala azumin 1447 A.H cikin ƙoshin lafiya da natsuwa.

