Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet), ta yi hasashen cewa wasu jihohin Ƙasar za su fara samun Ruwan Sama da wuri a shekarar 2026. Sai dai, hukumar ta yi gargaɗi ga Manoma da ka da su yi gaggawar fara shuka, domin har yanzu ba a shiga cikakkiyar Damina ba.
Ministan Harkokin Sufurin Jiragen Sama da Ci gaban Sararin Samaniya, Festus Keyamo, ne ya bayyana hakan a Abuja yayin ƙaddamar da Rahoton Hasashen Yanayin Damina na 2026 (Seasonal Climate Prediction – SCP).
Ya ce, duk da cewa an samu Ruwan Sama a wasu wurare kamar Legas da Ribas, hakan ba ya na nufin Damina ta kankama gaba ɗaya ba. Ya ƙara da cewa, ana iya fuskantar matsanancin yanayi tsakanin watan Maris zuwa Mayu.
Jihohin da Damina za ta faɗa da wuri
Rahoton NiMet ya nuna cewa, ana sa ran fara Damina da wuri a Jihohi da dama da suka haɗa da: Bayelsa, Ribas, Akwa Ibom, Kuros Riba, Binuwai, Kogi, Nasarawa, Oyo, da wasu sassan Kebbi, Neja, Jigawa, Katsina, Kano, Adamawa da Taraba.
Sai dai a Jihar Borno, ana hasashen jinkirin faɗawar Damina.
Tsawon Damina da Ƙarshenta
A cewar rahoton, wasu Jihohi za su iya samun Damina mai tsawo fiye da yadda aka saba, yayin da wasu za su fuskanci gajeriyar Damina. Haka kuma, ana iya samun ƙarshen Damina da wuri a wasu Jihohi, yayin da wasu za su fuskanci jinkirin ƙarewar daminar.
Yiwuwar Fari da “August Break”
NiMet ta kuma yi hasashen yiwuwar Fari na kwanaki da dama a wasu sassan ƙasar, musamman tsakanin Maris da Agusta. Bugu da ƙari, ana sa ran “Ƙaramar Damina” wato ‘August Break’ za ta fara daga ƙarshen Yuli, in da wasu Jihohi za su iya shafe makonni ba tare da samun Ruwan Sama ba.
Muhimmancin Rahoton
Sakataren dindindin na Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama, Dakta Yakubu Adam Farmata, ya bayyana cewa, wannan rahoto na taimaka wa Gwamnati, Manoma da sauran masu ruwa da tsaki wajen tsara tsare-tsare bisa ingantaccen bayanin yanayi.
Haka kuma, NiMet ta jaddada cewa, duk wanda ke harkar Noma ya kamata ya bi shawarwarin masana yanayi domin kauce wa asarar amfanin gona sakamakon sauyin yanayi ko jinkirin Damina.

