Ku Kasance Tare da Mu!

Yi rijista don samun sabbin labaranmu nan take!

Al'amuran Yau Da Kullum

Hauhawar Farashin Kayayyaki a Najeriya ya Ragu – NBS

Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa, (NBS), ta bayyana cewa, hauhawar farashin kaya (inflation) a Najeriya ya ci gaba da sauka, in da ta kai kashi 15.1% a watan Janairu 2026, daga kashi 15.15% da aka samu a watan Disamba 2025.

Rahoton ya nuna raguwar kashi 0.05% idan aka kwatanta da watan da ya gabata (Janairu), abin da ke nuni da cewa farashin kayayyaki na ci gaba da sassautawa a hankali.

Kwatanta da Shekarar da ta Gabata

Idan aka duba daga shekara zuwa shekara (year-on-year), hauhawar farashin ya ragu sosai idan aka kwatanta da Janairu 2025, lokacin da ya kai kashi 27.61%. Wannan na nuna cewa matsin lambar hauhawar farashi ya lafa idan aka kwatanta da irin halin da ake ciki a bara.

Hukumar ta kuma bayyana cewa, saurin tashin matsakaicin farashin kayayyaki a Janairu ya ragu idan aka kwatanta da Disamba 2025.

Farashin Abinci Ya Fi Sauka

Rahoton ya nuna cewa, hauhawar farashin Abinci a Janairu 2026 ya tsaya a kashi 8.89% idan aka kwatanta da bara. Wannan ya ragu da maki 20.74 idan aka kwatanta da Disamba 2025, wanda ya kai kashi 29.63%.

A ƙididdigar wata-wata (month-on-month), an samu saukar farashin Abinci da kashi -6.02%, alhali a Disamba 2025 ya kasance -0.36%.

Kayayyakin da Farashinsu Ya Sauka

NBS ta danganta wannan sauƙin da raguwar farashin wasu muhimman kayan Abinci kamar:

  • Kwai
  • Wake
  • Masara
  • Dawa
  • Waken Soya
  • Man Gyaɗa
  • Man ja
  • Naman Sa
  • Rogo
  • Kabewa (Egusi)

Me Wannan Ke Nufi?

Raguwar hauhawar farashi na nuni da cewa, tattalin arzikin ƙasar na nuna alamun daidaituwa a ɓangaren farashin kayayyaki, musamman na Abinci. Sai dai masana tattalin arziki na ganin cewa, ana buƙatar ɗorewar wannan yanayi domin jama’a su ji sauƙin rayuwa a zahiri.

Rahoton NBS na wannan watan ya kawo ɗan natsuwa da kwanciyar hankali, musamman ga masu saye da Manoma, bayan dogon lokaci na tashin gwauron-zabi a farashin kayayyaki.

Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Alaƙa

Al'amuran Yau Da Kullum

Qatar: Yawon Buɗe Ido na Bunƙasa a Gabas ta Tsakiya

Ƙasar Qatar ta sami kusan baƙi 730,000 a watan Janairu da Fabrairu na shekarar 2023, ƙaruwar kashi 347 a kowace
Al'amuran Yau Da Kullum

Mutum Mafi Tsufa a Duniya ya Mutu!

John Alfred Tinniswood ya mutu ne ranar Litinin a gidan kula da tsofaffi na Southport da ke Ƙasar Ingila. An