Shimfiɗa/Abstract
Wannan Muƙala ta yi nazari kan tasirin Ƙirƙirarriyar Basira (Artificial Intelligence), ga Marubuta da Masana’antar Wallafe-Wallafe. An duba fuska biyu na AI: yadda take zama barazana ta fuskar rasa ayyuka, rage ƙimar aikin rubutu, da matsalolin haƙƙin mallaka; da kuma yadda take zama ci gaba ta fuskar sauƙaƙa rubutu, tattara bayanai, da buɗe sabbin damar kasuwanci.
Haka nan, an kuma yi waiwaye zuwa tarihin fasahohin baya, kamar Injin Bugawa da Intanet, in da aka nuna cewar, kowace sabuwar fasaha ta na fara zuwa da tsoro da fargaba, daga baya kuma ta na zama dama.
Binciken ya nuna cewar, kusan kaso 45% na Marubuta a Duniya sun ri ga sun fara amfani da AI, kuma masana’antar AI a wallafe-wallafe ana hasashen za ta kai kusan $41.2 biliyan nan da shekarar 2033.
Sai dai kuma, akwai Marubuta da dama da suka ri ga suka rasa ayyuka musamman a fannin fassara da zayyanan Littattafai.
A ƙarshe, muƙalar ta kammala cewa, AI ba dole ta zama barazana ba idan aka yi amfani da ita da hikima, tare da bayar da shawarwari kan yadda Marubuta za su rungume ta a matsayin “Ƙawa abokiyar aiki.”
1.0 Gabatarwa
Ci gaban fasaha ya kasance wani ɓangare na tarihin Ɗan’adam tun fil azal. Daga lokacin da aka ƙirƙiri Alƙalami da takarda, zuwa lokacin da aka ƙirƙiri Injin Bugawa, Intanet, da wayoyin zamani, dukkan waɗannan abubuwa sun sauya yadda Mutane ke rubutu, karatu, da sadarwa.
A ƙarni na 21, sabon abu da ya fi jan hankali shi ne “Artificial Intelligence” (AI) – wata fasaha da ke ba Kwamfuta ikon yin abubuwan da ake ɗauka na Ɗan’adam: Rubutu, Magana, Fassara, Koyo, da yin hukunci. Bisa ga rahoton Hukumar Ilimi, Kimiyya da Al’adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNESCO) na 2021, AI na ɗauke da fa’ida da haɗari, kuma amfaninta ya danganta da yadda al’umma za ta tsara dokokin amfani da ita.
Sai dai tambayar da ta taso ita ce: AI barazana ce ga Marubuta ko wata hanya ce ta ci gaba? Wannan Muƙala za ta binciki ɓangarorin biyu: yadda AI ke zama barazana ga Marubuta, yadda kuma take zama ci gaba, sannan a kawo shawarwari kan yadda za a yi hulɗa da ita cikin hikima.
2.0 AI a Matsayin Barazana ga Marubuta
2.1 Rage Ƙimar Aikin Rubutu
AI na iya rubuta Labarai, Littattafai, da ma sharhi cikin gajeren lokaci. Wannan ya na iya sa masu wallafa Littattafai da Jaridu su rage buƙatar Ɗan’Adam, saboda amfani da AI zai fi rahusa kuma ya fi sauri.
2.2 Rasa Ayyukan Yi
Ma’aikatan Jarida, masu rubutun Talla (copywriters), da Marubuta na iya rasa ayyukansu idan Kamfanoni suka rungumi AI a matsayin hanyar rage kuɗi. A Birtaniya, bincike ya nuna cewa 36% na masu fassara da 26% na masu zanen kwalliya sun ri ga sun rasa ayyukansu saboda AI (FT Strategies, 2024).
2.3 Rashin Asalin Tunani
Abin da ya bambanta Ɗan’Adam shi ne; ikon ƙirƙira daga Zuciya. Amma AI ta na dogaro ne da bayanan da aka koya mata. Rubutun da ta samar ba ya da asali sosai.
2.4 Matsalar Haƙƙin Mallaka
AI na iya ɗaukar rubutun wasu Marubuta ta haɗa shi cikin sabo ba tare da izini ba. Wannan na iya zama barazana ga haƙƙin mallaka.
2.5 Rashin Sahihanci
AI wani lokaci ta na ƙirƙirar bayanai marasa gaskiya (“Hallucination”), wanda zai iya lalata sahihancin rubuce-rubucen Marubuta.
3.0 AI a Matsayin Ci Gaba da Taimako
3.1 Taimako wajen Rubutu
AI na iya zama abokiyar aiki ga Marubuta wajen samar da rubutun farko (Draft). Wannan na rage lokaci da gajiya.
3.2 Sauƙaƙa Bincike
AI na iya tattara bayanai cikin gajeren lokaci, wanda zai taimaka wajen samun hujjoji cikin sauƙi.
3.3 Sababbin Damar Kasuwanci
AI ta buɗe ƙofofi ga wallafe-wallafen Dijital, tallace-tallace, da ƙirƙirar hotuna (Illustrations). Rahoton ePublishing (2024) ya nuna cewa, kusan 54% na masu wallafa sun fara amfani da AI wajen inganta rubuce-rubuce da tallata su.
3.4 Sauƙaƙa Hanya ga Sababbin Marubuta
Masu fara wa na iya amfani da AI wajen samun tsarin rubutu da shawarwari.
3.5 Inganta Ilimi da Adabi
AI na iya fassara Littattafai zuwa Harsuna daban-daban. Wannan zai bunƙasa Adabi da haɗin kai tsakanin al’umma.
4.0 Tarihi: Daga Barazana zuwa Dama
Idan aka waiwaya tarihin rubutu, kowace sabuwar fasaha ta fara a matsayin barazana, daga baya kuma ta zama dama da ɗorewar ci gaba.
A ƙarni na 15, lokacin da aka ƙirƙiri injin bugawa (Printing Press ), Marubuta sun ji tsoron rasa aikinsu. Amma daga baya wannan Injin ya taimaka wajen yaɗa Littattafai cikin yawan da bai taɓa yiwu wa ba da kai wa sassa daban-daban na Duniya.
Lokacin da Intanet da Social Media suka bayyana, mutane sun yi zargin cewa, za su lalata rubutu. Amma daga baya suka buɗe sabbin hanyoyin yaɗa rubutu.
Hakan na nuna cewa, kamar yadda ya faru a baya, AI ma za ta iya fara zama barazana amma daga baya ta zama abar karɓuwa da samar da damarmaki cikin al’umma.
5.0 Abubuwan da AI ba za ta iya Maye Gurbin Marubuta Ba
- Ƙwarewar Rayuwa (Lived Experience) – rubutun Ɗan’Adam na ɗauke da abubuwan da ya rayu.
- Zuciya da Motsin Rai (Emotions & Feelings) – Marubuci na iya nuna ƙauna, tsoro, ko farin ciki.
- Ƙima ta Al’ada da Harshe – Marubuci na iya amfani da Karin Magana da Al’ada, wanda AI ke da wahalar kwaikwaya.
6.0 Ƙalubale Nan Gaba
- Dogaro da AI fiye da kima zai raunana basirar Marubuta.
- Kasuwar Littattafai na iya shiga matsala idan rubuce-rubucen da AI ta samar suka mamaye saboda farashinsu mai arha.
- Ingancin ilimi zai iya shiga haɗari idan ba a bambance tsakanin rubutun Ɗan’Adam da na AI ba.
- Matsalar tsaro: amfani da AI wajen ƙirƙirar labaran ƙarya (Fake News).
7.0 Shawarwari ga Marubuta
- Yi amfani da AI a matsayin kayan aiki, ba mai maye gurbin kai ba.
- Ƙara horo da ilimi kan yadda ake amfani da AI cikin hikima.
- Kare haƙƙin mallaka da dokokin ƙasa da ƙasa.
- Ƙarfafa ƙirƙira ta hanyar rubutu mai ɗauke da tarihi, al’adu da motsin rai.
- Marubuta su kalli AI a matsayin abokin haɗin kai, ba abokin gaba ba.
8.0 Kammalawa
AI fasaha ce mai ɗauke da fuska biyu: ta na iya zama barazana idan aka yi watsi da hikima, kuma ta na iya zama ci gaba idan aka yi amfani da ita cikin tsari. Tarihi ya nuna cewa, kowace sabuwar fasaha ta fara zuwa da tsoro, daga baya kuma ta zama ginshiƙin ci gaba.
Don haka, amsar tambayar “AI barazana ce ga marubuta ko ci gaba?” ita ce: abin ya rataya a kan yadda Marubuta da al’umma za su rungume ta. Idan aka yi amfani da AI da hikima, za ta zama babbar dama don bunƙasa ilimi, Adabi, da al’adu.
9.0 MANAZARTA (References)
- UNESCO (2021). Recommendation on the Ethics of Artificial Intelligence. UNESCO Publishing.
- Author Media (2024). “Do 45% of Authors Already Use AI?”
- ePublishing (2024). The State of AI in the Publishing Industry.
- Market.us (2024). AI in Publishing Market Report.
- FT Strategies (2024). “How AI and Data is Changing the Book Publishing Industry.”
- Frontiers in Research Metrics and Analytics (2025). Artificial Intelligence in African Publishing.
- Publishers Weekly (2025). “AI is About to Turn Book Publishing Upside Down.”

