Wani rahoto da Ƙungiyar Kare Haƙƙoƙin Ɗan’Adam ta ‘International Human Rights Commission’ (IHRC), reshen Jihar Kano ta fitar, ya nuna matuƙar ƙaruwa a yawan mutuwar Aure a tsakanin shekarun 2022 zuwa 2023 a Jihar, da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.
Cikin sanarwar da babban jami’in ƙungiyar a Kano, Kwamared Hafiz Sunusi Sanka, ya sanya wa hannu, an bayyana damuwa kan yadda matsalolin Auratayya ke ƙaruwa cikin sauri, lamarin da ke barazana ga zamantakewar iyali da makomar Ƴaƴa.

Ƙididdigar da Rahoton ya Nuna
A cewar ƙungiyar: a shekarar 2022, an samu ƙorafe-ƙorafe 288 da suka shafi matsalolin Aure.
- A shekarar 2023, adadin ya haura zuwa 1,080, wato kusan ninki huɗu cikin shekara guda.
° Daga cikin ƙorafe-ƙorafen 1,080:
- 999 sun ƙare da mutuwar aure (fiye da kashi 90%)
- 50 na gaban Kotuna daban-daban
- Sauran kuma su na kan sulhu ko shawara.
Wannan ƙaruwa mai ban tsoro na nuna cewar, matsalar ba ta tsaya kan saɓani tsakanin ma’aurata kaɗai ba, har ta zama barazana ga zamantakewar iyali baki ɗaya.
Ƙarin Haske kan Matsalar
Bincike daga Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), ya nuna cewa, talauci da hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya sun ƙara tsananta matsin tattalin arziki a cikin Gidaje, musamman a jihohin Arewa. Haka kuma, alƙaluman kotunan shari’a a wasu manyan Birane sun nuna ƙaruwar shari’o’in saki a cikin shekaru biyar da suka gabata.

Masana zamantakewa na danganta hakan da:
- Matsin tattalin arziki da rashin aikin yi
- Rashin ilimin zaman aure da rashin haƙuri
- Shishshigi daga (iyaye, abokai, ƙawaye, dss)
- Tasirin kafofin sada zumunta
- Sauyin ɗabi’u da rashin tsayayyen tsari a rayuwar matasa
Rahoton ya jaddada cewa, yawaitar mutuwar Aure na jefa ƴaƴa cikin mawuyacin hali, in da wasu ke fuskantar tangarɗar tarbiyya, koma baya a karatu, ko shiga halayen da ba su dace ba.
Shawarar Aure (Marriage Counselling)
Masana da cibiyoyin bada shawara sun bayyana cewa, a baya-bayan nan an samu ƙaruwa a yawan ma’auratan da ke neman Shawarwarin Auratayya (Marriage Counselling) — wato zaman tattaunawa da ƙwararru ko malamai domin warware matsalolin aure kafin su kai ga saki.

A irin wannan shawara:
- Ana taimaka wa ma’aurata su fahimci juna
- Ana koya musu dabarun magance rikici cikin lumana
- Ana tattauna matsalolin kuɗi, shishshigi da rashin fahimta
- Ana sanar da su hanyoyin yin haƙuri da juriya
Masu ba da shawara sun ce, mafi yawan matsalolin da ake kai wa su ne, na matsin tattalin arziki da kuma rashin jituwa kan kula da iyali.

Dangantaka da Yara Masu Gararamba
Wani rahoto da ƙungiyar GIOPPINI (Global Initiative for Orphans, Poor and Physically Impaired in Nigeria) ta fitar ya nuna cewa, akwai kimanin Yara Miliyan Biyu da ke gararamba a titunan Jihar Kano.

Rahoton ya bayyana cewa:
- Mafi yawansu Yara ne masu shekaru ƙasa da 18
- Da dama daga cikinsu ba sa zuwa Makaranta
- Wasu sun fito ne daga gidajen da iyayensu suka rabu
- Wasu kuma na fama da rashin kulawar iyaye sakamakon talauci
Masana sun nuna cewa, rushewar iyali da yawaitar saki na daga cikin manyan abubuwan da ke ƙara jefa Yara cikin rayuwar gararamba a Titi.
Idan aka haɗa alkaluman mutuwar aure 999 cikin shekara guda da rahoton Yara miliyan 2 da ke Tituna, lamarin na nuna cewa matsalar na da zurfin tasiri ga makomar al’umma.
Auren Zaurawa: Shin Mafita Ce?
Dangane da shirin Gwamnati na aurar da zaurawa kyauta a Jihar Kano, ƙungiyar ta nuna goyon baya matuƙar an tsara shi da hikima da tsari mai dorewa.

Rahoton ya yi nuni da cewa, irin waɗannan shirye-shirye na iya rage:
- Baɗala
- Yawaitar Yara marasa gata
- Wasu laifuka da ke da alaƙa da rashin tsari a rayuwar Matasa
Sai dai ƙungiyar ta bayar da shawarwari domin tabbatar da dorewar auren:
Shawarwari

- Tallafin Tattalin Arziki
A samar da aikin yi ko tallafin sana’a ga ma’aurata, musamman masu ilimi ko fasaha.
2. Horaswa da Wayar da Kai
A riƙa shirya tarukan bita akai-akai tare da malaman addini, masana halayyar Ɗan’Adam, da ƙwararrun masu ba da shawara kan aure.
3. Bibiyar Zaman Aure
A kafa Kwamiti na musamman da zai riƙa sa ido kan zaman ma’aurata, domin warware matsala tun ta na ƙarama kafin ta rikiɗe zuwa saki.
4. Shigar Iyaye da Al’umma
A ƙarfafa rawar iyaye da shugabannin al’umma wajen sulhu da bada shawarwari.
KAMMALAWA
- Ƙaruwar ƙorafe-ƙorafe 288 zuwa 1,080 cikin shekara guda, tare da mutuwar aure 999, na nuna cewa, akwai buƙatar gaggawar ɗaukar matakan gyara tsarin zamantakewar aure a Jihar Kano.
- Haɗa wannan da rahoton Yara Miliyan Biyu da ke gararamba a tituna, matsalar na nuna babbar barazana ga makomar al’umma idan ba a ɗauki matakan gaggawa ba.
- Masana na ganin cewa, magance matsalar ba zai yiwu ba sai an haɗa kai tsakanin Gwamnati, malamai, iyaye, ƙungiyoyi masu zaman kansu da kuma kafafen yaɗa labarai domin ceto zamantakewar iyali – wanda shi ne ginshiƙin al’umma.
Bayani Kula: Idan ba a ɗauki mataki cikin gaggawa ba, matsalar na iya ƙara ta’azzara a nan gaba.


