Cibiyar Yaƙi da Cututtuka da Kariya ta Ƙasa a Najeriya (NCDC) ta sanar da ƙarin ɓullar zazzaɓin Lassa a faɗin Ƙasar.
Hukumar ta tabbatar da sabbin mutane 44 da suka kamu da cutar tare da mutuwar mutum shida a mako na biyar na shekarar 2026.
Sabbin masu kamuwa da cutar sun fito ne daga jihohi bakwai: Bauchi, Ondo, Taraba, Edo, Filato, Binuwai da Ebonyi.
Yawan Mace-mace da Halin da ake Ciki
Rahoton ya nuna cewa, daga mako na ɗaya zuwa na biyar na shekarar 2026, an samu jimillar mutuwar mutane 31. Wannan na nuna kason mace-mace (Case Fatality Rate – CFR) na kashi 18.8 cikin 100, wanda ya ɗan ragu idan aka kwatanta da kashi 19.6 cikin 100 da aka samu a irin wannan lokaci a shekarar 2025.
A jimlace, Jihohi tara sun tabbatar da aƙalla mutum guda da ya kamu da cutar a Ƙananan Hukumomin 33, lamarin da ke nuna cewa, cutar na ci gaba da yaɗuwa a sassa daban-daban na ƙasar.
Jihohin da Suka Fi Ɗaukar Cutar
Rahoton ya bayyana cewa jihohi biyar ne suka fi ɗaukar kaso mafi yawa na masu cutar, in da suka haɗa da kashi 92 cikin 100 na dukkan waɗanda aka tabbatar sun kamu:
- Bauchi – 47%
- Ondo – 18%
- Taraba – 14%
- Edo – 8%
- Filato – 5%
Sauran kashi 8 cikin 100 an same su ne daga wasu jihohi huɗu.
Shekarun Masu Kamuwa
An lura cewa, Matasa masu shekaru tsakanin 21 zuwa 30 su ne suka fi kamuwa da cutar. Sai dai cutar ta shafi kowane rukuni na shekaru, daga jarirai har zuwa tsofaffi masu shekaru 1 zuwa 74.
Haɗarin da Ma’aikatan Lafiya Ke Fuskanta
Ko da yake an samu raguwar waɗanda ake zargi da kuma waɗanda aka tabbatar sun kamu idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, an samu kamuwar ma’aikacin lafiya guda a mako na biyar.
Wannan na nuna cewa, ma’aikatan lafiya na ci gaba da fuskantar haɗari wajen kula da marasa lafiya.
Matakan Da Aka Ɗauka
Kamar yadda NCDC ta yi ƙarin bayani cewar, an ƙarfafa tsarin haɗin guiwa na Ƙasa kan zazzaɓin Lassa mai suna “Tsarin Gudanar da Lamurran Gaggawa na Ƙasa kan Zazzaɓin Lassa” (IMS) domin inganta daidaiton aiki da ƙarfafa matakan daƙile cutar a dukkan matakan gwamnati.
Hukumar ta kuma buƙaci jama’a da su kula da tsafta, su hana Ɓeraye shiga gidajensu, tare da kai rahoton duk wata alamar zazzaɓi mai tsanani zuwa cibiyar lafiya mafi kusa.

