Ku Kasance Tare da Mu!

Yi rijista don samun sabbin labaranmu nan take!

Tarihi

Wadi al-Salam: Maƙabartar Musulmai Mafi Girma a Duniya

Maƙabartar Wadi al-Salam da ke birnin Najaf a ƙasar Iraqi, ita ce maƙabartar Musulmai da ta fi kowace maƙabarta girma a duniya.

An binne sama da mutum Miliyan Shida a cikinta, in da wasu ƙaburburan da ke ciki suka samo asali tun ƙarnuka da suka gabata.

Mafi yawan waɗanda ake binnewa da kuma masu ziyara a maƙabartar mabiya aƙidar Shi’a ne.

Maƙabartar na da girman da ya kai eka 1,485.5, kuma wuri ne da ke karɓar baƙuncin miliyoyin Musulmai masu ziyara a kowace shekara.

Ana ganin cewa, kusancin maƙabartar da hubbaren Ali ibn Abi Talib, sahabin Annabi Muhammad SAW na daga cikin abubuwan da suka ƙara ɗaukaka darajar maƙabartar.

Maƙabartar Wadi al-Salam da ke birnin Najaf na ƙasar Iraqi. |Getty Images

Imam Ali shi ne halifan Annabi Muhammad na huɗu a mahangar Ahlussunnan, amma mabiya mazhabar Shi’a na ɗaukar sa a matsayin na farko daga cikin imamansu 12.

Wannan ya sanya akasarin mabiya Shi’a na Iraqi kan buƙaci a binne su a maƙabartar, kuma sanadiyyar sauƙin sufuri a zamunnan baya-bayan nan, wasu mabiya Shi’a daga ƙasashen Duniya kan so a binne su a maƙabartar.

Tsarin maƙabartar ya kasance cakuɗuwa ce ta gine-ginen hubbarai irin na zamanin baya, da hanyoyi masu tsuku da suka ratsa ta cikinta da kuma wasu wurare da ake yi wa kallon masu tsarki.

Me ya sa ake kiran Maƙabartar Wadi al-Salam?

Ƴan’uwa kan ziyarci mamatansu da aka binne a maƙabartar Wadi al-Salam a lokuta masu muhimmanci na Musulunci, kamar lokacin Idi. |Hoto: Getty Images

Ana kiran maƙabartar da sunan Wadi al-Salam, wato ‘Kwarin Aminci’ ne saboda dalilai na tarihi da dama.

Dalilai na Addini: Ana yi wa maƙabartar ɗaukar mai daraja, tare da imanin cewa waɗanda ke kwance a cikinta na cikin rahama.

Alaƙa da Imam Ali: Maƙabartar ta na maƙwaftaka da kabarin Imam Ali bin Abi Talib a birnin Najaf, wanda hakan ya sa Musulmai, musamman mabiya aƙidar Shi’a ke girmama ta kuma suke kwaɗayin ganin an binne su a cikinta.

Girma: Maƙabartar ta kasance mafi girma a Duniya, in da ta mamaye wuri mai girman gaske, ƙunshe da miliyoyin ƙaburbura, in da ta zamo tamkar wani birni na mamata.

Ziyara: Masu ziyara zuwa birnin Najaf, mai tsarki ga mabiya aƙidar Shi’a – sukan bi ta cikin maƙabartar tare da karanta Fatiha da kuma yin addu’o’in samun rahama ga waɗanda ke kwance, lamarin da ya mayar da wurin tamkar wuri na ziyarar ibada.

Waɗannan dalilai ne suka sanya tuntuni aka yi wa wurin laƙabi da ‘Kwarin aminci’ tun asali, kuma ake ci gaba da kiranta da hakan har yanzu.

Tarihin Kafuwar Maƙabartar Wadi al-Salam

Hoton maƙabartar Wadi al-Salam daga sama, wadda ita ce maƙabarta mafi girma a Duniya. |Hoto: Getty Images

Maƙabartar ta samo asali ne tun kafin zuwan addinin Musulunci a lokacin Annabi Muhammad, in da tun kafin wancan lokaci ake binne mutane a wurin.

Wuri ne mai muhimmanci wanda ke karɓar baƙuncin masu bincike na kimiyya da masana addini, musamman mabiya Shi’a daga sassa daban-daban na Duniya.

Wadi al-Salam na da ƙofofi da dama da ake bi wajen shigar ta, in da hakan ke sauƙaƙe zirga-zirga ga masu ziyara, kuma yawancin waɗannan ƙofofi na ƙaruwa ne bisa faɗaɗar maƙabartar.

A shekara ta 2016 ne Hukumar kula da ilimi da al’adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNESCO) ta ayyana maƙabartar a matsayin ɗaya daga cikin wuraren tarihi na Duniya.

Ƙalubalen da Maƙabartar ke Fuskanta

Yadda ake yanka filayen binne mamata a maƙabartar Wadi al-Salam |Hoto: Getty Images

Ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da maƙabartar ke fuskanta shi ne ƙaruwar Mutane da ake binnewa a lokacin yaƙi.

Misali, a lokacin da aka yi fama da rikicin ƙungiyar ISIS a Iraqi, yawan mutanen da ake binnewa a kowace rana a maƙabartar ya ɗaga zuwa 150 ko 200 a kowace rana, daga gawa 80 zuwa 120 da aka saba.

Wannan ya sanya wuraren binne sabbin mamata ya yi ƙaranci.

Farashin binne mamaci

Farashin binne mamaci a maƙabartar Wadi al-Salam ya danganta ne da lokaci da kuma halin da ake ciki na zaman lafiya.

Ya zuwa farkon shekara ta 2025, kuɗin sayen filin binne mamaci mai girman murabba’in mita 25 ya kai miliyan biyar na kuɗn ƙasar Iraqi, wato kimanin dala 4,100, in da hakan ya nunka farashin da ake biya a lokutan da ake zaman lumana sosai.

Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Alaƙa

Tarihi

Tarihin Ƙabilar Fulani

Fulani, suna ne na ƙabilar Fulɓe a Hausance. Ƙabila ce wadda take magana da harshen, Fillanci ko Fulatanci, abin da
Tarihi

Yadda Sauyin Yanayi Zai Rusa Wuraren Tarihin Afirka

Tun daga zane-zanen Dutse da ke Kudancin Afirka zuwa Dalar da ke gefen Kogin Nilu, al’ummar da suka gabata sun