Hukumar Hasashen Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi hasashen cewa za a samu yanayin Ƙura da Hazo a sassa daban-daban na Najeriya na tsawon kwanaki uku, daga Talata zuwa Alhamis.
A cikin rahoton Yanayi da hukumar ta fitar a Abuja, NiMet ta bayyana cewa, za a samu matsakaicin Ƙura da Hazo a yankin Arewacin Najeriya, in da nisan gani zai kasance tsakanin kilomita biyu zuwa biyar.
Sai dai a wasu sassan jihohin Katsina, Kano, da Jigawa ana iya samun raguwa sosai a nisan gani har zuwa mita 1,000 ko ƙasa da haka.
Haka kuma an yi hasashen Ƙura da Hazo matsakaici a yankin Arewa ta Tsakiya.
A yankin Kudancin Najeriya kuwa, ana sa ran sararin samaniya zai kasance mai Rana tare da wasu Gajimare kaɗan, tare da ƙaramin yiwuwar Tsawa da Ruwan Sama matsakaici da Yamma ko Dare a wasu sassan jihohin Legas, Bayelsa, Delta, Ribas, Kuros Riba, da Akwa Ibom.
Ranar Laraba
NiMet ta ce, Ƙura da Hazo matsakaici za su ci gaba da bayyana a yankunan Arewa ta Tsakiya.
A Kudancin ƙasar kuwa, ana sa ran sararin samaniya mai Rana tare da wasu Gajimare, amma akwai ƙaramar yiwuwar tsawa da ruwan sama mai sauƙi a wasu sassan jihohin Ondo, Bayelsa, Ribas, Delta da Edo daga baya a ranar.
Ranar Alhamis
An yi hasashen Ƙura mai sauƙi a yankin Arewa, yayin da yankin Arewa ta Tsakiya zai ci gaba da fuskantar Ƙura da Hazo.
A Kudancin Najeriya kuwa, sararin samaniya zai kasance mai Rana tare da gajimare kaɗan, tare da yiwuwar Tsawa da Ruwan Sama a jihohin Legas, Edo, Delta, da Bayelsa daga baya a ranar.
Shawarwarin NiMet ga Jama’a
Hukumar ta yi gargaɗin cewa, ƙwayoyin kura za su ci gaba da yaɗuwa a sararin samaniya, don haka jama’a su ɗauki matakan kariya, musamman masu fama da cututtukan numfashi kamar Asma.
- Direbobi su yi tuƙi cikin taka-tsantsan idan ana ruwan sama.
- Kamfanonin Jiragen Sama su riƙa neman rahoton yanayi daga NiMet domin tsara ayyukansu yadda ya kamata.
- Jama’a su riƙa bibiyar sabbin rahotannin yanayi ta shafin yanar gizon NiMet.

