Sabbin Attajirai 390 Sun Shiga Jerin Attajiran Duniya a 2026 — Beyoncé, Dr. Dre da Roger Federer na Cikin Kundin
Mujallar Forbes ta bayyana cewa, a cikin shekara guda kacal, Duniya ta samu sabbin attajirai 390 da suka shiga jerin masu dukiyar da ta kai Dala Biliyan Ɗaya ko fiye. Wannan na nufin; kusan kowace Rana ana samun sabon Attajiri aƙalla guda a Duniya.
Wannan adadi shi ne na biyu mafi girma a tarihi, bayan shekarar 2021 lokacin da bayan annobar COVID-19 ya haifar da sababbin attajirai 493.
A jimlance, sabbin attajiran wannan shekara sun fito daga ƙasashe da yankuna 40, kuma dukiyarsu gaba ɗaya ta kai kusan Dala Biliyan 755, wato kusan Dala Biliyan 1.9 ga kowane mutum a matsakaici.
Fitattun Mutane da Suka Shiga Jerin
Daga cikin shahararrun Mutane da suka shiga jerin Attajiran Duniya a karon farko akwai:
- Mawaƙiya kuma fitacciyar Jaruma a harkar Waƙe-waƙe, Beyoncé Knowles-Carter, wacce dukiyarta ta kai kusan Dala Biliyan Ɗaya, sakamakon sayar da Waƙoƙinta, da rangadin waƙoƙi (Shows) da kuma fannin fasahar kaɗe-kaɗe. Mijinta, Mawaƙi Jay-Z, shi ma Attajiri ne da dukiyar kusan Dala Biliyan 2.8.
- Shahararren Mawaƙin hip-hop Dr. Dre ya shiga jerin da dukiyar kusan Dala Biliyan 1, shekaru sama da goma bayan sayar da waƙarsa mai taken ‘Beats by Dre’ ga kamfanin Apple a shekarar 2014 kan kusan Dala Biliyan Uku.
- Fitaccen ɗanwasan Tennis Roger Federer ma ya shiga jerin da dukiyar kusan Dala Biliyan 1.1, bayan nasarar lashe Grand Slam sau 20 da kuma jarinsa a kamfanin takalman ‘Switzerland On Running.’
- Daraktan Fina-finai James Cameron, wanda ya shirya shahararrun Fina-finai kamar Titanic, Avatar da The Terminator, shi ma ya shiga jerin da dukiyar kusan Dala Biliyan 1.1. Cameron ya lashe Lambobin Yabo uku na ‘Academy Awards’ kuma ana masa kallon ɗaya daga cikin Daraktocin da Fina-finansu suka fi samun kuɗi a tarihi, bayan Steven Spielberg.
Ƙasashen da Suka Fi Samar da Sabbin Attajirai
Rahoton ya nuna cewa:
- Amurka ce ta fi samar da sabbin attajirai da mutum 106
- Sin ta zo ta biyu da 55
- Jamus ta zo ta uku da 42
- Indiya ta zo ta huɗu da 30
Daga cikin mafi arziki cikin sababbin attajiran akwai:
- Edwin Chen – Dala Biliyan 18, wanda ya kafa kamfanin fasahar AI Surge AI
- Peter Mallouk – Dala Biliyan 16.1, shugaban kamfanin Creative Planning
Yawancinsu Sun Gina Dukiyarsu Da Kansu
Rahoton ya nuna cewar, kusan kashi biyu cikin uku na sabbin Attajiran Duniya sun gina dukiyarsu ce da kansu, ba tare da gado ba.
Cikin su akwai matasa ƴan shekara 22 su uku da suka kafa Kamfanin Fasahar Ɗaukar Ma’aikata na AI Mercor:
- Brendan Foody
- Adarsh Hiremath
- Surya Midha
Kowannensu ya na da dukiyar kusan Dala Biliyan 2.2, kuma Midha shi ne mafi ƙarancin shekaru cikin attajiran da suka gina dukiyarsu da kansu a Duniya.
Haka kuma Kimbal Musk, ɗan’uwan Elon Musk, ya shiga jerin da dukiyar kusan Dala Biliyan 1.4, sakamakon hannun jarinsa a kamfanonin Tesla da SpaceX.
Mata da Matasa a Sabon Jerin
- Jennifer Gilbert ita ce Mace mafi arziki da ta shiga jerin a wannan shekara da dukiyar Dala Biliyan 5.7, bayan rabuwarta da mijinta Dan Gilbert, wanda ya kafa Rocket Mortgage kuma shi ne mamallakin ƙungiyar Cleveland Cavaliers.
- A jimlace akwai mata 76 da suka shiga jerin a karon farko, amma yawancinsu sun gaji dukiyarsu ne.
- Mafi ƙarancin shekaru a jerin ita ce, Amelie Voigt Trejes mai shekaru 20, wacce dukiyarta ta kai Dala Biliyan 1.1, sakamakon gadon Kamfanin Lantarki na Brazil WEG da kakanta Werner Ricardo Voigt ya kafa.
Masana’antu da Fasaha Sun Fi Samar da Attajirai
Rahoton ya nuna cewa:
- Masana’antu (Manufacturing) sun samar da sabbin attajirai 91
- Fasaha (Technology) ta samar da 70 — yawancinsu daga bunƙasar Ƙirƙirarriyar Fasaha (Artificial Intelligence)
- Kuɗi da Zuba Jari (Finance & Investments) sun samar da 51
Daga cikin attajiran fasahar AI akwai waɗanda suka kafa kamfanin Perplexity AI, da kuma wasu daga kamfanin Cursor AI.
Muhimmin Saƙo
Sabon rahoton ya nuna yadda fasaha, musamman Ƙirƙirarriyar Fasaha (AI), da Masana’antu suke ƙara zama manyan hanyoyin samar da arziki a Duniya a wannan zamani.

