Ku Kasance Tare da Mu!

Yi rijista don samun sabbin labaranmu nan take!

Rana Kamar Ta Yau

Yau Shekaru 123 Da Turawan Ingila Suka Ƙwace Sakkwato Da Yaƙi

A yau 13 ga Maris, an cika shekaru 123 da fara yaƙin da ya kai ga faɗuwar birnin Sakkwato a hannun Turawan Mulkin Mallaka na Birtaniya. Wannan yaƙi ya gudana daga 13 zuwa 15 ga Maris, 1903, wanda ya zama ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da suka kawo ƙarshen ikon Daular Usmaniyya da A
Usman Ɗanfodio ya kafa tun a farkon ƙarni na 19.

Dalilin Turawan Ingila na kai Hari Sakkwato

Tun da wuri Turawan Ingila sun fahimci cewa, Birnin Sakkwato ita ce Cibiyar Siyasa da addini ta Daular Usmaniyya. Saboda haka, rushe wannan cibiyar shi ne zai ba su damar shimfiɗa Mulkin Mallaka a duk faɗin Ƙasar Hausa da sauran Masarautun da ke ƙarƙashin Daular.

Tun bayan zuwan ɗan binciken Turawa Hugh Clapperton a gaban Sarkin Musulmi Muhammadu Bello a shekarar 1824, Turawa suka fara tattara bayanai da leƙen asiri kan yadda za su karya lagon wannan Daula.

Rundunar Turawan Ingila

Rundunar sojojin Birtaniya da ta nufi Sakkwato ta ƙunshi:

  • Manyan hafsoshin Soja 25
  • N.C.O. 5
  • Likitocin Soja 2
  • Likitan N.C.O. 1
  • Maɗaukan bindiga 68
  • Sojojin musamman 656
  • Sojojin kariya 400
  • Bindigogin manya 4
  • Zungurorin bindiga masu tsawon milimita 75 guda 4

Kafin isa Sakkwato, rundunar ta fara yada zango a Ƙaura Namoda, sannan ta ratsa ta Argungu da Shagari kafin ta isa birnin Sakkwato.

             Mayaƙan Sakkwato

A lokacin da Turawa suka iso, mayaƙan Sakkwato kimanin 6000 suka fito domin kare daular:

  • 2000 mahaya dawakai
  • 4000 sojojin ƙasa (ƴan baka, ƴan bindiga da sauransu)

Da farko mayaƙan Sakkwato sun yi tsayin-daka wajen kare birnin, amma saboda tsofaffin makaman da suke amfani da su—kamar Takuba, Baka, Kwari da bindigar harbi-ka-ruga—Turawan Ingila da ke da manyan Bindigogi da sabbin makamai suka samu galaba.

            Hijirar Sarkin Musulmi

Bayan faɗuwar rundunar Sakkwato, Sarkin Musulmi Attahiru I ya jagoranci jama’a zuwa Gabas domin yin Hijira. Wannan mataki ya samo asali ne daga shawarwarin manyan malamai irin su:

  • Qari Abdullahi
  • Qari Ahmad bn Sa’ad

Sun gabatar da zaɓuɓɓuka uku:

  • Ci gaba da yaƙar Turawa
  • Yin Hijira kamar yadda Annabi SAW ya yi daga Makka zuwa Madina
  • Ko yin sulhu bisa koyarwar Littattafan Shehu Usmanu Ɗanfodiyo

Naɗin Sabon Sarkin Musulmi

Bayan Turawa sun mallaki Sakkwato, suka naɗa Muhammadu Attahiru II a matsayin Sarkin Musulmi a 21 ga Maris, 1903.

Yaƙin Burmi da Ƙarshen Daula

Turawan Ingila sun bi sahun rundunar hijirar Attahiru I har zuwa garin Burmi (wanda wasu ruwayoyi ke kira Dutsin Bima). A arangamar farko Musulmi sun samu nasara, amma bayan ƙarin Sojoji daga yankuna irin su:

  • Sierra Leone
  • Ghana (Gold Coast)
  • Legas

Aka sake kai hari a 27 ga Yuli 1903. A wannan Yaƙi ne aka harbi Attahiru I a goshi har ya rasu.

Tasirin Wannan Lamari

Mutuwar Sarkin Musulmi Attahiru I ta kawo ƙarshen tsayayyar da aka yi wa Turawan Ingila, wanda ya haifar da:

  • Rushewar ikon Daular Sakkwato
  • Kafuwar Mulkin Mallaka na Birtaniya a Ƙasar Hausa
  • Fara sabon tsarin Siyasa da Mulki a Arewacin Najeriya.
Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Alaƙa

Rana Kamar Ta Yau

Yau Shekaru 32 da Fara Tura Saƙo na ‘SMSC’ a Duniya

A Rana Mai Kamar Ta Yau Neil Papworth, Injiniya mai shekaru 22 da ke aiki a Sema Group Telecoms, ya
Rana Kamar Ta Yau

Ranar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Duniya!

Kowace shekara a ranar 9 ga Disamba, ita ce Ranar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Duniya. Ana amfani