Ku Kasance Tare da Mu!

Yi rijista don samun sabbin labaranmu nan take!

Jiya Da Yau

Dr. Hamid Choi Kil, Mafassarin Al-kur’ani na Farko a Harshen Korean

A tarihin yaɗuwar Musulunci a Gabashin Asiya, akwai wasu Mutane da suka tsaya tamkar gada tsakanin al’adu da addini. Ɗaya daga cikin fitattun su shi ne Dr. Hamid Choi Kil — Malami, Masani, Jagora, Mafassari, wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen kawo Al‑Kur’ani da Hadisan Sahih al‑Bukhari cikin Harshen Korean.

        Tarihi da Ilimin Farko

An haife shi a ranar 24 ga Afrilu, 1949, a Koriya ta Kudu. Sunan sa na asali Choi Young‑gil ne, amma bayan karɓar Musulunci ya sauya zuwa Hamid.

Ya yi karatunsa a Jami’ar Hankuk ta Nazarin Harsunan Ƙasashen Waje (University of Foreign Studies) da ke Seoul, in da ya kammala Digiri a fannin Harshe da Adabin Larabci a shekarar 1975. Daga baya ya zurfafa iliminsa a Jami’ar Musulunci ta Madina a Saudi Arabiya, sannan ya sami PhD a Nazarin Addinin Musulunci (Islamic Studies) daga Jami’ar Musulunci ta Omdurman, Sudan a shekarar 1986.

Dalilin Da Ya Sa Ya Yi Wannan Fassara

Dr. Choi ya fahimci cewa, Mutane da yawa a Koriya su na da ƙalubale wajen fahimtar Musulunci saboda rashin wadataccen asali na Littattafan addini a cikin yarensu. Don haka, fassarar ta zama hanya ta bayar da sahihan ilimi ga Musulmai da masu sha’awar addini.

Fassarar Al‑Kur’ani da Sahih al‑Bukhari

Ayyukan Dr. Choi mafi shahara shi ne fassara Al‑Kur’ani mai girma daga Larabci zuwa harshen Korean — aikin da ya ɗauki kimanin shekaru bakwai kafin kammala shi.

Fassarar ba kawai sauya kalmomi ba ce, har ila yau ta haɗa da zurfin fahimtar ma’anar addini domin masu karatu su samu tushen ilimi mai inganci.

Bayan Al-Kur’ani, ya fassara Sahih al‑Bukhari, ɗaya daga cikin Littattafan Hadisi mafi sahihanci a Musulunci, wanda ke ba masu karatu damar samun fahimta kai-tsaye a harshensu.

Dr. Choi, ya rubuta kuma ya fassara fiye da Littattafai 90 da maƙaloli da suka shafi Musulunci, tarihi, da al’adu, wanda ke taimakawa wajen gina tushen ilimi a cikin Harshen Korean.

      Matsayin Aiki da Jagoranci

Dr. Hamid Choi Kil

Dr. Choi, ya yi aiki a matsayin Farfesa a fannin Kimiyyar Musulunci da Harshen Larabci (Islamic and Arabic Studies) a Jami’ar Myongji a Seoul, in da yake koyar da darussa kan Musulunci da Larabci.

Har ila yau, shi ne Shugaban ‘Korea Muslim Federation’ (KMF) — ƙungiyar da ke jagorantar harkokin Musulmai a Koriya ta Kudu, tare da gudanar da ayyuka kamar tarbiyya, ilimi, da haɓaka zaman lafiya tsakanin ƙabilu da addinai.

Lambobin Yabo da Girmamawa

  • King Abdullah bin Abdulaziz International Award for Translation (2009)
  • King Faisal Prize in Service to Islam (2023)
  • Award for Service to Islam daga Regional Council for Islamic Call in Southeast Asia (2023)

Waɗannan lambobin yabo sun nu na yadda aikinsa ya yi tasiri a Ƙasa da Ƙasa baki ɗaya.

             Tasirin Fassarar Sa

Aikin fassara littafan Al-kur’ani mai girma na Dr. Hamid Choi Kil.

Fassarar Al-Kur’ani da Sahih al‑Bukhari ta Dr. Choi ta zama babban tushen ilimi ga Musulmai da masu sha’awar addini a Koriya, in da suke iya karatu kai-tsaye cikin harshen su ba tare da dogaro ga wasu Harsuna ba. Wannan aikin ya kuma haɓaka tatttaunawa tsakanin addinai da nazarin ilimi a Jami’o’i.

            Ƙimar Aikinsa a Al’umma

A ƙasar da Musulunci ya kasance mara rinjaye sosai, aikin Dr. Choi ya taimaka sosai wajen ɗabbaƙa ilimi da addini.

  • Musulmai sun sami sahihiyar hanya ta fahimtar addini
  • Masu sha’awa sun samu tushen addini mai inganci
  • Ilimin Musulunci ya ƙaru a Jami’o’i da Cibiyoyi
  • Tattaunawa tsakanin addinai ta ƙaru da fahimta

Wannan ya sa Dr. Choi ya zama shahararren mutum a tarihin Musulunci a Koriya ta Kudu.

     Musulunci a Koriya ta Kudu

Musulunci ya fara samun tushe sosai bayan Yaƙin Koriya ‘Korean War’ (1950–1953), lokacin da sojojin Turkiyya Musulmai suka kawo addini, suka gina Masallatai da wuraren tarbiyya.

Masallacin Seoul Central Mosque an gina shi a 1976, ya zama Cibiyar Addini.

                         Ƙididdiga

Yawan Musulmai:

  • 140,000–200,000 (~0.4% na yawan jama’a)
  • Birnin Seoul: kusan 40% Musulmai ne
  • Yawancin Musulmai: baƙi daga Pakistan, Indonesia, Bangladesh; da ƴan ƙasa ƙananan yara ne.

                        Halin Yanzu

  • Ƙalubale: fahimta mai iyaka, ƙarancin Masallatai, ƙarancin abincin Halal
  • Ci gaba: haɓakar yawan masu sha’awar Musulunci, karatun addini, da tattaunawa tsakanin addinai

                      Muhimmanci

Dr. Hamid Choi Kil ya zama alamar haɗin kai tsakanin al’adu da addini, in da fassarar Al-Kur’ani da Sahih al‑Bukhari da Harshen Korean ta ba Mutane damar karatu, fahimta, da tattaunawa cikin harshensu, tare da haɓaka ilimi da zaman lafiya.

                         MADOGARA

  • Wikipedia – Hamid Choi
  • GloQur – Tarihi da fassarar Kur’ani
  • Wikipedia – Islam in Korea
  • Wikipedia – Seoul Central Mosque
  • Wikipedia – Korea Muslim Federation
  • Halal Weekly
Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Alaƙa

Jiya Da Yau

Tarihin Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Al-Hussaini CON, RTA

Fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya, wadda ya rubuta fiye da Littattafai 400 na addinin Musulunci. Malamin, wadda jigo ne
Jiya Da Yau

Taytu Betul: Shahararriyar Sarauniyar Sarakuna

Taytu Betul ta kasance sarauniyar Habasha daga 1889 zuwa 1913 kuma matar sarki Menelik na biyu. Jarumi mai tasiri wajen