Ku Kasance Tare da Mu!

Yi rijista don samun sabbin labaranmu nan take!

Al'amuran Yau Da Kullum

Dalilan Da Ke Sa Ma’abota Basira Ba Su da Yawan Abokai – Bincike

A duniyar yau, ana yawan ɗaukar cewa yawan abokai alama ce ta farin ciki da walwala. Amma bincike a fannin Psychology ya nuna akasin hakan—musamman idan aka zo kan Mutane masu basira.

Wani bincike da aka wallafa a Mujallar ‘British Journal of Psychology,’ wanda masana irin su Satoshi Kanazawa, da Norman Li, suka gudanar, ya yi nazari kan Mutane sama da 15,197. Sakamakon ya nuna cewa; yayin da yawancin Mutane ke samun farin ciki daga yawan hulɗa da jama’a, masu basira su na samun akasin haka—yawan hulɗa na iya rage musu nutsuwa da jin daɗin rayuwa da kusan 5% zuwa 10%, yayin da ga sauran Mutane, hulɗa kan ƙara farin ciki da kusan 10% zuwa 15%.

Wannan bincike ya ginu ne a kan fahimtar da ake kira ‘Savanna Theory of Happiness,’ wadda ke cewa, halayen Ɗan’Adam na yau su na da alaƙa da yadda Iyaye da kakanninsa suka rayu a wasu rukunin matsugunai—kimanin mutane 100 zuwa 150 a lokaci guda. A wancan yanayi, hulɗa da jama’a na da matuƙar muhimmanci ga rayuwa da tsaro. Sai dai a yau, masu basira su na da ikon kaucewa wannan tsohon tsarin; ba sa buƙatar yawan hulɗa domin jin daɗi.

Idan aka zurfafa cikin sakamakon binciken, an gano cewa yawan zama cikin cunkoson jama’a ma ya na da tasiri. Ga yawancin Mutane, rayuwa a wuraren da suka cika da jama’a na iya rage farin ciki da kusan 8%, amma ga masu basira wannan tasiri ya na raguwa sosai—har zuwa kusan 2% ko ƙasa da haka. Wannan na nuna cewa hankalinsu ya na ba su wata kariya daga tasirin hayaniya da cunkoso.

A ɓangaren abota kuwa, nazarin zamantakewa ya nuna cewa, matsakaicin Mutum ya na da abokai na kusa tsakanin biyar zuwa goma, amma masu basira galibi su na taƙaita wannan dafa ɗaya zuwa uku kacal—ba don sun kasa samun Mutane ba, sai dai don sun fi daraja inganci a kan yawa. A gare su, abota ba yawan Mutane ba ce, zurfin fahimta ce.

Haka kuma, idan aka duba yadda suke amfani da lokaci, bincike ya nuna cewa matsakaicin Mutum na kashe kusan 70% na lokacinsa a hulɗa da jama’a ta kai-tsaye ko ta kafofin sadarwa (Social Media). Amma masu basira sukan rage wannan zuwa kusan 40% zuwa 50%, su na mai da sauran lokaci ga tunani, bincike, da ƙirƙire-ƙirƙire—abubuwan da ke ƙara musu basira da ƙwarewa.

Saboda haka, yayin da suke ƙara shekaru, ba wai su na rasa abokai ba ne, a’a su na rage hulɗa ne bisa fahimta. Haka nan, su na gane cewa, ba kowa ne ya dace da tafiyar rayuwarsu ba, kuma lokaci abu ne mai daraja wanda ba za a ɓata shi ba a kan hulɗa marar amfani.

A ƙarshe, wannan bincike ya na rushe wata fahimta da ta daɗe ta na wanzuwa; cewa, yawan abokai shi ne ma’aunin farin ciki. A maimakon haka, ya na nuna cewa ga wasu—musamman masu basira, abokai ƙalilan masu inganci sun fi dacewa da rayuwa mai ma’ana. Domin a wasu lokuta, zama kai kaɗai ba kaɗaici ba ne; wata hanya ce ta kiyaye tunani, da gina kai, da kuma kauce wa abin da ke rage amfani da darajar lokaci.

Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Alaƙa

Al'amuran Yau Da Kullum

Qatar: Yawon Buɗe Ido na Bunƙasa a Gabas ta Tsakiya

Ƙasar Qatar ta sami kusan baƙi 730,000 a watan Janairu da Fabrairu na shekarar 2023, ƙaruwar kashi 347 a kowace
Al'amuran Yau Da Kullum

Mutum Mafi Tsufa a Duniya ya Mutu!

John Alfred Tinniswood ya mutu ne ranar Litinin a gidan kula da tsofaffi na Southport da ke Ƙasar Ingila. An