Ku Kasance Tare da Mu!

Yi rijista don samun sabbin labaranmu nan take!

Al'amuran Yau Da Kullum

Mun Yi Rijistar Haihuwa 36,000 a Kano Cikin Watanni Tara – NPC

Rahotanni daga Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa (NPC) sun nuna cewa, an yi rajistar haihuwar Yara sama da 36,000 a Jihar Kano, da ke Arewa maso Yammacin Najeriya, cikin watanni tara kacal.

Wannan adadi, duk da yake alama ce ta ƙoƙarin Gwamnati wajen inganta rajista, ya buɗe wata babbar ƙofa ta tambaya: shin Najeriya na shirin karɓar wannan ƙaruwa?

A zahiri, yawaitar haihuwa a Najeriya na ci gaba da ƙaruwa cikin sauri fiye da yadda tsarin tattalin arziki, ilimi da kiwon lafiya ke iya ɗauka. A yankuna da dama, musamman a Arewa, ana haihuwar Yara da yawa ba tare da tsayayyen shiri na rayuwa ba—ba tabbataccen ilimi, ba ingantaccen kiwon lafiya, ba kuma damar samun aikin-yi a nan gaba.

Wannan yanayi na haifar da abin da masana ke kira “Al’umma marar makoma,” in da Yara ke tasowa cikin yanayi na ƙunci da rashin tsari, wanda daga bisani kan haifar da matsalolin tsaro, zaman banza, da kuma ƙaruwar talauci. Duk da cewa, haihuwa albarka ce a addini da al’ada, rashin tsari da kulawa na iya mayar da ita ƙalubale ga ci gaban Ƙasa.

Duk da ƙoƙarin haɗin-guiwa tsakanin Ƙungiyar Ƙananan Hukumomin Najeriya (ALGON), da Hukumar Kula da Shaidar Ɗan Ƙasa ta Najeriya (NIMC), da tallafin UNICEF, da kuma Gwamnatin Netherlands, har yanzu akwai giɓi mai yawa tsakanin rajistar haihuwa da kula da rayuwar yaran bayan haihuwa.

Rajistar haihuwa muhimmi ne—amma ba shi kaɗai ba ne mafita. Abin da ake buƙata shi ne:

  • Tsare-tsaren ilimi masu inganci
  • Wayar da kan iyaye kan iyakance yawan haihuwa
  • Samar da ayyukan-yi da tallafin rayuwa
  • Inganta kiwon lafiya da walwalar Yara

Idan ba a ɗauki matakan da suka dace ba, yawaitar haihuwa za ta ci gaba da zama nauyi maimakon albarka—ta haifar da ƙarnin da babu cikakkiyar dama ko makoma.

                Kammalawa

Najeriya na buƙatar sauya tunani daga kawai “Yawan jama’a” zuwa “Ingancin rayuwar jama’a.” Domin a ƙarshe, ba yawan Mutane ne ke gina Ƙasa ba, illa ingancin rayuwarsu da irin gudunmowar da za su bayar.

Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Alaƙa

Al'amuran Yau Da Kullum

Qatar: Yawon Buɗe Ido na Bunƙasa a Gabas ta Tsakiya

Ƙasar Qatar ta sami kusan baƙi 730,000 a watan Janairu da Fabrairu na shekarar 2023, ƙaruwar kashi 347 a kowace
Al'amuran Yau Da Kullum

Mutum Mafi Tsufa a Duniya ya Mutu!

John Alfred Tinniswood ya mutu ne ranar Litinin a gidan kula da tsofaffi na Southport da ke Ƙasar Ingila. An