Ku Kasance Tare da Mu!

Yi rijista don samun sabbin labaranmu nan take!

Al'amuran Yau Da Kullum

Iskar Ƙasar Chadi ce Mafi Muni da Rashin Inganci a Afirka a 2025

A nahiyar Afirka da ake alfahari da yalwar albarkatun ƙasa da yanayi, akwai wani ɓangare da ke fuskantar wata babbar barazana — Iska mai ɗauke da Ƙura da Hazo.

Rahotanni na baya-bayan nan sun nuna cewa, Ƙasar Chadi na daga cikin wuraren da wannan matsala ta fi ƙamari a shekarar 2025. Amma tambayar ita ce; shin wannan yanayi wani abu ne na ɗabi’a kawai, ko kuma wata alama ce ta ƙalubalen da ke tunkarar rayuwar Ɗan’Adam?

        Me Rahoton Ya Nuna?

Binciken da Kamfanin Kula da Ingancin Iska na Duniya, (IQAir) ya fitar, ya bayyana cewa, Chadi na cikin ƙasashen da Iska ta fi ɗauke da Ƙura da gurbatacewa a Afirka.

Duk da cewa, ta sauko daga matsayi na farko a 2024 zuwa na huɗu a 2025, har yanzu matsalar na nan daram.

An gano cewa, yawan ƙananan ɓurɓushi masu hatsari (PM2.5) a cikin Iska ya haura ƙa’idar da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta gindaya. Wannan na nufin Iskar da Mutane ke shaƙa na iya zama barazana ga lafiyar su — musamman ma a yankunan da Iska ke kaɗawa da ƙarfi.

Bodele: Cibiyar Ƙura ta Duniya

Yankin Bodele da ke Arewacin Chadi, ya shahara a Duniya a matsayin ɗaya daga cikin wuraren da ke samar da ƙura mafi yawa. Iskar da ke tasowa daga wannan yanki na ɗaukar Ƙura zuwa sassa daban-daban na Duniya.

A tarihi, irin wannan Iska ta na taka muhimmiyar rawa wajen yaɗa Sinadarai zuwa wasu ƙasashe, musamman wajen ƙarfafa Ƙasar Noma a wasu yankuna. Amma a yau, wannan “Fa’ida” na gamuwa da babbar illa ga lafiyar Ɗan’Adam.

Me Ke Haddasa Wannan Matsala?

Akwai manyan dalilai da ke haddasa wannan matsala:

  • Sauyin yanayi (Climate Change): Ƙaruwar Zafi da Fari na ƙara yawan Ƙura a sararin Samaniya.
  • Rashin Ciyayi: Sare dazuzzuka da lalacewar Ƙasa na sauƙaƙa tashiwar Ƙura.
  • Yanayin Hamada: Kusancin Chadi da Hamadar Sahara na ƙara tsananta matsalar.

Haka kuma, rufe wasu shirye-shiryen Sa-ido kan Yanayi da ƙasashe kamar Amurka suka yi ya rage yawan bayanan da ake samu, wanda ke sa fahimtar matsalar ta ƙara wahala.

   Tasirin Matsalar ga Al’umma

Iska mai ɗauke da Ƙura ba wai kawai matsala ce ta muhalli ba, ta na da tasiri kai-tsaye ga rayuwa:

  • Ƙaruwar kamuwa da cututtukan numfashi
  • Rage ingancin rayuwa
  • Tasiri ga Noma, Kiwo, da tattalin arziki

A al’adance, Iska da Ƙura ba sabon abu ba ne ga al’ummomin Sahel, amma a yau yawanta da tsananinta sun zarce yadda aka saba a tarihi.

Duniya baki ɗaya: Wata Matsala ce ta Gama-gari

Rahoton ya nuna cewa, ba Chadi kaɗai ke fuskantar wannan matsala ba. Fiye da Ƙasashe 130 daga cikin 143 sun ka sa cika ƙa’idar WHO. Kasashe kamar: Pakistan, Bangladesh da Tajikistan na gaba a jerin masu fama da gurɓatacciyar iska.

Haka kuma, Birane da dama a Duniya — musamman a yankin Asiya — na fama da irin wannan ƙalubale, abin da ke nuna cewa matsalar ta wuce Ƙasa ɗaya.

                  Ina Mafita?

Yayin da ake ci gaba da fuskantar wannan ƙalubale, tambaya mai muhimmanci ita ce; shin za mu ci gaba da ɗaukar wannan a matsayin ƙaddara ta yanayi, ko kuma za mu ɗauki mataki?

Akwai buƙatar:

  • Ƙarfafa kula da muhalli
  • Rage sare dazuzzuka
  • Inganta tsarin sa-ido kan ingancin Iska

Domin a ƙarshe, Iska ba ta da iyaka — abin da ke faruwa a Chadi na iya shafar Duniya baki ɗaya.

Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Alaƙa

Al'amuran Yau Da Kullum

Qatar: Yawon Buɗe Ido na Bunƙasa a Gabas ta Tsakiya

Ƙasar Qatar ta sami kusan baƙi 730,000 a watan Janairu da Fabrairu na shekarar 2023, ƙaruwar kashi 347 a kowace
Al'amuran Yau Da Kullum

Mutum Mafi Tsufa a Duniya ya Mutu!

John Alfred Tinniswood ya mutu ne ranar Litinin a gidan kula da tsofaffi na Southport da ke Ƙasar Ingila. An