Ku Kasance Tare da Mu!

Yi rijista don samun sabbin labaranmu nan take!

Al'amuran Yau Da Kullum

Ƙasashe 10 Mafi Walwala da Farin Ciki a Afirka

A Nahiyar Afirka, wannan jadawalin ya na nuna yadda zamantakewa a cikin al’umma da kuma ingancin shugabanci ke tasiri sosai wajen yadda Mutane ke jin farin ciki da walwala a rayuwarsu.

A zahiri, farin ciki ya na nufin yadda rayuwa ke tafiya gaba ɗaya—wanda ya haɗa da Kuɗi, Lafiya, dangantaka mai kyau da iyali da abokai, da kuma ƴancin yanke shawarar rayuwa.

A kowace shekara, Rahoton Farin Ciki na Duniya (World Happiness Report) ya na tantance ƙasashe bisa abubuwa guda shida:

  • Tattalin Arziki (GDP ga kowane mutum)
  • Tallafin zamantakewa
  • Tsawon Rai da Lafiya
  • Ƴancin yanke shawara
  • Kyautatawa (Generosity)
  • Ƙarancin cin hanci da rashawa

Haka kuma, Kafofin Sada Zumunta su na da tasiri—su na iya sada Mutane, amma a lokaci guda su na iya haifar da damuwa da kuma sa Mutane su riƙa kwatanta kansu da wasu.

A ƙarshe dai, farin ciki haɗuwa ce ta dama, dangantaka, da al’adu waɗanda ke tsara yadda Mutane ke rayuwa a zahiri.

Ga Jerin Ƙasashe 10 Mafi Farin Ciki a Afirka a 2026:

1) Mauritius (5.939)

Mauritius ce ta 73 a Duniya. Wannan ya samo asali ne daga tsarinta na taimakon juna a tsakanin al’umma, tsarin kiwon lafiya, wadda ke tsare kamuwa da cuttuka, da kuma daidaiton tattalin arziki. Ƙasar na haɗa Yawon Buɗe Ido mai ɗorewa da bunƙasar hada-hadar Kuɗi, wanda ke samar da kyakkyawar rayuwa ga ƴan Ƙasar.

2) Libya (5.731)

Libya ce ta 81 a Duniya, duk da rikice-rikicen Siyasa da ta fuskanta. Dangantakar al’umma na da ƙarfi, kuma Mutane na da ƴancin rayuwa. Duk da rashin daidaiton tattalin arziki, haɗin kan ƴan Ƙasa da kyautatawa juna, na rage tasirin matsaloli.

3) Aljeriya (5.714)

Aljeriya ce ta 83 a Duniya. Ƙasar na da ƙarfi wajen zumunci da haɗin kan jama’a. Haka nan, ana samun tallafin Gwamnati a fannin Ilili, kiwon lafiya, da ababen more rayuwa, da ke taimakawa samun farin ciki da walwalar al’umma.

4) Mozambique (5.336)

Mozambique ce ta 93 a Duniya. Ƙasar na cin gajiyar jajirtatattun al’ummomi da Al’adun Gargajiya. Tsawon rai ya na ƙaruwa, kuma tallafin juna na taimakawa mutane jure ƙalubale.

5) Gabon (5.167)

Gabon ce ta 96 a Duniya. Farin ciki a ƙasar ya samo asali daga kuɗin shiga mai yawa (saboda albarkatun ƙasa) da kuma kyakkyawar hulɗar jama’a. Akwai kwanciyar hankali, ingantaccen kiwon lafiya, da damar ilimi.

6) Côte d’Ivoire (5.148)

Côte d’Ivoire ce ta 98 a Duniya. Ta na nuna ci gaba a walwala sakamakon bunƙasar tattalin arziki da ci gaban Birane. Haka nan, Dangantakar iyali da al’umma na da muhimmanci sosai, duk da akwai ƙalubale a yankunan Karkara.

7) Kamaru (5.083)

Kamaru ce ta 100 a Duniya. Ta na da haɗin guiwa tsakanin ci gaban tattalin arziki da tallafin al’umma, in da iyalai ke taka muhimmiyar rawa wajen tallafawa juna. Sai dai kuma, Birane na samun dama fiye da Karkara.

8) Afirka ta Kudu (5.009)

Afirka ta Kudu ce ta 101 a Duniya. Duk da ƙarfinta a Al’adu da tallafin jama’a, ta na fuskantar matsaloli kamar rashin daidaito, aikata manyan laifuka, da matsalolin kiwon lafiya. Birane kamar Johannesburg da Cape Town na ba da dama, amma Karkara na da ƙalubale.

9) Jamhuriyar Nijar (4.940)

Jamhuriyar Nijar ce ta 103 a Duniya. Duk da talauci da ƙarancin ababen more rayuwa, akwai ƙarfi a zumunci da juriya a tsakanin jama’a, wanda ke taimakawa wajen jin daɗin rayuwa.

10) Tunisiya (4.798)

Tunisiya ce ta 105 a Duniya. Duk da matsin tattalin arziki da sauye-sauyen siyasa, ta na da ƙarfi a tallafin al’umma. Tsawon ran al’umma na ƙaruwa, kuma ana bai wa kiwon lafiya muhimmanci.

Wannan rahoto ya nuna cewa, farin ciki ba wai yawan Kuɗi ko ci gaban tattalin arziki kaɗai yake tabbatarwa ba. Haɗin kai tsakanin al’umma, taimakon juna, kwanciyar hankali, da jin cewa mutum ya na da muhimmanci a cikin al’umma, su ne manyan ginshiƙan rayuwar farin ciki.

Haka nan, ko da wasu ƙasashe su na fuskantar matsalolin tattalin arziki ko siyasa, ƙarfafa dangantaka da al’adu na taimakawa mutane su ci gaba da jin daɗin rayuwa.

A ƙarshe, farin ciki ya na kasancewa ne daga yadda mutane ke rayuwa tare, suke tallafa wa juna, da kuma yadda suke samun bege da kwanciyar hankali a rayuwarsu ta yau da kullum.

Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

4 Comments

  1. Dora1483

    07/05/2026

    https://shorturl.fm/qLtxY

  2. Cristian678

    07/05/2026

    https://shorturl.fm/zrqMW

  3. Cornelius1153

    07/05/2026

    https://shorturl.fm/46903

  4. Alfred1151

    07/05/2026

    https://shorturl.fm/lofQ8

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Alaƙa

Al'amuran Yau Da Kullum

Qatar: Yawon Buɗe Ido na Bunƙasa a Gabas ta Tsakiya

Ƙasar Qatar ta sami kusan baƙi 730,000 a watan Janairu da Fabrairu na shekarar 2023, ƙaruwar kashi 347 a kowace
Al'amuran Yau Da Kullum

Mutum Mafi Tsufa a Duniya ya Mutu!

John Alfred Tinniswood ya mutu ne ranar Litinin a gidan kula da tsofaffi na Southport da ke Ƙasar Ingila. An