Ku Kasance Tare da Mu!

Yi rijista don samun sabbin labaranmu nan take!

Al'amuran Yau Da Kullum

Elon Musk na dab da zama mutum na farko da dukiyarsa za ta kai Tiriliyan guda

Shugaban kamfanonin Tesla da SpaceX Elon Musk, na dab da kafa sabon tarihi a fannin arziki.

Shugaban Tesla da SpaceX, Elon Musk, na kan hanyar kafa tarihi a matsayin mutum na farko da dukiyarsa za ta kai dala tiriliyan guda ($1 trillion), kuma hakan na iya faruwa a shekarar 2026.

A cikin watan Fabrairu 2026, dukiyarsa ta kai kusan Dala Biliyan 850 — lamarin da ya sa ya zama mutum na farko da ya haura Dala Biliyan 800 a tarihin masu kuɗi.

A yanzu haka, dukiyarsa ta fi jimillar dukiyar mutane uku masu biye da shi a jerin masu arzikin Duniya a haɗe: Larry Page ($251bn) da Sergey Brin ($231bn) na Google, da kuma Mark Zuckerberg ($219bn) na Meta.

Haɗakar SpaceX da xAI

Babban abin da ya ƙara dagula kasuwar arziki shi ne yarjejeniyar haɗa SpaceX da xAI. Sabon kamfanin da aka samar an kimanta darajarsa da Dala Tiriliyan 1.25.

Ana hasashen Musk na da kashi 43% a cikin sabon kamfanin, wanda hannun jarinsa kaɗai ya kai sama da Dala Biliyan 530. Wannan na nufin SpaceX yanzu na bada kusan kashi biyu cikin uku na dukiyarsa gaba ɗaya.

Kalubalen da ke Tasowa

Sai dai wannan haɗaka ta zo ne a daidai lokacin da kamfanin AI ɗin ke fuskantar bincike a Turai, Asiya, Ostiraliya da California. Binciken ya samo asali ne daga yawaitar hotunan batsa da na bogi (deepfake) da aka ƙirƙira ta hanyar manhajar Grok a dandalin sada zumunta na Musk.

Hasashen Kasuwa

Dandalin hasashen kasuwa na Kalshi da ke Manhattan ya nuna yiwuwar kashi 75% cewa Musk zai zama Trillionaire a wannan shekara.

  • Kashi 91% na masu kasuwa na ganin zai kai wannan matsayi kafin 2029
  • Kashi 86% na ganin hakan zai faru a shekara mai zuwa ne (2027)
  • Kashi 72% na ganin zai faru kafin 2027

Tasirin IPO da Tesla

Idan har aka fitar da SpaceX kasuwar hannun jari (IPO), hakan na iya ƙara ɗaga dukiyarsa har zuwa Dala Tiriliyan 1.5.

A gefe guda kuma, duk da faduwar farashin hannun jarin Tesla a baya-bayan nan, Musk na da kashi 12% na kamfanin wanda darajarsa ta kai Dala Biliyan 178, baya ga wasu zaɓuɓɓukan hannun jari (stock options) da darajarsu ta kai kusan Dala Biliyan 124.

Bugu da kari, ana sa ran zai samu ƙarin hannun jari da darajarsa za ta iya kai wa Dala Tiriliyan 1 sakamakon wata babbar yarjejeniyar albashi da masu hannun jarin Tesla suka amince da ita a watan Nuwamba.

Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Alaƙa

Al'amuran Yau Da Kullum

Qatar: Yawon Buɗe Ido na Bunƙasa a Gabas ta Tsakiya

Ƙasar Qatar ta sami kusan baƙi 730,000 a watan Janairu da Fabrairu na shekarar 2023, ƙaruwar kashi 347 a kowace
Al'amuran Yau Da Kullum

Mutum Mafi Tsufa a Duniya ya Mutu!

John Alfred Tinniswood ya mutu ne ranar Litinin a gidan kula da tsofaffi na Southport da ke Ƙasar Ingila. An