Ku Kasance Tare da Mu!

Yi rijista don samun sabbin labaranmu nan take!

Kimiyya Da Fasaha

Ɗalibar Najeriya ta Samu Lambar Yabo ta Duniya a Fagen Fasaha

Ɗalibar Najeriya ta ƙera Na’urar gano Tsatsa mai amfani da Ƙirƙirarriyar Basira (Artificial Intelligence)

Ɗalibar digirin-digirgir (PhD) ƴar Najeriya daga Kano, Maimuna Umar Zarewa, ta samu babbar nasara a fagen kimiyya bayan ta lashe kyautar Duniya ta “Carbon Neutrality Cup.”

In da aka Gudanar da Gasar

An shirya gasar ne ƙarƙashin jagorancin Gulf Petrochemicals and Chemicals Association (GPCA), a Otel ɗin Sheraton Manama Hotel da ke Manama.

Mahalarta daga ƙasashen yankin Gabas ta Tsakiya – ciki har da Qatar, Kuwait, Oman, Bahrain da Saudiyya – sun gabatar da sabbin dabaru kan ɗorewar Muhalli da bunƙasar Masana’antu.

          Mene ne ta Ƙirƙiro?

Zarewa, wadda ke karatun digirinta na uku a King Fahd University of Petroleum and Minerals (KFUPM), ta ƙera wata Na’ura mai sarrafa kanta wadda ke amfani da Ƙirƙirarriyar Basira (AI) domin gano lalacewar Ƙarfe (corrosion/tsatsa) da kare muhimman kayayyakin more rayuwa na Man Fetur da Makamashi.

Na’urar ta haɗa abubuwa kamar haka:

  • Shirya samfur (sample preparation)
  • Gano sinadarai
  • Fasahar mutum-mutumin (robotics)
  • Nazarin bayanai ta hanyar AI

          Abin da ya Bambanta ta

Sabuwar na’urarta ta bambanta da tsofaffin hanyoyin gano Tsatsa (corrosion) da kan buƙaci na’urori da dama da kuma aiki da hannu. Ita kuwa, ta yi amfani da Sinadari mai haske (fluorescence sensor) da aka samar daga tarkacen Man Fetur, wanda ke ba da damar gano lalacewa tun da wuri, cikin sauri, tare da rage kuɗaɗen aiki da dogaro da ma’aikata.

Tattalin Arziki Mai Zagaye (Circular Economy)

Ɗaya daga cikin muhimman fannoni na wannan ƙirƙire-ƙirƙire shi ne:

Ta hanyar mayar da tarkacen Man Fetur zuwa Sinadari mai amfani, wannan ƙirƙire-ƙirƙire ta dace da manufar tattalin arziki mai zagaye (circular economy), tare da tallafa wa kare muhalli da rage gurɓacewar yanayi.

              Sabon Mataki

A yanzu haka, Zarewa na haɓaka sabuwar sigar na’urar wadda za ta ƙunshi:

  • Rumbun tattara sinadarin kariya
  • Riƙa fesawa kai-tsaye idan an gano alamun lalacewa

Wannan zai sauya ta daga na’urar gano matsala zuwa na’urar gano matsala tare da magance ta kai tsaye.

        Muhimmancin Fasahar

Masana sun bayyana cewa, tsatsa na jawo asarar Biliyoyin Daloli a masana’antar Mai da Iskar Gas a duk shekara.

Sabuwar fasahar Zarewa na da damar:

  • Rage waɗannan asarori
  • Ƙarfafa tsaron kayayyakin Makamashi
  • Inganta dorewar muhalli

                 Matasan Najeriya

Maimuna Umar Zarewa, PhD

Nasarar Zarewa ta nuna yadda matasan Najeriya ke taka rawa a fagen binciken kimiyya na Duniya, tare da tabbatar da cewa, basira da ƙirƙire-ƙirƙire na iya sauya al’umma da masana’antu baki ɗaya.

Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Alaƙa

Kimiyya Da Fasaha

Yadda Ƙirƙirarriyar Basira ta Artificial Intelligence za ta Shafi Ayyuka a Afirka

Bankin ci gaban Afirka (Africa Development Bank) ya yi hasashen cewa kimanin Matasa Miliyan 100 da ke Nahiyar ba za
Kimiyya Da Fasaha

Taron Ƙolin Masana Kimiyya na 2024 na Haɓaka Ƙarfin Ƙirƙirar Matasa

Taron Ƙolin Masana Kimiyya na Ƙasa da Ƙasa na 2024 na Haɓaka Ƙarfin Ƙirƙire-ƙirƙiren Matasa Daga: Amina Xu An gudanar