Ku Kasance Tare da Mu!

Yi rijista don samun sabbin labaranmu nan take!

Rana Kamar Ta Yau

Rana Kamar ta Yau: Musulmi sun ci Garin Makkah

A ranar 20 ga watan Ramadan, shekara ta 8 bayan Hijira (630 Miladiyya) ne Musulmai ƙarkashin jagorancin Annabi Muhammadu (SAW) suka ci garin Makka tare da rundunar Sahabbai kusan 10,000, ba tare da zubar da jini ba.

Wannan nasara ta kawo ƙarshen rikicin da aka shafe shekaru ana yi tsakanin Musulmai da Quraysh, tare da sauya Makka daga mulkin mushrikai zuwa mulkin Musulunci.

           Dalilin Cin Makka

Bayan Hijirar Musulmai zuwa Madina, an yi yaƙe-yaƙe da dama tsakaninsu da Quraysh. A shekara ta 6 bayan Hijira an ƙulla Yarjejeniyar Hudaybiyah ta zaman lafiya na shekaru 10.

Sai dai, Quraysh sun karya yarjejeniyar ta hanyar taimaka wa Banu Bakr su kai hari ga Banu Khuza’ah (abokan Musulmai), har aka kashe mutane daga cikinsu. Wannan ne ya sa Annabi SAW ya shirya runduna domin tafiya Makka.

           Yadda Aka Ci Makka

Rundunar Musulmai ta tashi a 10 ga Ramadan kuma ta shiga Makka cikin kwanciyar hankali. Annabi SAW ya karanta ayar Alƙur’ani:
“Gaskiya ta zo, ƙarya kuma ta gushe.” (Suratul Isra’i 17:81)

An rushe Gumaka da ke cikin Ka’aba, aka dawo da ibadar Tauhidi.

Gafarar Annabi ga Quraysh

Duk da irin azabar da suka yi wa Musulmai a baya, Annabi SAW ya gafarta musu ya na mai cewa:
“Ku tafi, kun ƴantu.”

Wannan ya nuna rahama da adalcin Musulunci, kuma bayan wannan lamari mutane da yawa suka rungumi Musulunci.

Muhimmancin Wannan Rana

Cin Makka ya zama babban juyi a tarihin Musulunci, domin ya kawo ƙarshen shirka a Ka’aba tare da fara sabon zamani na yaɗuwar Musulunci.

Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Alaƙa

Rana Kamar Ta Yau

Yau Shekaru 32 da Fara Tura Saƙo na ‘SMSC’ a Duniya

A Rana Mai Kamar Ta Yau Neil Papworth, Injiniya mai shekaru 22 da ke aiki a Sema Group Telecoms, ya
Rana Kamar Ta Yau

Ranar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Duniya!

Kowace shekara a ranar 9 ga Disamba, ita ce Ranar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Duniya. Ana amfani