Dr. Maryam ta Zama Farfesa Mace ta Farko kan Magungunan Gargajiya da Al’adun Hausa
Daga: Muhammad da Nazir Adam Ibrahim Majalisar Gudanarwar Jami’ar Bayero da ke Kano, ta amince da ɗaga darajar Dr. Maryam Mansur Yola, ta Sashen Koyar da Harsunan Najeriya, da ke Jami’ar zuwa matsayin Farfesar Magungunan Gargajiya da Al’adu, kamar yadda wata sanarwa da Jami’ar ta fitar a ranar Juma’a 27 ga Disamba, 2024 ta bayyana. […]














