Al'ada

Yadda aka Gudanar da Bikin Al’ada na Irreecha

Bikin Irreecha, wani shahararren bikin al’ummar Oromo ne na ƙasar Habasha (Ethiopia), wanda ake gudanarwa duk shekara domin nuna godiya ga Ubangiji (Waaqaa) bisa ni’imar rayuwa, amfanin gona, da zaman lafiya. Ana gudanar da bikin ne a ƙarshen Damina da farkon Bazara — lokacin da albarka ta yawaita, Gonaki suka yi kyau, kuma Mutane ke […]

Masarautu

Asali da Tarihin Jukunawa: Masarautar Wukari a Idon Duniya

Wukari, kamar yadda aka fi kiranta, ita ce Hedikwatar Masarautar Wukari. Asalin sunanta shi ne ‘Ukari,’ wacce kuma kalma ce ta Jukunanci, wacce ke da ma’anar; ‘Ka fifita’ (you have surpassed). Masarauta ce da aka kafa ta a shekarar 1596 bayan rushewar Daular Kwararrafa.                           TUSHE Bayan rushewar Daular Kwararrafa wacce ke da Hedikwata a […]

Rana Kamar Ta Yau

Rana Kamar ta Yau

A Ranar 19 ga watan Agusta na shekarar 1839, Gwamnatin Ƙasar Faransa ta sanar da cewar, Louis-Jacques-Mandé Daguerre, ya ɗauki hoto mai kyau da tsari irinsa na farko a Duniya. Boulevard du Temple, Hoto wadda aka ɗauka na titin Paris da aka yi a cikin 1838-1837, ya na ɗaya daga hotunan farko na ‘daguerreotype’ wanda […]

Harshe

Yadda aka gudanar da taron tsarin rubutun Hausa na Gargajiya

Taron wadda ya gudana a Jami’ar Bayero da ke Kano, ƙarƙashin shiryarwar Sashen Nazarin Harsunan Najeriya ta Jami’ar; tare da haɗin guiwar Sashen Ilimin Harsuna Ƙasashen Waje, da Sashen Taskace Tarihi, da Cibiyar Bincike da Nazarin Harsunan Najeriya da Fassara. Taron ya mai da hankali ne kan asalin Baƙaƙen Hausa tun kafin zuwan rubutun A-ba-ja-da, […]

Yawon Buɗe Ido

Zanzibar ta kafa Tarihi a Yawon buɗe Ido

Zanzibar na ci gaba da ƙarfafa matsayin ta a fannin Yawon buɗe Ido a Afirka, inda matakan Gwamnati da shirye-shiryen haɗin guiwa ke haifar da tabbataccen ci gaba mai ɗorewa. Tsibirin Zanzibar da ke cikin ƙasar Tanzaniya ya kafa sabon tarihi a fannin Yawon buɗe Ido, inda aka karɓi masu yawon buɗe ido 106,108 a […]